NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Tun da Ameen ya shigo Dad yake binsa da kallo cikin mamakin irin ramar da ya yi, duk da Mama ta masa bayani a waya amma bai yi zaton abun ya kai haka ba, Ameen ya zauna a ƙasan kujerar da Abba yake tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Dad ya nisa ya ce “Muhammad cuta ka yi a can barrak ɗinne ba mu sani ba?” Ameen ya ce “A’a Daddy” Dad ya ce “To wannan ramar fa ta menene?” Shafa lallausar sumar kansa ya yi tare da lasar lips d’insa na ƙasa, cikin girmamawa ya ce “Dad yanayin aiki ne kawai” Dad yay shiru ya na kallonsa ba tare da yarda da abin da ya ce ɗin ba, sanin halinsa koda zai kwana yana tambayarsa ba faɗa masa abin da ke damunsa zai yi sai ya kyale shi kawai, amma tabbas ya san akwai abin da ke damun ɗan nasa. Sauke numfashi Dad ya yi ya ce “Shikenan Captain, Allah ya taimaka ya ba da sa’a” Ameen ya amsa da “Amin” Dad ya gyara zama ya ce “Ɗazu kafin na fita mun yi magana da Doctor akan shirye_shiryen bikin Daughter, tunda bikin ya matso, ya kamata mu san abin yi mu fara shiri” Ameen ya ce “Hakane, Allah ya kai mu Lokacin da rai da lafiya, ya kuma sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya” Dad ya ce “Amin ya Allah, ta mun Magana kuma a kanka kaima, ya kamata a ce zuwa yanzun kaima ka fitar da matar Aure, dan mu da son samu ne ma a haɗa bikinka da na Daughter” Ameen ya d’ago kansa da sauri ya na duban mahaifinnasa amma bai ce komai ba, Dad ya ce “Kayi shiru Captain” Ameen ya sauke Numfashi ya ce “Dad a dan ƙara mini time, zuwa bayan bikinnata insha Allahu zan fitar da mata nima” Dad ya ce “To shikenan, Allah ya kai mu da rai da lafiya, ya kuma haɗa ku da abokan zama na gari, Allah ya muku Albarka” Ameen ya ce “Amin ya Allah” Wata hirar suka shiga daban akan aikinsu na sojoji.

Neehal tun tana sallah take jin wayarta na ringing, sai da ta idar ta yi shafa’i da wutri sannan ta ɗakko wayoyinnata dake cikin jakarta.

Wayarta da personnal sim ɗinta yake ciki ake kira, missed call ɗin Mama ta gani da na masoyinta, Layin Mama ta fara kira, ringing daya Mama ta d’aga, Neehal ta ce “Hello Mama” Mama ta ce “Wato Neehal har yanzu ba ki koyi sallama a waya ba ko?” Neehal ta ce “Sorry Mamanah” Mama ta ce “Sorry for your self, kin dawo gida ne?” Neehal ta ce “Eh tun ɗazu” Mama ta ce “Dad fa?” Neehal ta ce “Shima na ga car ɗinsa a parking space, amma ban je part d’in shi ba, na tsaya Sallah ne” Mama ta ce “Ok, kin ci abinci dai ko? Dannasan halinki da zama da yunwa” Neehal ta ce “Na ci snaks” Mama ta ce “Haka dai ki ka iya, Ina Hajiya?” Neehal ta ce “Ta na ɗakinta, Yaushe za ki dawo Mama?” Mama ta ce “Sai 10, dama kira na yi in ji ko kin dawo, zan yi abu yanzu ki kula” Neehal ta ce “Toh Mama sai kin dawo” daga haka ta katse wayar. Number’n Anwar ta dannawa kira, sai da ta kusan katsewa ya ɗauka, Neehal ta ce “Amincin Allah ya tabbata ga farin cikin zuciyata, dafatan ka wuni lafiya, kaina bisa wuya na, yau nasan Queen ta yi lefi” Anwar ya lumshe idansa cikin jin daɗin kalamanta da tsananin farin cikin jin muryarta ya ce “Tare da ke tauraruwar da ke haskaka birnin zuciyata, amma tabbas yau kam Queen ta mini laifi babba ma” Neehal ta waro kyawawan idanunta waje tana murmushin jin daɗin kasancewarta da masoyinnata ta ce “Haba my Habibi, a yi haƙuri mana insha Allahu Queen ba za ta kuma ba” Yanda ta yi maganar cike da shagwab’a ya sa sai da tsigar jikin Anwar ta tashi, ya ɗan sauke numfashi ya ce “Shikenan ai Queen ɗita ta wuce gaban komai a gurina, amma dai yau ta mini k’wauron jin muryarta wanda hakan ya sa na rasa nutsuwata gabad’aya” Neehal ta ce “Am so sorry mijin, missed call ɗin farko da ka mun ina bacci ne, da na tashi kuma na kira ka ba kai picking ba, har na je gurin aiki na dawo ba ka kira ba, sai yanzu” Anwar ya ce “Sarkin bacci, to ya kike?” Neehal ta ce “Alhamdulillah sai kewarka da ta cikamun zuciya da gangar jikina” Anwar ya ce “Missd You too my love, ya Mamana da Yayanah da Dad ɗinmu?” Neehal ta ce “Duk sunanan lafiya k’alau, ya Amminah?” Anwar ya ce “Masha Allah, Ammi tananan klu” Neehal ta ce “Ka gaidata Please da sauran ‘yan gidan” Anwar ya ce “Za su ji Insha Allah, yaushe zan zo in ganki ne na yi missing kyakkyawar fuskarnan taki” Neehal ta ce “Gobe mana” Anwar ya ce “Allah ya kai mu amaryata” Hira suka ci gaba da yi irin ta masoya mai cike da nishad’i da farin ciki, ba su wani jima ba su ka yi sallama Neehal ta ce za ta part d’in Dad ne.

Da sallama ta shiga falon Dad, Dad na zaune akan kujera ya na karatun jarida time ɗin Ameen ya fita, Dad ya d’ago tare da amsa sallamar Neehal ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, Neehal ma murmushin ta ke yi ta ƙaraso cikin falon tana faɗin, “My Dad yau na yi missing ɗinka over” Dad ya ce “Nima haka my daughter, ya aikin” Neehal ta ce “Alhamdulillah” tare da zama a gefen Dad d’in, Dad ya ce “Ɗazu bayan mun fito daga meeting na kunna TV na ce bari in ga daughter nah, time ɗin ki na labaran yamma” Neehal ta yi murmushi “Dad ya ce, yanzu nake shirin kiranki na ce ki had’o mini fruits” Neehal ta Mik’e tana faɗin “Bari na had’o maka to” Dad ya ce “Yawwa ɗiyar albarka” Neehal ba ta wani jima ba, ta dawo ɗauke da vowl wanda ta yayyanka fruits d’in a ciki, ta ajiye akan Centre table ɗin dake gaban Dad, Dad yana dubanta da murmushi a kan fuskarsa ya ce “Thank you Amarya” Neehal ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Tare su ka sha fruits d’in da Dad, ya na ta zolayarta da yake Dad mutum ne mai barkwanci, hirar su suke irin ta ɗa da mahaifin da ya ja ƴaƴansa a jiki, har sai da Mama ta dawo sannan Neehal ta koma part ɗinsu. Sau da ta biya ɗakin Hajiya ta mata sai da safe sannan ta wuce nata ɗakin, wanka ta fara yi sannan ta ɗauki wayoyinta ta kwanta akan lumtsumeman gadonta bayan ta kashe light d’in ɗakin, data ta kunna ta shiga yanar gizo, sai wajen 1pm ta kashe datar bayan ta gama shan hira da masoyinta Anwar da besty’nta Haneefah da sauran freinds ɗinta da ‘yan’uwa da abokan aiki. Misalin ƙarfe uku da ƴan mintuna na daren Mama ta kirata, ɗagawa ta yi muryarta cike da bacci ta yi sallama, Mama ta amsa mata tare da faɗin “Ki tashi ki yi Sallah toh” Neehal kamar za ta yi kuka ta ce “Mama dan Allah ki bar ni na yi bacci na, gobe fa da safe za ni aiki, kuma ban daɗe da kwanciya ba” Mama ta ce “Ni na hanaki kwanciya da wuri, ai kin san da sallar ki ka tsaya chat” Neehal ta ce “Ba fa chat na yi ba, karatu na yi, kin san 2 weeks ya rage mu fara exam” Mama ta ce “Na ji, ki tashi ki yi Sallar dai, ko raka’a biyu ce, kin ga auren ki ya kusa, ki roƙi Allah ya kawar muku da fitintunu a zama auranku, yanda auren yanzu ya zama na zamani, dole sai mun dage da addu’a” Neehal ta ce “To Mama” Mama ta ce “Yawwa my daughter, ki yi addu’a sosai, sharrin mutum da Aljan Allah ya kare mu” Neehal ta ce “Ameen, bye” Mama ta katse wayar, Neehal ta yunk’ura ta tashi ta shiga toilet dan d’auro alwala.

Washegari, bayan ta idar da sallar asuba ta yi karatun Alkur’ani mai girma izifi biyu, sannan ta ɗauko materials ɗinta na school ta ɗan dudduba, gari na fara haske ta tashi ta gyara ɗakinta, sannan ta faɗa toilet ta yi wanka. 7:30 ta sakko ƙasa cikin shirinta na zuwa gurin aiki, ta na sanye da hijabinta wanda ya zo mata har ƙasa, Mama ta na kitchen ta na haɗa break fast, ƙarasawa kitchen d’in ta yi ta ce “Morning Mum” Mama ta ce “Morning dear, har kin fito” Neehal ta ce “Ehh, kin san yau Sunday za mu haɗa labaran week d’in gabad’aya dole sai na je da wuri” Mama ta ce “Amma dai ki tsaya ki yi break” Neehal ta ce “Idan na je can zan ci, bari na ɗiba cake” Mama ta ce “A’a ki dai tsaya ki ci abincin ko kaɗanne nasan halinki ba ci za ki yi ba” Neehal ba ta musa ba, ta haɗa tea a ƙaramin cup ta d’ebi soyayyayen phatatoe d’in da Mama ta soya kaɗan, ta koma falo ta ci. Kayan ta dawo kitchen ta ajiye bayan ta gama ci, ta yi wa Mama sallama, Maman ta mata addu’a ta fice. Sai da ta biya part d’in Dad sharp_sharp ta gaishesa sannan ta fito ta tafi……..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button