NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Neehal tana kwance a ɗakin hutun da aka kaita ita kaɗai, Mama da Daddy suna can tare da Babies ɗin. Ameen ya shigo ɗakin kamar an jefo shi, ya ƙarasa gaban gadon ya kama hannunta yana kiran sunanta cikin damuwa. Bacci ya fara ɗaukar ta hakan yasa daƙyar ta iya buɗe idonta ta kalle shi. Ya ce. “Baby kina lafiya? Ya jikin naki? Mene yake miki ciwo yanzu? Kin sha wahala ko? Sannu Allah ya yi miki albarka.” Ta ɗaga hannunta a hankali tana murmushi ta shafi sajen fuskarsa ta ce. “Yaya me yasa baka zo ba, ina ta kiran ka ina son na gan ka.” Ya ƙanƙame hannunta a cikin nasa ya ce. “Ban sani ba ne Baby, ban san kina labour ba wallahi, da sai na zo mun yi tare, Mum bata faɗa mun ba.” Ta ɗora hannunsa akan cikinta cikin shagwab’a ta ce. “Na sha wahala fa sosai Yaya, haihuwa akwai wahala, ni bazan kuma ba, karka kuma mun ciki ka ji.” Ya kwantar da kansa akan ƙirjinta ya ce. “Sorry Baby, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, sannu kin ji, yanzu ina ne yake miki ciwo?” Ta ce. “Duka jikina da kaina, more especially cikina.” Kamar wanda aka tsikara ya ɗago kansa ya ce. “Sannu Allah ya baki lafiya, insha Allahu zaki samu lafiya soon.” Ta gyaɗa masa kai. Ya shiga shafa cikinta ya ce. “Ina Babyn da kika haifa? Mece ce ko Namiji?” Kamar amsar tambayarsa sai ga Mama ta shigo ɗakin rungume da Baby, ya miƙe da sauri ya karb’e shi, Mama ta ce. “Ka jira ai in baka ko?” Ya yi murmushi tare da sakin wata kakkafar ajiyar zuciya, rungume yaron ya yi kam a ƙirjinsa cikin tsananin farin ciki. Ya koma ya zauna a gaban Neehal ya zubawa yaron ido kamar zai cinye shi yana murmushi, cikin ransa kuma yana godiya ga Allah. Mama ta miƙa masa dabino da Zamzam ta ce. “Ka tauna ka ba shi tare da ruwan, ka kuma yi masa addu’a ba kallo kawai ba.” Neehal ta yi murmushi, Ameen ya yi kamar yadda Mama ta ce. Ya ɗago ya kalle ta ya ce. “Mum me yasa baki kira ni ba da tana labour?” Mama ta ce. “In ka zo me zaka yi?” Ya ce. “Addu’a mana.” Mama ta ce. “Yanzu dai tunda ta sauka lafiya shikenan.” Shigowar Daddy dake ɗauke da ɗayan Babyn ne ya hana shi magana. Ya saki baki yana kallon sa, Daddy ya ƙaraso ya miƙa masa Babyn yana murmushi ya ce. “Ga Al_hussain nan.” Waro ido Ameen ya yi ya ce. “Dad! Twins ta haifa?” Sai kuma ya juya ya kalli Mama. Ta gyaɗa masa kai tana murmushi. Matsar da na hannunsa ya yi Daddy ya ɗora masa ɗayan akan cinyarsa, ya haɗa su duka ya rungume cikin tsananin farin cikin da bazai misaltu ba, yana ƙara godiya ga Allah da wannan baiwar da ya yi masa.” Ya yi mintuna uku a haka sannan ya miƙa wa Daddy Al_hassan ya yiwa Al_hussain addu’a kamar yadda ya yiwa Al_hassan. Ya sunkuya dai-dai fuskar Neehal ya ce. “Thanks You so much Darling, ban san me zan ce miki ba saboda tsananin farin ciki, Allah ya yi miki albarka ya raya mana su, ya sa mu zamto ababen alfahari a gare mu.” Idanunta a lumshe ta amsa da Amin cikin jin kunyar su Mama. Ya ɗago yana ɗan jijiiga yaron dake ta mulmul da baki saboda dabino da Zamzam da aka saka a bakin. Mama ta ce, “Tunda ba ki yi baccin ba tashi ki gwada feeding ɗinsu.” Ta buɗe ido a hankali tare da tashi zaune tana yamutsa fuska. Ameen ya yi saurin saka mata pillow a bayanta ta jingina da shi sannan ya ɗora mata yaron akan cinyarta. Ƙurawa kyakkyawar fuskarsa ido ta yi tana jin duk duniya babu abun da take so kamar shi da ɗan’uwansa a yanzu, wani irin feeling take ji a kansu wanda baki bazai iya faɗa ba, wannan ita ce soyayyar ɗa da Uwa data ji ana faɗa kenan. Daddy ya miƙawa Ameen ɗayan ya fita dan zuwa Masallaci jin an fara kiran assalatu, Mama ta mara masa baya dan akwai abun da zata yi a office ɗinta yanzu. Ameen ya zauna a kusa da Neehal bayan fitar su yana murmushi ya ce. “Ki bashi mana.” Ba tare data ɗauke idonta daga kan ɗanta ba ta ce. “Me?” Ya ce, “Abincinsu mana.” Ta yi murmushi tare da zuge zip ɗin rigarta ta ciro Brest ɗin ta ɗan raba bakin yaron ta saka masa a hankali. Kamar bazai sha ba sai kuma ya fara zuk’a, ta ɓata fuska tare da runtse ido. Ameen da ya kura mata ido ya ce. “What?” Ta ce. “Zafi na ji.” Ya matsa jikinta sosai ya ce. “Sorry.” Ta shafa kuncin yaron hannunsa ta ce. “Kamarku ɗaya da su.” Ya ce. “Eh mana, ai saboda na fi ki son su ne.” Ta ɓata fuska bata ce komai ba. Gyara Babyn hannunsa ya yi ya rungume ta, kwantar da kanta ta yi akan kafaɗarsa idanunta akan yaranta, jin abun take kamar a mafarki, yau ita ce da ƴaƴa har biyu, gaskiya ikon Allah ya wuce gaban komai a rayuwa. A haka Mama ta turo ƙofa ta same su, saurin barin jikin Ameen ta yi tana ƙara yin ƙasa da kanta. Mama ta dube shi ta ce. “Baza ka yi Sallar ba ne kai?” Ya shafa kansa bai ce komai ba, ya miƙa mata yaron ya fita, ta bi shi da kallo sannan ta mayar da kallon ga Neehal ta ce. “Ruwan Nonon ya zo kenan?” Neehal ta ce. “Ban sani ba, yana dai ta tsotsa.” Mama ta ɗauke shi ta saka mata ɗayan ta ce. “Shi ma bashi ya sha, idan ma bai zo ba sosai nan gaba zai zo.”
Kafin ƙarfe goma na safe Mama ta rubuta musu sallama tunda lafiya ƙalau take ita da Babies ɗin. Da daddare Neehal tana zaune akan gado a ɗakin Mama ita da Ameen ya ce mata. “Baby Wanne suna za’a saka musu ne?” Ta ce. “Duk wanda kake so Yaya.” Ya shafi kan na hannunsa ya ce. “Wannan tunda shine Babba a saka masa Muhammad, Sunan Ma’aiki S.A.W, mun kuma yiwa Daddy da Abba takwara.” Sannan ya shafi kan na hannunta ya ce. “Wannan kuwa Abubakar Sadik.” Ta yi murmushi ta ce. “Masha Allah, sunaye masu daɗi da asali, Allah ya raya su ya saka su biyo hali da dabi’un masu sunan.” Ya ce. “Amin, me za’a na ce musu?” Ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce. “Sudais da Shureim.” Ya ce. “Masha Allah, Allah yasa su kasance masu karatun Alqur’ani kamar masu sunan.” Ta ce. “Amin.” Suka cigaba da hirar su wadda gaba-d’aya akan yaran ne, idan ka ga yanda suke yiwa yaran sai ka rasa waye ya fi son yaran a cikinsu….. Tunda aka yi haihuwar kullum gidan cikin baƙi ƴan zuwa barka yake, Twins da Mamansu gwanin sha’awa kodayaushe tsaf_tsaf da su an shirya su cikin kaya masu kyau da tsada suna ta tashin ƙamshi. Da safe kafin Ameen ya tafi aiki yake zuwa sai kuma bayan Magriba idan ya dawo, idan ya ɗauki yaran nan daƙyar ake karɓar su daga hannunsa, Neehal kawai yake bawa su ta daɗin rai, ita ma wai dan saboda feeding ɗinsu ne. Saura kwana uku suna Hajiya ta zo, tunda ta zo ta sakawa Ameen ido, bai isa ya shiga sun zauna da Neehal a ɗaki ba sai ta fara mita tana cewa “Jego dai take yi Manne mata.” Shi kuma yana sane sai yay ta yin wasu abubuwan yana ƙara kunna ta. Neehal tay ta yi musu dariya. Ana i gobe suna Ahmad ya zo ya ga Babies shi da twins, waɗanda farin ciki ya kusa kashe su saboda Aunty ta haifo musu k’anne guda biyu, kowa da nasa a cewarsu. Kayan Barka sosai Daddy ya siyawa yaran bayan wanda Ameen ya siya already tun kafin a haife su, ga waɗanda mutane suke ta kawowa, sai kayan suka yi yawa sosai Masha Allah. Ranar Suna aka sha shagali a gidan Mama, an yi komai cikin bajinta da wadata. Mai Jego ta sha kyau ita da Babies ɗinta har ma da Angon ƙarnin. Neehal ta cigaba da zama a gidan Mama, shi Ameen ya ɗauka da an yi suna zata koma, Mama ta ce sai bayan ta yi arba’in.