NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Me ki ke yi a ƙasan?”
“Bak’o na yi fa Yaya, ina….”
“Alright Gud.”
Ya katseta da faɗin haka tare da kashe wayar. Neehal ta bi wayar da kallo bayan ta cire ta daga kunnenta, dama tunda suka fara wayar ta ji kamar ransa a ɓace yake, bakinta ta tab’e ta ajiye wayar ta koma ta cigaba da abun da take yi a laptop d’inta. Ta na cikin aikin a ka ƙara kiran wayarta, ba dan taso ba ta tashi ta ɗauko wayar, baƙuwar number ta gani, kamar ba za ta d’aga ba sai kuma dai ta d’aga. Sallama a ka mata cikin murya mai tattare da nutsuwa, Neehal ta amsa ba tare da ta gane mai magana ba, sai dai kuma ta ji kamar ta san muryar.
“Tunda ba ki kira ni kin ji ya na je gida ba, ni na kira ki na ji dafatan na barki lafiya.”
Neehal ta sauke ajiyar zuciya dan ta gane Sadik ne, a hankali ta ce “Am sorry, tunda muka rabu aiki nake yi ne shi yasa.” Sadik ya ce “Ok, amma ko ba haka ba nasan ko Number ta ba ki da shi.” Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba. Sadik jin ta yi shiru ya ce “Ki je ki cigaba da abun da ki ke yi, sai da safe.” Neehal ta ce “Allah ya kai mu, thank you.” Sadiƙ ya ce “Gud night daga haka ya kashe wayar.”
.Washegari Friday Neehal ta dawo daga gurin aiki da yamma, ta na shiga Falon Mama ta ga Ameen zaune a kan kujera ya na latsa wayarsa, Neehal ta waro manyan idanunta cikin mamakin ganin sa, domin ba ya dawowa Ranar Friday sai dai Saturday or Sunday. Cikin murnar ganinsa ta nufi gurin shi ta na faɗin “Yaya yaushe ka zo.?” Kamar ba da shi take ba, ko d’ago kai ya kalleta ma bai yi ba, balle ya ba ta amsa. Neehal ta turo baki gaba ta wuce sama. Wannan weekend d’in gabad’aya Ameen ya ɗauke wa Neehal wuta, ko gaishe sa ta yi ba ya amsawa. Ita kam Neehal ko a jikinta domin ta saba da wannan halin nasa, idan muskilancin nasa ya motsa.
*****************
Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu a first semester Level 3, Neehal da Haneefah tare suke tafiya a matakin karatu, sai dai ba department d’aya suke ba, Neehal ta na Department of Mass communication, ita kuma Haneefan ta na karantar Law ne. Neehal zuwa yanzu ta fara sabawa da Sadik, domin Sadik cikin 1 Month sai da yasan yanda ya yi ya shiga jikin Neehal sosai, sam bai nuna mata sonta yake ba, suna mu’amalane a matsayin Yaya da K’anwa. Sosai Neehal take jin daɗin tarayya da Sadik, kusan kullum sai ya zo sun sha hira, ya yi ta bata labaran ban dariya da nishad’i, wani lokacin kuma idan an bata assignment a school tare suke yi, wani lokacin kuma ya yi ta tsokanarta ita kuma tai ta ɓata rai ta na turo baki gaba, haka za su rabu ta na fushi da shi, sai bayan ya tafi ya kira ta ya lallab’ata su shirya. A hankali kaso mafi yawa na damuwar rashin Anwar ya fara barin zuciyarta a sanadiyyar shigowar Sadik cikin rayuwarta………✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:34] Zeey Kumurya: ⚡NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
1️⃣6️⃣
INAYI MUKU ALBISHIR ????????????????DA SABON LITTAFINA NA KUD’I MAI SUNA(sarauniya SADDIK’A) PAID BOOK NE GA MASU SO SUYI MIN MAGANA NAN DA NEX WEEK 16 October, 2021 Ranar Asabar IDAN ALLAH YAKAIMU ????????????????????????
GAMAI BUKATAR KARANTA LITTAFIN SARAUNIYA SADDIKA
YAMIN MAGANA TA PC GA NUMBER (07089540330 Asmeety) Sai najiku kadda kubari abaku labari ????????????????????????????????
(Hot Sexy ????, Love❤️,and???? Romantic ???? than Funny ????)????
All in this Book (SARAUNIYA???? SADDIKA)????
KADDA KUBARI ABAKU LABARI???? ???? LOVE YOU FAN’S GOOD LUCK????
BY ASMEETY????
…………”Ke!” Neehal ta juyo da sauri jin yanayin da ya yi maganar a zafafe. Ganin yanda ya haɗe fuska tamau ya sa ta shiga nutsuwarta, cikin raunin murya ta ce “Na’am.” Ɗauke kansa ya yi kamar ba shi ya kira ta ba, dawowa cikin falon tay ta tsaya a gabansa tare da faɗin “Gani Yaya.” Abincin da ta kawo ya nuna mata da hannunsa, cikin rashin fahimtar abun da yake nufi ta ce “Ɗaukewa zan yi na kai dinning?.” Wani kallo ya watsa mata, ƙasa tay da kanta da sauri idanunta suka cicciko da k’walla, ta na ƙoƙarin mai da k’wallar ta ji ya ce “Da kike ƙoƙarin fita ki na rawar jiki saboda za ki gurin wani, Ni zan zuba wa kaina abincin.?” Neehal ta ce “Ka yi hak’uri ban san yanzu za ka ci ba.” Ta ƙarashe zancen hawaye na zubawa a kan kuncinta, a rayuwar Neehal kwata_kwata ba ta san a mata faɗa ko tsawa, shi kuma Yayan nata ta fuskanci ya na k’aunar hakan. Ta na share hawayen fuskarta ta tsugunna ta haɗa masa tea a ƙaramin cup d’in da ta haɗo da shi, miƙa masa tay ya karb’a tare da faɗin “Thanks.” Sauran kayan soye_soyen ta zuba mata a cikin plate ta ajiye masa a gefensa ganin ya sakko ƙasa ya fara shan tea d’in. Harta mik’e ya dawo da ita, ya na kallonta fuskarsa a ɗan sake ya ce “Kukan me ki ke.?” Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Hannunsa ya zira a aljihun wandonsa ya ɗakko handkerchief ɗinsa dake tashin daddad’an k’amshinsa ya mik’a mata, ba ta yi musu ba ta karb’a ta share hawayennata. Cikin sanyin murya kamar ba shi ya gama mata magana cikin faɗa yanzu ba, ya ce “Rigimammiya kawai, tashi ki tafi.” Neehal ta mik’e zumbur ta na ƙara turo baki gaba, Ameen ya bi ta da kallo har ta fice.
Parking space ta nufa kamar yadda Sadik ya ce mata ya na can. Sadik ya hangota ya buɗe Motarsa ya fito ya jingina da ita ya na kallonta, gabad’aya fushin da take a kan abun da Ameen ya mata nemar sa tay ta rasa a dalilin ganin Sadik, murmushi ne kawai yake bayyana a kan fuskarta. “Assalamu alaikum.” Neehal ta faɗa lokacin da ta ƙaraso inda Sadik yake, cikin sauke numfashi Sadik ya ce “Wa’alaikissalam.” Neehal ta na murmushi ta ce “Ashe da gaske ka zo, Ni fa na ɗauka wasan da ka saba mun ne, ba zuwa kai ba.” Sadik dake kallonta ta ce “Shi yasa ki ka shanya ni kenan.?” Neehal ta ce “A’a, Yaya ne ya saka ni abu fa, am sorry.” Sadik ya ce “Babu komai, kin san ai yanda amarya ba ta lefi ango ma haka, dan haka tunda aikin Yaya ki ka yi na hak’ura.” Neehal ta ɗan murmusa ta ce “Mu shiga ciki mana.” Sadik ya ce “Ai tunda ki ka ga na tsaya a nan wucewa zan yi, dan sauri nake, sak’o na biyo in kawo miki.” Neehal ta ce “Ba za ka shiga ba kenan.?” Ya ce “Eh, bari na baki na wuce ina sauri ne ana jira na.” Bai jira amsar ta ba ya buɗe murfin Motar ya ɗakko abu a cikin wata leda ya mik’o mata. Neehal ta karb’a ba tare da ta gane mene a ciki ba. “Me ne wannan Ya Sadik.”? Ta tambaye shi bayan ta karb’a. Ba tare da ya amsa mata tambayar ba ya ce”Ki gaida Mama sai mun yi waya.” Ya faɗa ya na shigewa cikin Motar sa, Neehal ta bi shi da kallo kawai cikin mamaki. Reverse ya yi ya d’ago mata hannu, itama hannun ta d’aga masa ta juya ta fara tafiya. Buɗe ledar ta yi kafin ta ƙarasa part d’in Mama, kuɗi ta gani bandir ɗin 1k, zaro ido waje tay cikin mamaki, da sauri kuma ta maida ledar yanda take sannan ta ɗauko wayarta tay dialing number’n Sadik amma bai d’aga ba. Part d’in Mama ta ƙarasa, Mama ba ta falon ƙasa hakan ya sa ta wuce sama, dakin Maman ta nufa direct, bayan ta yi sallama Maman ta amsa mata ta shiga. Mama ta ce “Sai yanzu Neehal daga kai abinci?” Neehal ta ce “Mama Ya Sadik ne ya zo, gurinshi na je.” Mama ta ce “To ya shigo mana, sai kuma ku tsaya a waje kamar wani bak’o.” Neehal ta ce “Har ya tafi ai, yace sauri yake yi, kinga ma ya bani wannan.” Mama ta karb’i ledar ta buɗe, ganin kuɗi ya sa ta d’ago ta na duban Neehal ta ce. “Kuɗin me ne wannan?” Neehal ta ce “Bani kawai ya yi ya wuce bai mun bayani ba.” Mama ta ce “Ke kuma ba sai ki tambaye shi ba.” Neehal ta ce “Ya na mik’o mun ya shige Motar ya tafi.” Mama ta ce “To ki ajiye may be wani abun za ki masa da su, idan kun yi waya sai ki tambaye shi.” Neehal ta ce “Toh.” Dan ita ko kaɗan ba ta yi tunanin kyauta Sadik ɗin ya bata ba.” Mama ta ce “Ki je ki ci abinci Driver ya kaiku ku karb’o ragowar ɗinkunanku ke da Ameerah.” Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga d’akin.