NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Har bayan isha’i Ameen bai dawo ba. Ta yi wankanta ta shirya cikin wasu riga da wando masu kyau, wandon irin mai buɗewan nan ne ta ƙasa, ta saka hula pink colour a kanta da yake kwalliyar jikin kayan pink colour ce, ta yi kyau sosai. Ta zauna a falo tana kallo sai baza ƙamshi take. Tara saura Ameen ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama. Ta kalle shi cikin wani irin salo ta juya masa ido tare da amsa masa sallamarsa cikin karyar da murya. Sandarewa ya yi yana kallon ta dan salon nata ya shige shi ba kaɗan ba. Bata motsa ba sai ido data zuba masa tana murmushi. Ya ƙaraso a hankali ya ajiye ledodin hannunsa ya rungume ta tare da sakin ajiyar zuciya. Ita ma ajiyar zuciyar ta sauke ta ɗan shafa kansa ta ce. “Welcome Yayana.” Ya lumshe idonsa yana ƙara shigar da ita jikinsa tare da shaƙar ƙamshinta da ya fara saukar masa da kasala. Ta ɗan ture shi ta ce. “Daga zuwanka zakai mun syqueising ɗin kaya.” Ya buɗe idonsa yana sauke numfashi ya ce. “Kin yi kyau sosai baby, ina son wannan ƙamshin naki.” Ya ƙarashe zancen yana shafa kwantaccen gashin gaban goshinta. Ta ɗan murmusa ta ce. “Thank you.” Sannan ta bar jikinsa ta tashi ta nufi fridge. Ya bi ta da kallo. Ruwa ta tsiyayo masa mai sanyi a cikin glass cup ta kawo masa, ya karɓa tare da yi mata godiya ya shanye. Ya janyo ta ya ɗora ta akan cinyarsa sannan ya buɗe ledodin da ya shigo da su, ice-cream ne da choculates da wafer da popcorn a ciki, abubuwan da ya san tana matuƙar son su sosai. A baki ya bata komai ta ci, shi kuma ya sha ice-cream kawai. Ta tattare sauran ta ajiye a fridge bayan sun gama. Ya Ɗauke ta cak ya kai ta ɗakinsa ya dire akan gado shi kuma ya shige toilet. Murmushi ta yi ta tashi ta fice ta koma ɗakinta ta kwanta. After 20 minutes ya biyo bayanta, ya shirya cikin wasu white ɗin kayan bacci. Ya hau kan gadon ya yaye bargon data lullub’a ya ce. “Da kika gudo nan ɗin bazan iya zuwa ba ne.”Cikin marairaicewa ta ce. “Ni fa Yaya bacci nake ji, ka koma ɗakinka.” Ya ɗora hannunsa a kan cikinta ya ce. “I can’t.” Ɓata fuska ta yi bata kuma magana ba, Ƙasa ya yi da hannun nasa a jikinta ya ce. “Ya jikin naki? I hope kin warke?” Kamar zata yi kuka tsoro ƙarara akan fuskarta ta ce. “Ni ban warke ba.” Ya kwanta tare da janyo ta jikinsa ya ce. “Kar ki mun kuka, babu abun da zan miki, I just want to sleep with you.” Ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido ta saka hannayenta ta zagaye bayansa da su kamar yadda ta ji ya yi mata……….✍️
Ban yi edit ba.
By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
8️⃣6️⃣
Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.
⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️
Jameey yar’mutan kankia
Promo Promo Promo
Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake.
300-sau biyu a rana
500 -sau ukku a rana
700 -sau hudu a rana
Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316
………Cikin one week Ameen ya koyawa Neehal son sa da k’aunarsa, wata shak’uwa ce ta ƙara shiga tsakaninsu mai ƙarfin gaske, a yanda suke jin junansu a zuk’atan su ko 1 second basa son su yi ba tare da junansu ba. Ameen ƙarshe ne a iya soyayya da kula da tattali da tarairayar mace. Through out yana gida manne da Baby love ɗinsa suna zuba k’auna, Sallah ce kawai take fitar da shi zuwa Masallaci, sai kuma idan ta yi baƙi, dan kusan kullum a cikin Family ko friends ɗinta wasu sai sun zo mata, Haneefah ma ta zo ta wunar mata. Neehal ta yarda ta kuma gasgata cewa Ameen ba ƙaramin so yake mata, kwata_kwata yanzu babu wannan miskilancin bare haɗe rai. Ita ce ma take ɗan taɓa masa idan class ɗin ya motso mata. Neehal an samu abun da ake so tay ta zuba masa shagwab’a yana lallab’a ta. Sai dai har yanzu bata daina jin kunyarsa ba, tana dai ɗan daurewa ta ƙoƙarta ta nuna masa soyayya dan ta lura yana jin daɗin hakan sosai. Za su wuni tare manne da juna sai dare ya yi ta gudu ɗaki ta kulle, shi kuma ya yi amfani da spare key ya buɗe ɗakin ya bita ya nuna mata bai san wannan zancen ba, tay ta bab’b’ata fuska tana rigima amma duk da haka sai ya yi abun da take gudun, idan ya gama sai ya shiga aikin rarrashi.
Yau asabar, wanda ya kama kwana takwas da tarewar Neehal. Misalin ƙarfe goma sha biyu na rana tana tsaye a kitchen tana aikin girkin rana. Sanye take cikin wani straight skirt Black colour mai tsaga a baya, sai riga mai ƙaramin hannu light Brown, irin roban nan ce mai bin jiki, ta kama jikinta sosai. Kanta babu ɗankwali sai bana data saka kalar rigar jikinta, ta yi parking ɗin gashinta sai sheƙi yake ya sha oil na man kitso mai ƙamshi. Sauri take yi ta kammala aikin nata kar Ameen ya tashi daga baccin data bar shi yana yi, tun bayan kwana uku da Mama ta daina kawo musu abinci ita take girkinta. Idan zata yi girkin kodayaushe Ameen yana manne a jikinta, duk inda ta ɗora ƙafarta nan zai saka tashi, in ta yi complain ya ce taya ta aikin yake yi, alhalin ba haka ba ne delay ma yake ja mata a aikin nata, abun da zata yi shi in one hour sai ta yi kusan 2 hours. Tana aikin tana tunanin a ka’ida fa jiya Ameen zai bar gidanta ya koma gidan Hafsah, amma sai ta ga ya ƙara kwana. Ta yi ta mamakin abun amma dai bata yi masa magana ba, yau ma kuma ta ga bashi da alamar zuwa gidan Hafsan. Amma ta ƙudurce a ranta zata yi masa magana anjima akan hakan.
Ƙamshin turaren Ameen ta ji ya cika mata hanci da kuma sign na ana kallon ta, ta juya da sauri ta gan shi tsaye yana kallon ta, jikinsa sanye da single da threequarter wando. Bata ce masa komai ba ta juya ta cigaba da aikinta. Ya ƙarasa inda take a hankali ya rungume ta, ta baya tare da sakin ajiyar zuciya. Ta lumshe ido ta buɗe ta juya tana kallon shi tare da ɓata fuska ta lakuce masa hanci ta ce. “Wa ya ce ka tashi yanzu?” Ya langwab’ar kai ya ce. “Saboda kin tashi mana.” Ta ɗan ture shi ta ce. “Ka koma baccinka ka bar ni in yi aikina.” Ya jingina da jikin cabinet bai ce komai ba, sai kalar tausayi da ya yi da fuskarsa kamar sabon maraya. Ta juya ta cigaba da aikinta tana murmushi ƙasa_ƙasa. After 5 minutes ta juyo ta ce masa. “Ya da shiru kuma?” Ya ɓata fuska kamar wani yaro tare da ɗauke kai. Ta ƙarasa jikinsa ta saka hannayenta duka ta zagaye wuyansa ta ce. “Wa ya taɓa mun Yayana a tsakar ranar nan?” Bai kalle ta ba shi a dole fushi yake ya ce. “Ke ce mana, na zo zan taya ki aiki kin gwale ni.” Ta kwanta a jikinsa ta ce. “Ka taya ni aiki ko ka ƙara mun wani aikin?” Ya zagaye bayanta da hannunsa ya ce. “Duk a cikin tayin aikin ne ai.” Ta ɗago daga jikinsa ta ce. “To mu je a taya nin.” Ya yi murmushi yana bin ta da kallo. Ta juya masa ido. Ya ƙara janyo ta jikinsa ya ce. “Ko dai barin aikin nan zamu yi ne mu je mu yi wani.” Cikin shagwab’a ta ce. “Um,um Yaya baƙi fa zamu yi, sai sun zo bamu tanadar musu komai ba.” Ya kwantar da kansa akan kafaɗarta bai ce komai ba. A haka ta cigaba da aikin yana jikinta kamar kullum. Sai da aka kira Sallar Azhar sannan ta samu ya bar ta ya tafi masallaci.