NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan komai ya lafa tana kwance a ƙirjinsa ya yi mata kyakkyawar runguma kamar zai mayar da ita ciki, idanunsa a lumshe ya cusa kansa a cikin gashin kanta yana shaƙar ƙamshin gashin, hannunsa ɗaya yana kan gadon bayanta yana shafawa a hankali cikin sigar rarrashi. Ita kuma ban da hawaye da sakin ajiyar zuciya babu abun take. Jikinta gaba-d’aya ciwo yake mata, ko ɗan yatsanta bata tunanin zata iya d’agawa. Sassauta riqon da ya yi mata ya yi ya ɗago fuskarta cikin tsananin tausayinta da k’aunar ta ya ce. “Please Miemerh ki bar kukan nan haka, zaki ƙarawa kanki wani ciwon fa.” Ta cinno masa baki kamar zata yarda shi a ƙasa ta bar jikinsa cikin dauriya tare da juya masa baya tana ƙara ƙanƙame bargo a jikinta ta cigaba da kukanta. Ya yi murmushi kawai sannan ya tashi zaune, yau jin zuciyarsa yake fess tamkar wani baƙin ciki bai taɓa wanzuwa a cikinta ba saboda farin cikin da ya cika ta, yanda yake jin kansa cikin nishad’i da annashuwa ba zai misaltu ba. Jallabiyarsa ya lalubo ya zira a jikinsa sannan ya miƙe ya kunna light ya shiga toilet, bayan wasu mintuna ya fito ya hau kan gadon ya kama bargon jikinta da nufin ya yaye shi. Ta ƙanƙame bargon idanunta a runtse tana ƙara volume ɗin kukanta, ita kaɗai ta san azabar da take ji a cikin jikinta, jin cikinta take kamar an yi mata yasa, ƙafafuwanta kuwa kamar ba’a jikinta suke ba, ƙasanta kamar an jajjaga mata attaruhu a gurin saboda radad’in da yake mata. Ya rank’wafa ya ce. “Baby wanka zan miki fa.” Ta ture fuskarsa da hannunta ta ƙara juya masa baya, wata irin kunyarsa ce ta ninku a cikin zuciyarta akan wadda take ji a da. Bata ankara ba sai ji ta yi ya ɗauke ta cak ita da bargon. Ƴar ƙara ta saki saboda ji ta yi kamar ya fama mata ciwon jikinta, ya rungume tsam yana rarrashinta sannan ya miƙe da ita a jikinsa ya kai ta toilet ya ajiye ta a cikin tub bayan ya zare bargon jikinta. Zabura ta yi ta ruk’unk’ume shi kamar zata janyo shi cikin tub ɗin saboda azabar data ji tana ratsa ta a sakamakon jin ta da ta yi a cikin ruwan zafi. Ya riƙe ta ya mayar da ita cikin ruwan ganin tana ƙoƙarin miƙewa. Sannu kawai yake jera mata cikin kulawa da soyayya, ita kuma sai taɓara take zuba masa, sai dai ta ƙi bari ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai da ruwan ya huce sannan ya fita ya bar ta dan ta yi wankan tsarki. Ya dawo ɗakin ya cire zanin gadon ya sake wani sannan ya fice daga ɗakin ya je ɗakinsa ya yi wanka ya dawo. Ta ji sauƙin radad’in da gurin yake mata sanadiyyar ratsa ta da ruwan zafin ya yi. Bayan ta yi wankan, ta fito daga cikin tub ɗin daƙyar, a lokacin ya dawo toilet ɗin. tsugunnawa ta yi da sauri tana dunk’ule jikinta guri guda tare da fashewa da kuka. Ya dafe kansa a ransa yana faɗin ‘Yau fa sai Allah Neehal da kuka, dama yaya lafiyar kura bare kuma ya taɓo ta.’ Towel ya ɗauko ya ɗaura mata duk da daƙyar ta bar shi ya ɗaura matan wai ita bazai ga jikinta ba, sannan ya lullub’e mata kanta da wani ya ɗauko ta suka fito ya kwantar da ita ya shiga tsane mata kanta da towel. Sai da ruwan gashin nata ya ɗan tsana sannan ya kwanta ya janyo ta jikinsa ya ce. “Please Baby ki bar kukan nan mana, ko so kike zuciyata ta fashe ne?” Cikin kuka ta ce. Ni ka kai ni gurin Mama mutuwa zan yi.” Ya shafi pink lips ɗinta ya ce. “Wai gurin da zafi ne sosai?” Shiru ta yi masa a ranta tana cewa. ‘Dan ba jikinka ba ne ai.’ Ya kai hannu ƙasan mararta ya ce. “Mu ji ya gurin yake.” Ture hannun ta yi da sauri ta matse ƙafafuwanta. Ya ƙara rungume ta a jikinsa ya ce. “Gani fa zan yi ko da ciwo a gurin.” Ta fashe da kuka sosai ganin shi nishad’in shi ma yake ita ya bar ta da jin azaba a jikinta, Cikin kuka ta ce. “Kuma sai na haɗa ka da Mama.” Yana dariya ƙasa_ƙasa ya ce. “Me zaki ce mata ƴar gidan Mama?” Shiru ta yi masa ta cigaba da kukanta, ya yi murmushi sannan ya shiga rarrashinta, cikin lokaci ƙanƙani bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara mata kwanciya. Ya shiryawa dukkan wata rigimarta dan ya san dole ya sha ta a wannan stage ɗin tunda ya siya da kuɗinsa. Ya lumshe idonsa d’umin jikinta na ratsa shi yana saukar masa da nutsuwa, bai san sanda shi ma baccin ya yi awun gaba da shi ba…….✍️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

8️⃣2️⃣

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

………Da kansa ya haɗa mata tea cikin cup, ya zuba mata Irish da soyayyiyar waina ƙwai a cikin plate, ya ɗora bread a kai bayan ya shafa mata jam a jikinsa. Kallonsa kawai take yanda yake yin komai cikin natsuwa, ta dunk’ule jikinta guri guda gaba-d’aya ta kasa sakewa. Ya ɗago ya kalle ta fuska a sake ya nuna mata cinyarsa tare yi mata alamar ta je ta zauna akai. Ta waro ido tare da ɗauke kanta kamar bata gane me yake nufi ba. Ya matso kusa da ita a hankali ya daga ta cak ya ɗora ta akan cinyar tasa. Ta fara mutsu_mutsu tare da ƙoƙarin sauka daga jikinsa, ya riƙe ta sosai tare da juyo da fuskarta ya zuba mata narkakkun idanunsa a cikin nata, ba shiri ta lumshe nata idon ƙirjinta ya fara bugun da ya saba. Ya shafi gashin girarta tare da ƙara gyara mata a jikinsa. Gaba-d’aya sai ta rikice ta fara ƙoƙarin yi masa kuka, ko da wasa ta ƙi buɗe idonta saboda tsoron kar su ido. A hankali ya cusa kansa a wuyanta yana shaƙar ni’imtaccen ƙamshin jikinta. ‘Ya Allah, wannan bawan naka zai kashe ni da raina, wannan abun kunyar har ina?’ Ta faɗi haka a ranta. Rawar da jikinta ya fara yi ne yasa ya ɗago da kansa daga jikinta, murya ƙasa ƙasa ya ce. “Ni fa bana son wannan tsoron da kunyar sun ishe ni haka.” Ta tura masa baki tare da ɓata fuska. Ya ce. “Okay, I know how I treat you tsoro da kunyar su tafi.” Ya karashe zancen tare da kai hannunsa bayanta ya fara jan zip ɗin rigarta ƙasa. Saboda dimauta bata san sanda ta ƙanƙame shi ba tare da sakin kuka, sosai ta rikice, al’amarin Ameen ya girmewa kwanyarta. Ya tsaya da abun da yake yi yana murmushi ya ja karan hancinta bai ce komai ba. Juyar da ita ya yi yana faɗin. “Let us eat first, sai mu fi samun full energy.” Ta zame ta sauka daga jikinsa da sauri tare da ƙoƙarin tashi, a nufinta ta ruga da gudu ta koma ɗaki. Ya kama hannunta tare da mayar da ita ta zauna akan cinyarsa. Ya ɗora kansa akan kafaɗarta yana kallon gefen fuskarta ya ce. “Common, wai wannan abun da kike yi na mene ne? Wannan Ameen ɗin fa ba Yayanki ba ne Mijinki ne?” Ta marairaice fuska ta ce. “Ni dai dan Allah ka barni in zauna a ƙasa.” Ya ce. “Yanzu a sama kike?” Ta yi shiru tana ƙara marairaice fuska, shi bai san me take ji a jikinta ba da zuciyarta idan ya taɓa amma yay ta nanik’ar ta. Ya kama hannayenta da suka sha jan ƙunshi yana kallo, a hankali ya kai hannun bakinsa ya yi kissing sannan ya ce. “I like this.” Ita dai ji take kamar ta fasa ihu, kunyarsa take ji sosai kamar zata hallaka ta, amma shi ta ga kamar bai san da wata aba kunya ba. Ya ɗauko cup ɗin da ya haɗa tea ya kai bakinta, ba musu ta buɗe bakin ta fara sha saboda so take su yi su gama ya sake ta ta huta, ita kam baza ta iya da wannan abun kunyar ba. Tea ɗin har ya fara hucewa amma haka take sha saboda a ganinta sake ƙara haɗa wani ma sabon wastern time ne da ƙara yawan kasancewarsu tare. Shi ya ciyar da ita amma shi bai ci komai ba, kamar ta share sai kuma zuciyarta ta kasa haquri da hakan. Kanta a ƙasa ta ce. “Kai baka ci ba.” Ya yi shiru kamar bai ji ta ba. Ta ɗan ɗago kanta ta ce. “Yaya baka ci abincin ba.” Ya shafi lips ɗinta ya ce. “Kina son in ci ne?” Da sauri ta gyaɗa masa kai. Ya ce. “To bani in ci.”Bata kuma magana ba ta janyo cup ta haɗa masa sabon tea sannan ta zuba masa komai na gurin a cikin plate. Ta zame daga jikinsa ta zauna a ƙasa, ta gyara zip ɗin rigarta da ya fara zuge mata. Ta janyo kayan zuwa gabansa. Ya tallafe fuskarsa da hannunsa yana kallon kayan break ɗin ya ce. “What is this?” Ta ce. “Ci zaka yi.” Ya ce. “Sai dai ki bani.” Ta rufe fuskarta da hannunta kamar wadda ta yi sab’o tana girgiza masa kai. Ya ce. “To ɗauke abinki daga gabana.” Ta cire hannun kamar zata yi kuka ta ce. “Dan Allah Yaya ka ci , ni dai bazan iya baka ba.” Bai ce komai ba ya janyo ta jikinsa sannan ya fara cin abincin. Sai ta ji daɗi a ranta har da sakin ajiyar zuciya. Tana jikinsa har ya gama sannan ta samu ya sake ta. Tattara kayan gurin ta yi ta kai kitchen ta tsaya wanke su. Kafin ta gama har ya shiga dakinsa ya d’auko laptop ya dawo falon yana lallatsawa. Data fito har ta fara murna zata sarara babu takurarsa tunda yana aiki, ta yi hanyar balcony zata shiga ɗakinta ta ji ya ce. “Come here.” Ta ɓata fuska sosai kamar zata fashe da kuka, ta ƙarasa inda yake tana k’unk’uni a cikin ranta. Ya zaunar da ita a gefensa tare da kwantar da kanta akan kafaɗarsa ya cigaba da aikinsa. Ta ce. “Yaya Mama fa zan kira.” Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. “Not now.” Ta turo baki wanda ya zame mata jiki, yana jin ta sai mutsu_mutsu take, she is totally uncomfortable, bata da damar tashi ne kawai. Ya yi ɗan murmushi tare saka hannunsa ɗaya ya shiga shafa bayanta, a ransa yana faɗin dole ya yi maganin rashin sakin jikin nan nata da shi tare da cire mata kunya da tsoronsa soon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button