NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
By
Zeey Kumurya
⚡NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
9️⃣0️⃣
ELEGANT ONLINE WRITER’S
I DEDICATED ALL THIS NOBEL TO MY LOVELY MOTHER, ONE IN THE BILLIONS, ONE LIKE NO OTHER, SUPER WOMAN, *HAJIYA FATIMA KUMURYA* ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA MAI AMFANI, AMEEN.
SPECIAL THANKS TO
Abubakar Ak saraki,
Muhammad Kareem,
Mu’az,
S deen and
Yareema.
Mutanen kirki kenan wanda basa gajiyawa da yin share, Allah ya saka muku da Alkhairinsa.
………Rayuwa na tafiyarwa su Neehal yadda ya kamata cikin kwanciyar hankali da farinciki. Sosai Ameen yake k’aunar cikin jikinta tun kafin ya fito duniya, da daddare idan sun kwanta haka zai ta shafa cikin yana magana shi kaɗai, wai magana yake yi da ɗansa, wataran har ta yi bacci ta bar shi yana ta faman latsa mata ciki, da safe ma haka yana tashi zai ɗora daga inda ya tsaya wai gaisawa suke yi. Ita dai sai dai tay ta yi masa dariya, in ta gaji kuma ta ture hannunsa daga jikinta. Cikin Neehal ya shiga wata na uku lokacin farkon azumin watan Ramadan Haneefah ta haifi ƴarta mace mai kama da ita sak. Murna gurin Neehal ko ita ta haihu sai haka, ranar da ta je Barka daƙyar take bari a ɗauki yarinyar, tana hannunta ta rungume ta sai kallon ta take. Mommyn Haneefah ta yi ta mata dariya tana cewa in da rai ita ma kamar yau ne zata haifa, da yake gida aka mayar da Haneefan. Duk da azumi ne kuma ga laulayin da take fama da shi amma zuwanta uku kafin ranar suna. Ranar suna yarinya ta ci sunan Mommyn Haneefah Maryam, Haneefah ta ce Neehal za’ana ce mata. Neehal ta ji daɗin wannan karar da Haneefah ta yi mata sosai, kayan barka sosai Ameen ya siyawa takwararsu da ita kanta Haneefan, ita ma Neehal ta ƙara da nata kayan. Ba’a yi taron suna ba kasancewar azumi ne.
Wataranar Laraba Neehal tana kitchen tana girki da yamma ta ji ana knocking ɗin ƙofar parlour. Ta goge hannunta ta fito ta nufi ƙofar, lokacin cikinta ya fito ɗan wata shida, ya yi mata das a jikinta abun sha’awa, yanzu an bar laulayi. Sai da ta tambayi waye? Sannan ta buɗe ƙofar. Ɗaya cikin yaran gidan ne masu bawa flowers ruwa da yi mata aike. Bayan ya gaishe ta ya ce. “Hajiya wasu baƙi ne suka zo wai suna san ganin ki.” Neehal ta ce. “Baƙi kuma? Maza ko Mata?” Ya ce. “Maza ne dattijai haka kamar almajirai.” Neehal ta ce. “Kuma suka ce Ni suke son gani?” Ya ce. “Eh, dan sun ce daga can gidan Hajiya babba (Mama) aka turo su.” Neehal ta ce. “Okay ka ce su shigo.” Ta juya ta koma ba tare da rufe ƙofar ba a ranta tana Mamakin baƙin da aka ce ta yi, ɗakinta ta shiga ta ɗauko hijabi ta zira akan doguwar rigar abayar dake jikinta. Ta duba time ta ga biyar ta wuce lokacin dawowar Ameen gida ya kusa. Jin ƙarar turo ƙofa yasa ta fita parlour’n. Maza ta gani su biyu kamar yadda yaron gidan ya ce mata dattijai ne kuma kamar almajiran, tabbas ta san fuskokinsu amma ta kasa tuno inda ta san sun. A kan Carpet ta zauna tana bin su da kallo, su kuma sai aikin kalle_kalle suke a parlour’n suna baza ido a lungu da sak’o na cikinsa. Cikin girmamawa ta ce musu. “Sannunku da zuwa.” Suka amsa da “Yawwa.” Tare da dawo da kallon su gare ta. Ta ce. “Ina yininku?” Suka amsa mata sannan ɗaya daga cikinsu ya gyara zama ya ce. “Ikon Allah, Neehal ke ce kika zama haka? Girman ɗan Mutum babu wahala.” Ta yi murmushi kawai. Ya cigaba da magana cikin sanyin murya. “Ga dukkan alamu baki shaida mu ba, amma hakan ba’abun mamaki ba ne bisa ga yadda muka wofintar da rayuwarki duk da kasancewar muna gari guda dake, Neehal Salisu ne da kuma Sani ƴaƴan Baffa mariki’n mahaifanki.” Da mugun mamaki Neehal ta ɗago tana kallon su tare da tambayar kanta abun da ya hana ta gane su. Zuciyarta ta bata amsa da cewa ‘Tsufan da suka yi mana’ wanda ya wuce yawan shekarunsu a duniya, kuma ta manta rabon da ta gan su a, duk da Kawu Musa ya ce sun zo bikinta, amma da yake cikin hada_hada ake bata gan su ba. Cikin tsananin mamaki ta ce. “Kawu Sani da Kawu Salisu?” Kawu Sani ya gyaɗa mata kai. Ruwan hawaye fal cikin idonsa ya ce. “Mu ne Neehal, abun ya baki mamaki ko? Na ganinmu da kika yi a gidanki, mun zo ne mu roqe ki gafara akan abun da muka yi miki ko ma samu sassaucin k’uncin rayuwar da muka shiga, mahaifinki ya riqe mu tamkar ƴan’uwansa da suke ciki ɗaya a lokacin da yana raye haka ma mahaifiyarki, mahaifinki shine komai namu, ya yi mana komai a rayuwar nan, amma saboda butulci da wani tunanin banza da wofi muka wofantar dake ƴarsa ƙwaya ɗaya tal a duniya, muka yarda zumunci muka kasa riqe ki saboda muna gudun wahalar d’awainiya dake. Amma da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai gashi Allah ya ɗaukaka ki, mu kuma ya bar mu da iyawar mu, dan Allah Neehal ki yafe mana, wallahi muna cikin tsananin k’uncin rayuwa. Abun da zamu kai bakinmu ma gagarar mu yake, karayar arzik’i Ubangiji ya ɗoro mana lokaci ɗaya, hatta da muhallin da muke rayuwa a cikinsa ba mu tsira da shi ba, yanzu a wani rubab’b’en gidan haya muke tare da iyalanmu, shi ma wani bawan Allah ne ya ji k’an mu ya biya mana kuɗin shekara ɗaya…..” Sai ya fashe da kuka.
Neehal Sarkin kuka har ta fara hawaye, ta ce. “Innalillahiwa’inna’ilaihirra’un, Kawu ni ba ku yi mun komai ba dama, ko kun mun na yafe muku.” Kawu Salisu yana matsar ƙwalla ya ce. “Kayya Neehal, ba iya wannan ne cutar da muka yi miki ba, Mahaifinki kafin ya rasu ya ranta mana wasu kuɗaɗe masu kauri da muka buƙata daga gare shi dan mu ƙara jarinmu, amma bayan rasuwarsa saboda son zuciya irin tamu muka ƙi kawo kuɗin a haɗa a raba muku haqqinku ku iyalansa, muka riqe saboda mun san ba mu da gadonsa, muna baƙin cikin a ce ba mu ci komai ba daga cikin dukiyarsa. Dan Allah ki yafe mana Neehal ko za mu samu sassauci a gurin Ubangiji bayan mutuwar mu.” Neehal ta ce. “Na yafe muku Kawu, dan Allah ku bar waɗan nan maganganun komai ya wuce.” Bata jira cewar su ba ta miƙe ta kawo musu drinks masu sanyi, ai ko bi takan cups ɗin data kawo ta ajiye musu ba su yi ba suka buɗe robar suka shiga kuk’k’uta. Kitchen ta koma ta ƙarasa girkin da take, ta zubo musu a cikin tire ta kawo musu. Shi ma ba su bi takan spoons ba suka saka hannu duk da tururin da abincin yake suka shiga zabga lauma, kana ganinsu ka ga wanda suke tattare da yunwa. Cikin mintunan da ba su fi biyar ba suka share abincin, suka fara sakin gyatsa. Neehal dai kallon su kawai take cike da tausayawa. Suna wanke hannu suka miƙe za su tafi suna zabga mata godiya, ɗakinta ta shiga ta tattaro duka kuɗin dake hannunta ta fito ta miƙa musu ta ce. “Kawu ga wannan a yi cefene, ku yi haquri bani da enough cash ɗin kuɗi a hannuna, amma insha Allahu cikin week ɗin nan zan zo har gida, sai ku bani address ɗin gidan.” Ai kamar za su yi mata sujjada saboda murna da godiya, ita abun ma kunya ya bata. Sai da suka bata address ɗin sannan suka tafi. Tattare kayan gurin ta yi ta kai kitchen jikinta a sanyaye, ta dawo ta gyara gurin ta ƙara fesa room freshener a ɗakin. Hijabin jikinta ta cire ta zauna akan kujera ta fara tunanin rayuwa da yanda al’amuran cikinta suke wakana. Ta tuna su Kawu Salisu a da sanin data yi musu ƴan gayu ne masu ji da kansu, amma ƙarshe ga yanda Ubangiji ya yi da su, ba su da maraba da almajirai gashi duk sun tsofe. Ta tuna Uncle Umar da yanda shi ma rayuwa ta juya masa baya, ga ƴarsa Iman ta haifa masa ɗan gaba da Fatiha, Aunty Fauziyya kuwa ta koma kamar zautacciya saboda tension ɗin rayuwar da take ciki. Ta nuna a baya yanda duk suke jin daɗin rayuwarsu suke yin abun da suka ga dama, a lokacin ba sa tunanin akwai lokacin da zai zo da zasu girbi ABIN DA SUKA SHUKA, shi yasa aka ce a rayuwa ka yi mai kyau sai ka ga mai kyau a gaba. Allah yasa mu dace, Amin.