NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Mama tana ɗakin Daddy tana haɗawa su Ummin Ahmad kayan biki, sun zo yi mata sallama ne gobe da sassafe za su wuce kiran Ameen ya shigo wayarta. Ta ɗauko ta ɗaga tare da yin sallama. Ameen ya amsa mata sannan suka gaisa ya yi mata godiyar kayan garar da aka kawo. Ya kalli Neehal wadda kaɗan ya rage ta fashe masa da kuka saboda ya ƙi bata wayar ya ce. “Ƴar rigimarki ce take son ta yi magana da ke.” Mama ta yi murmushi ta ce. “To bata wayar mana, ko sai ka gama ja mun ran ƴa tukunna.” Ya miƙawa Neehal wayar yana murmushi. Ta karɓa da sauri a hankali ta ce. “Mamana.” Mama ta ce. “Na’am Daughter, ya kike?” Ta ce. “Lafiya kalau, ina Daddy?” Mama ta ce. “Yana nan ƙalau, ya baƙunta? Da fatan babu matsalar komai dai?” Ta ce. “Alhamdulillah babu komai Mama sai kewarku da nake.” Sai kuma ta ɓata fuska ta fara hawaye ta ce. “Mama shine yau baki kira ni ba tun safe, yanzu ma sai da na kira ki.” Mama ta ce. “Ki yi haquri Neehal, kin san har yanzu da baƙi a gidan ban samu zama ba.” Ta ce. “Shikenan to.” Suka cigaba da magana tana zubawa Mama shagwab’a. Ameen ya k’wace wayarsa ya yiwa Mama sallama ya kashe kiran. Ta turo masa baki. Ya tsaya kawai yana kallon ta, ta yi masa kyau ba kaɗan ba, gaba-d’aya ta sauya masa saboda dad’ewar da ya yi bai gan ta ba kafin biki, abun da ya fi komai ɗaukar hankalinsa a gare ta daddaɗan ƙamshin dake tashi a jikinta, jiya kawai dauriya ya yi amma ba ƙaramin tasiri ƙamshin ya yi a gare shi ba. A hankali ya saka fuskarsa a wajen wuyanta yana sakin sassanyar ajiyar zuciya, ya lumshe ido yana shaƙar ni’imtaccen ƙamshinta. Dif ta yi ta ƙi motsi saboda razana, numfashi kawai take saukewa a hankali, sosai gabanta yake fad’uwa tsoro ya cika mata zuciya. Ya ɗago kansa ya zubawa ƙirjinta ido yana kallon yanda yake d’agawa da komawa saboda bugun da zuciyarta take yi da sauri da sauri. A hankali ya kai hannunsa kan ƙirjin nata, ta yi saurin ture hannun nasa gami da fuskarsa a lokaci ɗaya. Ya janyo ta da sauri ya haɗe bakinsu guri guda ya fara kissing ɗinta…..
Kiran Sallar Magriba ne ya cece ta daga hannunsa, ta tashi da sauri tana mayar da numfashi ta yi ɗakinta ta kulle ba tare da ta kalli side ɗin da yake ba. Ta jingina bayanta da ƙofa tana sakin ajiyar zuciya. Tana jin shi ya buɗe tashi ƙofar ɗakin ya shiga. Daƙyar ta iya jan ƙafarta ta ƙarasa ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta yi Sallah. Bayan ta idar ta koma toilet ta yi wanka saboda yanda take jin jikinta wani iri. Har aka yi isha’i bata ji shigowar Ameen gidan ba, ta zauna a bakin gado ta rafka tagumi maganganun Haneefah na yawo a kwanyarta, ta san wani abun ba haka ba ne Haneefan ta faɗa ne kawai, amma wani abun data faɗa kuma gaskiya ne. Hakan ya ƙara tsorata ta, ga abubuwan da Ameen ɗin yake mata su ma suna ƙara firgita ta, ita bata son wannan abun gaskiya tsoro take ji sosai. Gashi wannan Ameen ɗin ba wanda ta sani ba ne a da, new Ameen ne a gurinta. Ta lumshe ido tana tunanin sabbin abubuwa a gare ta da yake mata. A hankali ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo, ta buɗe idonta suka sauka a kansa yana ƙarasowa ciki bayan ya yi sallama hannunsa ɗauke da ledodi guda biyu……….✍️
By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
8️⃣4️⃣
Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.
………..Ya riga ta tashi da asuba, da ya tashe ta Sallah daƙyar ta tashi saboda baccin dake kanta, shi ya kaita toilet ta yi alwala saboda ƙin tafiya ta yi, wai ita tsoro take ji kar ta yi tafiya ciwon da take ji a jikinta ya ƙaru. Ya zira mata doguwar riga da hijabi cikin lallab’awa yana ta yi mata sannu ita kuma tana ta yi masa shagwab’a da rakin ciwon da jikinta yake mata. Bayan ya shimfid’a mata darduma ya fita zuwa masallaci. A tsaye ta yi Sallah amma ba ƙaramar dauriya ta yi ba, dan har jiri_jiri take ji yana k’wasarta. Tana idarwa ta cire hijibin jikinta ta koma gado ta kwanta, ko 2 minutes bata yi da kwanciyar ba bacci ya ɗauke ta. Bayan ya dawo ya yi mamaki da ya tarar har ta yi bacci, niyyarsa idan ya dawo ya haɗa mata tea ta sha sannan ya bata magani. Ac’n ɗakin ya kunna bayan ya yaye bargon data rufa ya ga yanda take haɗa gumi. Jallabiyar jikinsa ya cire ya kwanta tare da janyo ta jikinsa, ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara lafewa a jikinsa. Kyakkyawar Fuskarta ya zubawa ido yana jin yanda k’aunarta take ƙara mayaye ko wanne gurbi na zuciyarsa. Bambancinsu dake bayyane na zahiri ita da Hafsah yake aunawa a cikin zuciyarsa. Hafsat tana da kyawunta dai-dai gwargwado, amma Neehal ta fi ta kyawun fuska dana jiki kuma ta fita tsaho da cikar gashi, Tsayi kawai Hafsat zata ɗara Neehal shi ma da kaɗan, hasken fata kuma dukkanninsu Farare ne, sai dai kowacce kalarta daban. Ɓangaren tarbiyya da addini kuwa ko hanya Hafsat ba su haɗa da Neehal ba, Hafsat Sallah ma akan lokaci sai ya zanzare mata take yi, balle kuma su azkar da karatun Alqur’ani zai cewa bai fi sau a ƙirga yaga tana yi ba a zaman auransu. Neehal kuwa ya san perfect ce a wannan fannin. Batun iya girki ma baza a haɗa Neehal da Hafsah ba ko kaɗan, Hafsat tana yi ne kawai dan gudun ɓacin ransa, kuma rabi da kwata Ƴan aiki ne suke yi, zai iya cewa ita taya su kawai take yi dan kar a ce bata yi ba. Batun tsafta ma Neehal ta ɗara Hafsat, musamman tsaftar muhalli, jikinta ne dai bata barin shi da ƙazanta, ta wannan fannin kam zai yabe ta, dan ƴar gayu ce sosai Hafsat. Amma gayun nata har ya yi yawa ya koma iyayi da firirita. Duk da haka baza ta nunawa Neehal gayun ba, amma nata ya fi na Neehal fitowa dan ita over acting take yi masa. Ya sauke numfashi tare da lumshe ido ya fara shafa fuskar Neehal a ransa yana yiwa Allah godiya da ya mallaka masa ita a lokacin da ya gama fitar da rai da samunta. Jin ta ɗan motsa yasa ya buɗe idonsa, sai ya ga ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba cikin baccin. Ya shafi lips ɗin nata tare da ɗan murmusawa, ya lura hakan ya zamar mata jiki saboda tsabar shagwab’arta. Ya yi mata light kiss sannan ya lumshe idonsa hannayensa zagaye da bayanta, a haka bacci mai daɗi ya ɗauke shi.
Ta riga shi tashi da safe, ta yi wajen 5 minutes da farkawa amma ta ƙi koda buɗe idonta ne balle ta yi ƙoƙarin tashi. Ciwon da jikinta yake mata har yanzu yana nan, Ciwon kai ne dai ta samu sauƙin shi. A hankali ta buɗe kumburarrun idanunta da suka canza kala saboda kukan da ta sha a daren jiya. Ta yi ƙoƙarin tashi ta ji ta gam a jikinsa ya riƙe ta. ɓata fuska fuska ta yi, tana son tashi kuma tana tsoron kar ya farka. A hankali dai ta lallab’a ta tashi zaune tana taune lips ɗinta saboda yanda take jin jikinta. Fuskarsa ta zubawa ido da saman cikinsa zuwa ƙirjinsa da ya bayyana sakamakon tashi zaunen da ta yi bargon da suka lullub’a ya yi ƙasa. Kalamansa na jiya da ya faɗa mata ne suke dawowa cikin kunnenta kamar a yanzu yake faɗa mata. Ta lumshe ido tana tuna yanda ya kira sunayenta guda biyu na gaskiya dana inkiya. Abun da bata taɓa ji ya faɗa ba, sai ta ji sunan ya yi daɗi a cikin muryarsa, ta ji kamar babu wanda ya iya faɗar sunanayen nata sai shi. Wani murmushi ne ya kufce mata ba tare data shirya masa ba. Wani baƙon al’amari ne yake riskar zuciyarta a game da yayan nata. Ta buɗe idonta tana kallon kyakkyawar fuskarsa, ji ta yi kamar ta kai hannu ta shafi kyakkyawan sajen fuskarsa ko kwantaccen gashin ƙirjinsa mai sheƙi wanda hasken farar fatarsa ya ƙara fito da baƙinsa. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta yunk’ura da nufin ta fice daga cikin bargon ta sauka daga kan gadon. Caraf ta ji ya riqo qugunta, ta juyo a tsorace ta kalle shi. A hankali ya buɗe idonsa dake cike da bacci, cikin muryarsa data ɗan sirka sakamakon baccin da ya yi ya ce. “Kina tunanin zan iya cigaba da bacci ne bakya tare da ni?” Kawar da fuskarta ta yi gefe bata ce komai ba. Ya ɗan ɗago kansa ya ce. “Ina zaki in kin tashi?” Ta girgiza masa kai alamun babu ko’ina. Ya janyo ta sai gata zaune akan ruwan cikinsa. Cikin shagwab’a ta ce. “Aushh!” Ya shafi fuskarta ya ce. “Sorry Dear, ciwon ne har yanzu ko?” Ta yi ƙasa da kanta ta ƙi cewa komai, ita fa kunyarsa take ji sosai kamar zata nitse, amma ta lura shi ko a jikinsa. Ya ɗago kanta ta yi saurin runtse idonta tare da saka hannayenta ta rufe fuskarta. Ya yi murmushi ya ce. “Open your eyes please.” Mak’e masa kafaɗa ta yi. Ya ce. “Okay, in hana ni ganin fuskarki sai in kalli other part ai.” Ya ƙarashe maganar idanunsa akan ƙirjinta. Ko ba’a faɗa mata ta san inda yake nufi zai kalla, hakan yasa ta yi saurin kwanciya akan ƙirjinsa tana keɓe fuska. Ya ƙara yin murmushi tare da ɗora hannunsa akan bayanta ya fara shafawa slowly. Luf ta yi a jikinsa tana shaƙar daddaɗan ƙamshinsa da take masifar so a rayuwarta. Kamar mai rad’a ya ce. “Ya jikin naki?” A shagwab’e ta ce. “Da sauƙi.” Ya ce. “Bari na ga gurin, kar na je da rauni sosai.” Saurin tashi ta yi daga jikinsa ta fara hawaye ta ce. “Ni ba sai ka gani ba.” Bai kula ta ya tashi zaune sosai ya kwantar da ita, tana mammatse ƙafa da kuka ya duba ya ga babu raunin da ya yi tunani. Rungume ta ya yi yana aikin rarrashi, daƙyar ya samu ta yi shiru ta bar kukan. Amma fa ko da wasa ta ƙi bari su haɗa ido. Cikin tsokana ya ce. “Babu rauni a gurin dan haka bari na ƙara.” Ya rank’wafa jikinta kamar gaske. Ta fashe da kuka jikinta har rawa ya fara saboda tsorata, ta ɗauka da gaske yake. Ya lakuci hancinta ya ce. “Raguwa kawai.” Ta tura masa baki. Yana tsokanarta ya tashi ya fice daga ɗakin dan samar mata abun da zata ci. Ta samu ita ma ta tashi ta shiga toilet tana tafiya daƙyar, wanka ta yi tare da ƙara gasa jikinta. Tana fitowa ta shirya cikin sauri dan kar ya dawo ya same ta ba kaya. Wani yadi ta saka maroon colour ɗinkin riga da skirt, ya yi mata kyau sosai ta yi ɗaurin ɗankwalinta simple sannan ta shiga ƙoƙarin gyara ɗakin. Tana cikin jera pillows akan gado ya dawo hannunsa ɗauke da ƙaramin tea flaks da cups da spoons. Ya ajiye kayan a ƙasa sannan ya ce. “Wa ya aike ki aiki ke da ba lafiya ba?” Ta ɗago ta ce. “Mene aikin a nan?” Tsayawa ya yi yana kallon ta dan ta yi masa kyau ba kaɗan ba, a hankali ya taka zuwa inda take ya rungume ta ya ce. “You look so beautiful Baby love.” Sannan ya yi kissing check ɗinta ya sake ta ganin har ta fara keɓe fuska. Ya juya ya fita ita kuma ta cigaba da abun da take tana sakin ajiyar zuciya. Bai jima ba ya dawo da kayan su Madara da milo da ledar magunguna a hannunsa. Ya zauna akan Carpet ɗin bakin gado ya fara haɗa mata tea ɗin. Ta dube shi ta ce. “Yaya share ɗakin fa zan yi.” Ba tare da ya dube ta ya ce. “Ki bar shi ki zo ki sha tea.” Bata ce komai ba ta ƙaraso ta zauna a gefensa. Ya miƙa mata tea ɗin ta karɓa dan ba karya tana jin yunwa. Sai da kusa shanyewa ta ajiye cup ɗin. Yana kallon ta ya ce. Ki ƙara mana. Ta ce. “Na ƙoshi.” Bai ce komai ba ya janyo ledar magungunan da ya shigo da ita ya fara fito da su. Ya miƙa mata bottle water ya ce. “Bari na b’aro miki magungunan.” Ta kalli maganin ƙwayar dake gabanshi kusan kala biyar tana yatsina fuska ta ce. “Yaya duk ni zan sha magungunan nan?” Ya ce. “Eh.” Ta ce. “Na mene?” Ya ce. “Akwai na ciwon jiki dana rage zugi dana zazzaɓi.” Ta ɓata fuska ta ce. “Ni fa lafiya ƙalau.” Ya ce. “I knew.” Kamar zata yi kuka ta ce. “Da gaske fa.” Duk da ita ma tasan ba hakan ba ne dauriya kawai take, amma ita kaɗai ta san me take ji a jikinta. Ya miƙa mata maganin ta ƙi karɓa, ta ce. “Kai fa ba doctor ba ne Yaya.” Ya kalle ta yana murmushi ya ce. “Amma ai ɗan Doctor ne ko?” Ta turo baki ta ce. “Nima ai ƴarta ce.” Ya janyo ta jikinsa ya ce. “Dama waya ce ba ke ƴarta ba ce? Wa ma ya isa ya faɗa.” Shi ya bata maganin tana bab’b’ata fuska kamar zata yi kuka ta haɗiye. Ya kwantar da ita cikin mintuna kaɗan ta yi bacci, saboda harda maganin da yake saka a bacci a cikin wanda ya bata. Bayan ya kwashe kayan ya kai kitchen ya dawo ya yi karatun Alqur’anin da bai samu ya yi ba bayan Sallar Asuba kamar yadda ya saba kullum. Ƙarfe goma da mintuna Mama ta turo aka kawo musu breakfast, ya ɗiba ya ci sannan ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya. Falo ya koma ya kira abokansa da suke ta yi masa missed call tun jiya, abun da ya guda shi suka dinga yi masa wato shak’iyanci, wai saboda ya yi amarya ya b’uya kwana biyu ko d’uriyarsa ba’a ji. Sai da 12 na rana ta wuce sannan Neehal ta tashi, Alhamdulillah jikin nata ya yi mata sauƙi sosai, ciwon jikin da zugin da take ji duk sun tafi sai kaɗan. Jikinta ne kawai take jin shi fayau babu k’wari. Abincin da Mama ta kawo ya haɗa mata ta ci sannan ya fita Masallaci dan yin Sallar Azhar. Ita kuma ta shiga gyaran gidan, bayan ta gama ta yi Sallah sannan ta dawo falo ta kunna kallo dan ta gaji da kwanciya, shi kuma bai dawo ba dama ya ce mata zai biya ta wani guri kafin ya dawo. A tunaninta gidansa zai je gurin Hafsat dan ita har yanzu bata san Hafsan ta yi yaji tana gidansu ba, tunda babu wanda ya sanar mata………✍️