NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Goma saura Sadik ya ƙarasa gida, kamar yadda ya yi zato duka ƴan gidan nasu suna zaune a falon har Abbansu, bakinsa ɗauke da Sallama, gaba-d’aya suka zuba masa ido tare da amsa masa sallamar. Kusa da mahaifiyarsa ya je ya zauna a ƙasan kujerar da take ya mata sannu da gida, sannan ya gaishe da Abbansa da kishiyar Maamah wadda suke kira da Umma, k’annenshi kuma suka gaishe shi. Abbansa ya ce “Abubakar daga ina haka?” Sadik ya yi ƙasa da kansa tare da shafa sumar kansa, Abban ya kalli Maamah Wadda ke murmushi ƙasa_ƙasa yana murmushin shima, Umma kuwa tab’e baki ta yi ta ce “Hmmmm, Sadik dai ya soma ɓata wayonsa da yawon dare, da dai ba ya yi amma yanzu…..” “Wacce irin magana ce wannan Ruqayyah kike yi?” Abba ya katse Umman a ɗan fusace, Maamah da annurin fuskarta ya ɗauke lokaci ɗaya jin kalaman Umma ta sauke numfashi cikin jin daɗin yanda Abban ya katse Umman ga aikabata mata ɗa da take ƙoƙarin yi.” Sadik ma ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin yanda zugar Umman bata samu shiga ba a gurin Abban kamar yadda ta saba kodayaushe. Umma ba ta da aiki sai yi masa sharri a gurin Abbansa, kuma Maamah ba ta isa ta yi magana ba sai ta saka kuka ta ce tana nuna mata iko akan Sadik dan ta ga ita ba ta ƴaƴa maza, ai itama ɗanta ne ba zata cutar da shi ba. Shiru Umma ta yi ganin yanda Abban ya haɗe rai. Shima Abban shiru ya yi ganin yaransu na falon, miƙewa Sadik ya yi ya nufi bedroom ɗinsa dan yana da aikin da zai yi akan wani case da yake bincike akai.

Asalin Mahaifin Sadik mutumin Kano ne, ɗan kasuwa ne da yake da rufin asirinsa dai_dai gwargwado. Mahaifiyar Sadik kuma ƴar asalin garin Maiduguri ce kabilar Shuwa, aure ne ya kawo ta Kano. Fara ce kyakkyawa ga gashi har baya, a gurinta su Sadik suka gado kyau. Umma kuwa ƴar asalin jihar Kano ce, iyayenta a cikin gari suke, Maamah ba ta fi shekara 5 da aure ba Abba ya auro Umma, lokacin an haifi Sadik yana yaro. Ana zaton wuta a mak’era sai aka same ta a masak’a, domin kuwa Umma ce take da tsananin kishi da shegen makirci, ita kuwa Maamah da zuciya ɗaya take zaune da Umma, kuma duk kasancewarta Shuwa ba ta nuna wannan kishin na hauka, ga ta da haquri da addini. Su Sadik su biyar ne kawai a gurin mahaifinsu, a ɗakinsu su uku ne, Shine babba sai k’aninsa mai bi masa Bashir, sai autarsu Batul. Ita kuma Umma ƴaƴanta biyu kuma duk mata ne, kuma ta fi shekara goma kafin Allah ya bata haihuwar. Makirci kala_kala Umma ta dinga haɗawa Maamah a gurin Abba kafin ta haihuwa, wai Maamah tana mata gorin haihuwa. Hakan yasa Abba ya ce ƴaƴan Maamah itama ƴaƴan ta ne tunda Ƴaƴansa ne dan haka tana da iko akansu. Tun daga wannan rana fa Umma ta samu damar yiwa Sadik sharri iri_iri a wajen Abbansa, a matsayin tana faɗa masa gaskiya wadda Maaman take bo’yewa a cewar ta, kasancewar Abba matafiyi ne bai fiya zama a gari ba, saboda sha’anin kasuwancinsa. Haka Abba zai samu Sadik yay ta masa faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, itama Maamah bata tsira da faɗan Abban. Inda Allah ya taimaka kakarsu Sadik mahaifiyar Abba tana son su sosai, to wani sharrin idan Umma ta k’ulla ita take taka mata burki ta ci mata mutunci, ta kuma hana Abba ɗaukar hukunci akan Sadik ko Maamah. Ita kuwa Maamah kullum cikin tausar Sadik take tana ba shi baki akan Abinda Umma take masa, duk da abun na damunsa amma haka yake haquri ba ya nuna ɓacin ransa saboda nasihar mahaifiyarsa. Bashir ne ma sarkin zuciya wataran yake ƙoƙarin tankawa Umma idan ta ƙure shi akan abun da takewa Mahaifiyarsa da ɗan’uwansa, duk da shi ɗinma tana masa ba tsira ya yi ba, amma shi tana ɗan shayin shi ganin yaron a tsaye yake, Sadik kuwa haqurin mahaifiyarsa ya ɗauko shi yasa tafi raina shi kuma tafi tsanar shi.

Misalin ƙarfe 11 na dare Maamah ta kwankwasa masa ƙofa, yana zaune gaban laptop, ya d’ago ya dubi ƙofa tare da faɗin “Come in.” Maamah ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin “Au Maamah ke ce, na ɗauka ma Basheer ne.” Maamah tana murmushi ta ce “Ni ce Son ya aiki?” Ya ce “Alhamdulillah gashi muna ta fama.” Maamah ta ce “Allah ya taimaka ya bada sa’a.” Ya amsa da “Ameen.” Cikin ladabi. Maamah ta dube shi ta ce “Daga ina kake ne Sadik?” Sunkuyar da kanshi ya yi yana murmushi ya ɗan sosa kai ya ce “Gidan su Neehal.” (Da yake Maamah ta san Sadik yana zuwa gurin Neehal.) Maamah ta yi murmushi ta ce “Ka baro su lafiya?” Ya ce “Eh, tana gaishe ki ita da Mama.” Ta ce “Ina amsawa.” Ta miƙe tay masa sai da safe sannan ta fice zuciyarta fal da farin ciki, kullum addu’arta Allah ya bawa Sadik mace ta gari yay auransa ko ya huta da addabar Umma da kuma faɗan mahaifinsa, tunda ba su isa dai sun bi shi gidansa sun masa ba.

Washegari Mama ta koma bakin aiki, Neehal kuma gidansu Haneefah ta je dan yi musu ban gajiya ita da Twins ɗinta. Bayan sati ɗaya, Neehal ta koma gurin aiki, kuma har yanzu babu wanda ya kira akan su Afrah. Kullum Mama cikin saka ran kira take amma sai ta ji shiru, abun yana ɗaure mata kai sosai, dan yanda aka baza hotunan su Afrah a gidajen Televisions ya ci ace wani nasu ya gani, kuma kullum sai an yi cikiyar iyayensu a gidajen rediyo da Talabijin. Yau Juma’a Neehal aikin safe ta yi, 12pm da mintuna ta dawo gida, kasancewar Ran Monday za su yi resuming School Mama ta ce ta shirya ta je gidan Ameen, kar ta koma School ta zo bata samu damar zuwa ba, tunda every weekend tana gurin aiki, Monday to Friday kuma tana school. Ameen ɗin kuma yana ta yiwa Mama mitar ta hana Neehal zuwa gidansa. Neehal murna kamar ta kashe ta dan ba ƙaramin kewar Yayan nata ta yi ba, dan tunda yay aure ko waya ba su taɓa yi ba, kuma kusan kullum sai ya zo amma ba sa haɗuwa, duk time ɗin da zai zo tana gurin aiki. Cikin Sauri ta shirya Twins ɗinta itama ta shirya, ana sakkowa daga masallaci Driver ya tafi kai su, dan ita ba ta san gidan ba, duk da tana jin mararta na mata ciwo kaɗan_kaɗan amma ta daure, dan tana faɗa Mama cewa za ta yi ta fasa zuwan wani lokacin ta je, ita kuwa zuciyarta cike take da kewar Yayan nata…………✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:44] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

2️⃣4️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………..Direct gida Ameen ya nufa da ita, domin ya san duk taimakon da za a bata a asibiti Mama za ta bata. Mama tana zaune a falo tana azkar ɗin yamma ta ga Ameen ya shigo mata da ƴa a hannu, a ruɗe a tashi tana dubansa ta ce “Al’ameen me ya same ta?” Sai da ya kwantar da Neehal a kan kujera sannan ya ce “Mama ciwon cikinta ne ya tashi.” Mama ta ƙarasa inda take tana mata sannu, Neehal dai hawaye kawai take. Mama ta ce Ameen ya kai mata ita sama bari ta haɗa allura ta mata, insha Allah ciwon zai lafa mata yanzu.

Bayan 10 minutes Neehal har ta samu bacci saboda allurar da Mama ta mata, Mama dake zaune a gefen ta ta sauke ajiyar zuciya cikin tausawa Neehal ɗin, gyara mata kwanciya ta yi daga ruf da cikin da ta yi sannan ta fice. Ameen yana falo tare da Twins har time bai tafi ba. Ameen ya dubi Mama ya ce “Ya jikin nata?” Mama ta ce “Alhamdulillah ta samu ya lafa mata har bacci ya ɗauke ta, dama haka ciwon nata yake kamar aljanu, lokaci ɗaya zai zo amma tana shan magani ko aka mata allura zata ji sauƙin shi 70%.” Jinjina kansa ya yi kawai, a ransa yana mamakin wannan ciwon nata da baya jin magani, dan idan bai manta ba kusan 10 years kenan Neehal take fama da shi. Sun ɗan taɓa hira da Mama akan rashin bayyanar wanda ya san su twins har yau, sannan yay wa Mama Sallama ya tafi. Ko da ya koma gida Hafsah bata nuna masa komai na ɓacin rai ba, sai ma tambayarsa jikin Neehal da ta yi. Washegari da Neehal ta tashi lafiya k’alau ta tashi, sai dai ɗaurewar ciki kawai wanda duk lokacin period ɗinta haka yake mata, sai ta gama take jin ta normal.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button