NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

GUDA ƊAYA 300
GUDA BIYU 500
GUDA UKU 600
GUDA HUƊU 800

ACCT NO: 0116886423 SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK

EVEDANCE OF PAYMENT
0814 210 5218

MASU TURA KATI KUMA SU TURA TA NAN????????
0816 788 8934

GA MUTANAN NIGER KUMA SUYI MAGANA TA NAN????????
+227 96 51 58 05

????????????????????????????????Mun shirya tsaf domin sanya zuƙatan masoyan mu farin ciki, Muna fatan zaku fara bibiyar FITATTU HUƊU tun a ZAGON FARKO????????????.

Dan Allah share fisabilillahi Habibaties????????????????????????????????????????.

FITATTU HUƊU ✍????

Team fittattu huɗu????

…………Misalin k’arfe hud’u da mintuna na yamma Neehal ce ke shiryawa a bedroom d’in Mama saboda d’akinta cike yake da bak’i ‘yanmata, sauri take ta yi ta gama shirin nata saboda su Haneefah dake jiranta za su gurin kwalliya. Doguwar rigar abaya ta zira ta d’ora hijabi akai, turarukanta masu sanyin k’amshi ta feshe jikinta da shi, tana gama shiryawa wayarta dake kan mudubi ta fara vibrate, d’auka ta yi ta duba ta ga Ameen ne yake kiranta, a fili ta furta “Yaya kuma?” Kafin ta d’aga wayar ganin tana k’ok’arin tsinkewa ta kara a kunnenta bakinta d’auke da sallama. Ameen ya amsa mata ya k’ara da fad’in, “Ki kawo mun coffe part d’ina yanzu.” Neehal ta ce “Ok gani nan.” Kamar za ta yi kuka ta yi maganar, domin a haka ma tasan sai ta sha jarabar su Haneefah na jiranta da suke, gashi Yayan nata ya k’ara tsayar da ita, zata k’ara b’ata musu time. Fitowa ta yi daga d’akin ta shiga d’an k’aramin kitchen d’in dake saman wanda ba su fiya amfani da shi ba dan dafa masa coffee d’in.

Cikin mintuna qalilan ta gama had’a masa coffee ɗin, kafin ta gama ta window’n kitchen d’in ta hango Haneefah ta zo ta shiga d’akin Mama fuskar nan tata a cukule, ta san bayanta ta biyo. Bayan ta juye masa a k’aramin tea flaks ta d’auka ta nufi part d’in nasa tana ta sauri. Da sallama ta shiga falonsa bayan ta k’arasa, ba ya falon sai k’amshinsa kawai ke tashi a ciki, bedroom d’in sa ta nufa ta tsaya a bakin qofa ta fara knocking, mintuna biyu ya bud’e qofar tare da tsayawa yana kallonta. Neehal ba tare da ta kalle shi ba ta mik’a masa flaks d’in, cikin d’akin ya koma yana fad’in “Kika sake sa ya fad’i ya zube wani zaki sake had’awa.” Neehal ta d’ago tana duban bayansa tare da turo bakinta gaba, shiga d’akin ta yi ta ajiye masa a kan bedside, ta juya zata fita ta tsinkayi muryarshi yana fad’in ta d’auko masa cup, ba tare data amsa masa ba ta je ta d’auko masa ta dire, zata kuma fita ya ce ta zuba masa coffe d’in a cikin cup, Neehal kamar ta zunduma ihu dan takaicin tsaida ta da Ameen yake gashi har 5 ta kusa, gashi Haneefah tana ta kiranta a waya, zuba masa ta yi ta mik’a masa, ya karb’a yana bin hannunta da ya sha jan lalle da kallo, lallen ya kama ya yi kyau gwanin sha’awa. “Ki jira ni a falo.” Ya fad’a cikin had’e rai, Neehal ta marairaice ta ce “Yaya gurin kwalliya za mu tafi fa, su Haneefah na jiran….” Wani kallo ya watsa mata wanda yasa ba shiri ta had’iye sauran managarta ta juya ta nufi qofa ta fice daga d’akin. Tana fita kiran Haneefah na k’ara shigowa cikin wayarta, sai da ta zauna a kan kujera sannan ta d’aga wayar, cikin k’ufula Haneefah ta ce “Wai Neehal ina kika shiga ne tun d’azu inata neman ki amma ban ganki ba, kuma kin san jiran ki muke fa amma kika shanya mu, idan ba za ki taho ba mu za mu yi tafiyarmu.” Neehal ta ce “Ki yi hak’uri Haneefah Yaya ne ya kira ni ina part d’in shi.” Haneefah ta ce “Yaya kuma? Me kike masa toh?” Neehal ta ce “Coffe na had’o masa, yanzu kuma ya ce na jirashi a falo ban san me zai kuma sani ba.” Ta yi maganar kamar za ta yi kuka, Haneefah ta ce “Yanzu dai kinga 5 ta kusa, kuma muna da yawa wad’anda za’ayiwa make up d’innan, bana so mu yi late a gurin zuwa dinner nan.” Neehal ta ce “Idan 5 d’in ta yi ku wuce kawai zan taho ni kad’ai ko’a Napep ne.” Haneefah ta ce “Shikenan.” Tare da katse wayar. Neehal tana zaune a falo Ameen ya shanya ta, har k’arfe biyar ta wuce, su Haneefah sunyi wucewarsu gurin kwalliyar, gashi dinner d’in k’arfe bakwai na dare ne, kuma bata son ta yi African time.

Ameen bai fito daga dakinshi ba sai da 6 ta wuce, zuwa lokacin Neehal harta fara hawaye, gashi Haneefah nata kiranta ita har angama mata make up d’inta, kuma kayan da zata saka yana gurin Haneefah ta tafi da shi a had’e da nata, da sai ta hak’ura da kwalliyar ta zira kayanta kawai ta tafi, get past d’inta ma dana Sadik duk yana hannun Haneefan.” K’amshi turarensa da ta ji ya k’ara cika mata hanci shi yasa ta d’agowa da sauri ta kalle shi, shima ita d’in yake kallo hakan yasa suka had’a Ido, Neehal ta d’auke idanta da sauri tana yaba tsananin kyawun da ya yi a cikin zuciyarta, ya fito sak angonsa cikin dakakkiyar shadda mai tsadar gaske sky blue wadda aka maka aiki da Kalar Royal blue, tunda Neehal take ba zata iya tuno ranar da ta ganshi da hula ba a rayuwarta, domin shi mutum ne ma’abocin saka k’ananun kaya, idan ka ganshi da manyan kaya Juma’a ce ko kuma Sallah ko kuma idan za shi d’aurin aure, kuma suna masa kyau sosai idan ya saka, yau kam gashi harda babban riga (Malin_Malin) a kan kayan. Kiran shi ake tayi a waya amma ya k’i picking, Neehal kanta na k’asa ta ce “Yaya dan Allah ka barni in tafi, su Haneefah fa har an gama musu kwalliyar za su tafi ni kaɗai na rage.” Ameen ya mata banza tamkar ba da shi take ba, tsadadden agogon hannunsa kawai ya kalla sannan ya zauna akan d’aya daga cikin kujerun falon ya shiga latsa wayarsa hankali kwance. Sosai ran Neehal ya b’aci a kan abunda Ameen ya mata, haka kawai ya tsaidata kuma babu abunda zata masa, ita kuma bai barta ta je ta yi uxurin gabanta ba. Kiran Sadik ne ya shigo wayarta domin sun yi da shi zai d’auko su daga gurin kwalliyar ya kaisu gurin bikin, ba ta san me zata fad’a masa ba, shi yasa ta k’i d’aga wayar ta barta harta gaji ta katse.

6:30 pm, Ameen ya mik’e ya dubi Neehal dake ta hawaye ya ce “Tashi mu je.” Fuskarsa babu walwala ko kad’an ya yi maganar, Neehal ta mik’e da sauri kamar wadda ke zaune a kan k’aya ta yi gaba, sai da ya kulle qofar part d’in sannan ya bi bayanta, har ta nufi part Mama ya tsayar da ita Neehal ta tsaya cike da mamakinsa gami da tsoro, domin ta kasa gane me yake nufi da ita, bayan zaman banzan daya sa tayi na fiye da awa ɗaya bai ishe shi ba sai ya k’ara tsayar da ita, to me yake nufi da ita ne? Gurin bikin ne baya son taje ko kuma me?” Dan ita zuwa yanzu ta hak’ura da kwalliyar kayanta kawai take so taje ta saka ta tafi tunda lokaci ya k’ure, gashi Sadik sai kiranta yake a waya ta k’i d’agawa, tafi son sai taje gurin kwalliyar sai ta kira shi ya je ya d’auke ta su wuce. Ameen ya nufi parking space bayan ya mata alamar ta biyo shi, harabar gidan Neehal ta kalla taga duk babu mutane an tafi gurin kwalliya wasuma sun fara tafiya gurin bikin. Bata da zab’i wanda ya wuce bin nasa, Motarsa ya shiga mazaunin driver, hakan yasa ita kuma ta shiga gurin mai zaman banza ta zauna zuciyarta na mata k’una, tana rufe murfin Motar ta fashe da kuka, Ameen ya dube ta da sauri ya ce “Me ne haka?” Neehal cikin kuka ta ce “Yaya wai me kake so na maka ne kake ta tsaida ni? alhalin kafi kowa sanin inda za ni, ga mutane suna ta jira na, kasan Mama ma Idan tasan ina gida har yanzu sai ta yi fad’a.” Ameen ya tab’e bakinsa bai ce komai ba, yay wa Motar key suka fice daga gidan. Neehal ta cigaba da kukanta, a d’an fusace ya dube ta ya ce “Kar na k’ara jin kukan nan, yana cika mun kunne.” Yanayin yanda yay maganar yasa Neehal ba shiri ta had’iye kukanta, Handkerchief d’insa ya zaro daga aljihu ya mik’a mata tare da fad’in “Share hawayenki, kuma kar na k’ara ganin ko d’igonsu.” Ba musu Neehal ta karb’a ta share hawayen ta ci gaba da kukan zuci. Tafiyar mintuna k’alilin suka yi ya faka a gaban wani shago, wayarsa ya d’auka ya yi kira, mintuna uku wata matashiyar mata ta fito fuskarta d’auke da fara’a, Ameen ya zuge glass d’in Motar bayan ta qaraso suka gaisa tana tsokanarsa da ango ka sha k’amshi, nuna mata Neehal wadda idanunta ke lumshe ya yi ya ce “Gata nan, sai ki yi sauri please dan time ya qure.” Matar ta yi murmushi ta ce “Kai dama wa ya fad’a maka sai i’yanzu ake zuwa make up? ai tun rana ake zuwa.” Neehal wadda ta yi dif kamar bata Motar ta bud’e idanta da sauri jin an ambaci make up Tana kallon Matar, a hankali ta sauke numfashi ta ce “Ina yini.” Matar ta amsa fuskarta d’auke da fara’a, ta k’ara da fad’in “Kai Masha Allah qanwar taka kuma kyakkyawa da ita, harma ta so ta fi ka kyau.” Ameen ya yi murmushi kawai ya juyo da dubansa ga Neehal ya ce “Ki je ta miki, inanan ina jiran ki.” Neehal ta ce “Amma Yaya kayana fa suna gurin Haneefah.” Yana latsa wayarsa da ake ta kira ya ce “Zan kawo miki wasu.” Neehal ta waro Ido ta ce “Yaya wasu kayan kuma? Anko ne fa wanda zan saka, kenan ni daban zan tashi?” A ɗan hasale ya ce”Kin san bana son musu ko?” Neehal ta turo Baki gaba cikin qoqarin maida hawayen da ya tarar mata a Ido ta bud’e Motar ta bi bayan Matar wadda ta koma cikin shagon nata tun sanda Ameen suka fara magana da Neehal. Ameen ya bita da kallo harta shige shagon sannan ya ja Motarsa ya tafi dan zuwa masallaci jin an fara kiran Sallah. Neehal ma sai da ta yi Sallah tukunna aka fara mata make up d’in, zuwa lokacin wayarta ta gaji da shan kiran Haneefah da Sadik harda ma da Mama. Matar da kanta ta yi wa Neehal kwalliya, sab’anin wasu a shagon da yaranta ne suke musu, gata da sauri cikin abun da bai wuce 40 minutes ba ta tsantsarawa Neehal kwalliya irin light d’innan amma ta yi masifar kyau, kowa dake shagon sai da ya furta “Wow, Masha Allah.” Har wasu na tambayar ko Neehal amarya ce? Matar na ba su amsa da fad’in “K’anwar wani class mate d’inta ce da suka yi Secondary school, auransa ake shine ya kawo ta, ta yi mata kwalliya.” Bayan kammalawa Neehal kwalliyar ta kira Ameen a kan ya kawo mata kayan Neehal, ya shaida mata ta fito bakin shagon ta karb’a. Neehal ta cika da mamaki ba kad’an ba ganin kayan da Ameen ya kawo mata ta saka, wata had’ad’d’iyar wedding gown ce sky blu, sai head Royal blue da takalmi da su sark’a harda pos wanda duk bata san da su ba, babu b’ata lokaci ta zira kayan me make up ta kafa mata had’ad’d’en d’aurin da ake yayi, nan fa Neehal ta qara fitowa bayan ta gama shiryawa tsaf, babu ta yanda za a yi ka ce ba amarya ba ce, matar ta ba ta turaruka masu sanyi da dad’in k’amshi ta feshe jikinta da shi. Neehal ta kasa d’auke idanunta saga kan mudubi saboda ganin kyawun da ta yi, sai tambayar kanta take a ranta tana fad’in “Ashe make up zai mata kyau sosai irin haka?” Matar ta mata pictures a wayarta sannan suka fito, dan itama matar zata je bikin, Ameen ya yi invited d’inta. Tunda suka fito Ameen ya kafe Neehal da Ido, ganin wani irin sihirtaccen kyau da ta yi, tana tafe tana faman rik’e Riga saboda jan k’asar da take ta baya, duk da kuwa takalmin k’afarta yana da tsini. Neehal ta bud’e front seat ta shiga, Matar kuwa ta shiga baya, zuciyar Neehal cike take fal da tarin tambayoyi ga Ameen, akan hanata zuwa gurin kwalliyar da ta yi niyya da ya yi, ya kawota wani wajen daban, sannan kuma ya bata wasu kayan daban wanda suka yi colour d’aya da nashi, Amma dole tabar tarin tambayoyinta a ranta saboda ba su kad’ai ba ne a Motar kuma ba taga fuskar hakan a gurin shi ba dan tana shigowa ya wani tsare gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button