NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Yau Asabar wanda ya kama wata guda cif da haihuwar Neehal. Tana zaune a parlour ita kaɗai tana chatting a wayarta ta ci kwalliya ta yi kyau sosai sai tashin daddaɗan ƙamshi take. Ameen ne ya shigo parlour’n da sallama. Ta ɗaga kai ta kalle shi cikin mamakin ganin sa a dai-dai wannan lokacin, kasancewar time ɗin tsakiyar rana ne bai fi ya zuwa a irin time ɗin ba. Ta gyara zama tare da yi masa sannu da zuwa tana murmushi. Ya zauna a gefen ta yana kallon ta bai ce komai ba. Hannunsa ɗaya ta kama ta ce. “Ya dai?” Ya langwab’ar da kai ya ce. “Baby kullum ƙara kyau kike hankalinki kwance, but me ko bacci bana iyawa saboda rashin ki.” Ta ce. “Who told you? Ina missing ɗinka sosai fa Yaya.” Ya ce. “Ba wani nan, ni ban gani ba.” Ta ce. “Me zan yi ka yarda to?” Ya ce. “Ki cewa Mum kin gaji ke gidanki zaki koma.” Ta yi murmushi sosai bata ce komai ba. Ya ɓata fuska ya ce. “Oh dariya ma kike ko?” Ta kwanta a jikinsa tare da rungume shi ta ce. “No, kai ma ka san bazan iya faɗawa Mama haka ba, kuma idan ka yi haquri kwanaki kaɗan suka rage in koma.” Ya ce. “Kafin lokacin na gama jiga ta kenan?” Tana yi masa tafiyar tsutsa a bayan kunne ta ce. “Tunda ka daure na baya zaka daure na gaba ma.” Ya saka hannayensa ya zagaye bayanta cikin marairaicewa ya ce. “Ni dai ki sakawa Mama kuka ta bar ki mu tafi gidanmu, wankan ya isa haka.” Ta ce. “Ka yi haquri Yayana Please mu ƙarasa sauran kwanakin.” Banza ya yi mata ya ɓata fuska sosai. Ta kai finger ɗinta ta fara zagaye lips ɗinsa da shi tana faɗa masa wata magana a cikin kunnensa, ya lumshe idonsa tare da yin murmushi ya ce. “Ina Twins love?” Ta ce. “Suna gurin su Aunty Dije sun goya su.” Ya ce. “Ke kullum sai dai a goya miki su, ke bakya goya su?” Ta ce. “Ban iya ba ni.” Ya ce. “In mun koma gidanmu fa?” Ta ce. “Ai zaka na goya mun su ko?” Ya ja karan hancinta ya ce. “Sai dai ke in na goya ki.” Ta ce. “Tom Yayana, su sai su yi ta kwanciyar su kawai.” Wani kallo yay mata da ya saka ta yi dariya. Tashi ta yi ta karb’o Sudais Zulai ta biyo ta da Shureim, Ameen ya karb’i Shureim ɗin, wasa ya fara yi masa yana ɗan ɗaga shi. Ya ce. “Baby kin ga yana mun dariya.” Ta ce, “Shureim ɗin ko? Yaushe ya iya dariyar?” Ya ce. “Gashi nan kuma.” Ta ce. “Na gani ai.” Ya ɗago ya dube ta ya ce, Wai ina Mum ne?” Ta ce. “Bacci take yi, jiya Sudais bai bar ta ta yi baccin kirki ba.” Ya ce. “Kamarya?” Ta ce. “Kukan dare ya yi ta yi, ni kuma na kai mata shi ta rarrashe shi, tunda ni na yi na yi ya ƙi yin shiru.” Ameen ya shafi fuskar yaron ya ce. “Ka daina kukan dare kana hana Mum da Baby bacci, dan wannan Mum ɗin taka raguwa ce, wataran in ka ƙi yin shiru taya ka kukan zata yi.” Ta tura masa baki ba ta ce komai ba. Ya kalli lips ɗin da suke zuba k’yalli ya ce. “I want it.” Ƙara tura masa su ta yi, ya matso da fuskarsa a hankali ya ɗora nasa akai….. Daƙyar ta samu ya cika ta, shi ma dan Shureim ya fara kuka ne. Ya dungure masa kai sannan ya miƙa mata shi, ta yi murmushi tare da bashi Sudais sannan ta fara feeding ɗinsa. Ƙura nata mata ido ya yi, kallon shi tare da saka hannunta ta kwantar da kansa akan kafaɗarta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta……..Kwanan su Neehal Arba’in da biyu ta koma gidanta ita da Dije domin tana taya ta rainon su Sudais, lokacin sati ɗaya da yin bikin Salma da Sadik. Sabon shafin soyayya Neehal suka buɗe ita da Ameen bayan ta koma wadda tafi ma ta farkon Auransu. Ranar Anniversary ɗinsu Ameen ya yi celebrate ɗinta sosai, kyaututtuka masu tarin yawa ya yi mata na k’auna tare da nuna mata tsantsar soyayya. Washegari kuma suka tafi yawon shak’atawa zuwa other countries su da twins ɗinsu wanda suka yi wayo sosai kamar ba ƴan wata biyu da kwanaki ba……….

AFTER FIVE YEARS.

Katafaren parlour ne babba mai ɗauke da duk wani abun ƙawata parlour a cikinsa, ƙamshi mai daɗi ne ke tashi a cikin parlour’n. Wasu yara ne ƙanana guda biyu kaɗai a cikin parlour’n Mace da Namiji waɗanda baza su wuce shekara uku ba. Macen tana zaune a kan kujera ta keɓe fuska kamar zata yi kuka. Namijin kuma yana zaune a kan Carpet yana playing game. Hanif da Haneefah kenan second born ɗin su Neehal. Turo ƙofar parlour’n aka yi aka shigo, gaba-d’aya yaran suka kalli bakin ƙofar. Ameen ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Da gudu Haneef ya tashi ya je ya rungume ƙafafunsa, Ameen ya ɗaga shi sama ya shilla sannan ya sauke shi ya kamo hannunsa suka ƙaraso cikin parlour’n. A gaban Haneefah ya tsaya ya ce. “Wa ya taɓa mun Hany Baby ɗita?” Yarinyar mai kama da uwarta exactly ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba ta ce. “Ba Mommy ce ta koro mu downstairs ba, kuma ta ce baza ta ƙara kai mu gidansu Yaya Afrah da gidansu Yaya Neehal da gidan Mama gurinsu Ya Sudais ba.” Ameen ya yi murmushi ya ce. “Rashin ji kuka yi mata ko?” Ta ce. “Hanif ne ya barbaza mata kayan kwalliyarta.” Hanif ya yi saurin cewa. “Allah Abbu ita ta ce in zo in taya ta kwalliya irin wadda Mommy take yi.” Ameen ya ce. “How many times I told you ku daina yiwa Mummy rashin ji kuna saka ta magana saboda bata lafiya?” Haneefah ta ce. “Sorry Abbu mun daina.” Ameen ya ɗauke ta ya ce. “Yawwa yaran albarka, ku zo mu je mu bawa Mummy haquri.” Ya kama hannun Hanif suka nufi upstairs. A k’aton bedroom ɗin Neehal suka tarar da ita tsaye a gaban mudubi tana gyara kayan dake kan shi. Ta juyo a hankali ta kalle su sau ɗaya ta ɗauke kanta. Suka ƙarasa kusa da ita, Ameen ya ce “Mummy mun zo bayar da haquri.” Ta kalle shi ta ce. “Bazan haqura ba yau kar ma ku ɓata bakinku.” Haneefah data fi Hanif surutu ta marairaice fuska ta ce. “Please Mummy we are sorry.” Harararta ta yi ta ce. “Kin fi kowa iya rashin ji da bakin bayar da haquri.” Ameen ya ce. “Yanzu dai Please Mummy forgive us.” Neehal ta ce. “Shikenan, amma kar ku kuma.” Yaran suka rungume ta suna murna. Haneefah ta ce. “Mummy yanzu zaki kai mu gidansu Yaya Afrah da Yaya Neehal da gidan Mama ko?” Haneef ya ce. “Da gidansu Abul (Ɗan Sadik da Salma) ko Mummy?” Neehal ta ce. “Insha Allah.” Ameen ya zaro choculates daga cikin aljihunsa ya ba su sannan ya ce. “A je a parlour asha ban da ɓata jiki da rashin ji.” Da gudu suka fice, Neehal ta bi su da kallo a ranta tana jinjina rashin jin su, shi yasa Mama su Sudais ne ƴan wajenta, yanzu ma suna gidanta za su yi mata weekend, su Haneef kuwa ana kai mata su take tattaro su da kayansu ta bayar a dawo da su, dan baza ta iya ciwon bakin bari_bari ba.

Ameen ya janyo ta jikinsa ya ce. “Me ya faru ne Babyn Baby?” Ta shagwab’e fuska ta ce. “Kai ne mana, daga fita Masallaci tun ɗazu sai yanzu zaka dawo.” Ya kama hannunta suka ƙarasa ya zauna a bakin gado ya zaunar da ita akan cinyarsa ya kwantar da kansa akan kafaɗarta ya ce. “I’m sorry Baby love, mun tsaya da Barrister ne, amma ke ma kin san duk inda nake my heart is with you.” Ta yi murmusa tare da shafar sumar kansa bata ce komai ba. Cikinta dake ɗauke da Unborn ɗan wata huɗu ya shafa ya ce. “My Unborn Twins, Abbu missed you.” Neehal ta ɓata fuska ta ce. “Na ce maka bazan ƙara haifar twins ba insha Allah, da su Haneef zan ji ko da su in na haife su?” Ya ce. “To ba tare muke rainon ba?” Ta ja kunnen shi ta ce. “Kaima ai rainon naka nake yi.” Ya yi murmushi ya ce. “Exactly ƴar Aljannah, yanzu ma a zo a ji da ni.” Ta kwantar da kanta a jikinsa ta ce. “Dole ne ma ai, I love You so much Nurul qalbi.” Ya ƙara rungume ta tsam kamar zai mayar da ita ciki, cikin wani irin yanayi da ƙamshin jikinta ya jefa shi a ciki ya ce. “Love You too My Baby.” Tare da ɗago fuskarta ya haɗe bakinsu guri guda cikin tsananin shauk’i……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button