NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
1️⃣2️⃣
………..Ya ƙara yin shiru a karo biyu sannan ya cigaba da magana kamar haka. “Abun da ya sa nake tsoron tunkarar Neehal da maganar saboda ina tunanin kamar ba za ta amince ta karb’i tayin soyayyata ba.” Haneefah ta ce “Ya Sadik na ji batun da ka zo mun dashi, kuma na ji dad’i sosai, amma maganar gaskiya tunkarar Neehal da maganar soyayya a yanzu abu ne mai matuƙar wahala, domin har yanzu ba ta warware daga rasuwar tsohon saurayinta Anwar ba.” Sadik ya ce “Allah sarki, ai dole dama sai a hankali za ta warware daga rad’ad’in mutuwar ta sa, Allah ya ji k’an sa ya gafarta masa.” Haneefah ta ce “Amin, amma kar ka damu Ya Sadik ka bar komai a hannuna zan san ta yadda ta ɓullo mata.” Ta yaya kenan?” Anwar ya tambaye ta. Haneefah ta ce “Ka bani nan da wani lokaci, na san me zan yi.” Sadik ya ce “Shikenan Na gode, sai na jiki.” Daga haka suka yi sallama. Haneefah ta yi shiru kawai ta na tunanin ta yanda za’a yi Neehal ta amince da soyayyar Sadiƙ. Ta dad’e ta na tunanin abun kafin ta mik’e ta koma falo. Mommy har yanzu ta na zaune a falon, Haneefah ta zauna a kusa da ita ta ce “Mommy kin san me?” “Sai kin faɗa.” Cewar Mommy da ta juyo ta na kallonta. Haneefah ta ce “Ya Sadik ne ya ce min wai ya na son Neehal.” Mommy ta faɗaɗa fara’a a fuskarta ta ce “Kai Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi.” Neehal ta ce “Amin, amma fa Mommy akwai matsala.”
“Matsala kuma tame Haneefah?”
“Mommy Neehal mana, na san ba za ta taɓa amincewa da soyayyar Ya Sadik, saboda kwanaki mun yi magana da ita, ta ce mun ita ba za ta ƙara kula wani ɗa Namiji da sunan soyayya ba, Tun da Anwar ya rasu.” Mommy ta ce “Zancen banza, to haka za ta yi ta zama ba ta yi aure ba ko kuma me take nufi? Mace ma take yin Aure mijinta ya rasu kuma ta sake wani auran su zauna lafiya, balle ita da yake Saurayinta, yarinta ce kawai ke damunta.” Haneefah ta ce “To ai ita Mommy dan ta ga ankashe Jameel da Anwar wai karta ƙara yin soyayya da wani shima a kashe shi.” Mommy ta ce “Wannan duk ba hujja ba ce, mutuwa da rayuwa duk na Allah ne, su ma da suka mutun kwanan su ne ya ƙare, Allah dai ya ji k’an su, ita kuma Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta.” Haneefah ta ce “Amin.”
Washegari da yamma Neehal ta zo gidansu Haneefah suna zaune a d’akin Haneefah Neehal ta dubi Haneefah ta ce “Besty ban baki labari ba.” Haneefah ta ce “Labarin me?” Neehal ta ce “Yayanah ya kusa aure.” Haneefah ta waro ido waje ta ce “Wow, nice story, ki ce su Aunty Hamida an kusa shiga daga ciki.?” Neehal ta ce “Hmmm, na yi farin ciki sosai da Yaya zai yi aure, sai dai kuma harna fara kewar shi.” Haneefah ta ce “Iskancin banza, abun da ba kullum ki ke ganin sa ba.” Neehal ta ce “Duk da haka, amma i will miss him over.” Haneefah ta ce “Sai ki bishi gidan nashi, dama ba kwa shiri da Aunty Hamida sai ku yi ta fafatawa.” Neehal ta ce “Ke ba fa ita zai aura ba.” “Kamarya. Haneefah ta tambaya cikin mamaki. “Kamar yadda Allah ya yi, wata tsohuwar budurwarsa zai aura, Hafsat.” Neehal ta bata amsa da faɗin haka. Haneefah ta jinjina kai ta ce “Allah sarki Aunty Hamida ta bani tausayi wlh, yanda take son Yaya ban taɓa tunanin ba ita zai aura ba.” Neehal ta ce “Nima haka Besty, na yi mamaki, Mama ma duk ta damu.” Haneefah ta ce “Allah ya sanya Alkhairi ya kai mu da rai da lafiya mu sha shagali.” Neehal ta ce “Amin dai.” Haneefah ta numfasa ta ce “Dama a haɗa a muku auren tare da Yaya.” Neehal ta mata wani kallo ta ce “Sai dai a haɗa dake, dama na ji Mama ta na cewa Month d’in bikin da za a sa kamar ɗaya da naki.” Haneefah ta ce “Sai a haɗa mu duka a mana tare.” Neehal ta tab’e baki ta ce “Ke nifa na cire wani zancen aure a tsarina, karatuna kawai zan yi ta yi.” Haneefah ta ce “Zance ma ki ke, idan ke kin yarda kin zauna ai Mama ba za ta yarda ki zaunar mata ba aure ba.” Neehal ta ce “To za ta mun aure ba miji ne? Ina dai sai na kawo mata mijin?” Haneefah ta ce “Ai miji ba zai miki wahalar samu ba, duk tarin masoyan da ki ke da su.” Neehal ta ce “Kan ki ake ji, ni dai na riga na hak’ura da wata maganar soyayya a rayuwata balle kuma har na kai ga aure.” Haneefah ganin yanda Neehal take magana bil hak’k’i, ya sa ta saki baki kawai ta na kallon ikon Allah, amma ta mata uzuri, domin ta san har yanzu Anwar ya na nan a cikin ranta, shi ya sa take ganin kamar ba za ta iya ƙara tarayya da wani ɗa Namijin ba…..
*** ABUJA ***
Mommy’n Hameedah ce tsaye a falonta ta na zarya cikin tsananin ɓacin rai da damuwa. K’awarta mai suna Haj. Saratu dake zaune a falon ta dube ta da mamaki ta ce “Wai Suwaiba lafiya kuwa, na ga kin fito daga d’aki kin hau zarga kamar wata me fareti?” Mommy ta ja wani dogon numfashi ta sauke cikin tsantsar ɓacin rai ta ce “Ina fa Lafiya Saratu, waccan munafukar matar ‘yar abu ta kazar uba ta shirya makircin da ta saba.” Haj. Saratu ta ce “Wake nan.? Mommy ta ƙaraso kujerar da Haj. Saratu take ta zauna a gefenta, cikin ɗacin rai ta fara magana. “Yanzu nan Yaya Gen. ya kira ni, ya ce mun za mu yi wata magana, na tattara hankalina duka na bashi dan na ɗauka wata maganar arzik’in ce, buɗar bakinsa sai ce mun yayi. Suwaiba! Magana za mu yi a kan yaran nan Ameen da Hameedah. Na gyara zama cikin jin daɗi na ɗauka zai ce mun za a yi maganar bikin su ne, amma sai na tsinkayi muryarsa da faɗin akasin haka, wai ya kira Ameen ya masa maganar Aure ya ce ya fitar da mata, shine Ameen ɗin ya ce ba ya son Hameedan wata yake so, yanzu maganar da yake mun har sun je gidan su yarinyar an yi magana, next week za su kai kuɗi a yi Engagement ɗinsu haɗe da sa rana.” Wani uban ashar Hajiya saratu ta narka ta ƙara da faɗin “Eh, lallai kam dole ki ce makira ta yi markici, dan wannan ko tantama ba na yi shirin wannan Matar tasa ne, me ji da kanta kamar tafi kowa.” Mommy ta ce “Ai dama ni na san za a rina, domin matar nan ba ta k’auna ta da ni da ƴaƴana, amma wlh wannan karon ba ta isa ba, zan nuna mata asalina za ta san ko wacece Suwaiba, shima Yayan dan takaici kashe wayata na yi, ya tsaya ya na mun wata nasiha wai matar mutum kabarinsa, komai na Allah ne, Ni ko gama saurararsa ma ban yi ba.” Haj. Saratu ta ce “To yanzu mene abin yi?” Mommy ta ce “Ni na san me zan yi, dan idan kinga ba a yi auran Ameen da Hameedah ba to wlh sai dai in ba na numfashi. Amma kafin na yi abin da zan yi bari na fara kiran ita makirar na ci mata mutunci.” Mommy ta ƙarashe Zance tare da mik’ewa ta shiga d’akinta ta ɗauko wayarta, jikinta har tsuma yake ta nemo number’n Mama ta danna mata kira. Mama ta na asibiti ta na ƙoƙarin tafiya gida ma tunda yamma ta yi kiran Mommy ya shigo wayarta. Ba tare da tunanin komai ba ta ɗauka, dan ita ba ta masan Dad ya kira Mommy’n ya mata maganar ba.
“To makira, munafuka Algunguma, wato kin yi halin naki da ki ka saba kin hana ɗanki Auren ‘yata, dan nasan Ameen haka kawai ba zai ce ba ya son Hameedan ba, wa ya sani ma ko hadda siddabarunku na Fulani ki ka haɗa masa saboda ya ƙi amincewa.” Kalaman da Mama ta ji kenan lokacin da ta kai wayar kunnenta, wani ɗan guntun murmushi ta yi, cikin maganarta mai cike da aji da nutsuwa ta ce “Na isa ne ai Suwaiba na hana Ameen abu kuma ya hanu, dan haka ki yi duk abin da za ki yi a kan hakan.” Kamar mahaukaciya Mommy ta ce “Wlh kuwa za ki ga abun da zan yi, za ki san da ni Suwaiba ki ke maganar.” Ta ƙarashe zancen ta na bubbuga k’irjinta. Mama ta yi tsaki ta na ƙoƙarin cire wayar daga kunnenta ta ji Mommy na faɗin. “Kuma nasan duk saboda me ki kai haka, dan tun ba yau ba na fuskanci wannan figaggiyar yarinyar da danginta suka kasa riƙe ta ki ke son bawa Ameen.” Mama harda za ta bata amsa sai kuma ta kashe wayarta, domin ba ta da time ɗin Mommy’n. Mommy kuwa jin Mama ta katse wayar hakan ya ƙara k’ular da ita, ta yi ta masifa da d’uran_d’uran ashariya kamar sabuwar kamu. Haj. Saratu na ƙara zugata.