NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
2️⃣1️⃣
……….A hankali ta buɗe ƙofar falonsa ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, kanta na ƙasa ba ta yarda ta d’ago ba saboda falon cike yake da abokanansa. Suka amsa mata suna binta da kallo, Salman ganin yanda ta takure a tsaye ya dube ta ya ce “Shiga mana Neehal, yana ciki ai.” Neehal ta ce “Toh.” Tare da gaishe su a lokaci ɗaya, ba ta jira amsarsu ba ta wuce. Wani a cikinsu da ya bita da kallo ya ce “Salman, wannan kamar ƴar jaridar nan ta ASTV?” Salman ya ce ba kama ba ce ita ce.” Ya ce “Wow yarinyar me kyau tana burge ni wlh.” Kafin ya ce wani abu ya ji wani a cikinsu yana faɗin “Ita ce wadda suka zo tare da Al’ameen ranar dinner ai, dama ƙanwarsa ce?” Salman ya ce “Yeah.” Wanda ya fara magana da farko ya ce “To ai ni ranar na ɗauka ita ce ma Amaryar saboda ta yi kyau sosai har ma tafi Amarya…..” Haka dai sukaita magana akan Neehal.
A hankali take knocking ƙofar bedroom ɗinsa kamar me tsaron wani abu, Ameen dake shiryawa a gaban mudubi don bai jima da fitowa daga wanka ba ya ɗan yamutsa fuska ya ce “Waye?” Neehal tay shiru yanayin da take jin jikinta da zuciyarta na ƙara tsananta, Ameen ya taho ya buɗe ƙofar zuciyarsa cike da masifa, a tunaninsa a cikin abokansa ne wani ya zo zai ƙara masa ciwon kai akan wanda suka sa masa d’azu. Cike da mamaki yake kallonta, kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Ameen ya koma ciki yana faɗin “Come in.” Neehal ta shiga kamar munafuka ta zauna a gefen gado, yana fesa turare ya ce “What happened.” Ganin ta ƙi cewa komai tunda ta shigo. A hankali ta d’ago ta kalle shi amma yanda ba za su haɗa ido ba ta ce “Yaya…” Sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zuba daga idonta, Ameen ya sauke numfashi sannan ya dawo kusa da ita ya zauna ya kama hannunta murya ƙasa_ƙasa ya ce “Tell me what happened?” Neehal ta share hawayenta ba ta ce komai ba, Ameen ya ƙura mata ido domin yasan dalilin kukanta a hankali ya ce “Kin fara missing Yayanki ko?” Neehal ta d’aga masa kai da sauri sannan ta ce “Shikenan Yaya na dena ganinka every weekend?” Ameen ya girgiza mata kai tare da faɗin “Wa ya faɗa miki? Zan dinga zuwa kodayaushe.” Neehal ta ce “Na san baza ka zo ba tunda ka yi aure.” Ameen ya ce “Dolena ma inzo inga my Mum da little sis ɗina.” Neehal ta ce “Dagaske?” Ya d’ago kanta ya saka idanunsa a cikin nata yana mata wani kallo ya gyaɗa mata kai, Neehal ta kumshe idanta da sauri gabanta na fad’uwa. Ameen ya sakar mata fuska yana sauke numfashi, tashi ya yi ya ɗauko wayarsa ya shiga gallery ya miƙa mata, ta karb’a tana dubawa. Waro idanta ta yi tana murmushi ta ce “Wow Yaya pics ɗin sun yi kyau sosai.” Ya yi murmushi kawai yana kallonta, ita kuma ta cigaba da kallon hotunan. Pictures ɗinsu ne wanda aka musu ranar dinner ita da shi, wani suna zaune wani kuma a tsaye lokacin da ta je yi musu lik’i, sosai hotunan sukai kyau, kuma babu ta yanda za’ai ka gani ka ce ba Neehal ce amaryar ba. Ta ajiye masa wayar bayan ta gama ta gani tare da mik’ewa ta ce “Yaya Bari in koma.” Ameen ya mata wani kallo ya ce “Ba za ki raka ni gidan Amaryata ba?” Neehal ta waro Ido ta ce “Ni kuma Yaya? ga Freinds ɗinka nan.” Ya kau da zancen da faɗin “Ina new kids ɗinki?” Neehal ta ce “Suwa?” Ya ce “Twins.” Neehal ta ce “Oh, suna gurin Haneefah.” Ya ce “Me yasa ba ki zo mun da su ba?” Ta ce “Na ga baka son hayaniya ne kar su dame ka.” Ameen ya ce “Ok, me kike so in baki a ɗakin nan?” Neehal ta hau juya ido a ɗakin ganin babu abun da zata buƙata a ɗakin, ta ce “Nothing.” Ya ce “Sure?” Ta gyaɗa masa kai, sai kuma ta kalli kan mudubi ta ɗan shagwab’e fuska ta ce “Na tuno, your perfumes.” Ya ce “Ai is only for male.” Ta turo baki gaba ta ce “Ai ba ajikina zan dinga sawa ba, kawai zan dinga jin k’amshin ina tunawa da kai.” Ameen yay murmushi ya buɗe wata jaka ya ɗauko mata turaruka kala uku ya bata, Neehal ta karb’a da murnarta ta ce “Thank you so much.”
Tare suka fito daga ɗakin, Neehal ta fice shi kuma ya zauna yana haɗe rai dan kar su cigaba da tsokanarsa, aikwa kamar ma ya ce su yi suka fara, daga baya kuma suka koma zancen Neehal kowa yana faɗin yana kamu. Shi dai ko kanzil bai ce musu ba. Neehal tana koma Haneefah ta miƙa mata su Afrah da suke ƙoƙarin saka kuka ganin shiru_shiru ba su ga Neehal ɗin ba, Neehal ta kama hannunsu suka shiga ɗakinta, ta adana turarukan. Bayan Magriba aka tafi ɗaukar Amarya, su Neehal kam ba a je da su ba, Mama ta ce sa je daga baya. Bayan isha’i mutane suka fara watsewa, gidan ya rage daga su Aunty Sadiya sai na nesa waɗanda za su tafi gobe da safe, Hameedah ma da Mamanta suna nan. Sai yau Mamansu Anwar ta zo ita da k’annenshi, ba ta jin dad’i ne shi yasa tunda aka fara bikin ba ta zo ba. Neehal dai tana kwance a ɗakin Mama tana ta matsar kwalla, Twins na manne a jikinta suna cin Cheese, tunda ta idar da Sallah ta haye gadon tay kwanciyarta. Hajiya ce ta shigo ɗakin tana ƴan mitocinta da ba ta rabo da su, kallon Neehal ta yi ta ce “Ke kuma lafiya kike kwance?” Neehal tay mata shiru, ta tab’e baki ta ce “Wai waɗannan Yaran ina uwarsu ne?” Daidai nan Mama ta shigo ɗakin, Hajiya ta ce “Yawwa, Ta Abuja (Da yake haka take ce mata idan fulatancin ya motso mata) yanzu nake tambayar wannan uwar langwan ta mun shiru, waɗannan Yaran waye ne haka, take ta wahala da su?” Kafin Mama ta ce wani abu Neehal ta juyo da sauri idanunta da guntun hawaye ta ce “Ƴaƴan ƙawata ne, ba ta da lafiya ba ta samu zuwa ba shine ta aiko aka kawo mun su.” Mama ta kalle ta kawai, Hajiya ta ce “Ayyo, ga su kuwa kyawawa kamar Ƴaƴan Turai.” Mama dake kallon Neehal ta ce “Kukan me kike?” Kafin ta yi magana Afrah ta yi karaf ta ce “Ba ta da lafiya.” Da yake haka Neehal ɗin ta ce musu da suka dame ta da tambaya ganin tana kuka. Mama ta ce “Allah ya sauwaqe.” Ta juya ta fice. Hajiya ta ce “Sannu gajiyar biki ce.” Ciki_ciki Neehal ta ce “Yawwa.” Hajiya ta fara yiwa su Afrah surutu da tambayoyi kamar wasu manya, su dai shiru kawai suka yi suna kallonta tare da ƙara lafewa a jikin Neehal, ta gaji ta tashi ta fita.
Da daddare wajen 12 Mama suna zaune ita matar Yayan Daddy da Hajiya dake ta gyangyad’i, ance ta koma ɗaki ta ƙi. Neehal ce ta fito daga ɗakin Mama wadda bacci ya ɗauke ta bayan ta gama shan kukanta, yanzu ma Amrah ce ta tashe ta, idanunta kuwa har sun kumbura. Mama ta bita da kallo kafin ta ce “Wai lafiyarki kuwa Neehal, me aka miki kike kuka?” Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Mama ta ce “Ba na son halin kin nan fa, ana miki magana kina ji ki yi shiru.” Neehal ta ce “Ba komai kawai dai..” sai kuma ta yi shiru, Mama ta ce “Kawai dai me?” Neehal ta ce “I start missing Yaya.” Mama ta tab’e baki ta ce “Shine kuma zaki zauna kina kuka, kamar wanda ya mutu, ko ce miki aka yi ya tafi kenan?” Neehal ta ce “To ai ba zai dinga zuwa kodayaushe ba.” Mama ta ce “So you can follow him ai, tunda tare aka haife ku.” Matar Yayan Dad wadda ake kira da Umma ta ce “Ai da gaskiyarta dole ta yi kewar ɗan’uwanta.” Hajiya data wartsake tun fitowar Neehal ta ja tsaki ta ce “Wai dama akan Ameen kike asarar hawayenki saboda baki san ciwon kanki ba, Ameen ɗin da ba wani k’aunarki yake ba, ai daɗi ma ya kamata ki ji yanzu zaki wataya babu mai ƙara takura miki a gidan nan, kafin kema Allah ya kawo miki miji ki tafi.” Neehal ta turo baki gaba ta nufi kitchen dan haɗawa Amrah tea.