NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
2️⃣0️⃣
……….Bayan wasu mintuna wani likita ya fito daga ɗakin da Ahmad yake yana goge fuskarsa da handkerchief, Matar ta riga kowa mik’ewa tana faɗin “Doctor, ya ya jikin nasa?” Likitan ya sauke numfashi yana dubanta ya ce “I’m sorry to say Hajiya, just pray.” Bai jira amsarta ba ya juya ga Alhajin ya ce “Ka biyo ni office Alhaji.” Matar tana sheshshek’a ta ce “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, likita me kake nufi? Har yanzu kenan Ahmad be farfaɗo ba?” Alhaji ya dube ta ya ce “Ki zauna ki yi addu’a kamar yadda Doctor ya ce, zan je inji bayaninsa.” Matar ta gyaɗa kai tana salati ta koma ta zauna jagwab, yarinyarta ta matso kusa da ita tana sauke numfashi ta ce “Ummi, tunda har yanzu ba’a gansu ba ki kira gidan su Ammi ki sanar musu, ya kamata zuwa yanzu su ma su san halin da ake ciki.” Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Tun d’azu naso kiran su Zahra, Abbanku ne ya hana ya ce kar a tayar musu da hankali a bari aga abun da hali zai yi, amma yanzu tunda ba a gansu bari na kira Yaseer na faɗa masa, kin san Ammin tana da hawan jini yanzu in ta ji sai ya tashi, amma shi Yaseer ɗin ya san ta yanda zai faɗa mata hankalinta ba zai tashi ba sosai.” Zahra ta gyaɗa mata kai kawai cikin sanyin jiki.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
KANO
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Jiki a sanyaye su Mama suka kwantar da yaran a wani ɗaki dake part ɗin Daddy, sosai al’amarin yaran ya girgiza kwanyar Mama, tafi 5 minutes tana kallon yaran kafin ta sauke numfashi ta juya ta fita bayan ta lullub’a musu bargo, Haneefah dama suna kwantar da yaran ta fice. A falo suka ci karo da Aunty Sadiya da Aunty A’isha. Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce “Ya Fatima kin ga Neehal ɗin?” Mama ta ce “Eh, ashe gida ta dawo wai kanta na ciwo.” Aunty A’isha ta ce “Ayya, hayaniya ce Allah ya sauwaaqe.” Aunty Sadiya dake kallon Mama ta ce “Lafiya kuwa na ganki wani iri?” Mama ta sauke numfashi ta ce “Ina fa lafiya Sadiya.” A rude Aunty Sadiya ta ce “Me ya faru?” Mama ta ce “Ku zauna maganar ba ta tsaye ba ce.” Sosai Aunty A’isha da Aunty Sadiya suka jimanta al’amarin, zargika kala_kala suka yi akan yarda yaran da akay, Mama ta ce “Sanin gaibu sai Allah.” Ɗakin da yaran suke suka shiga suka gan su, Amma Mama ta roƙe su a kan kar su sanar da kowa hatta da Hajiya kuwa. Bayan Neehal ta idar da Sallah ta ɗauko wayarta ta kira Sadik, rejected yay kamar ko da yaushe sannan ya kira ta. Tana d’agawa ta ce “I’m sorry Ya Sadik Please.” Sadik ya kwaikwayi yanda take magana ya ce “Um um, ba zan yi sorry’n ba.” Neehal ta yi murmushi me sauti jin yanda ya yi ta ce “Haba Yayanah na kaina, idan baka hakura ba kuka fa zan yi.” Ta ƙarashe maganar cikin shagwab’a. Sadik ya sauke numfashi ya ce “Shikenan komai ya wuce dear, amma ina kika shiga?” Neehal ta ce “Kaina ke ciwo shi yasa.” Cikin tausayawa Sadik ya ce “Subhallah, sannu Allah ya sauqaqe, amma dai kin sha magani ko?” Neehal ta ce “Yanzu dai zan sha.” Sun taɓa hira kaɗan suka yi sallama, saboda ta samu ta sha magani ta kwanta ta huta.
Hameedah ce zaune ta ɗora kanta akan cinyar mahaifiyarta tana kuka ƙasa_ƙasa, ganin tabbas ta rasa Ameen tunda gobe zai angonce da wata. Mumy wadda ta gaji da rarrashi tun a gurin bikin ta ce “Wai Hameedah meke damunki ne? so kike har sai mutane sun fuskanci halin da kike ciki, masu dariya su yi miki suna Allah ya ƙara, na ce miki daure zuciyarki za ki yi ki nuna kamar baki damu ba, a yi bikin nan a gama.” Hameedah ta d’ago kanta cikin sheshshek’a ta ce “Mumy na yi iya yina nayi ƙoƙarin hakan amma na kasa, wallahi Mumy ba ki ji yanda nake ji a cikin zuciyata ba kamar ana rura mun garwashin wuta.” Mumy ta ce “Na san abun da ciwo, kuma nima ina jin yanda kike ji, amma ki daure dai, na faɗa miki ko mai daren daɗe wa sai kin auri Ameen in dai da bokaye a cikin duniyar nan, yanzu dai ki share hawayenki in faɗa miki wani abu kin ji My daughter.” Hameedah ta gayd’a mata kai ta fara share hawayen nata.
Misalin ƙarfe 12:30 na dare Ameen ne zaune a falon Daddy shi da Mama da ta kira shi, ya tattara duka hankalinsa yana sauraren abun da zata faɗa masa. Mama ta ce “Dama d’azu kai ka tsayar da Neehal?” Ya ce “Eh.” Mama ta ce “Akan wanne dalili?” Ya yi shiru, Mama ta ce “Ka yi shiru ina maka mgn.” Ya ce “Babu komai Mama.” Mama ta girgiza kai ta ce “To me ne dalilin da yasa ka bata kayan data saka? bayan ga wanda suka ɗinka za su saka ita ƴan’uwanta.” Ameen ya ce “Mama wai dama wannan shine kiran da kika mun? wallahi na ɗauka wani babban abunne ya faru.” Mama ta harare shi ta ce “Ban sani ba.” Shigowar Neehal falon ya hana Ameen faɗar abun da zai faɗa. “Ke kuma daga ina?” Mama ta tambayi Neehal tana kallonta, Neehal ta turo baki gaba ta ce “Bacci zan yi a nan saboda ina son na kwana tare da yaran.” Mama ta nuna mata dakin da suke da hannu tana faɗin “Suna nan, zaki wani kwaso jiki a daren nan ki taho kamar da tare da su kike kwana.” Neehal ba ta ce komai ba ta shige, Ameen da ya bita da kallo har ta shige dakin sannan ya dubi Mama ya ce “Wanne Yara ne kuke magana akansu.” Mama kamar ta share ta ƙi faɗa masa sai kuma dai ta sanar masa, don abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Shima ya girgiza da lamarin, amma dai ya ce wa Mama da safe sai akai yaran gidan Radios da Televisions a bada cikiyarsu ko za a dace a samu iyayensu. Mama ta yi na’am da shawarar shi. Neehal ta daɗe kafin bacci ya ɗauke ta, tana ta aikin kallon yaran, tana jin ƙaunar su na mamaye mata zuciya.
Washegari da safe Neehal tana tattare ɗaki Yarinya ɗaya ta tashi tana kiran sunan Daddy, Neehal ta ajiye tsintsiyar hannunta ta ƙarasa gadon ta d’ago ta tana faɗin “Kin tashi, mu je ki yi fitsari to.” Yarinyar dake binta da kallo ta gyaɗa mata kai. Bayan ta yi fitsarin Neehal ta wanke mata baki da fuska suka fito, suna fitowa ta ga itama ɗayar ta tashi zaune tana ta mutsitsika ido, Neehal ta kama ta itama ta kaita toilet, Bayan sun fito ta kalle su ta ce “What is your names?” Wadda tafi surutu ta ce “Afrah, amma Daddy yana ce mun Princess, a lesson da islamiyya kuma FATIMA AHMAD.” Neehal ta jinjina kai ta ce “Nice name Darling.” Sannan ta juya ta kalli Ɗayar ta ce “Ke fa.” Yarinyar ta ce “Amrah, amma Daddy yana ce mun Jewel a lesson da islamiyya kuma AISHA AHMAD.” Neehal ta Jinjina kai tana murmushi ta ce “Nice name sweetheart.” Afrah ta ce “Aunty safiyar ta yi zaki kai mu gurin Daddy ko?” Neehal ta gyaɗa mata kai zuciyarta cike da k’aunar yaran. Mama ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da tea flaks da ƙananun cups, yaran suka bita da kallo kafin su haɗa baki a tare su ce “Ina kwana.” Mama ta ajiye kayan hannunta tare da amsa musu, ta ƙaraso ta shafa kansu da cike da kaunarsu, dan yaran sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba, musamman da suka gaishe ta, ga dukkan alamu daga gidan tarbiyya suke. Mama ta dubi Neehal ta ce “Ɗauko musu kayansu a saka musu, bari na haɗa musu breakfast su yi.” Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, yaran suka bita da kallo kamar za su bita. Bayan sun yi breakfast Neehal ta musu wanka ta shirya su cikin rigunansu na jiya. Kasancewar yau ne d’aurin Aure yasa gidan ya ƙara cika da baƙi mata da maza, duk inda Neehal ta ɗora k’afarta su Afrah na biye da ita a baya, duk wanda ya tambaye ta yaran waye sai ta ce na wata Friend ɗinta ne. Ɗaya daga cikin sojojin gidan ta bawa kuɗi ya siyo wa musu kayan sakawa da takalma da panties, kafin Azhar ya kawo mata ta shirya su tsaf suka yi kyau sosai. kowa so yake ya ɗauke su ko ya musu hoto, amma yaran sun ƙi yarda da kowa sai Neehal, saboda ganin taron jama’a, ita kuwa ta cika su da kayan zaƙi dangin su chocolate da sweet suna ta sha. Mama kanta ya ɗau caji tana da hidima da mutane, hakan ya sa ba ta bi takan zancen yaran ba, dama kuma da taywa Daddy maganar su ya ce a bari bayan biki sai a san abun yi. Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura Auren AL’AMIN MUHAMMAD TAFIDA da amaryarsa HAFSAT AHMAD ƊAN GASKE. Anan babban masallacin Juma’a dake cikin Narasawa G.R.A. Yau ma Neehal ta yi kyau sosai, shadda ta saka da safe Wadda aka mata akai mai kyawun gaske, ta kafa ɗaurinta. Su Afrah sai faɗin “Kin yi kyau Aunty.” suke, Murmushi Neehal take idan suka faɗi haka. Ta ce musu “Thank you Dearies.” Wajen ƙarfe uku Sadik ya ƙaraso gidan. Neehal ta fito tare da twins ɗinta, tunda ta fito ya ƙura mata ganin irin kyawun da ta yi. Neehal ta gaishe shi ya amsa yana kallon yaran, Neehal ta ce “Ya su Maamah da Abba?” Sadik ya ce “Suna Lafiya, Ya taro?” Neehal ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce “Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya, saura naki kuma.” Neehal ta yi murmushi ta ce “Yau har na gaji da jin wannan furucin, kowa muka haɗu sai ya ce sai mun zo naki kuma.” Sadik ya ce “To ai gaskiya ne, gwara Mama ta aurar dake ta huta da rigimarki.” Neehal ta ce “hmmm.” Kawai, Sadik yace “Wannan cutes babies ɗin fa?” Neehal ta ce “Yaran wata Friend ɗina ne.” Sadik ya ce “Masha Allah, Allah ya raya su.” Neehal ta ce “Ameen.” Tare da dubansu ta ce “Ba ku gaida Uncle ba.” Amrah ce ta fara gaishe shi da faɗin “Ina kwana.” Sannan itama Afrah ta gaishe shi, ya kama hannunsu tare da amsa musu. Bai wani jima ba ya tafi saboda Ameerah data zo kiran Neehal. Suna tafiya Ameerah ta ce “Amma Yaa Neehal wannan saurayinki ne?” Neehal ta girgiza kai tare da faɗin “Ko ɗaya, he is just Friend.” Ameerah ta yi shiru amma ba dan ta yarda ba. Ƙarfe huɗu aka tafi gurin da za ai Mother’s Day, sai bayan magriba aka tashi. Yau kam amarya ba ta zo ba, tana gida suna nasu suma, shima Ameen ɗin bai je ba, hakan yasa yau kwata_kwata ba su haɗu da Neehal ba. Twins kam ganin hada_hadar mutane yasa ba su ƙara takurawa Neehal akan ta kai su gurin Daddy’nsu ba, sai da suka zo bacci nema suka so yi mata rigima ta lallaɓawa su da faɗin sai an gama biki zata kai su. Washegari ma anyi taro a gida inda akai kidan ƙwarya manyan mata suka cashe, tun kafin Azhar aka fara har bayan la’asar ana yi. Yau za a miƙa Amarya gidan angonta, misalin ƙarfe biyar na yamma Neehal dake jin duk jikinta a sanyaye ba tare da tasan dalili ba ta barwa Haneefah twins ta nufi part ɗin Ameen…………✍️