NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Sai da aka kira Sallar Azhar ya ajiye system ɗin, lokacin har ta yi bacci a jikinsa. Kamar kar ya tashe ta amma dai ya tashe tan dan ta yi Sallah. Ta buɗe idonta kaɗan, ya shafi saman idon ya ce. “Lokacin Sallah ya yi, idan kin yi Sallar sai ki koma baccin.” Ta gyaɗa masa kai kawai. Ya taɓa goshinta ya ce. “Ya jikin naki da kan?” Ta ce. “Sun yi sauƙi.” Ya ce. “Allah ya ƙara sauƙi.” Sannan ya kama hannunta suka miƙe dan yin alwala. Bata koma baccin ba bayan ta idar da sallar kamar yadda faɗa. Gyaran gidan ta shiga yi duk da babu wani datti a cikinsa, cikin 1 hour ta gyara ko ina, ta kunne burner ta saka turaren wuta ƙamshi ya bud’ad’e gidan. Ameen bai dawo ba har 2 ta wuce, hakan ya yi mata daɗi ba kaɗan ba, dan ita al’amarin sa ya daina bata mamaki sai tsoro, sai tambayar kanta take ‘dama haka auren yake miji ya yi ta manne maka kamar wani cingum.’ Wayarta ta ɗauko ta kunna data ta shiga WhatsApp.
Ko gama shigowa messages ba su yi ba ya buɗe ƙofa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Ta amsa masa tare da ajiye wayar hannunta ta miƙe ta ce. “Sannu da zuwa.” Ya ce. “Yawwa, ki shiga daki za’a shigo da kaya ne.” Ta juyo ta nufi ɗakin. Slindern gas ne ya yi repiling sai kuma cartoons ɗin lemuka da ruwa wasu samari guda biyu suka shigo da su. Bayan sun tafi ya shiga ɗakinta ya tarar da ita a kwance. Ya tsaya a bakin gadon ya ce. “Baccin kenan?” Ta tashi zaune ta ce. “Yanzu zan yi, gyaran gida na tsaya yi.” Ya miƙa mata hannunsa ya ce. “Taso mu je ki ga wani abu.” Bata yi musu ba ta sakko ya kama hannun nata suka fita, suna fita falo ta ga babu wayarta a inda ta ajiye. Ta kalle shi ta ce. “Yaya wayata ban gani ba.” Ya ce. “Ni na ɗauka, i want check something.” Bata kuma magana ba suka shiga kitchen. Lemukan suka sassaka a cikin fridge sannan Ameen ya kunna shi ya fice. Ita kuma tsayawa ta yi tana ƙara ƙarewa kitchen ɗin kallo, ya yi mata kyau sosai bata gajiya da kallonsa, dama ita a rayuwarta tana k’aunar kitchen. Ta fita falon ta tarar da shi kwance akan doguwar kujera ya kunna TV. A hankali ta ce masa. “Su Aunty sun ce za su zo kuma har yanzu na ji shiru.” Ya kalle ta ya ce. “So?” Ta ce. “Ka bani wayar in kira su in ji me ya tsayar da su, sannan in yi magana da Mama.” Ya miƙa mata hannunsa, ba musu ta taho ta kama amma fa a tsorace take da shi. Ya zaunar da ita a gabansa bai ce komai ba. Ta ɓata fuska zata fara shagwab’arta suka ji ƙarar shigowar Mota gidan. Da murna ta ce. “Ga su nan ma insha Allah.” Ya mintsine ta a hannu ya ce. “So kike su zo saboda in rabu da ke ko? Ai ba kwana zasu yi ba zasu tafi ne.” Ta sosa inda ya mintsine tan tana cinno baki gaba, dalle mata bakin ya yi ta keɓe fuska zata fara sana’ar tata. Knocking ɗin ƙofa ne ya hana ta yin abun da ta yi niyya. Ta tashi da sauri cikin murna, yana kiran ta ma bata ji ba. Da Haneefah ta fara cin karo bayan ta buɗe ƙofar. Ta doka tsalle ta rungume ta. Aunty Sadiya dake bayanta ta ce. “To kayar da ita ki yi muku asarar babyn.” Ta saki Haneefan tana murmushi ta ce. “Da kuwa Ya faruq ya yi ƙasa ƙasa da ni a garin nan.” Haneefah dai bata ce komai ba sai bin ta da kallo take tana murmurshin munafurci. Ta basu hanya suka shige, sai a lokacin ta ga Hameedah da Aunty Hauwa da Matar Uncle Usman. Ta yi mamakin ganin Hameedah amma bata nuna ba. Ameen ya tashi zaune yana yi musu sannu da zuwa. Aunty Sadiya ta shiga tsokanarsa, ya yi murmushi kawai ya ƙi biye mata. Haneefah sai kunshe dariya take, ya harare ta sannan ya gaishe da su Aunty Hauwa, Hameedah ta gaishe shi ya amsa mata ba tare da ya kalle ta ba sannan ya miƙe ya fice. Kaya aka shiga shigowa da su falon, kayan abinci da kayan lefen Neehal da kayan sawanta na gida, sai manyan robobi dake ɗauke da cincin, dubulan da alkaki. Neehal ta buɗe store aka zuba mata kayan abincin, kayan lefen kuma su Aunty suka shigar mata da su daki. Bayan sun gama shigar da kayan ta kawo musu drinks sannan ta ɗauko plates ta zuba musu abincin da suka zo da shi a ƙatuwar warmer. Ta dubi Aunty ta ce. “Ina Mama da Aunty A’isha da Hajiya?” Aunty Sadiya ta ce. “Suna nan ƙalau, daa da Ya A’ishan ma zamu zo ta ce mu taho kawai ta zo daga baya, Hajiya ma har ta shirya Ya Fateemah ta hana ta zuwa.” Neehal ta ce. “Kai Mama, ita bata zo ba shine zata hana ta zuwa, ina twins ɗina?” Aunty Sadiya ta ce. “Sun tafi gidan Mamy ai tun jiya da daddare.” Ta ce. “Okay.” Barinsu ta yi su suna cin abinci ta shiga ɗakinta, Haneefah da gulma da tsegumi ke cin ta ta biyo bayanta. Cikin tsokana ta ce. “Ka ga amaryar Yayanta, um’um.” Sai ta saka dariya ta ce. “Ɗan bani labarin daren jiya mana.” Neehal ta harare ta, ta ce. “Da kin sani ai shi kika tambaya tunda kin tarar da shi a gidan.” Haneefah ta ce. “Na san ma babu abun da ya faru tunda na gan ki ragal, Yaya ya daga ƙafa kenan.” Neehal ta ce. “Ke kika sani dai.” Haneefah ta ce. “Ke dai zaki sani, yarinya zaki gane kuranki ne.” Bata kula ta ba, ita kuma Haneefah ta cigaba da tsokanarta tana zuzuta mata wahalar abun.” Da abun ya ishe ta sai ta keɓe fuska kamar zata yi kuka. Haneefah ta kyalkyale da dariya ta ce. “Ki adana kukanki zuwa dare yarinya zai fi miki amfani a lokacin.” Da Neehal ta ga abun nata iskanci ne kawai da tsokana sai ta fice ta bar mata ɗakin.
Har bayan laasar suna gidan anata hira, Hameedah sai shishshigewa Neehal take. Ita da Matar Uncle Usman suka jerawa Neehal kayan sakawarta a cikin wardrobe. Bayan sun gama kintsa mata gidan tsaf suna shirin tafiya Aunty Sadiya ta ja Neehal daki, ƴar nasiha ta ƙara yi mata akan zaman aure sannan ta bata wasu magunguna ta ce ta dinga sha kafin ta kwanta. Neehal ta karɓa a kunya ce, ta mik’o mata wani abu a leda ta ce. “Ga hand dryer nan, tun ranar da za mu zo jere na manta ban taho da ita ba, na san zaki buƙace ta sosai a yanzu.” Neehal ta karɓa ta ciro ta a kwalinta ta gani tare da yi mata godiya. Aunty Sadiya ta miƙe tana faɗin. “Ki dinga shiga ruwan zafi akai_akai, na san ki da shegen son jiki duk zafin da zaki ji idan kin shiga ki daure na ɗan lokaci kaɗan ne, amma zaki ji daɗin jikinki sosai.” A kunyace ta amsa mata da “Toh.” Amma ko kaɗan bata tunanin abun da suke nufi zai faru tsakaninta da Yayanta nan kusa.
Ganin da gaske tafiya zasu yi Neehal ta marairaice ta ce. “Dan Allah ku bari sai dare sai ku tafi, in kuka tafi fa ni kaɗai zan zauna a gidan.” Haneefah ta ce. “Zabuwa uwar tsoro, na ga da mai gadi a gidan.” Aunty Hauwa ta ce. “In mun kai daren ma idan zamu tafi haka zaki ce.” Ta yi ƙwalƙwal da ido kamar zata yi kuka, Aunty Sadiya ta tallab’a ta sannan suka tafi Haneefah na yi mata dariya. Sai da ta ga fitar su daga gidan sannan ta koma ciki daga rakiyar da ta yi musu. Tana shiga falon ta zauna tana hawaye, sosai take kewar gida da su Mama, gashi ya ɗauke mata waya bare ta kira Maman ta ji muryarta ko zata ji daɗi. A haka Ameen ya dawo ya same ta. Ya zauna a kusa da ita ya janyo ta jikinsa ya ce. “Su Aunty sun tafi sai kuka kuma?” Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta ƙara volume ɗin kukan nata. Ya shiga bubbuga bayanta cikin rarrashi ya ce. “Sorry, bari na miki Mama amma sai kin yi kin bar kukan.” Da sauri ta haɗiye kukan ta ce. “Na daina.” Tana share hawayenta. Ya taya goge hawayen sannan ya ɗauko wayarsa a aljihunsa ya yi dialling numbern Maman, Neehal kamar ta k’waci wayar dan zumuɗi da ƙaguwa.