NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A hankali ta tashi ta ɗauko wayarta ta duba time, ƙarfe goma sha ɗaya saura na safe ta gani. Gyaran ɗakin ta shiga yi bayan ta gama ta fita da niyyar gyara falo suka ci karo da Ameen. Ya kama hannunta ya ce. “Mu je mu yi breakfast Mamanki ta kawo mana abinci.” Ta yi ƙasa da kanta kewar Mama na ƙara cika mata zuciya, cikin sanyin murya ta ce. “Waya kawo breakfast ɗin?” Ya shafi kuncinta ya ce. “One of our soldiers staff.” Bata kuma magana ba ya ja hannunta suka ƙarasa tsakiyar falon inda abincin yake akan Centre Carpet. Har ya d’auko plates da cups da spoons da kayan tea duk ya ajiye a gurin, tana mamakin yanda yake ɗauko mata duk abun da ya san zata buƙata in time tun kafin ta yi yunk’urin ɗaukowar, Shi da a gida komai sai dai a ɗauko masa yana daga zaune. A ranta ta ce. ‘Ko Matarsa yakewa hakan shi yasa itama yake mata.’ Haka kawai ta ji gabanta ya fadi tunowa da ta yi da Hafsat……….✍️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

8️⃣3️⃣

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

………Saurin yin ƙasa da kanta ta yi daga kallon sa tare da amsa masa sallamarsa. Ya ajiye ledodin hannunsa a gaban gadon sannan ya zauna a kusa da ita. Ba tare data kalle shi ba ta ce. “Sannu da zuwa.” Ya amsa mata a can ƙasan mak’oshi, sannan cikin kulawa ya ce. “Kin ci abinci?” Ta ce. “Eh.” Ya ce. “Na dare fa nake nufi bana rana ba.” Ta girgiza masa kai alamar a’a. Ya ce. “Okay sakko mu ci wannan.” Ya yi maganar yana nuna ledodin gabansu. Ta ce. “Akwai sauran abincin da Mama ta kawo fa.” Ya ce. “Mu je ki bani na kaiwa mai gadi sai mu ci wannan ɗin.” Ta miƙe ba tare da ta yi magana ba ya bi bayanta. Abincin duka ta juye masa sannan ta ɗauko plates da cup da spoon kamar yadda ta ga ya yi jiya. Sai a lokacin ta tuna data tashi yau da safe ba ta ga ragowar kazar jiya ba. Ta kai kayan ɗakinta ta zauna jiransa, mintuna kaɗan ya dawo, ya zauna a ƙasan gado ya janyo ledar kazar ya ce. “Me kike jira baki fara ci ba?” Ta nuna masa kansa da hannunta, tana ƙoƙarin sarving ɗinsu ya katse ta da faɗin. “I forgot something.” Ta kalle shi da alamun tambaya, ya ce. “Je ki yi alwala.” Ta ce. “Na yi Sallah fa.” Ya ce. “Wata zamu sake.” Ba tare da tunanin komai ba ta je ta yo alwalar, kafin ta fito har ya shimfid’a musu darduma. Ya miƙe bayan ta saka hijabinta ya ja su suka yi Sallah raka’a biyu, ya dad’e yana yi musu addu’ar zaman lafiya da wanzuwar farin ciki a rayuwar auransu a cikin sujjadarsu ta ƙarshe. Bayan sun idar ya kama kanta ya yi mata addu’a kamar yadda ma’aiki (S. A. W) ya koyar da mu ga sabbun ma’aurata, sannan ya umarce ta data yi masa shi ma kamar yadda ya yi mata. Bata yi musu ba ta yi masan, ya ce su je su ci kazar. Tare suka ci amma wannan karon bai bata a baki ba, ko taɓa ta bai yi ba bai nuna alamar ma zai yi hakan ba, hakan yasa ta ji daɗi amma duk da haka a takure take jin ta, masifar tsoron da take ji a ɗazu ne dai ya ɗan ragu tun da ta ga bai yi mata komai ba tunda ya shigo ɗakin. Bayan sun gama tana tattare kayan ta ce. “Jiya ya ka yi da ragowar kazar nan?” Ya ce. “Tun a daren na kaiwa mai gadi.” Ta gyaɗa masa kai sannan ta fice da kayan. Sai da ta dauraye su sannan ta komo ɗaki, ta tarar ya fita baya ɗakin. Ajiyar zuciya ta saki ta jin daɗi sannan ta rufe ƙofar ɗakin, toilet ta shiga ta yi ƴan uzurarrikanta, ta fito ta cire kayan jikinta ta saka wani riga da wando masu taushi na bacci, ta mitsitsika humra a jikinta kamar yadda mai gyaran jikin da ta yi mata ta ce tana yi duk dare sannan ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta ba tare da ta kunna bedside lamp ba. Bacci take ji sosai, ta bararraje akan gado tana murna a ranta zata yi baccinta cikin kwanciyar hankali babu fargaba da tsoron komai a ranta. Sai dai ko 5 minutes ba ta yi da kwanciyar ba ya turo ƙofa ya shigo, a lokacin bacci ya ɗan fara ɗaukar ta. Ta buɗe idonta a hankali gabanta na fad’uwa. Kunna torchlight ɗin wayarsa ya yi ganin ɗakin da duhu, ta yi saurin runtse idonta tana addu’ar Allah yasa idan ya ga bacci take ya k’yale ya koma ɗakinsa. Shi kam dama abun da yake so kenan, so yake ta saki jikinta sai ta sakankance sai ya dawo ɗakin. Ya ɗan tsaya yana haska ta sannan ya hau kan gadon ya yaye bargon data rufe jikinta da shi. Tana jin shi ta ƙi motsawa duk dan ya yi tunanin bacci take. Ya haske fuskarta yana murmushi cikin sanyin murya ya ce. “I know you are not sleeping.” Ta buɗe idonta kaɗan tana kare fuskarta da hannunta bata ce komai ba. Ya matsar da wayar daga saitin fuskarta sannan ya matsa jikinta ya saka hannunsa akan lallausan gashinta ya fara shafawa a hankali. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali tare da lumshe ido saboda yanda ƙamshinsa yake ratsa k’ofofin hancinta, a shagwab’e ta ce. “Yaya I want to sleep.” Ya ajiye wayar hannunsa sannan ya ɗauki kanta ya ɗora akan cinyarsa, cikin wata irin murya da idan da za’a ce mata Yayan nata yana da ita baza ta yarda ba ya ce. “Ni kuma tunanin ki da san kasancewa dake ya hana ni bacci Baby love.” Saboda tsananin mamaki bata san lokacin data buɗe idonta cikin sauri ta kalle shi ba, dan tabbatar da abun da ta ji ba kunnenta ne ya jiye mata ba dai-dai ba. Ya ja kumatunta tare da kashe mata ido ya ce. “It’s so amazing ba?” Ta yi shiru kawai tana kallon shi. Ya yi murmushi, sannan ya rank’wafar da fuskarsa daf da ta_ta, cikin murya mai kama da rada ya ce. “Na san zaki yi mamaki idan na ce miki am in love with you tun lokacin da ban san menene so ba, ban ma san me kalmar son take nufi ba, lokacin kina only 5 years a duniya da muka zo gidanku da Mama kika zo kina mun ihu a cikin kunnena. Tun ranar tunanin ki yake manne a cikin raina, da shi nake kwana nake tashi. Sometimes sai in zauna ni kaɗai idanuna a lumshe ina hango ki a cikin raina kina yiwa Aunty shagwab’a ko kuma kina surutunki ko kuka da tsalle_tsallenki, sai in ji ina son na kuma ganinki, a lokacin ban gane ma’anar hakan ba sai daga baya na fahimta. Duk yanda zan miki bayanin yanda soyayyiyar ki ta azabtar dani baza ki gane ba Miemerh, amma dai na sha wahala. Bayan Allah ya yiwa su Abba rasuwa kin dawo hannunsu Mum da zama bazan iya kwatanta miki farin cikin da na ji ba a wannan lokacin, na tabbata ko Mum bata kai ni farin ciki da hakan ba, tunda ko ba komai idan na zo gida duk weekend zan gan ki in ji daɗi a raina. Dalilin da yasa ban bayyana miki soyayyata a gare ki ba a lokacin da ya dace, da na yiwa Daddy maganar ina sonki sai ya nuna mun in bar maganar dan bazai bani ke ba, ban kuma san dalilinsa na faɗar hakan ba har yau. Na haqura da maganar ko Mum ban faɗawa ba, ba kuma wai dan na daina son ki ba ne, ko kaɗan soyayyar ki bata ragu ba a cikin zuciyata sai ma ƙaruwa da take yi, saboda in yiwa Dad biyayya ne kawai na haqura.” Ya yi shiru na wasu sakanni yana goga mata sajen fuskarsa a kuncinta sannan ya cigaba da magana. “FATEEMAH….! I LOVE YOU WITH ALL MY HEART, I LOVE YOU MORE THAN WORD CAN EXPLAIN, I LOVE YOU MORE AND MORE NEEHAL.” Ta lumshe idonta tana jin ta kamar a cikin gajimare saboda wani irin shauk’i from no where da yake mamaye dukkan zuciyarta, an sha faɗa mata kalaman soyayya babu adadi a rayuwarta, an furta kalmar i love You babu adadi, amma bata taɓa jin waɗanda suka yi tasirin da wanda Yayanta yake faɗa mata a yanzu ba a cikin zuciyarta. Kalamansa sun ratsa dukkan zuciya da gangar jikinta. Ta ji kamar ta ce ya cigaba da yi mata kalaman kar ya daina. Hannunsa ta ji yana dawo a sassan jikinta cikin wani irin salo da yasa ta ji kamar jinin jikinta zai tsinke ya tsiyaye. Ya ƙara yin ƙasa muryarsa bakinsa akan kunnenta ya ce. “Baki ba zai iya faɗar irin tarin k’aunar ki dake cikin raina ba saboda yawanta, but i want to show you ta yadda zaki gamsu ki tabbatar da abun da nake faɗa miki.” Ya ja numfashi tare da lumshe idonsa ya ɗora bakinsa akan nata, a tare suka saki wasu tagwayen sanyayan ajiyar zuciya. Cikin lokaci ƙanƙani Ameen ya juye mata daga wanda ta sani zuwa wani daban, sarrafa ta yake cikin wani irin salo mai tsayawa a rai da wuyar mantawa cikin k’warewa da nutsuwa. Da farko sak’onnin nasa sun fara tasiri a kanta, daga baya da ta ga yana ƙoƙarin kaiwa ga abun da take matuƙar tsoron faruwarsa sai ta fara ƙoƙarin k’watar kanta tare da saka masa kuka, amma ina bai gane wannan yaren ba, inda yake son zuwa kawai yake hanqoro. Bata ƙara firgicewa da al’amarinsa ba sai da ta ji yana karanta addu’ar data san mana’arta da dalilin da yasa ake yin ta, ta fara ture shi tana dukan duk inda hannunta ya kai a jikinsa a ƙoƙarinta na son ya k’yale ta amma bai ma san tana yi ba, burinsa kawai yakai inda ransa yake da murad’in zuwa. Duk yadda Haneefah ta dinga kwatanta mata wahalar abun ta ji fiye da hakan, sai da ta yi tunanin baza ta farka ta gan ta a duniya ba saboda azabar da ta sha, Mama da Daddy da duk sunan wanda ya zo bakinta sun sha kira da neman agajinsu, kuka kam har sai da muryarta ta dashe saboda yin sa………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button