NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ga mamakin Ameen ta san ko ina da ake siyar da abubuwan data lissafa, suka je ya siya mata har da ƙarawa da wasu abubuwan. Sai da ya biya ta restaurant ya siyi abincin da zai ci, duk da ta ce masa zata iya girki idan sun koma gida, ya ce mata ya hutashshe ta, dan ya san girkin nan daƙyar zai yiyu. A daren yau kuma sai jikinta ya yi zafi zazzaɓi ya rufe ta, ko baccin kirki ba su yi ba. Washegari da sassafe kuwa suka shirya sai asibiti, dan ya ce ya kai ta gurin Mama ta ƙi yarda. Bayan an yi mata gwaje_gwaje da test aka tabbatar tana da shigar ciki na 7 weeks. Murnar da Ameen ya nuna ba zata faɗu ba, ya yi sujjada tare da yin godiya ga Ubangiji. Neehal kuwa sai kunya amma ita ma a cikin ranta farin ciki ne fal. Bayan sun dawo daga asibitin ya kwantar da ita akan gado ya ce. “Ki kwanta ki huta Baby zan je in yi gyaran gida, ko me kike so ki kira ni in miki karki wahalar mun da kanki da Small Babyna.” Ta shafa sumar kansa ta ce. “Aikin fa? Baza ka je ba?” Ya ce. “Baki da lafiya ina na ga ta zuwa aiki Baby.” Ta ce. “Na warware fa, zan iya yin komai.” Ya ce. “No, ko toilet zaki shiga just call me in zo in ɗauke ki in kaiki, kar ki yi tafiya ki wahala.” Ta yi murmushi kawai. Ya yi kissing goshinta da cikinta sannan ya fita. Yana fita ta miƙe ta je ta tsaya a gaban mudubi ta ɗaga rigar jikinta tana kallon cikin, murmurshin farinciki ɗauke akan fuskarta. Jin abun take kamar a mafarki, ita ce da ciki very soon da yardar Allah she will be come a Mother. A haka Ameen ya shigo ya same ta, cikin tsokana ya ce. “Wasa kike masa ne?” Saurin rufe cikin ta yi ta rufe fuskarta da hannunta. Ya ƙaraso ya rungume ta yana dariya ƙasa_ƙasa. B’oye fuskarta ta yi a ƙirjinsa tana murmushi. Ya jata suka faɗa kan gado ya ce. “Bari na duba lafiyar Babyn.” Ya fara ƙoƙarin cire mata riga. Ta marairaice ta ce. “Bani da lafiya fa.” Shi ma marairaicewar ya yi ya ce. “Nima haka.” Ta ja karan hancinsa da ƙarfi bata ce komai ba…….. Sosai Ameen yake kula da tattalin Neehal, dan sai yanzu kuma ta fara laulayi, idan ta ci abun da bai yi mata ko ta shak’i ƙamshinsa sai amai, ga zazzaɓi daren da take kwana da shi kullum. Kwad’ayi kuwa da bacci sai abun da ya yi gaba, shi yasa duk abun da Ameen ya gani a hanya ko bata ce masa tana so ba sai ya siyo mata, wani ta ci wani ta ƙi ci. A haka take lallab’awa take zuwa aiki, duk da ya hana ta ya ce ta ɗauki hutu ta ce masa ita bata son zaman gidan, ta fi son tana fita tunda ba wani jin jiki take sosai ba. Amma idan ta je gurin aikin ba wani abun arzik’i take yi ba rabi da rabi bacci ne, a yi ta tsokanar ta kuwa a gurin aikin, sai dai ta yi murmushi kawai cikin jin kunya. Ta ƙi barin Ameen ya faɗawa su Mama tana da ciki, wai ita kunya take ji. Ya yi dariya ya ce. “Indai Mum ce gani ɗaya zata yi miki ta gane, kin sani ke ma.” Jin haka sai ta ƙi zuwa gidan Maman, sai dai kullum cikin faɗar tana son ganin Maman take, idan suka yi waya tay ta yi mata mitar ta ƙi zuwa gidanta. Ranar wata Sunday Daddy ya cewa Mama ta shirya ta je ta gano Neehal ɗin ta ga gidanta tunda bata taɓa zuwa ba. Ai kuwa ranar Neehal murna kamar me, ta shiga kitchen ta yiwa Mama abubuwa na tarb’ar ta. Sai yamma Maman ta je gidan. Neehal ta tafi da gudu ta rungume ta, Ameen ya bi ta da wani kallo data san ko na mene ne, juya masa ido ta yi tana murmushi. Mama ta zauna suka gaggaisa tana bin Neehal da ido, Neehal ta tashi ta je ta kawo mata abinci da drinks. Mama dai kallon ta kawai take yi tana noticing ɗinta, ta lura da yanda take yin komai a sanyaye da kuma yanda jikinta ya d’ashe ta yi wani irin haske. Ta yi sarving Mama ta koma kusa da ita ta zauna tana ta yi mata hira. Can ta kalli Ameen ta turo baki ta ce. “Mamana ta zo shine baza ka ba mu guri mu yi sirri ba?” Harararta ya yi bai ce komai ba. Ta kwanta a jikin Mama tana ɓata fuska. Kafin Mama ta tafi ta shiga ɗaki dan yin fitsari, bayan ta yi fitsarin ta fito daga toilet sai ta kwanta akan gado, duk yanda ta so daurewa kar ta yi bacci amma ina baccin ya ce bai san wannan zancen ba, saboda rabon ta da yi tun safe, tana kitchen tana ta aiki. Mama ganin shida saura ta yi ta dubi Ameen ta ce. “Ina Neehal ɗin ne? Tafiya zan yi fa.” Ya ce. “Tun yanzu?” Mama ta ce. “Tunda na zo na gan ku mai zan zauna yi kuma.” Ya miƙe ya shiga ɗakin Neehal, mamaki ne ya kama shi ganin ta kwance tana baccinta hankali kwance. Ya juya ya fita ya ce wa Mama. “Kin ga Mum daga shigar ta har bacci ya ɗauke ta.” Mama ta ce. “Bacci kuma?” Ya gyaɗa mata kai. Tashi Mama ta yi ta shiga ɗakin ta zauna a gefen Neehal, tafin hannunta ta kama ta dudduba sannan ta kalli Ameen dake tsaye a bakin ƙofa ta ce. “Wani abu yana damunta ne ko ta yi rashin lafiya?” Ameen ya ce. “Tana yin zazzaɓin dare dai, amma yanzu da sauƙi tana shan magani.” Mama ta ce. “Kun je asibiti?” Ya ce. “Eh.” Mama ta ce. “Me aka ce yana damunta?” Ya shafa gashin kansa tare da yin ƙasa da kansa ya ce. “She is pregnant.” Mama ta mayar da kallon ta ga Neehal cikin tsananin farin ciki ta shafi fuskarta ta ce. “Allah ya sauke ki lafiya Daughter, ya baku lafiya ke da unborn.” Can ƙasan mak’oshi Ameen ya amsa da Amin. Dama Mama tun zuwansu Gombe data ga yanayin Neehal ɗin ta fuskanta. Ta miƙe ta fita Ameen ya bi bayanta dan yi mata rakiya, suna tafe tana ƙara faɗa masa yanda zai kula da Neehal da abubuwan da zata yi da wanda baza ta yi ba, tana kuma tambayar sa abubuwan da Neehal ɗin take yi. Sai daf da Magriba Neehal ta tashi, ta dinga yiwa Ameen mita akan ƙin tashinta da ya yi da Mama zata tafi, shi dai bai ce mata komai ba har ta gaji ta haqura, kiran Maman ta yi ta ji ya ta koma gida, Mama ta sanar mata lafiya ƙalau, sannan ta faffaɗa mata addu’oin da zata dinga yi a matsayinta na mai juna biyu, cikin jin kunya take amsa mata. Suna gama wayar ta juyo zata yiwa Ameen complain ya yi saurin cewa. “Bani na faɗa mata ba, ita ta gane da kanta, ai dama na faɗa miki.” Ta yi murmushi kawai a ranta tana hasaso irin farin cikin da Mama ta yi da ta ji labarin cikin. Bata ƙara nutsewa da jin kunya ba sai da Daddy ya kira ta ya yi mata ya jiki, dan ta san definitely Mama ta sanar masa da batun cikin jikinta.

A ɓangaren Hafsah kuwa kamar yadda Dad ɗinta ya faɗa a ranar ta bi Aunty Jamila zuwa gidanta tana gunjin kuka. Saboda kuka da damuwar data saka kanta a ciki har jinyar kwana biyu ta kwanta. Bayan ta warware Aunty Jamila ta fara koyar da ita abubuwa kamar yadda Dad ya buƙata daga gare ta, da farko bata mayar da hankali akan abubuwan ba sai dai ta zauna ta yi ta koke_koke da tunane_tunane. Daga baya cikin dabara Aunty Jamila ta ce mata idan bata gyara dabi’unta ta koyi zaman rayuwar duniya ba babu ta yanda za’a yi Ameen ya mayar da ita, sannan ta fara mayar da hankali. Ta kan addini Aunty Jamila ta fara yi mata dan sai ya gyaru sauran abubuwan za su gyaru. Wata yarinya ƴar mak’otansu Aunty Jamila ta ɗauko take yiwa Hafsan karatun addini, za su yi ƙarin Alqur’ani da sauran littatafai. Ita kuma Aunty Jamila sai ta ƙara mata da bayanin wasu abubuwan akan addinin. Sannan kuma idan zata yi girki tare suke yi, dan Hafsan tana gani tana koya. A hankali Hafsah ta fara sakin jikinta zaman gidan Aunty Jamila ya fara yi mata daɗi, ta kuma mayar da hankali akan karatun da ake yi mata. Sai dai fa kullum da tunanin Ameen take kwana take tashi a ranta. Lokuta da dama tana zama tay ta tunanin zaman Auransu, babu shakka ita akaran kanta ta san Ameen ya yi haquri da ita, a kodayaushe idan ta yi masa laifi uzuri yake mata ya dinga nusar da ita aibun abun da ta yi masa, sannan yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin ta gyara addinta ta ko yi ilimin addinin, ta kan tuna lokacin data zubar masa da ciki, da farko fushi ya yi mai tsananin gaske da ita, daga baya kuma ya koma yi mata nasiha da nuna mata girman lefin da ta aikata ga Ubangiji. A lokacin gani take kamar rashin wayewa ne yasa ya kasa fuskantar abun da take nufi na ta yi ƙanƙanta da fara tara ƴaƴa a yanzu, sai yanzu da ilimi ya fara ratsa ta sannan ta gane ashe ita ce mara wayewar da kuma tarin duhun jahilci a kanta. Ranar suna zaune lokacin an yi wata biyu da sakinta take bawa Aunty Jamila labarin magungunan da Aunty Safiyya ta dinga kawo mata a matsayin su ne za su janyo da hankalin Ameen gare ta. Aunty Jamila ta yi salati ta ce. “Yanzu ita Safiyya an girma ma amma bata bar halin yarinta ba na bin Malam tsibbu? To Allah ya shirya ta yasa ta gane gaskiya. Ita kuma Yaya tana kallo bata yi magana ba?” Hafsah ta ce. “Bata ce komai ba.” Aunty Jamila ta ce. “Dama ita Yaya haka take, duk abun da zaka yi bata k’wabar ka, na dai-dai ko na rashin daidai. Ke kuma wannan ya ishe ki izna, ki gane komai na Allah ne, ɓata wayonki da kika yi kika bi ɓata shi yasa Ubangiji ya barku da halinku, da a ce Sallah kika dage da ita da addu’a kamar yadda kika dage da yin amfani da magungunan nan da watak’ila al’amarin bai kai har haka ba, amma da kika kasa tsayar da Allah a al’amarinki kin ga illar hakan ai, tunda maganin bai yi aikin komai ba. Mutane su yi ta asarar kuɗaɗen su saboda jahilci suna zuwa gurin wani mutum ɗan’uwansu wai da sunan shi zai biya musu buƙata, ya baku maganin k’arya da wofi ya ci kuɗinku a banza, ga kuma tarin zunubi a gurin Ubangiji, dan shirka ba ƙaramar masifa ba ce, Allah ya raba mu da ita.” Hafsah ta gyaɗa kai ta ce. “Amin Aunty na gode da tunatarwarki a gare ni. Amma Aunty kullum sai na saka ran ganin Ameen, ko ya turo wani nasa, ko ya kira ni amma shiru har na kusa gama iddata.” Cikin tausayinta Aunty Jamila ta ce. “Ki ƙara haquri Hafsah kin ji, komai rubutacce ne a gurin Ubangiji, ki fawwala masa komai, idan ya nufa akwai sauran zamanku da Ameen a gaba sai ki ga kin koma, idan kuwa iya zaman kenan sai ki yi haquri, Allah ya kawo miki wani na gari.” Gyaɗa mata kai Hafsah ta yi a hankali jikinta duk ya yi sanyi akan Ameen, ta san tunda ya samu mace kamar Neehal zai yi wahala ya ƙara waiwayar ta a cikin rayuwarsa……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button