NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ƙarfe 9:30pm Neehal ta ja Haneefah gefe cikin damuwa ta ce “Besty Ina ta kiran Ya Sadik ba ya picking, Allah ya sa lafiya.” Haneefah ta ce “Nima tun d’azu nake son na ce miki banga Ya Sadik ba, amma bari na kira shi na ji.” Neehal ta ce “Ya kikkira ni fa, time ɗin ko gurin kwalliyar ba mu tafi ba, ina tunanin fa ya zo da ya kira ni ban ɗauka ba shine ya tafi.” Haneefah da hankalinta ke kan wayarta ta ce “To ke me yasa kika ƙi d’agawar?” Neehal ta ce “I think in ya ji ban d’aga ba zai kira ki shi yasa.” Haneefah ba ta kuma cewa komai ba jin wayar Sadik ta shiga, har ta yi zaton ba zai d’aga ba sai kuma ta ji ya d’aga tare yin sallama. Ta kalli Neehal tare da amsa masa, ta ƙara da faɗin “Ya Sadik ina yini.” Ya ce “Lafiya k’alau, Ya taro?” Haneefah ta ce “Alhamdulillah, ya na ga ban ganka a wurin bikin ba?” Sadik ya ce “Na zo ai na kira Neehal ba ta ɗauka ba, kawai na wuce.” Haneefah ta ce “Ayya da ka kira ni ai, dan get pass ɗinka ma yana wurina.” Sadik ya ce “Don’t worry, Allah ya sanya Alkhairi.” Haneefah ta ce “Ameen.” Tana shirin ce masa ga Neehal ta ji ya katse wayar, Neehal dake kallon Haneefah ta ce “Me ya ce?” Haneefan ta ce “Ya zo ya tafi.” Neehal cike da damuwa ta ce “Fushi ya yi da ni kenan? Shi yasa ma naita kiran shi ya ƙi pick.” Ta ƙarashe zancen kamar zata yi kuka.” Haneefan ta ce “Ki kuma kiran shi yanzu nasan zai d’aga, d’azun ma may be ba ya kusa da wayar ne.” Neehal ta ce “Toh.” Sai da ta fice daga hall ɗin saboda hayaniya sannan ta kira shi amma still bai ɗauka ba. Text ta tura masa kamar haka. I’m sorry Ya Sadik, Please ka d’aga wayata Sadik ya yi murmushi lokacin da ya ga text ɗin Neehal, kafin ya kirata har wani kiran nata ya kuma shigowa, rejected ya yi sannan ya kira ta. Ta d’aga da sauri cikin shagwab’a Ta ce “Ya Sadik I’m sorry please, time ɗin da ka ki……” “Kar ki damu ba komai, ya taron?” Sadik ya katse ta da faɗin haka. Neehal ta turo baki gaba ta ce “Ai na yi fushi tunda baka dawo ba.” Sadik ya ce “Haba ‘yar ƙanwata a yi mun afuwa mana.” Neehal ta ce “Um, um nidai sai ka zo zan haqura.” Sadik ya ce “Shikenan ki ba ni 15 minutes gani nan zuwa.” Neehal ta ce “Yawwa Yayanah sai ka zo.” Sadik ya katse wayar yana murmushi, yana jin farin ciki a cikin zuciyarsa. Neehal tana yin taku kaɗan ta ga wasu maza biyu a gabanta a tsaye, ta canza hanya da sauri ta ga sun ƙara shan gabanta, ɓata fuska ta yi sosai tare da tsayawa ta ce “Lafiya?” Suka yi murmushi sannan wani a cikinsu ya ce “Lafiyar kenan ƴan’mata.” Neehal ta ja ɗan ƙaramin tsaki ta wuce da sauri ta bar su a gurin. Tunda ta koma cikin hall ɗin ta ji kanta na mata ciwo, ta yi tunanin ko yunwa ce dan rabon ta da abinci tun safe hakan yasa ta nemo abinci ta ɗan ci, amma a banza kamar ma ƙara mata ciwon kan aka yi har wani jiri_jiri take ji, gaba-d’aya gurin bikin ya gundure ta, so take kawai ta ganta a gida. Gurin Aunty Sadiya ta je ta ce mata “Aunty dan Allah ara mun key ɗin Motarki idan da ita kika zo.” Aunty Sadiya ta ce “Me za ki yi da shi?” Neehal ta ce “Wata Friend ɗina zan kai gida yanzu zan dawo.” Aunty Sadiya ta ce “Ina?” Neehal ta ce “Anan cikin Narasawan suke.” Aunty Sadiya ta ce “Ta bari a tashi mana, ai an kusa tashi sai a kaita.” Neehal da take magana cikin dauriya saboda ciwon kai ta ce “Ana ta kiran a gida ana cewa ta dawo, a hakan ma sai an mata faɗa.” Aunty Sadiya ta buɗe Pos ɗinta ta ɗauko key ɗin Motar ta bawa Neehal tana faɗin “Take it, amma ki yi sauri, ki kuma kula da hanya sosai kin ga dare ne.” Neehal ta ce “Insha Allahu Aunty, thank you.” Aunty Sadiya ta faɗa mata inda ta yi parking Motar ta fito ta nufi gurin.

A hankali take driving saboda ciwon kai gashi kuma dare ne, ta cikin layika take bi saboda ta yi saurin zuwa gida, abunka da G.R.A ko ina tsit babu mutane, amma akwai wadatuwar haske, tana shiga wani layi ta taka wani wawan burki da ƙarfin gaske cikin tsananin razana saboda abun da ta gani, ƙara dallare gabanta ta yi da hasken filitar Motar dan ta ƙara tabbatar da abun da idanunta suke gane mata……….✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

1️⃣9️⃣

………..Dafe kanta dake barazanar tarwatsewa ta yi saboda yanda yake sara mata, tattaro dukkan dauriyarta ta yi ta buɗe Motar ta fito ba tare data kashe ba, da fitilar wayarta ta haske Yaran mata guda biyu wanda suke ta kuka manne da juna, ga haushin da wasu karnuka suke yi wanda ga dukkan alamu shike ƙara firgita Yaran. Neehal addu’a take acikin ranta zuciyarta cike da tsoro, domin ba tasan yaran mutane ba ne ko aljanu, ƙura musu ido ta yi cike da tausayawa a ranta tana faɗin “Idan har Yaran nan mutane ne to duk wanda ya ajiye su anan bai da imani ko kaɗan, yanda duniyar nan ta lalace ace yara ƙanana a daren nan amma su kaɗai a bakin layi, layin ma irin wannan da babu mutane, ga su ƴaƴa mata, yanda duniyar nan ta lalace idan wani mugun ya ƙyalla ido ya gansu ai sai ya ɓata musu rayuwa.’ Lokaci ɗaya Neehal ta nemi ciwon kan dake damunta ta rasa tunanika kala_kala ta shiga yi akan yaran, cike da faragaba ta kama ƙafar ɗaya daga cikin yaran ta duba, jin kamar ƙarar tahowar Mota cikin layin yasa ta yi addu’a ta kamo hannun yaran wanda ganin tana haska su yasa suka ƙara rukunkume junansu. Babu musu yaran suka biyo ta still suna cigaba da kuka, Neehal ta buɗe bayan Motar ta saka su sannan ta shiga gaba ta tada Motar ta nufi gida, har suka je gida yaran ba su dena kuka ba tare da kiran sunan Daddy a kofar part ɗin Mama ta yi parking Motar, ta fito da sauri ta fito da yaran suma da har yanzu ta gaza ce musu ko ƙala, ɗaukar ɗaya ta yi ta ja hannun ɗaya suka shige ciki, babu mutane sosai a gidan duk suna gurin dinner, sai tsoffi kawai da waɗanda ba a rasa ba. Neehal ta gaida mutanen data tarar a falo sannan ta wuce sama, babu wanda ya tambaye ta game da yaran tunda biki ake za su yi tunanin ko ƴaƴan wata ne.

Direct Neehal ɗakinta ta nufa ta sauke yarinyar dake hannunta wadda ta yi shiru tare da yin luf a jikinta, Neehal ta zauna a gefen gado tasa yaran duka a gabanta tana kallo, koda ba’a faɗa mata ba tasan yaran twins ne, saboda komai nasu da ya kasance iri ɗaya. Kyawawa ne kuma farare ga gashi an musu two babies, babu alamar talauci a jikin yaran, fatarsu luwai_luwai ga dukkan alamu daga gidan kuɗi suke, sai k’amshin turaren yara mai daɗi suke. Neehal ta fara tambayar kanta da faɗin “To wa ya ajiye su a waje a wannan daren? Ko dai fitowa suka yi suka kasa gane gida, ko kuma sato su aka yi? Gashi yaran da shigarsu tsaf cikin doguwar riga ƴan kanti masu kyau da tsada, ƙafafuwansu ne kawai babu takalmi ga…..” “Aunty ki kai mu gurin Daddy.” wadda da Neehal ta ɗauka da za su shigo ta katse ta da faɗin haka cikin maganarta ta yara. Neehal ta sauke numfashi tare da shafa kan yarinyar ta ce “Ina Daddy’n yake?” Ɗayar da hanyar yanzu bata daina kuka ba tace “Yana gida.” Neehal ta janyo ta jikinta ta ce “Wa ya ajiye ku a waje?” Yarinyar ta ce “Wasu ne.” Neehal ta ce “Ina mom ɗinku.” Suka haɗa baki gurin faɗin “Daddy ya ce ta tafi ba zata dawo ba.” Neehal ta yi shiru kawai tana kallon yaran, lokaci ɗaya suka cigaba da kuka suna kiran “Daddy Daddy, su dai akai su gurin Daddy’nsu.” Neehal ta rungume su a jikinta tausayin yaran na ratsa dukkan jikinta, domin ta fahimci ba su da uwa saboda yanda suke kiran sunan Daddy kawai da kuma abun da suka ce mata. A hankali kuma ta d’ago su daga jikinta ta shiga goge musu hawayen fuskokinsu, tsabar kuka idanunsa sun yi jajir fuskarsu ma haka. Neehal cikin lallashi ta ce “Ku yi hakuri da safe zan kai ku gurin Daddy kun ji.” Yaran suka d’aga mata kai suna sakin ajiyar zuciya. Neehal ta ce “Kun ci abinci?” Suka girgiza mata kai alamar a’a, Neehal ta shafi fuskokinsu ta ce “Bari na dafa muku indomie da tea, kuna ci ko?” Wadda tafi magana ta ce “Eh, Daddy Yana dafa mana every Morning.” Neehal ta ce “Bari in dafa muku to.” Ta mik’e ta cire ɗan kwallin dake kanta, tana cire ɗan kunne yarinyar ta ce “Aunty amarya ce ke.?” Neehal ta yi murmushi tare da d’aga mata kai, Ta lura yarinyar na da wayo da surutu saɓanin ɗayar data fahimci miskila ce. Neehal ta cire gown ɗin jikinta ta ɗauko wata riga mara nauyi ta nufi kitchen yaran na biye da ita a baya, ta lura duk a tsoro ce suke.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button