NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
A can gurin biki kuwa Sadik ya ƙaraso ya kira wayar Neehal ba ta ɗauka ba, sai ya kira Haneefah ta zo ta shigar da shi, Haneefah ta kai shi suka gaisa da Mama da Ya Ameen ya musu Allah ya sanya Alkhairi. Haneefan tana ta neman Neehal amma bata ganta ba, ta kira wayarta kuma bata ɗauka ba, ta bawa Sadik hakuri ya ce babu komai. Sai wajen 11 aka tashi daga dinner, Aunty Sadiya tana ta neman Neehal itama dan ta bata car key ɗinta. Mama ta kira Haneefan ta ce mata “Ina Neehal ne? Ta zo mu wuce gida.” Haneefan ta ce “Mama tun d’azu ban ganta ba, da Ya Sadik ma ya zo nay ta neman ta za su gaisa amma ban ganta ba.” Mama ta ce “Kin kira wayarta kuma?” Haneefan ta ce “Eh, bata ɗauka ba.” Mama ta yi shiru kawai tana sauke numfashi. Sai da za su shiga Mota Aunty Sadiya take faɗa mata yanda suka yi da Neehal, Mama tay ta faɗa tana cewa Aunty Sadiya “Me yasa zata bawa Neehal Motar a daren nan ta yi driving?” Aunty Sadiya ta ce “Mu yi fatan Allah yasa tana lafiya kawai.” Ameen ma yana ta baza ido ko zai ga Neehal su tafi tare amma bai ganta ba.
Kallon yanda yaran suke cin abinci kawai Neehal cike da tausawa, a nutse suke ci amma kana gani ka san suna tattare da yunwa, sun ci sosai ɗaya ta fara kakarin amai, Neehal ta yunk’ura ta dauke ta da sauri ta yi toilet da ita, aikwa suna shiga ta fara kela amai, kafin ta gama itama ɗayar ta shigo tana yi, Neehal sai sannu take musu cike da tausayawa. Ta wanke musu baki bayan sun gama, ta cire musu rigunan jikinsu saboda sun ɓaci, ta dawo da su ɗaki suna ta sauke numfashi, Neehal ta lallaɓa su da ƙyar suka sha tea kaɗan, sannan ta kai su toilet ta musu wanka, dan duk sun yi kashi a cikin pampers ɗin jikinsu. Neehal tay ta mamakin yanda yara sun girma kamar waɗannan amma ake sa musu pampers, kuma da bakinsu za su iya cewa za su yi kashi. Komai na yaran iri ɗaya ne, babu wani abu daya bambanta a jikin su, harta da fingers ɗinsu iri ɗaya ne. Neehal ta naɗo su da ƙananun towels ɗinta, ta shafe su musu jiki da lotion sannan ta karkaɗe gado ta kwantar da su, har sun kwanta wadda tafi magana ta tashi kamar za ta yi kuka ta ce “Aunty ki kai mu gurin Daddy.” Neehal ta matso ta janyo su jikinta sannan ta ce “Zan kai ku insha Allah, amma yanzu dare ya yi ku kwanta ku yi bacci da safe sai na kai ku.” Yaran suka yi lamo a jikin Neehal ba su ƙara cewa komai ba, cikin 5 minutes ta ji saukar Numfashinsu alamun bacci ya ɗauke su, sai sakin ajiyar zuciya suke. Neehal ta raba su da jikinta a hankali tare da gyara musu kwanciya, ƙura musu ido ta yi zuciyarta cike da tunanika kala_kala. Jin hayaniyar mutane sun fara dawowa ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi zaune, addu’a ta tofa musu sannan ta tashi ta ɗauko blanket ta lullub’e musu dukkan jiki da shi kansu ne kawai a waje. Toilet ta shiga, rigunan yaran ta fara wanke wa sannan ta goge make up ɗin fuskarta da tissue, tana cikin wanke fuskarta da sabulu Haneefan ta shigo ɗakin tana kiran sunanta. Turus Haneefan ta tsaya bayan ta ƙaraso tsakiyar ɗakin tana kallon yaran dake bacci akan gadon cikin mamaki, a hankali ta ƙarasa gadon ta zauna tana duban yara cike da sha’awa, a rayuwar Haneefan tana bala’in son twins, kan yaran ta shafa tana addu’ar Allah ya bata twins itama. Neehal ta fito daga toilet tana faɗin “Kiran me kike mun haka kamar sabuwar makauniya?” Haneefan ta harare ta tace “Makauniyar ce, ashe kina nan hankalinki kwance mu muna can namu a tashe.” “Akan me?” Neehal ta tambaya tana shimfida Darduma domin yin Sallah. Shigowar Mama dakin ya hanata tada Sallar, Mama ta tsaya kawai tana bin ta da kallo. Neehal ta ce “Sannu da zuwa Mama.” Rai a ɓace Mama ta ce mata “Kin kyauta Neehal Na gode.” Neehal data san kwanan zancen ta ce “Ki yi haquri Mama, wallahi kaina ne ke ciwo kamar zan mutu shi yasa na dawo gida dan na huta.” Mama ta ce “Shine ba za ki faɗa a dawo dake gidan ba sai kin yi ƙarya.” Neehal ta yi ƙasa da kanta ta ce “I’m sorry ban san na wahalar da kowa ne.” Mama ta tab’e baki ba ta ce komai ba, ta juya zata fita idanta ya sauka akan twins dake bacci akan gado. Ta dubi Haneefan wadda ta kasa ɗauke idanunta daga kansu ta ce “Haneefan Waɗannan Yaran fa ?” Haneefan ta ce “Nima anan na zo na same su Mama.” Mama ta maida dubanta ga Neehal wadda gabanta ke fad’uwa dan bata san ya Mama zata karb’i zancen yara ba, ta ce “Ƴaƴan waye?” Neehal ta sauke numfashi ta ce “Mama long story ne.” “Long story kuma?” Mama ta tambaya cikin rashin fahimta, Neehal ta gyaɗa mata kai tare da bata labarin yanda ta samu yaran. Ta ƙara da faɗin, “Na ji tsoro sosai a time ɗin da na gan su, har da zan wuce na barsu sai kuma na yi tunanin kar na barsu wani abun ya cutar da su, gashi sai kuka suke suna kiran Daddy.” Mama ta yi shiru kawai tana kallon Neehal, tana son gano gaskiyar abun da Neehal ɗin ta faɗa, ta san Neehal bata mata ƙarya dan ko ta yi ma sai ta gano ta. Mama ta ce “Neehal kin san bana son ƙarya ki faɗa mun gaskiya yaran waye?” Neehal ta ce “Wallahi Mama abun da na faɗa miki shine gaskiya ki yarda mana.” Mama ta ce “A ina kika gan su?” Neehal ta ce “Titin Ahmadu Bello ta cikin layika amma.” Mama ta yi shiru tana tunani tare da kallon yaran cike da tausayawa, Haneefan ta ce “Allah sarki ko dai sato su aka yi Allah ya yi nufin kub’utar da su shine aka yarda da su a gurin.” Mama ta sauke numfashi ta ce komai ma zai iya faruwa, ɗauko ɗaya Haneefan bari na ɗauki ɗaya mu kai su part ɗin Daddy, tunda nan akwai baƙin da za su kwana, kafin safiya mu san abun yi akan su.” Haneefan ta ce “Toh.” tare da lallaɓawa ta ɗauki ɗaya, yarinyar ta ɗan firgita cikin bacci ta ce “Daddy.” Haneefan ta rungume ta ajikinta tana shafa bayanta. Mama ta ce “Babu kaya ajikinsu dama?” Neehal ta ce “Akwai, ya ɓaci da amai ne shine na wanke suna toilet.” Mama ta ɗauki ɗayar itama suka fice daga ɗakin. Neehal ta bisu da kallo kafin ta tada Sallah, tana hamdala a ranta da Mama ta fuskanci lamarin Yaran cikin sauƙi.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
ABUJA
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Wata matashiyar budurwa ce ke kai kawo a cikin wani madaidaicin bedroom hannunta riƙe da waya ƙirar iPhone, yanayinta ya nuna tana cikin wani tashin hankali, wayar hannunta ce ta ɗau ruri wanda hakan yasa ta ɗan firgita tare duba wayar da sauri, jikinta har rawa yake ta d'aga wayar ta kara a kunne. A ɗan zafafe ta ce "Haba Gaye ya zan yi ta kiran ku amma ku ƙi d'aga mun waya, kun sa hankalina gaba-d'aya ya tashi ina tunanin ko an samu matsala ne a aikin." Gayen ya ƙyalƙyale da dariya cikin wata ƙatuwar muryarsa ta ƴan shaye_shaye ya ce "Haba haba, ki yi hanzarin tofar da yawunki domin ni bana taɓa yin aiki a samu matsala kuma bana son ana ambata mun ita a cikin aikina, yanzu nan yarana suka kira ni akan aiki ya kammala yanda ake so, yanzu ke kawai nake jira da cikon kuɗina." Wata doguwar ajiyar zuciya budurwa ta sauke ta sharce gumin dake goshinta ta ce "Baka da matsala Gaye indai kuɗi ne yanzu nan zaka ji alert har da ƙari ma akan wanda na ce zan baka." Gaye ya yi murmushi ya ce "Sai na jiki." Tare da kashe wayar. Wani tsalle budurwar ta yi ta faɗa kan gado tana ƙyalƙyala dariyar farin ciki da samun nasara. A fili ta fara faɗin "Ahmad dole yanzu hankalinka ya dawo gare ni tunda na rabaka da abun da yake hanaka kallon mata da sunan soyayya." Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya tare latsa wayarta domin turawa Gaye kuɗinsa.
Had’ad’d’en asibiti ne wanda daga gani babu tambaya na masu hannu da shuni ne, wata mata ce tsaye a Emergency ward tana kaiwa da komo wa tare da karanto duk addu’ar da ta zo bakinta cikin kuka, kallo ɗaya za kai mata ka fuskanci tana cikin tashin hankali ba kaɗan ba. A gefe guda kuma wata yarinya ce zaune akan kujerun dake gurin wadda ba za ta wuce shekara 15 ba, tana rufzar kuka da dukkan ƙarfinta. Wani Babban Mutum ne ya ƙaraso gurin tare da wasu mutane biye a bayansa, matar na ganinsa ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin, “Alhaji ba a gansu ba ko? Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, ya ALLAH ka bayyana mana yaran nan a raye ko a mace, Allah ka kare su da kariyarka a duk inda suke, Allah kasa suna hannu na gari, Allah ka dubi maraicinsu.” Sai kuma ta fashe da kuka abun gwanin ban tausayi. Ta ƙarasa inda mutumin yake ta riƙe hannunsa tana faɗin “Alhaji dan Allah ka taimake ni kasa a nemo yaran nan, ko dan mummunan halin da mahaifinsu yake ciki sanadiyyar ɓatansu, dan Allah Alhaji karna rasa ɗanaa.” Mutumin wanda ga dukkan alamu mijinta ne cikin lallami ya ce, “Police suna can suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun nemo yaran, kuma insha Allahu muna saran za a gansu, ki kwantar hankalinki kin ji.” D’ago da jajayen idanunta da suka ci kuka suka koshi ta yi tana duban sa ta ce “Ta yaya hankalina zai kwanta Abbansu, alhalin ga yarona can kwance rai a hannun Allah, jikokina kuma an neme su an rasa ka faɗa mun ta yaya hankalina zai kwanta!” Ta ƙarashe maganar cikin tsananin kuka. Mutumin ya sauke numfashi cikin ƙoƙarin ɓoye tasa damuwar ya ce “Allah yana sane da mu Fatima, kuma insha Allahu shi zai kawo mana mafita, ke dai kawai ki dage da addu’a.” Ta gyaɗa masa kai tare da sakin hannunsa ta zauna saboda jirin dake neman yar da ita, mutumin ya nufi gurin da yarinyar dake ta kuka take ya zauna tare da janyo ta jikinsa ya fara rarrashinta. Mutanen da suka zo tare da mutumin suka jinjina kai zuciyoyinsu cike da tausayin wannan ahali. Matar ta d’aga hannunta sama a fili take faɗin, “Ya Ubangiji na roƙe ka ka tashi kafaɗun AHMAD ɗina, ka bayyana masa yaransa da gaggawa a duk inda suke, Allah duk wanda yake da hannu a ɓatan yaran nan Allah ka tona asirinsa.” Gaba-d’aya mutanen wurin suka amsa da “Amin ya Allah.”………✍️