NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. Komai nisan dare gari zai waye, komai nisan jifa ƙasa zai dawo, sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba’a je ba. Yau 02/06/2022 Ubangiji Mai girma da ɗaukaka ya nufa na kammala wannan book ɗin nawa mai suna NEEHAL, Kuskuren da na yi a cikinsa Allah ya yafe mun, abun da na faɗa dai-dai Allah ya haɗa mu a ladan. Da fatan za’a ɗauki darussan dake cikin labarin, a yi kuma watsi da abubuwan cikinsa marasa kyau. Masoya masu bibiyar littafin Neehal tun daga farko har kawo yau ina godiya tare da yi muku fatan Alkhairi, alkhairin Allah ya kai muku har gadon baccinku. Ina roqon wanda na ɓatawa a cikin wannan tafiyar ya yafe mun, domin ɗan Adam ajizi ne. Waɗanda suke ganin kamar ban yi musu dai-dai ba a cikin labarin su yi haquri haka na tsara labarin tun farko, Na gode Na gode Na gode sosai MASOYA, Allah ya bar k’auna. Sai mun haɗu a sabon Nobel ɗina nan ba da jimawa ba da yardar Allah. NEEHAL, AMEEN AND MAMA they will miss you????????.
DOMIN GYARA KO SHARHI AKAN LITTAFIN NEEHAL, Contact Me.
????
09047871750
By
Zeey Kumurya