NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

zuciyarta cike da tausayinta ya ce, “Babu komai fa Mum, ni babu wani abu da ya ke damuna, idanma da akwai addu’arki kawai nake buƙata” kallonsa kawai Mama ta tsaya ta na yi, duk wannan uwar ramar da ya yi amma ya ce mata babu abun da yake damunsa. Ajiyar zuciya ta sauke, dan tasan tunda ya faɗa mata haka ba zai taɓa faɗa mata abun da yake damunnasa ba, kome zata masa kuwa, kamar yadda ya faɗa addu’ar kawai za ta cigaba da masa. Ganin yanda take kallonsa ya ce “ki yi haƙuri UMMUNAH, ba na son ki sa damuwa a ranki, dagaske nake miki babu abun da yake damuna ki yarda da ni mana” Mama ta nunfasa ta ce “Shikenan, Allah ya sa mu dace” a saman lab’b’ansa ya amsa da “Amin” tare da sakin hannun mahaifiyartashi. Mama ta ƙara fuskantarshi ta ce “Saura kuma maganar da muka yi kwanaki, na gaji da

yawo da hankalin da kake mini Ameen, ka fitar da mata ka ƙi” ɓata fuska ya yi ya ce “Har yanzu ban sami wadda tamun ba ne” Mama ta masa wani kallo ta ce “Ita kuma Hamidan da take jiranka kusan shekaru goman fa, koma ba Hamidan bama ai ba rasa masu sonka ka yi ba, dan haka banason wani zancen banza, wannan itace last Maganar da zan yi maka akan ka fitar da matar Aure, zan d’aga maka ƙafa zuwa bayan bikin Neehal, idan ba ka zaɓi mata da kanka ba Ni zan zab’a maka, danni da son raina ne ma a yi bikinka tare da na Neehal” jinjina mata kai kawai ya yi ya mik’e ya fice daga ɗakin, dan kwata_kwata baya son maganar Auren da Mama take yi masa a kodayaushe. Mama ta bishi da kallo zuciyarta babu daɗi.

Neehal ta na shiga kitchen ta dakko tukunya ta d’aurayeta ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora, wayarta dake kan locker kitchen ce ta fara ringing, dakkowa ta yi ta sauri ta duba sunan HEART CRUSH ta ga ya na yawo akan screen ɗin, ɗagawa ta yi da murmushi akan fuskarta ta ce “Aloo” daga ɗaya ɓangaren Haneefah ta ce “Na bi Aloo d’in da gudu, dan iskanci na kiraki tun ɗazu amma shine ba za ki iya biyo bayan kirannawa ba” Neehal ta na murmushi mai sauti ta ce, “Sorry Bestynah, time ɗin da kika kira ina bacci ne, ban jima da tashi ba mama ta tura ni kitchen girki, so nake na ɗan rage aikin dama na kira ki ke da MY HUSBAND” Haneefah ta tab’e baki ta ce “To me miji, mun dai kusa miƙa ki gidansa kowa ya huta

da rashin kunyarki” Neehal ta yi ‘yar ƙaramar dariya ta ce “Na ji ɗin, ya kike ya Mommy?” Haneefah ta ce “Mommy tana Lafiya nima haka, ya Mama da Hajiya da Husband d’in naki?” Neehal ta ce “Suna lafiya ƙalau” Haneefah ta ce “Masha Allah, dama kiran ki na yi in ji ko kin dawo daga school” Neehal ta ce “Tun 12 na dawo” Haneefah ta ce “Da wuri haka?” Neehal ta ce “Kin manta yau Saturday lecture ɗaya gareni 10_12” Haneefah ta ce “Hakane fa, na sha’afane” Neehal ta ce “Yaushe za ki fito ne?” Haneefah ta ce “Ni yanzuma na gama shiryawa shiyasa na ƙara kiranki” Neehal ta ce “Toh ki zo mana, sai ki tayani na ƙarasa girki sai mu wuce kawai” Haneefah ta ce “In zo in taya ki girki ko kuma ki ce in zo in ƙarasa Miki girki?” Neehal ta ce “Ni dai koma yaya ne ki yi sauri ki zo” Haneefah ta ce “Toh Mommy ganinan” Neehal ta yi dariya ta ce “Sai kin ƙaraso” ta kashe kiran ta lalubo number’n masoyinta kuma mijinta nan da watanni biyu masu zuwa insha Allah wato ANWAR, kiransa ta yi amma no Answer, ajiye wayar ta yi batare data ƙara kirannasa ba, dan tasan ya na wani uzurinne da ya hanashi d’aga wayar tata, komawa ta yi ta cigaba da aikinta.

After 15 minutes Haneefah ta ƙaraso gidan, Mama tana sama har time ɗin, Hajiya ce kawai kwance akan kujera bacci ya ɗauketa, Ameen kuwa part ɗinshi ya yi bayan ya dawo daga ɗakin Mama. Kitchen Haneefah ta nufa bayan ta ajiye handbag d’inta da mayafinta a kan kujera, Neehal tana cikin slicing d’in cabbage da za ta yi co’slow da shi Haneefah ta yi sallama a kitchen d’in, da sauri Neehal ta ajiye abun hannunta tare da juyawa cikin farin cikin ganin besty’ntata ta amsa mata sallamar, itama Haneefah cike da murnar ganinta ta ƙaraso inda take, rungume juna suka yi Neehal tana faɗin “Welcome dear” Haneefah ta saketa tana faɗin “Thank you” Neehal ta ce “Yau gabad’aya ban ji d’uriyarki da takurarki ba, na yi missed ɗin ki” Haneefah ta ce “Nima haka diarling, ina Mama fa?” Neehal ta ce “Ta na sama may be” Haneefah ta ce “Na ga mutuniyartamu ana ta shan bacci ai” Neehal ta ce “Hajiya rigima, ta kusa tafiya ai mu huta da magana, yawwa dear dan Allah ɗan ƙarasa mini girkinnan na je na shirya kar mu yi latti” Haneefah ta harari Neehal ta ce “Ba wani dan ki shirya, kawai dai ki ce kin ga ji da aikin” Neehal ta b’ata fuska ta ce “Kamar kin sani kuwa” Haneefah ta ce “Hmm, yarinya idan ma za ki daure ki na girki ta daɗin rai ki daure, dan idan aka kai ki gidan ki dole ki yi” Neehal ba ta ce komai ba ta fice daga kitchen d’in.

Ta na fitowa falo ta ji mayen k’amshin turaren Ameen da har time ɗin bai bar falon ba, tunawa ta yi ashe fa ya dawo, kallon saman steps ta yi ta juya kamar wata mara gaskiya tana tafe ta na waige ta buɗe ƙofar falon a hankali ta fice ta nufi part d’in Yayannata dake kusa da nasu part d’in…….✍️

Neehal it’s free book, your comments and share kawai nake buƙata

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: 0️⃣3️⃣

………….Lumshe idanunta ta yi tana shaƙar daddaɗan kamshinsa da ya mamaye falon, numfashi ta sauke ta buɗe idanunta a hankali cikin ƙoƙarin dai_daita nutsuwarta ta cigaba da tafiya kanta a ƙasa, sallama ta yi masa cikin siririyar muryarta tana kyab’e fuska ita a dole fushi take da shi, ba tare da ya d’ago ba ya amsa mata sallamar a can ƙasan mak’oshi, har ta ɗan wuce shi za ta haura saman steps ya kirata ta hanyar faɗin “Miemah!” Tsayawa ta yi tare da juyowa amma ba ta ƙaraso inda yake ba, kamar ba shi ya kira ta ba ya wani waske abunsa yana ta aikin latsa wayarsa, sanin halinsa ya sa ta ƙaraso inda yake ta zauna a ƙasan kujerar da yake ta ce “Ga ni Yayah” Be kulata ba, kusan 2 minutes kamar ya manta da ita a gurin, sai kuma ya d’ago ya mata wani kallo, cikin daddaɗar muryarsa mai daɗin sauraro ya ce “Sau nawa zan hanaki bulbula turare a jikinki idan zaki fita?” Turo baki ta yi gaba ta ce “Kaɗan fa na saka” ya ce “Ƙarya na miki kenan?” Girgiza kanta ta yi alamar a’a, maida hankalinsa ya yi kan wayarsa, Neehal na son wucewa sama amma ta na tsoro tun da bai bata umarni ba, shikuma ya cigaba da al’amuransa kamar ya manta da ita a gurin, kuma ya na sane umarninsa take jira, ɗayar wayarsa da ke ajiye a kusa da shi ce ta yi ƙara alamun shigowar kira, dubawa ya yi, ganin sunan Dad na yawo akan wayar ya sa shi d’agawa da sauri. Dad ya ce “Muhammad ka dawo daga masallacin ne?” Ameen ya ce “Eh” Dad ya ce “Daughter din ta dawo ne” ya ce “Eh” Dad ya ce “Ok, ina son ganinka yanzu a part ɗina” Ameen ya ce “Ganinan zuwa yanzu” ya katse wayar tare da miƙewa ya nufi part d’in Daddy wanda akwai ƙofar da za ta sadaka da part d’in Daddy’n ta cikin falon Mama. Neehal ta mik’e da sauri kamar wadda ke zaune a kan ƙaya ta haye sama. Ɗakin da Hajiya take ta lek’a, Hajiya dake zaune kan darduma ta na lazimi ta dubi Neehal ta ce “A’a kin dawo ne?” Neehal ta ce “Ba gashi kin ganni ba” Hajiya ta ce “To sannunki da dawowa, ina ja’irar ƙawar taki?” Neehal ta ce “Ta wuce gida, Mama ba ta dawo ba?” Hajiya ta ce “Sai bayan magriba fa ta tafi, na yi_na yi ta haƙura da zuwa asibitinnan ta huta itama amma ta ƙi, kamar wadda aka yi wa wahayi haka ta tafi a darennan, dan ma aikin Allah za ta yi, tun da duba marasa lafiya ne” Neehal ba ta ce Komai ba ta juya ta fice ta nufi ɗakinta. Tana ajiye jakarta ta fito ta nufi kitchen, cake ta ɗauko da meatpie saboda wata irin yunwa ta ke ji, ɗakinta ta koma bayan ta ɗau drink a falo, sai da ta ci ta yi k’at, sannan ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala dan yin sallar isha’i.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button