NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan sun ci abinci sun yi wanka sun shirya suna zaune a parlour akan kujera 2 seater suna game a wayar Neehal aka yi knocking ƙofar parlour. Neehal ta bar jikinsa tana dariya ta yi masa gwalo sannan ta tashi cikin sauri dan kar ya cafko ta, ta nufi ƙofa. Haka take yi masa kodayaushe idan ta yi baƙi, ya yi murmushi tare da yi mata alamar zan kama ki ne. Kamar yadda ta zata Salma ce wadda ta raka ta gidansu Sadik ita da sistern ta. Neehal ta ce. “Sannunku da zuwa, amma fa na yi fushi sai yanzu zaku zo?” Salma ta ce. “Ki yi haquri, sai da muka yi girki ne.” Neehal ta ba su hanya suka wuce sannan ta mayar da ƙofar ta rufe. Suka gaisa da Ameen cikin mutuntawa da fara’a sannan ya tashi ya shige ɗakinsa. Neehal bata zauna ba sai da ta kawo musu drinks da abinci da kayan snacks ɗin gararta. Suka ƙara gaisawa sannan Salma ta ce. “Amarya kin sha ƙamshi, kin ga yanda kika yi kyau kuwa? Anya kuwa idan Mama ta gan ki zata gane ki?” Murmushi kawai Neehal ta yi dan ita akaran kanta ta san cikin one week ɗin nan ta sauya. Sai bayan Magriba su Salma suka tafi, saurayin Salman ne ya zo ɗaukar su, har bakin Motarsa ta raka su. Ga mamakinta sai ta ga Sadik ne. Ta riƙe haɓa tana kallon sa cikin tsananin mamaki, shi kuma ya shiga tsokanarta da amarsu ta Ango yana murmushi. Ta dubi Salma zata yi k’orafi Salman ta yi saurin ce mata. “Bari na yi ki gani da idonki dama.” Suka yi dariya gaba-d’aya sannan ta yi musu fatan Alkhairi suka yi sallama ta koma cikin gida, a ranta tana jin daɗin haɗewar Salma da Sadik . Da daddare suna shan fruits a falo ta dubi Ameen cikin nutsuwa ta ce. “Wai Yaya ba tun jiya ya kamata ka koma gidan Aunty Hafsah da kwana ba ne? Ya ɗago ya kalle ta bai ce komai ba amma fuskarsa ta sauya. Sai ta ji babu daɗi gabanta har fad’uwa ya yi saboda ta dad’e bata gan shi a cikin irin wannan yanayin ba. Sai ya daina shan fruits ɗin ma, ita ma ganin haka sai ta daina sha. Tana shirin tattare sauran yay mata wani kallo data san mana’ar shi, dole ta koma ta cigaba da sha. Sai da suka kwanta ta ga har lokacin ransa a b’ace yake sannan ta bashi haquri har da hawayenta. Ya rungume ta ya nuna mata komai ya wuce amma kar ta sake yi masa maganar. Abun ya bata mamaki ba kaɗan ba. Ta dinga tambayar kanta me zai saka Ameen ɗin ya yi haka?

Washegari da murna ta tashi dan Ameen ya gaji da rigimar da take masa na son ganin Mama ya ce zai kaita bayan Magriba ta gan ta. Da yamma tana aiki a kitchen ya shigo kitchen ɗin ya tsaya a kusa da ita. Ta dube shi tare da turo baki ta ce. “Kallon kenan?” Ya ce. “Na gaji da watching TV na zo kallon ki.” Ta ɓata fuska ta ce. “Dan Allah Yaya ka barni in yi aikin nan, yanda ka koyi cin nan idan ban yi maka abinci ba me zaka ci?” Ya ce. “Au acici ma na zama?” Ta ce. “Eh mana, da ai baka cin abinci sosai.” Ya ce. “A da ɗin ma Soyayyar ki da damuwar rashin mallakar ki ya saka hakan, yanzu kuma na same ki bani da wata sauran damuwa.” Ta yi murmushi kawai. Ya kwanta a jikinta yana sakin ajiyar zuciya. Cikin shagwab’a ta ce. “Allah Yaya kana takura mun fa a gidan nan, zan haɗa ka da Mama fa.” Ya ce. “Ke ce kike yin kyau ai ki yi ta ƙamshi mai daɗi, duk ki saka in zauce.” Ta yi murmushi kawai ta cigaba da aikinta.

Bayan Magriba kamar yadda ya alƙawarta suka je gidan Mama. Murna da zumuɗin Neehal suka kasa b’oyuwa. Dije ce ta buɗe musu ƙofa, cikin murna ta rungume ta suka gaisa sannan ta shige ciki tana ƙwalawa Mama kira. Girgiza kai kawai Ameen ya yi ya zauna a falon ƙasa. A ɗakin Mama ta tatar da ita akan darduma tana jan carbi, faɗawa jikinta ta yi ta rungume ta. Mama ta shafa kanta cikin farin cikin ganin ta, ta ce. “Yau Amarya ce a gidan namu?” Ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya. Mama ta ce. “Ina Ameen ɗin?” Ta ce. “Yana falon ƙasa, ina yini Mamana.” Mama ta ce. “Lafiya ƙalau.” Tare da bin ta da kallo ganin yadda ta ƙara kyau ta murje alamun tana cikin kwanciyar hankali. Ta ɓata fuska ta ce. “I missed you so much my Mum.” Mama ta ce. “Nima haka Daughter, kwana biyu gidan ya mun faɗi Ni kaɗai, babu mai zuwa ya ɗane mun jiki, sometimes da shagwab’a sometimes da murna.” Ta yi murmushi ta ce. “Ina Daddy?” Mama ta ce. “Yana masallaci, kin san sai an yi isha’i yake shigowa.” Neehal ta gyaɗa mata kai sannan ta ce. “Mama yanzu wa ya ke yi miki girki?” Mama ta yi murmushi ta ce. “Ni nake abuna mana.” Ta marairaice fuska ta ce. “Kullum kuma, ni bana son kina wahala.” Mama ta ce. “Mene abun wahala? Kin fi so in jibge inta zama babu ɗan motsa jiki.” Ta girgiza kai. Mama ta ce. “Ki bari In kin haifi Baby girl sai ki bani ita in ta girma sai ta dinga yi mun girkin.” B’oye fuskarta ta yi a jikin Mama tana murmushi. A haka Ameen ya shigo ya same su. Bayan Daddy ya dawo ta je part ɗinsa, ya yi farinciki sosai da ganin ta da yanayin data gan ta a ciki. Ta zauna suna ta shan hirarsu. Shi kuma Ameen yana can Mama ta saka shi a gaba tana yi masa faɗan ƙin zuwa gidan su Hafsah. Tana mitar suka je part ɗin Daddy, shi dai Ameen bai ce mata komai ba. Suna zama ta dubi Daddy ta ce. “Ka yi masa magana ya je gidansu yarinyar nan tunda ni ya ƙi jin tawa maganar.” Daddy ya ce. “Ba ƙi ya yi ba nina sani, baki san dalilinsa na ƙin zuwan ba, shi yasa kika ga ni ban shiga cikin maganar ba.” Mama ta ce. “Babu wani dalili, kullum sai dai ya dinga ce mun zai je zai je amma ya ƙi zuwa, ita rayuwa ai komai ɗan haquri ne, dama haka zaman tare yake zo mu zauna zo mu saɓa. Amma yarinya ta kusa wata biyu a gida ka ƙi zuwa, sai yaushe kenan zaka je?” Ya ɗago cikin sanyin murya ya ce. “Ki yi haquri Mum, insha Allahu gobe da yamma zan je.” Mama ta ce. “Yanzu na ji batu, ko kai fa, Allah ya kai mu goben lafiya.” Suka amsa da Amin. Sai a yanzu Neehal ta gano bakin zaren, dalilin da yasa ba ya zuwa gidan Hafsah ashe yaji ta yi, ita fa ta ce ko waya bata taɓa ganin sun yi ba, kuma bai taɓa ce mata zai je gidan ba. Sai ta ji babu daɗi a ranta tausayin Hafsan ya kamata.

Mama ta kawo abinci nan part ɗin Daddyn, Neehal ce kawai ta ci kaɗan shi Ameen ko ruwa bai sha ba. Tana gamawa ya ce ta taso su tafi. Ɓata fuska ta yi ta ce. “Ni anan zan kwana.” Bai ce mata komai ba ya yiwa su Mama sallama ya tashi ya fice. Har ta fara murna Mama ta ce. “Mu je in baki abun da zan baki ku wuce kar ya yi ta jiran ki.” Ta shagwab’e fuska ta ce. “Mama ya bar ni kwanan fa.” Mama ta ce. “Banga alama ba.” Daddy ya yi murmushi ya ce. “Ki yi haquri Daughter ki je ku tafi, idan an kwana biyu sai ki zo ki kwanan.” Ta gyaɗa masa kai sannan ta yi masa sallama suka fice da Mama. Ameen yana cikin Mota ya hango ta tana tahowa fuskar nan a keɓe, ya yi murmushi dama ya san Mama baza ta taɓa barin ta kwana ba. Ta buɗe Motar ta shiga ta ƙi kallon inda yake, ya kalle ta ya ga harda hawayenta. Ya matso ya kama hannunta ya ce. “Fasa kwanan kika yi?” Ta turo baki ta ce. “Mama ce ta koro ni, kuma kai ma ka ƙi tafiya, daka tafi ai zata barni in kwanan.” Ya janyo ta jikinsa ya ce. “Tunda Mama ta koro mu sai mu tafi namu gidan mu ma.” Ya kashe mata ido tare da rad’a mata wata magana a cikin kunnenta. Fuskarta ta yi saurin rufewa da hannunta tana murmushi ta ƙara cusa kanta a ƙirjinsa………✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button