NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ku yi hak’uri da wannan Please, wlh na shiga wani uzurinne, sai yanzu na samu time, da k’yar ma na iya typing ɗinnan saboda ciwon kai da nake fama dashi.????????
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
1️⃣1️⃣
BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES????????
500MB 200
1GB 300
2GB 600
3GB 900
6GB 1800
(CHECKING BALANCE * 461*4# )
VALIDITY : 1 MONTH
For more enquiry Call or Whatsapp this number: 08066268951
………..Ƙoƙarin b’oye baƙon yanayin da ya risketa lokaci ɗaya ta yi dan kar Haneefah ta fuskanta. Yanda take ta sauke numfashi a kai_a kai ya sa Haneefah dubanta da mamaki ta ce “Ya dai?” Neehal ta girgiza mata kai. Haneefah ta ce “Mu tsaya a nan mu samu Napep ɗin, tunda kin samu tafiyar ƙasa, gashinan ba’aje ko ina ba kin gaji.” Neehal ta ce “Ni na ce miki na gaji?” Haneefah ta ce “Ba ki faɗa ba, amma na ga alama, sai sassauke numfashi ki ke kamar wadda ta yi tseren gudu raguwa kawai.” Neehal ta harareta ba ta ce komai ba, suka tsaya domin duba abun hawa. A hankali yake yo baya da Motar tasa cikin tsananin zak’uwa da son ƙara ganin fuskar Neehal, tabbas idan har idanunsa ba gizo suke masa ba, matashiyar ‘yar jaridar nan ya gani wadda take matuƙar burge sa tare da abokiyar aikinta. Duk yadda ya so ya wuce ba tare da ya musu magaba amma ya kasa, duk da tarin gajiyar dake addabar gaɓɓan jikinsa, hakan ya sashi bin shawarar zuciyarsa na bin su domin ya musu magana. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya hango su tsaye a bakin titin, da alamun abun hawa suke jira. Neehal da har lokacin zuciyarta ba ta daina bugawa ba ta ga Mota kamar daga sama ta yi parking a gabansu. Kallon juna suka yi ita da Haneefah da sauri da alamun mamaki. Ba su gama mamakinsu ba suka ji wata daddadar murya mai sanyi daga cikin Motar ta na faɗin “Assalamu alaikum.” Haneefah ce ta yi ƙarfin halin amsa wa, Neehal kuwa ƙasa ta yi da kanta gabanta na ci gaba da fad’uwa. “Ina yininku?” Ya gaishe su idanunshi a kan Neehal. Haneefah ta yi ɗan murmushi haka kawai ta ji Matashin ya burgeta, “Lafiya k’alau, amma na ji kunyar amsawa, saboda mu yakamata mu gaishe ka, tunda ka na gaba da mu.” Cikin jin daɗin kalaman Haneefah ya ce “Haba k’anwata kar ki ji komai, ai durk’usawa wada ba gajiyayawa ba ne.” Haneefah ta ce “Hakane.” “Ita k’awar taki ba ta magana ne?” Ya yi maganar idanunsa a kan Neehal. Haneefah ta ce “Hmmm, gajiya ta yi ne daga ɗan…….” “Ke! ki zo mu tafi, ki na sane Mama ta ce kar mu yi dare, a hakan ma kin san sai ta yi faɗa.” Neehal ta katse Haneefah a ɗan zafafe. Murmushi ya yi har yanzu ya kasa ɗauke idonsa daga kanta, cikin wani irin salo mai narkar da zuciya ya ce “Gaskiya ba na so Mama ta muku faɗa, idan babu damuwa ku shigo in kai ku gidan mana.” Neehal ta yi sauri ta ce “A’a mun gode.” Ta ƙarashe maganar ta na turo baki gaba ganin yanda ya tsareta da ido, duk ya bi ya wani dabaibaye ta.” “Please and please, ba danni ba, ‘yar k’anwata.” Ya fadi maganar cikin marairaicewa. Haneefah ta ce “Ka yi hak’uri, idan ka kai mu gida za’a yi mana faɗa.” Ya ce “Waye zai muku faɗan?” Haneefah ta ce “Mama, za ta ce me yasa ba mu kira an ɗauko mu ba.” Ya ce “Sai in shiga in mata bayani, In ce sabon ɗa ta yi shine ya kawo k’annensa gida.” Haneefah za ta kuma magana ya katse ta da faɗin “Kar mu tsaya ja_in_ja daku, ku shigo kawai mu tafi, kunga kun ce za’ai muku faɗa idan ku kai dare, ni kuma bazan barku ba sai na kai ku gida.” Haneefah ta yi murmushi ta ce “To Mun gode.” Neehal ta ɓalla mata wata uwar harara, Haneefah ta mata gwalo ta wuce ta zagaya ta buɗe murfin Motar ta shiga, ita ma Neehal ba ta da zaɓi wanda ya wuce ta shiga Motar tunda Haneefah ta riga da ta shiga. Karon farko a rayuwarta da ta shiga Motar wani wanda ba ta sanshi ba, amma fa ta ɓata rai sosai alamun ba ta so. Sadik ya yi murmushin jin dad’i, wani irin nishad’i yake ji a ransa, gajiyar da take damunsa tuni ya neme ta ya rasa. Neehal ta lumshe idanunta ta na sauke numfashi saboda k’amshin da ta shak’a da ta shiga Motar, wanda ya haɗe da sanyi Ac. K’amshin ya mata daɗi sosai domin har shige ta ji ya mata da na Yayanta. Sadik ya tambayi Haneefah unguwar su ta faɗa masa, kunna Motar ya yi suka hau titi suka fara tafiya. Su na tafiya su na hira da Haneefah wadda ta saki jiki sosai da shi kamar sun dad’e da sanin juna, Neehal kuwa sai harara take bankawa bayan Haneefah, ita ko ba ta ma san ta na yi ba. Har layinsu Neehal ya kai su, daidai k’ofar wawakeken gate d’in gidan Haneefah ta ce ya tsaya, bayan ya yi parking Haneefah ta ce “To new Bro, mun gode sosai fa.” Sadik ya na murmushin da ya ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce “Haba sai kace wani abun, ai nine da godiya da har kuka yarda kuka shigo ‘yar akwalar Mota ta, kuna Manyan ‘yan jarida.” Haneefah ta yi murmushi ta ce “Kai Yaya na akwai ka da zoyala.” Neehal ta tab’e baki, kamar ba ta son magana ta ce “Mun gode, Allah ya saka da Alkhairi.” Ba ta jira amsar sa ba ta buɗe Motar ta fice ta fara tafiya. Sadik ya bita da kallo wani abu na yawo a cikin zuciyarsa game da ita, Haneefah ma fita ta yi tare da yi masa sallama. Mai da dubansa ya yi gareta ya ce “Sai yaushe kuma?” Haneefah ta ce “Sai ransa Allah ya kuma haɗa mu.” Complimentary card ɗinsa ya mik’a mata, Haneefah ta karb’a ta ce “Bye bye, Insha Allahu zan kiraka.”
A falo Neehal ta tarar da Mama zaune ta na kallo, Neehal ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a gefen ta, Mama ta juyo ta kalle ta ta ce “Sai yanzu?” Neehal ta ce “Ki yi hak’uri Mama akasi a ka samu.” Mama ta ce “Da Ameen ya na nan sai ki faɗa masa akasi a ka samu, kin san ba ya nan shi ya sa ki ka yi daren ai.” Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, “Ina Haneefan Kuma?” Mama ta tambayeta ta na maida duban ta ga TV. Kafin Neehal ta ba ta amsa Haneefah ta shigo falon bakin ta ɗauke da sallama, suka amsa mata a tare. “Ina ki ka tsaya kuma?” Cewar Mama ta na kallonta. Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ta na kallon Neehal. Neehal ta ɗauke kanta daga kallonta ta na ɓata rai. Mama ta tab’e baki ta maida hankalinta ga kallon da take. Haneefah ta ƙaraso ta zauna a saman carpet ta ce “Mama mun dawo, duk su na gaishe ku.” Mama ta ce “Muna amsawa, ya kuka baro su?” Haneefah ta ce “Lafiya k’alau.” Neehal ta tashi ta haye sama, Haneefah ta bi bayanta. Ta na ajiye card d’in da Sadik ya bata a kan mudubi ta ce “Ga card nan ya bani, ashe ma Barrister ne.” Neehal ta tab’e baki ta ce “Sai ki nemi ma’ajiya ki killace shi ai, daga ganin mutum ba ki san shi ba, sai uban surutu ki ke zuba masa.” Haneefah ta ce “Kin manta ne, I’m Jornalist fa.” Neehal ta ce “Ke dai ki ka sani.”
Rayuwa na ta tafiya kwanaki na ta wucewa, cikin ikon Allah har an yi sadakar arba’in Anwar, su Neehal har wannan lokacin cikin hutu suke ba su koma school ba. Sosai Haneefah suke zumunci ita da Sadik, tamkar ‘Yan’uwan juna tun da, dan Mama da Mommy’n Haneefah duk san Sadik a bakin Haneefah. Neehal ce dai sama_sama suke gaisawa, shima sai dai idan suna tare ya kira Haneefah sai ta bata su gaisa. Dad sun je sun samu Mahaifin Hafsat sun yi magana, sai dai har yanzu Hameedah da mahaifiyarta da sauran Family ba su da labarin Ameen ba Hameedah zai aura, kuma ƙarshen watan nan Insha Allahu za’a kai kuɗi gidansu Hafsat ɗin. Haneefah ta na kitchen ta na dafa Indomie da daddare ta ji Mommy dake zaune a falo ta na k’wala mata kira. Haneefah ta amsa tare da faɗin “Ina zuwa Mommy.” Sai da ta kammala ta juyo Indomie’n a plate sannan ta fito. Ta na ajiye Indomie’n a kan Centre table ta ce “Ga ni Mommy.” Mommy ta ce “Wayar ki a ke ta kira.” Haneefah ta ƙarasa inda ta ajiye wayar ta ɗauka ta duba missed call d’in, Saurayinta ne wanda za ta aura ya mata 1 missed call sai kuma Sadik da ya mata 2 missed call, kiran Saurayinta ta fara bi amma bai d’aga ba, bayan ta katse ta kira Sadik. Ringing biyu ya yi rejected ya kira ta. Haneefah ta d’aga tare da yin sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin. “K’anwata Ya kike? Ya Mommy?” Haneefah ta ce “Ina lafiya Yayanah, Mommy ma haka, kai fa?” Sadik ya ce “Lafiya k’alau nake, am Haneefah dama ina so mu yi wata magana dake yanzu idan babu damuwa.” Haneefah ta ce “Alright, to bari na ci abinci minti goma i will call you back.” Sadik ya ce “Ok sai kin gama.” Bayan ta gama ci ta koma d’akinta sannan ta kira sa, rejecting ya ƙara yi sannan ya kira ta. Bayan ta d’aga ya ce”Haneefah, Magana za mu yi a kan k’awarki Neehal.” Haneefah ta yi ɗan murmushi domin tun kafin yau ta gano nufin Sadik a game da Neehal. Ta ce “Ina jin ka Ya Sadik.” Sadik ya ɗan numfasa ya ce “Haneefah, tun kafin nu haɗu da ku na san ku a Television, kasancewar ni ma’abocin kallon labaranku ne, Sosai ku ke burgeni saboda yanda ku ke yin komai na ku cikin nutsuwa, ga shiga ta mutunci da kamala wanda yake nuna kun fito daga gidan tarbiyya. Ranar da na ganku a unguwarmu ji na yi tamkar mafarki nake dan farin ciki, hakan ya sa na kasa hak’uri har sai da na tsaya na muku magana, kuma wannan ita ce rana ta farko da na taɓa tsaida mace na mata magana.” Ya ɗan numfasa sannan ya cigaba da magana. “Haneefah maganar gaskiya, zuciyata ta kamu da matsanancin son k’awarki, amma ban san me ya sa nake tsoron tunkarar ta da maganar ba…………✍️