NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

After 2 weeks
Su Dad sun kai kuɗin Auren Ameen gidansu Hafsat, inda a ka tsaida ranar biki wata huɗu masu zuwa. Maganganu sun yi ta yawo a cikin Family’n su Dad sosai, wasu na faɗin Ameen ya yaudari Hameedah, wasu kuma na faɗin Ameen kuɗin mahaifin Hafsat ya bi zai aure ta, wasu kuma suna faɗin ai gwara ma da ba Hameedah zai aura ba, dan sam ba su dace ba. Mommy’n Hameedah kuwa kamar za ta yi hauka, duk da an kai kuɗin amma ƙara kwantarwa da Hameedah hankali take da faɗin indai ta na raye Ameen ba shi da mata sai ita. Su Neehal da Haneefah da sauran cousins d’in Neehal murna suke sosai da baikon Yayansu. Next week su Neehal za su yi resuming school, ta na cikin d’akinta ta na guge hijabs ɗinta Mama ta shigo d’akin. “Neehal yau fa Muna da baƙi a gidan nan.” Neehal ta ce “Suwa kenan Mama?” Mama ta ce “Ameen ya ce Hafsat za ta zo ta gaishe ni, ki bar gugar nan ki taso mu ki musu ɗan abun taɓawa.” Neehal cikin murna ta ce “Yanzu kuwa Mama, ashe yau mu na da manyan baƙi.” Mama ta ce “Ki dai yi sauri kar time ya k’ure.” Sosai Neehal ta zage jikinta ta shiryawa su Hafsat kayan ciye_ciye kala_kala ita da su Dije da suka taya ta. Bayan sun gama aikin ta na nunawa Mama abubuwan da suka yi Mama ta ce. “Um lallai Neehal, da ni na saki wannan aikin na san har kuka sai kin mun, amma da yake budurwa Ameen ce za ta zo ko nuna alamun gajiya ba ki yi ba.” Neehal ta yi murmushi kawai. Mama ta ce “Ki je ki yi wanka kafin su ƙaraso, su Dije za su jera musu abincin a dinning.” Neehal ta ce “Toh.”
Hafsat ‘Ya mace ɗaya tilo a gurin mahaifinta wanda ya kasance hamshaqin mai kuɗi, Hafsat ta so Ameen kamar ba gobe, amma Ameen ya nuna sam ba ya ra’ayinta. A wancan lokacin haka za ta yi ta zarya gidan Mama tun suna Abuja ta na gaishe ta, daga baya ne da ta ga Ameen ɗin dai ba ya k’aunar ta sai ta hak’ura ta k’yale shi amma ba don ta dena k’aunar shi ba. Cikin wata rantsatstsiyar Mota suka ƙaraso gidan, driver’nta a gaba ya na driving ɗinsu sai ita da k’awarta mai suna Fadeela a bayan Motar. Bayan ya yi parking Motar ya fito da sauri ya buɗe mata mota, cikin izzarta ta fito ta na kallon harabar gurin. Duk da kasancewar mahaifinta ya fi Dad kuɗi amma babu abun da gidansu zai nunawa gidansu Ameen a kyau da tsaruwa, sai dai ya fishi girma. Cikin takunta ɗai_ɗai ta fara tafiya k’awarta na bin bayanta. D’aya daga cikin ma’aikatan gidan ne ya musu jagora zuwa part ɗin Mama. Hafsat sosai take farin ciki da zuwanta gidansu Ameen ɗin, domin wannan zuwan ta zo ne a matsayin suruka ba kamar baya ba da take zuwa dan neman samun guri. Fadeelah ta dube ta tace “Hafsy na lura yau wani farin ciki ki ke na musamman kamar yau ne ranar auran naku.” Hafsat ta faɗaɗa fara’ar fuskarta ta ce “Hmmm Fadeelah kenan, wannan zuwan fa da na yi gidansu Ameen a matsayin suruka na zo, saɓanin da da nake zuwa da k’ok’on barata.” Fadeelah ta ce “Gaskiya ki na son Ameen da yawa.”Hafsat ta ce “Faɗar irin son da na kewa Ameen ms ɓata baki ne saboda tarin yawansa a cikin zuciyata.” Fadeelah ta ce “Amma me yasa be bari sai ya dawo daga Lagos ki zo yana nan ba?” Hafsat ta ce “Ni na matsu sai na zo na gaida Mum ɗinsa, shi ma da yaso na bari sai ya dawo na ce ni dai sai na zo…….” Buɗe k’ofar da Zulai ta yi ya katse mata maganar da take. Zulai ta ce “Sannunku da zuwa, ku shigo.” Fadeelah ce kawai ta amsa da “Yawwa” amma ita Hafsah ɗan yatsina fuska ta yi ta wuce ciki. Gurin zama Zulai ta nuna musu sannan ta haura sama domin ta sanarwa da Mama zuwansu. Hafsat ta dinga satar kallon falon dan ba ƙaramin kyau da burge ta ya yi ba, ga wani sassanyan k’amshi da yake tashi a cikin sa. Neehal Mama ta turo ta hawo da su sama. Neehal da murnarta ta taho dan tarar Aunty’n tata. Tun da ta fara sakkowa Hafsat ta ƙura mata ido cikin fad’uwar gaba, domin ta gane ita ce Neehal ɗin da kullum sai Ameen ya yi zancen ta, dama ta santa a ASTV amma sai ta ga kamar a TV’n ma rage mata kyau a ke a fili ta fi kyau. Haɗe rai ta yi sosai tare da ɗauke kanta daga kallon Neehal ganin ta ƙaraso cikin falon. Da fara’a sosai Neehal ta ce “You are highly Welcome Dear, sai dai ban san Aunty’n tawa ba da nake ta ɗokin zuwan ta, wacece acikin ku?”.” Fadeelah ta yi murmushi dan ita kam yanda Neehal ta musu ta burgeta, nuna Hafsat ta yi ta ce “Gata nan, tunda kin kasa hak’uri na gabatar miki da ita.” Neehal ta yi murmushi ta na kallon Hafsat ta ce “Masha Allah, gaskiya Yayanah ya iya zaɓe.” Ta ƙarashe zancen tare da ƙoƙarin rungume Hafsat ba tare da ta damu da ɗauke kan da ta mata ba. Wani kallon wulak’anci Hafsat ta jefa wa Neehal ta na yatsina fuska kamar ta ga kashi…………..✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:34] Zeey Kumurya: ⚡NEEHAL ⚡
By
Zeey Kumurya
1️⃣5️⃣
Ina ma’abota karatun littattafan HAUSA masu ilimantarwa ,nishaɗantarwa,wa’azantarwa gami da sa canjin rrayuwa????️????️????️.
AƘIDATA! AƘIDATA!! AƘIDATA!!!.
Idan baki karanta ba inason nabaki shawarar ki nemi naki
.
AƘIDATA! Labarin wata haɗaɗɗiyar hamshaƙiya ƴar hamshaƙin mai kuɗi ce????gata da izzah, taƙama,gadara,iko,ilimi,wayo da sauransu????Amma duk da wannan halaye nata tana da wasu wanda taɗaukesu AƘIDARTA, Akwai takun saƙa tsakaninta da matar babanta da kuma agololin da tazo dasu????
Ana bibiyar rayuwarta ta ko’ina hakan yasa rayuwarta taƙare aƙasar waje????
Bata da abokai da suka wuce dabbobi zomaye,maguna,tattabaru,dasauransu????sune abokan dariyarta da kukanta kuma suke ɗebe mata kewa????????????????
Bata tausasa lafazi ga kowa ciki kuwa hadda ma’aifinta ciki ????????????
????????????????Cikin rashin yaddarta tasaki jiki da direbanta wanda shine masomin ƙaddararsu ????????bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koyaci amanarta????????shin mezai faru idan tasan direbanta ma’aikacin sirri ne❔❔❔❔❔
Kutsen ƙaddara ya kutso rayuwarta ba tare da ta shirya ba, rayuwarta takoma wani gari dako ruwan famfo babu, sedai kududdufi wanda ake wanka da wanki aciki shine ruwan amfanin garin…. ????alhalin ita idanba ruwan jarka ba batasaba shan wani ruwaba????????????????????
Sabulun wanka kansa babu semai ƙarni alhalin tasaba wanka da shower jell????????????????????
Akwai tarin sarƙaƙiya da ƙulle ƙulle a cikin wannan labari me ban al’ajabi
ƘAƘA ƘARA ƘAƘA????????????
WIDAD????WIDAD????WIDAD????
Duk me son jin cikakken kabarin Widad da mahaifinta NASIR DAULA yanemi 2&3 akan farashi ƙalilan????????????????????daman part 1????????kyauta ne meso taimin magana nabata????????????????
LALLAI ????AYSHERCOOL ✍????ta dabance basirarta bazaka ganeta ba seka kranta AƘIDATA domin ta farantawa mu masoyanta fie da yadda tay AWATA KISSAR……..! SAI MATA????????.
????????????????????????????????????????AƘIDATA TAYYI DABAN DATA KOWA????????
Normal gro duka littafi biyun #300
Idan kuma laya zaki siya #200
Vip #500.
Idan kuma se angama zaki siyi complete documment #700.
Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja’iz Bank
Se aturo evidence of payment through 07063065680.
Share please????????????????????????.
………. Neehal ce zaune a office d’inta ta na operating system, sai sauke numfashi take akai_akai alamun wani abu na damunta. Haneefah dake zaune a kujerar da take fuskantar ta ta na latsa waya, lokaci zuwa lokaci ta na d’agowa ta na kallon ta. Ajiye wayar ta yi a kan table ɗin gabanta cikin kulawa ta ce “Wai Neehal meke damun ki ne.?” Ba tare da Neehal ta d’ago ba ta ce “Babu komai, me ki ka gani.?” Haneefah ta ce “Yanayinki ya nuna kamar wani na damun ki.” Neehal ta ce “Babu gaskiya, idan ma da akwai ba zai wuce Rashin jin Ya Sadik ba ne da banyi ba yau.” Haneefah ta ce “Kamarya rashin Ya Sadik.?” Neehal ta sauke numfashi ta ce “Tun jiya da yamma da muka yi waya har yanzu bai ƙara kira na ba, gashi last seen ɗinsa a WhatsApp tun 6:44 pm na jiya” Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ganin haƙansu ya kusa cimma ruwa ita da Sadik, domin ita ta bashi shawarar ka da ya nunawa Neehal ya na sonta a yanzu, ya bari sai ta shak’u da shi sosai sai ya sanar mata. Ita kuwa Neehal baiwar Allah, maganarta take bil hak’k’i ba tare da tunanin komai ba. “To ki kira shi mana ki ji ko lafiya.” Cewar Haneefah cikin nazartar ta. Neehal ta ce “Kuma fa hakane, bari mu koma gida zan kira shi.” Haneefah ta ce “To, Allah ya sa lafiya dai.” Neehal ta ce “Amin.” Bayan sun koma gida da yamma wanka kawai Neehal ta yi ta kira layukan Sadik amma duka ba sa tafiya. Zama ta yi a bakin gado tare da dafe kanta cikin damuwa, can kuma ta ja ɗan ƙaramin tsaki ganin damurwar na neman hanata sukuni. A fili ta ce “To mene ma na damuwar haka akan shi.?” “Sadik ya cancanci ki damu dashi fiye da haka ma, duba da tarin kyautatawarsa a gare ki, gami da kulawar da yake nuna miki.” Wata zuciyar ta ba ta amsa da faɗin haka. Mik’ewa tsaye ta yi zumbur kamar an tsikareta ta na sauke ajiyar zuciya, saboda wani tunani da ya ɗarsu a ranta. Wata doguwar rigar abaya purple color ta ɗakko ta zira a jikinta, turarukanta ta mutstsika ta yane kanta da ɗankwalin abayar, wayoyinta kawai ta kwasa a hannunta ta fice daga d’akin. A falon ƙasa ta tarar da Mama. “Ke ina zaki haka ki ke sauri kamar za ki tashi sama.?” Mama dake kallon Neehal tunda ta fara sakkowa daga kan steps ta fad’i haka.” Neehal ta tattaro nutsuwarta ta na ɗan sosa kanta ta ce “Gidan Aunty za ni, kuma sauri nake saboda in yi in dawo da wuri.” Cikin mamaki Mama ta ce “Gidan Aisha kuma da wannan sakaliyar yammar? Daga dawowarki daga aiki ko abinci ba ki ci ba.?” Neehal ta yi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Mama ta ce “Me ma za ki yi a gidan A’ishan?” Neehal ta ce “Gaishe ta zan yi, na dad’e ban je ba.” Mama ta mata kallon tsaf ta ce “Ki bari gobe kya je.” Neehal ta ce “Gobe fa sai six zan dawo daga school.” Mama ta ce “To kya je wani time ɗin.” Neehal ta marairaice ta ce “Please Mama.” Mama ta ce “Ba fa za ki fita ba Neehal a yamman nan, idan Dad ɗinki ya dawo me zan ce masa.?” Neehal ta turo baki gaba ta juya za ta koma sama. Mama ta katse ta ta hanyar faɗin. “Ki shiga kitchen ki zubo abinci ki ci.” Neehal ta yi hanyar kitchen ba tare da ta ce komai ba, abincin ta ɗebo kaɗan ta koma sama. Ta na shiga ɗakinta ta ajiye shi a kan bedside ta hau gado ta kwanta, sosai ta ji takaicin hana ta zuwa da Mama ta yi harda ‘yar k’wallarta, kiran Sallar Magriba ne ya tada ta. Bayan ta idar da Sallah ta ɗakko abincin ta fara ci, sai kuma yanzu take jin haushin kanta na damuwar da ta yi akan kawai yau rana ɗaya dan ba su yi waya da Sadik ba, tambayar kanta ma ta yi inda ta je unguwar su Aunty A’ishan gidansu Sadik ɗin za ta je neman sa ko kuma yaya? Sakin ranta ta yi ta cigaba da sabgarta duk da kewar Sadik ɗin na nuk’urk’usar ranta.