NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Washegari tun safe sauran baƙi suka tafi, su Aunty Sadiya ma suna gama gyaran gidan kafin Azhar suka wuce nasu gidajen, Hajiya ma ta bi Ammin Amirah sun wuce Gombe. Gida ya rage daga Mama da Neehal sai su Dije masu aiki da Twins, sai Hameedah da Mom ɗinta da Umma wanda suma da Yamma za su wuce Abuja. Driver Mama ta aika ya kaiwa su Ameen breakfast, da rana ma haka. Neehal kam wuni ta yi a ɗaki ita da Twins ɗinta. Sai can yamma Haneefah ta zo gidan. Da daddare bayan kowa ya tafi Mama ta je part ɗin Dad su yi magana akan su Afrah, Mama tana duban shi ta ce. “Daddy yanzu sai mu san abun yi akan yaran nan, dan yanzu na san duk inda hankalin iyayensu yake a tashe yake ba kaɗan ba.” Daddy ya ce “Hakane, tunda gobe Monday idan Neehal zata aiki sai mu tafi tare mu bada a yi cikiyar iyayensu, na san Insha Allahu za’a samu iyayen nasu ko a’ina suke a ƙasar nan, tunda babu inda ba’a kallon ASTV, daga nan sai mu biya wasu gidan Radios ɗin duk mu bada cikiya. Mama ta ce “Allah ya kai mu goben lafiya. Dad ya ce “Ameen, kira mun Neehal ɗin ma tunda aka fara biki haɗuwar mu ta yi wuya.” Mama ta ce “Kuma a part ɗin nan take kwana, dan dai ana sha’anin biki ne.” Mama ta kira Neehal a waya ta ce ta zo part ɗin Daddy. Ba jimawa ta ƙaraso tare da Twins. Mama ta ce mata “Kai Neehal kina cika wa yaran nan kayan zaƙi, duk sanda zan gansu da sweet ko chocolate a hannunsa.” Neehal ta yi Murmushi tare da zama a kusa da Daddy. Ta gaida Daddy suma su Afrah suka gaishe shi, ya amsa musu cike da fara’a. Sun ɗan taɓa hira da Daddy har su Afrah suka fara bacci. Mama ta dubi Neehal ta ce “Gobe za mu je mu yi report akan yaran nan, daga nan mu biya mu ba da cikiyar iyayensu.” Gaban Neehal ya faɗi, dan bata k’aunar abun da zai rabata da yaran ko na second ɗaya, ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama data kula da yanayinta na canzawar da fuskarta ta yi ta ce “Sai ki shirya da wuri, dan ke zaki yi bayanin yanda kika tsince su.” Neehal da idanunta suka ciko da k’walla ta ce “Mama gobe ya yi wuri a bari a ƙara wasu kwanaki sai a….” Kallon da Mama ta watsa mata yasa ta had’iye maganarta. Mama ta ce “Kina cikin hankalinki kuwa? Yanzu kin san irin tashin hankalin da iyayensu suke ciki na rashinsu har na kwana biyu ba su san inda suke ba.” Neehal ta ce “To ni Mama ban san rabuwa da su.” Mama ta ce “Uhm, ke da kika same su sama ta ka kenan, kuma dudu kwana biyu kawai kuka yi tare, amma ba kyasan rabuwa da su, balle kuma mahaifiyarsu da ta haife su ta raine su na shekaru.” Neehal ta ce “Ai ba su da Uwa, ta rasu.” Mama ta ce “Who told you?” Neehal ta ce “Su ne, suka ce mun Daddy’nsu yace their Mom ta tafi ba za ta dawo ba for ever.” Mama ta ce “Allah ya ji k’anta, amma ai suna da Uba da dangi ko?” Neehal ta yi shiru ba ce komai ba sai hawaye take. Daddy dake kallon su Ya ce “Daughter me yasa bakya son su tafi?” Neehal ta ce “Dad I love them and kuma bana son na rabu da su, na ji ina son su sosai, kuma ga su marayu ina tausayin Maraya sosai because…..” Mama ta katse ta da faɗin “Shut up, Stupid, komai za ki ce yara dai sai an maida su gurin iyayensu, duk yanda kike son su ba ki kai iyayensu ba.” Tana gama faɗar haka ta mik’e ta shige bedroom ɗin Daddy. Dad ya rarrashi Neehal ta bar kukan da take sannan ya rakata part ɗin Mama da Afrah a hannunsa, ita kuma ta ɗau Amrah. Ko wanka ba ta yi ba ta kwanta rungume da yaran gam a jikinta kamar wanda za’a k’wace mata su……….✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:43] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
2️⃣3️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills
Whatsapp OR Call 08066268951
……….Cikin ƴan mintuna suka ƙarasa gidan Ameen dake Lamido Cresent. Driver ya danna horn mai gadi Ya zo ya buɗe masa madaidaicin gate ɗin gidan, tun daga farfajiyar gidan zaka tabbatar da gidan ya haɗu gami da tsaruwa. Bayan ya yi parking Neehal ta fito Twins suka biyo bayanta, sallama suka yi da driver sannan ta nufi inda take hango ƙofar shiga ainihin cikin gidan, Mota ɗaya ta gani a harabar gidan, hakan yasa take tunanin da ƙyar in Ameen yana gidan. Hafsah tana ɗakinta a kwance ta ji ƙarar door beil, a tunaninta Ameen ne ya dawo daga masallaci hakan ya sata tashi da sauri ta fito ta sakko ƙasa ta buɗe ƙofar falon. Kamar a mafarki ta ga Neehal tsaye a bakin ƙofa, haɗe rai ta yi sosai kamar ba ta taɓa dariya ba ta shiga ƙarewa Neehal kallo, wadda ke sanye cikin doguwar riga pink colour, an mata ado da blue color, rigar ta ci guga har wani ɗaukar ido take, ta yi sosai kamar ka sace ta. Neehal ta danne zuciyarta tana murmushi ta ce “Sannu da gida Aunty Amarya.” Ƙara haɗe rai Hafsat ta yi ta ce “Yawwa.” Sannan ta juya ta koma ciki, Neehal ta shiga Falon bakinta ɗauke da Sallama Twins na biye da ita, suna ta murna sun zo unguwa. Kan kujera suka yi da gudu suka haye, Hafsah ta dube su kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa. Amrah ta dubi Hafsah ta ce “Ina kwana.” Kafin ta gama rufe baki Afrah ma ta gaishe ta, ta amsa musu tana bin su da kallo. Neehal ta ƙaraso cikin falon ta zauna jikinta a sanyaye, a hankali ta ce “Ina yini Aunty.” Hafsah kamar an mata dole ta ce “Lafiya.” Daga haka ta wuce warta sama. Neehal ta bi ta da kallo duk murna da dokin zuwan da take ya koma ciki, gaba-d’aya ta ji dama ba ta zo ba, kamar ta tashi ta koma gida haka take ji, amma ta daure saboda idan ta koma gida ba ta san me zata cewa Mama ya dawo da ita ba. Falon ta shiga ƙarewa kallo, babu ƙarya falon ya haɗu, domin kuwa an narkawa Hafsah kaya. Komai dake cikin falon Dark and light purple colour ne. Neehal ta ɗauko wayarta daga cikin handbag ɗinta ta kira layin Haneefah ta sanar mata ta je gidan Ameen yau amma Haneefan ba ta ɗauka ba. Su Afrah kuwa tsalle_tsalle suka hau yi a falon, Neehal ta musu mgn su bari, ta nuna musu kusa da ita ta ce su dawo su zauna. Suka dawo suka zauna suna turo baki gaba. Har mintuna goma suka wuce Hafsah ba ta dawo gurinsu Neehal ba, kamar ma ba baƙi ta yi ba ta koma ta yi kwanciyarta. Afrah da ta gaji zama ta dubi Neehal ta ce “Aunty bari na kira Aunty’n data hau sama.” Neehal ta ce “Ban aike ki ba.” Yarinyar ta ɓata fuska. Neehal ta bi ƙasan Falon da kallo, tiles ɗin ta gani kamar da datti. A hankali ta tashi ta shiga duba falon ko za ta ga tsintsiya, a bakin ƙofa ta ganta tare da mopper, ɗauka ta yi ta shiga share falon, bayan ta gama ta yi mopping ɗin shi, tana cikin yi Hafsah ta sakko, da mamaki take duban Neehal, can kuma ta tab’e baki ta ce “Ina kika samu ruwan da kike mopping?” Toilet ɗin dake falon Neehal ta nuna mata da hannunta ba tare da ta yi magana ba, Hafsat ta wuce kitchen tana tab’e baki. Amrah ta dubi Neehal ta ce “Aunty zan ci abinci.” Neehal ta mata shiru, har sai da yarinyar ta ƙara maimaita mata sannan ta ce “Ba ki ci abinci ba ne a gida?” Amrah ta gyaɗa mata kai tana keɓe fuska, Neehal ta yi shiru kawai dan bata san me zata ce mata ba. Hafsah ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da lemo ta ajiye a gaban yaran, ta dubi Neehal a yatsine ta ce ki shiga kitchen ki dafa muku abin da zaku ci. Neehal ta mata wani kallo sannan ta ce “Toh.” a ranta tana faɗin ‘Ai ba yunwa na ce miki ina ji ba.’ Daga haka Hafsah ta koma sama, ashe Ameen ne ya mata waya yana hanya shi yasa ta yi sauri ta sakko ta kawo wa su Neehal drinks dan kar ya dawo ya ga bata basu ba. Bayan Neehal ta gama mopping ɗin ta koma ta zauna tana duban su Afrah dake shan lemo, Hafsah ta ƙara sakkowa hannunta ɗauke plate ta ajiye a gaban Neehal, A hankali Neehal ta ce “Thank you.” Hafsat ba ta ce komai ba ta juya ta koma sama. Cake ne da cin_cin da Donot a cikin plate ɗin, Neehal ta ce su Amrah su sakko su ci, ita kuwa ko kallon snacks ɗin bata ƙara yi ba. Su ma kaɗan suka ci suka ce sun k’oshi. Neehal ta duba time a wayarta ta ga uku saura, lumshe idonta ta yi ta kwanta akan kujera tana jin cikinta na juya mata, zuciyarta kuwa cike take da mamakin dalilin ya sa Hafsah ba ta k’aunarta, dan ita ba ta taɓa tunanin irin wannan tarb’ar daga gare ta ba, yanda tasan amare idan ka je gidajensu kamar su mai da mutum ciki dan murna amma….. Ƙarar buɗe ƙofar falon ya katse mata tunanin da take. Da Sallama ya shigo falon duk da be yi tunanin da mutane a ciki ba, dan yasan Hafsah ba ta zaman ƙasa. Waro ido ya yi ganin Twins fuskarsa na nuna mamakinsa na ganinsu. Su ma suna ganinshi suka nufe shi da gudu suna faɗin “Uncle !.” Dan ɗan zuwan da Ameen yake gida sun saba da shi. Ameen ya d’aga su ɗaya bayan ɗaya ya shilla yana murmushi, yaran suka shiga ƙyalƙyala dariya sannan suka gaishe shi, ya amsa musu cikin kulawa. Afrah ta ce “Uncle nan gidanka ne?” Ameen ya mata murmushi tare da gyaɗa mata kai. Neehal wadda ta tashi zaune tun shigowar shi, cikin boye ɓacin ran Hafsah da dauriyar ciwon cikin da take ji ta ce “Sannu da zuwa Yaya.” Ameen ya zauna a gefen ta yana kallonta cikin nazarta yanayinta ya ce “Yawwa.” Neehal ta yi ƙasa da kanta ganin yana binta da wani irin kallo, a sanyaye ta ce “Ina yini.” Ya amsa da “Lafiya k’alau, ya aiki?” Neehal ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce “Ina Haneefah fa, kika zo ke kaɗai?” ta ce “Tana Abuja ta je gidan Yayan Abbansu sai Sunday zata dawo.” Ameen ya gyaɗa kai tare da bin falon da kallo, sai kuma ya dawo da dubansa ga Neehal ya ce “Ina matar gidan?” Neehal ta ce “Yanzu ta hau sama.” Ameen ya miƙe hannayensa riƙe dana Twins suka hau saman, Neehal ta bi su da kallo tare da jan numfashi. Duk murna da d’okin ganin Yayan nata da take takaicin Hafsat ya sa ta ma dena. Ko minti biyar Ameen be yi da hawa saman ba suka sakko tare da Hafsah, wadda ta faɗaɗa fara’a akan fuskarta. Tana duban Neehal ta ce “Sister na bar ki ke kaɗai ko? Sorry toilet na shiga ne.” Mamakin Hafsat ne ya kusa kashe Neehal, shanye mamakinta ta yi ta kirkiro murmushi ta ce “Ba komai Aunty.” Hafsah ta dubi Ameen da ya zauna yana kallonsu ta ce “Honey Ka ga hira da Sister ta ɗauke mun hankali ko girki ban daura ba, duk da ma na tambaye ta mai za su ci ta ƙi faɗa mun, na ce kuma ta shiga ta girka da kanta ta ƙi, sai ka ce wata bakuwa.” Ameen yana duban Neehal ya ce “Why?” Neehal ta ce “Yaya mun ci fa snacks mun k’oshi.” Ameen ya ce “Snacks ai ba abinci ba ne, ki shiga kitchen ki dafa muku abun da zaku ci.” Neehal ba za ta iya musu da Yayan nata ba, hakan yasa ta miƙe ta nufi kitchen ɗin.” Hafsah na murmushi ta ce “Ko ke fa yar ƙanwata, amma da kin ƙi sakin jiki kamar wata baquwa.” Neehal dai bata yanka mata ba ta shige kitchen zuciyarta cike da mamakin kissa irin ta Hafsah. Duk da bata jin dadi haka ta dafa musu jallop ɗin sphagetti, kafin ta gama an shiga sallar Asr, hakan yasa da ta gama ta juye a warmer sannan ta dawo falon, Twins ne kawai a falon suna kallon cartoon ɗin da Ameen ya kunna musu, Ameen ya fita Masallaci ita kuma Hafsat tana sama. Ɗakin dake falon Neehal ta shiga ta yi Sallah, bayan ta idar ta fito falo ta tarar har Ameen ya dawo, Hafsah ma ta sakko. “Sannu da aiki my sister, Allah ya saka da Alkhairi ya baki miji na gari, bari na je na ga me aka girka mana haka ne, duk muna nan k’amshi ya buɗaɗe mu yawun mu sai tsinkewa yake.” Hafsah ta faɗi haka cikin iyayi tana murmushin da be kai zuci ba. Neehal ta yi ɗan murmusa kawai, dan mgn ma bata son yi saboda yanda take jin cikinta. Hafsah ta miƙe ta shiga kitchen ɗin, ɗauko warmer ta yi gaba-d’aya tare da plates da pork ta ajiye akan dinning, sannan ta ɗauko drinks shima ta aje. Ta dube su duka ta ce “Ku taso mu ci abincin.” Neehal dai kamar ta ce ta k’oshi, amma ta san ko ta faɗa Ameen ba kyale ta ze yi ba sai ta ci, hakan yasa ta miƙe tana taune lips d’inta ta nufi dinning ɗin. Ameen dai kallonta kawai yake amma ya gane akwai abun da ke damunta. Duban Hafsah ya yi ya ce “Ku ci kawai am full.” A karamin plate Hafsah ta zuba wa Twins na su abincin ta ajiye musu ƙasan carpet ɗin dake tsakiyar falon. Da kanta ta zuba wa Neehal abincin sannan ta zuba nata itama, ba kunya ta shiga durawa cikinta taliyar dan ta mata daɗi ba kaɗan ba. Neehal ta kasa cin abincin sai juya pork ɗin take a cikin taliyar, har taliyar ta fara sanyi. Da ƙyar dai ta daure ta tsakura ta kai bakinta, a hankali ta shiga taunawa cikin nutsuwa, Hafsat kuwa tana zuba lauma tana harararta a fakaice. Cokali uku Neehal ta ci ta ajiye pork ɗin da sauri saboda murd’awar da cikinta ya mata, dafe cikin ta yi tare da taune lips ɗinta sosai, duk yanda taso daurewa amma ta kasa, Ameen dake latsa wayarsa amma hankalinsa gaba-d’aya yana kanta ya ce “What happened?” Hafsah cikin nuna damuwa itama ta ce “Sister me ya faru?” Neehal cikin sanyi ta ce “Cikina.” Ameen ya miƙe da sauri ya ƙaraso dinning ɗin yana mata sannu, miƙewa ta yi ta nufi toilet ɗin dake falon da gudu ta fara kela amai. A rude Ameen yake faɗin “Sannu, Sorry, dama ba ki da lafiya?” Neehal dai bata samu damar ba shi amsa ba, bayan ta gama ya taimaka mata ta fito tana numfarfashi ta kwanta a ƙasa, Twins suka bita da kallo. Sai da ya tsaftace toilet ɗin sannan ya fito, sai a sannan Hafsah ta yiwa Neehal sannu, tana pretending kamar ta damu, nan kwa a zuciyarta ji take kamar ta ƙarasa ta dan tsanar da take mata. Neehal ta fara nuk’urk’usu a ƙasa tana hawaye, sosai Ameen ya rude dan ya san wahalar da take sha a ciwon ciki, hakan ya ƙara konawa Hafsah rai, dan ko first night ɗinsu da bata da lafiya be rude haka ba sai a kan wannan figaggiyar yarinyar. Neehal ta riko hannun Ameen a wahalce ta ce “Yaya cikina kamar zan mutu, ka kai ni gurin Mama Please.” Ameen ya tashi ya haura sama da sauri ya ɗakko car key ɗinsa ya ɗauki Neehal kamar jaririya ya yi waje da ita, Twins da ganin halin da Auntinsu take ciki yasa su kuka suka bi bayanshi da gudu. Takaici kamar ya kashe Hafsah ganin yanda Ameen ya wani gigice, tsaki ta ja ta ɗauki handbag da takalman su Neehal ta bi bayansu. Har ya kwantar da Neehal a bayan Motar su twins kuma yasa su a front seat. ajiye takalman ta yi a gaban Motar fuskarta ɗauke da jimamin ƙarya, Ameen bai bi ta kanta ba ya ja Motar ya danna horn, mai gadi ya taso da sauri ya buɗe masa gate ya fice daga gidan………..✍️