NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Sai bayan isha’i Ameen ya koma gida, ya tarar da Neehal ta shirya tana jiransa ya zo su fita, kamar yadda ya ce zasu je gidan wani abokinsa. Wanka ya yi sharp_sharp ya shirya suka tafi. Satin nan da aka shiga gaba-d’aya kullum sai sun fita bayan Magriba, ya kai ta gidan wani daga cikin abokansa daga nan su biya su sha ice-cream cikin soyayya da k’aunar junansu. Ameen ya manta da Hafsat da babinta a cikin ransa, kula da tarairayar Matarsa kawai ya saka a gaba. Neehal tana son ta ji inda aka kwana a zancen komen Hafsah amma tana jin tsoron ta tambaye shi, tunda ya ce karta ƙara yi masa maganar data danganci Hafsah. Ranar yana bacci suka yi waya da Aunty Sadiya take sanar mata Ameen ya saki Hafsah, yanda sakin ya daki zuciyar Neehal ba zai misaltu ba, har hawaye sai da ta yi, ta ji a ranta Ameen bai kyauta ba. Suna gama waya da Aunty Sadiya ta kira Mama ta dinga roqon ta akan ta saka Ameen ya dawo da Hafsah. Mama ta ce mata, ita ma burinta da fatanta kenan, bari ta yi Ameen ɗin ya gana hucewa sai a san abin yi. Ranar Ameen kasa gane kanta ya yi, ta ƙi kula shi ta dinga yi masa k’unci. Ya rarrashe ta ya lallab’a ta amma duk a banza, sai haqura ya yi ya k’yale ta, daga baya kuma da karan kanta ta saki ranta suka koma normal.

Yau Monday wanda ya kama kwana goma sha bakwai da Auran Neehal da Ameen. Da safe yana shiryawa zai tafi aiki da yake hutun 2 weeks aka bashi. Neehal tana tsaye tana kallon sa ta yi kalar tausayi da fuskarta kamar zata yi kuka. Ya ƙarasa saka talalmin ƙafarsa sannan ya ɗago ya kalle ta. Hannunsa ya miƙa mata ta ɗora nata akai a hankali. Ya riƙe hannun tare da janyo ta jikinsa ya zaunar da ita akan cinyarsa ya ce. “Mene ne.” Ta ɓata fuska ta ce. “Ni bana son ka fita.” Shafa bayanta ya shiga yi a hankali ya ce. “Ki yi haquri Baby, bazan dad’e ba fa zan dawo.” Ta ce. “Ai na san baza ka dawo da wurin ba.” Ganin tana shiri fara hawaye ya ce. “To ko in tafi dake ne?” Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya yi murmushi sannan ya sauke ta ya miƙe. Tun jiya da yake shirye-shiryen zuwa aiki yau take haka, jikinta gaba-d’aya ya yi sanyi, a yanda take jin sa yanzu a cikin zuciyarta bata k’aunar abun da zai rabata da shi ko na awa ɗaya ne balle na awanni. Ya ɗauki briefcase ɗinsa suka fita ta yi masa rakiya zuwa bakin ƙofar parlour. Ya ɗan tsaya yana kallon ta sannan ya kama fuskarta da hannunsa ya ce. “I will miss you Darling.” Ƙasa ta yi da kanta bata ce komai ba. Rungume ta ya yi ya ce. “Please Baby ki saki ranki, idan na tafi kina haka ai babu abun da zan iya ko na je gurin aikin, ko kuma in zauna in fasa zuwa ne?” Ta girgiza masa kai tare da d’agowa ta yi masa murmushi ta ce. “Ka je Yayana, ya za’ai ka ƙi zuwa aiki? Allah ya kiyaye hanya ya kare mun kai.” Murmurshin ya yi shi ma ya ce. “Amin, thank you so much dear, ko ke fa, harna ji daɗi.” Ta bar jikinsa ta ce. “Ka tafi kar ka yi late.” Ya ce. “Shikenan Baby, karfa ki damar mun kanki ki yi ta tunani, ina ƙarasawa office zan kira ki.” Ta ce. “Insha Allah Yaya, Allah ya kaika lafiya.” Ya ce. “Amin.” Sannan ya yi mata pick a kuncinta ya fice tana ɗaga masa hannu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakanin Ameen da Neehal cikin kwanciyar hankali da farinciki da tattali gami da kula da juna. Duk wanda ya zo gidansu sai sun burge shi sun ba shi sha’awa, zamansu gwanin sha’awa. Bayan sati biyu ita ma Neehal hutunta ya ƙare na gurin aiki da yake wata ɗaya aka bata. Ameen ya ce bai san zancen ba baza ta koma wani aiki ba, aikin ma na Jarida na gidan TV wanda ya dace da wanda bai dace ba ya kalle masa mata. Neehal har da Kukanta dan tana matuƙar k’aunar aikinta amma ya yi biris ya ƙi yarda, sai da ta kira Mama ta faɗa mata sannan ita kuma ta kira shi ta yi masa magana akan hakan, dole ba don son ransa ya yarda ta koma aikin, amma ta sha sharad’ai da dokoki, duk da yawan hijaban lefenta haka ya ƙara jibgo mata wasu dogaye har ƙasa da socks na ƙafa ya ce da su zata na fita. Ita dariya ma ya bata dan ita ma tafi son tana saka hijabin akan mayafi. Ranar data koma bayan ta dawo ya tasa ta a gaba da mita kamar zai yi kuka, wai ta yi kyau sosai da ya kalli labaran data gabatar, yanzu ya san wasu ma da suka kalla sun yaba kyawunta. Rarrashinsa ta yi da abun da ta son yana matuƙar so, da haka ta samu ya bar yi mata mitar. Bayan wata ɗaya wanda ya kama wata biyu da Auransu suka je Gombe aka sha shagalin bikin Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud. Duk wanda ya ga Neehal a bikin sai ya tanka kyawun da ta yi da irin canzawar da ta yi. Ta ƙara haske da ƙiba abun ta. Hajiya sai faman nan_nan take da ita tana cewa ciki gare ta, ita kuma sai ta ɓata fuska ta ce bata da komai ita. Ana shagalin biki amma suna manne da Ameen kodayaushe a waya. Har tsokanarta ake yi ana ce mata Cingam ne ita da shi. Daf da za su je bikin Ahmad ya kawo mata twins sun yi mata kwana biyu. A bikin ne labarin mutuwar Hafsat ya bazu a dangin su Mama, sakamakon rashin zuwanta bikin, daga masu cewa Allah ya raka taki gona sai masu cewa Allah yasa haka shi Alkhairi.

Bayan sun dawo daga Gomben sai zancen Hajiya ya zamto gaskiya, dan tunda suka dawo Neehal bata da aiki sai bacci, sai ta ɗora girki tana shiga d’aki ko ba da niyyar bacci ba sai ta kwanta ta yi bacci. Ga shegen kwad’ayi da ƙin cin abinci, ita dai ta wuni tana taunar abu a bakinta shine kwanciyar hankali. Daga ita har Ameen ba su gane ciki ne da ita ba, saboda bata laulayi kwata_kwata, ciye_ciye ne kawai da Bacci. Shi Ameen ya ɗauka zirga-zirgar zuwa gurin aiki ne take sanya mata gajiya take wannan baccin, ciye_ciye kuma dama ya san gwana ce ita a wannan fannin duk da na yanzu ya yi yawa, amma duk da haka bai kawo komai a ransa ba……….✍️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

8️⃣9️⃣

ELEGANT ONLINE WRITER’S

……….Yau ya kama weekend, ranar Sunday da rana Ameen yana parlour yana operating laptop, Neehal kuma tana d’aki tana aikin bacci. A hankali ta buɗe idonta dake cike da bacci, baccin bai ishe ta ba yunwace ta tashe ta. Miƙewa ta yi ta shiga toilet ta wanke bakinta tare da d’auraye fuskarta ta fito. Ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali ta lek’a kamar mara gaskiya, ganin Ameen zaune akan kujera yana aiki sai ta saki ajiyar zuciya ta mayar da ƙofar ta rufe ta koma ciki. Wardrobe ɗinta ta buɗe ta lalubo choculates ɗinta a inda ta b’oye su ta zauna a ƙasa ta fara sha tana lumshe idanu saboda daɗin dake ratsa ta. Sauri take yi ta yi ta shanye kar Ameen ya shigo ya gan ta, dan ya hana ta shan zaƙi saboda yanda ta mayar da su sweets abincinta, ba dare ba rana a ƴan kwanakin nan. Shi yasa ta koma sha a b’oye, kullum idan ta je gurin aiki sai ta bayar an siyo mata da yawa sai ta zo ta b’oye in ba ya gidan ta yi ta shan abin ta. Sai da choculate ɗin ta ishe ta sannan ta mayar da sauran ma’ajiyarta ta goge bakinta da tissue ta fita parlour.

Tunda ta fito ya ji ƙamshinta ya ɗago yake kallon ta, a gefensa ta tsaya tare da shagwab’e fuska. Ya saka hannunsa ya janyo ta ya ɗora ta akan cinyarsa. Ajiyar zuciya suka sauke a tare. Ya shafa fuskarta ya ce. “Har kin tashi daga baccin?” Gyaɗa masa kai ta yi. Ya ce. “Mene ne kuma ya faru Babyn Yaya?” Ta saka hannayenta ta zagaye bayansa ta ce. “Masara nake son ci dafaffiya.” Ya ce. “Masara kuma Baby? a ina za’a samo ta?” Kamar zata yi kuka ta ce. “Koma a ina ne, ni dai ita nake son ci.” Ajiyar zuciya ya sauke tare girgiza kai ya ce. “Bari na kira a kawo miki.” Ta ce. “A’a ni dai ka je da kanka, ka taho mun da gyaɗa mai gishiri da kwakumeti.” Tsayawa kawai ya yi yana kallon ta, ta fara yi masa shagwab’a. Ya rungume ta ya ce. “Yanzu dai kin ga aiki nake yi Baby ba sai na fita ba, ki bari na bayar a siyo miki, ni duk waɗan nan abubuwan ma ban san inda zan samo miki su ba.” Ta ce. “Ni na sani mu je tare.” Zai kuma magana ta fara yunk’urin kuka. Ya ce. “Shikenan bari na ɗan ƙarasa wani abu sai mu je.” Ta turo baki alamun ba haka taso ba amma bata yi magana ba. A hankali ya kai hannu ya shafi cikinta ya ce. “Rigimarki da kwad’ayin da kika koya yanzu da yawan bacci ina tunanin fa na yi ajiya ne.” Ta tura hannunsa bata ce komai ba ta lumshe idonta. Ya shafi saman idon yana murmushi, yana fatan a ce hasashen ya zama gaskiya. Kafin ya gama abun da ya ce zai ƙarasa har ta yi bacci a jikinsa. Bayan ya gama ya tashe ta dan su je su siyo abubuwan da ta ce, ɓata fuska ta yi ta ce. “Mafarki fa nake yi Yaya ina cin masarata ka tashe ni.” Ya ce. “I’m sorry, yanzu ai zamu je mu siyo ki ci a reality ba’a mafarki ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button