NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

ABUJA
Tun ranar da aka ba da cikiyar su Afrah misalin ƙarfe goma 12 na rana, budurwar nan ce zaune a falon gidansu tana kallon ASTV, 12 na yi aka fara labaran rana. Hankalinta ba ya kan TV’n dan bata damu da kallon labarai ba, kamar an ce ta d’ago idanunta suka sauka a kan hotunan twins ana cikiyar iyayensu. Wata muguwar zabura ta yi gabanta na tsananta bugu, ba ta san sanda ta cillar da wayar hannunta ba a matuƙar razane cikin ƙaraji ta ce “What?” Mahaifiyarta ce ta fito daga bedroom tana dubanta da kyau ta ce ” Safeenah! Ke da waye na ji kamar kina ƙara?” Tattaro nutsuwarta ta yi ta lalubi remote ta kashe TV dan kar mahaifiyartata ta ga cikiyar su Afrah da ake, ta sunkuya ƙasa ta ɗauki wayarta sannan ta dubi Mahaifiyartata ta ce “Ba komai Momma.” Daga haka ta miƙe ta shige ɗakinta gumi na karyo mata ta ko ina a jikinta. Tab’e baki Momma ta yi ta wuce kitchen. Wani narkeken ashar Safeenah ta danna ta fara zarya a ɗakin a fili take faɗin “Lallai Gaye ya ha’ince ni, amma wallahi sai ya yi dana sanin cin amanata da ya yi.” Ganin surutu ba mafita ba ne a gareta yasa ta ɗauki wayarta data cillar akan gado ta lalubo Numbern Aminiyarta kuma abokiyar shawararta. Bugu ɗaya ta ɗauka cikin tsananin tashin hankali Safeenah ta fara mata magana. “Na shiga uku Saudart, Gaye ya cuce ni ya ha’ince ni ashe Yaran nan be kashe su ba yar da su ya yi.” “Ke wa ya faɗa miki haka?” Saudat ta tambaye cikin tarar numfashi. Safeenah na kuka ta ce, “Gashi nan na gani ana cikiyarsu a gidan TV an tsince su a Kano, yanzu ya zan yi ƙawata dan Allah ki ba ni shawara, ina tsoron kar asirina ya tonu.” Ta ƙarashe zancen tamkar Numfashinta zai bar jikinta saboda tashin hankali. Saudat ta ce “Kin ga ƙawata ki kwantar da hankalinki, in dai ina raye ba zan bari hawayenki ya zuba ba, ki bani nan da zuwa yamma zaki sha mamaki, Gaye kuma zamu haɗu da shi zai san mu ya ha’inta.” Safeenah zata yi magana ta ji wayar ta katse, zama ta yi a ƙasa dab’as tare da dafe kanta cikin rashin sanin abun yi. Ta san Saudat shu’umar kanta ce, yarinya ce mai buɗaɗɗan ido, ga shegen bin bokayen tsiya, a makarantar ABU Zaria suka haɗu da Safeenah har suka zama abokan juna. Ita Saudat ƴar cikin garin Zaria ce, ita ta bawa Safeenah shawarar tasa a sace su Afrah a kashe su, ita kuma ta haɗa ta da su Gaye sukai mata aikin. Yinin ranar cikin fargaba da tsoro Safeenah ta wuni, har wata yar ƙaramar rama ta yi, kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin firgici. Kamar yadda Saudat ta mata alƙawari da yamma ta kirata ta shaida mata ta je gurin wani boka ya mata aiki akan ko da mutum ya ga cikiyar su Afrah a rufe bakinsa ya kasa magana akai, kuma ta tabbatar mata aikin bokan tamkar yankan wuk’a yake. Wannan magana ta Saudat ita ta sanyaya wa Safeenah rai, domin kuwa ta tabbatar aikinsu ya ci tunda gashi har an fi sati amma babu wanda ya yi magana akan ya ga cikiyarsu Afrah da ake ta yi, kuma inda an gani za ta ji labari tunda gidansu ɗaya da Kakarsu Afrah ta wajen uwa, Safeenah ƙanwar mahaifiyar Su Afrah ce ubansu ɗaya. (Tsafi gaskiyar mai shi, Allah ka tsare mana imaninmu, Ameen ya Allah.) Su kam gidansu Mahaifin su Afrah ba su da nutsuwar wani kallon TV, kodayaushe suna zaryar asibiti hakan ya sa ba su ga cikiyar da ake ta yi ba. A ɓangaren su Kakarsu Afrah ta wajen uwa ma haka ne, tashin hankali bai barsu damar wani kallon TV ko sauraren Radio ita ƴaƴanta ba, hakan ya sa suma ba su ga cikiyar ko sun ji ta ba.
Ranar Laraba Neehal ta dawo daga school da yamma ta tarar da Aunty Sadiya wadda zuwanta kenan gidan daga wurin aiki ta biyo ta gidan. Neehal ta rungume ta tana faɗin “Auntyna oyoyo.” Aunty Sadiya na murmushi ta ce “Oyoyo my Daughter, Ya school?” Neehal ta ce “Alhamdulillah, sai yau ma ni na koma.” Aunty Sadiya ta ce “Allah ya taimaka, saura semester uku ku gama ko?” Neehal ta ce “Insha Allah.” Mama ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da glass cup, ta ajiye a gaban Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta ɗauki ruwan tana faɗin “Sannu Yaya, kamar wata baquwa sai kin kawo mun drinks.” Mama ta ce “Ai na ga daga gurin aiki kike, kuma yanayinki ya nuna kin gaji.” Aunty Sadiya ta ce “Hmmm bari kawai Yaya, yau tun 7 na fita office sai yanzu na samu kaina, case ɗin wannan Yarinyar da na ce miki an mata fyaɗe ne har yanzu ya ƙi ƙarewa, so kike ku murd’e gaskiya ƙarshe ma idan ba ai wasa ba su kori shari’ar.” Mama ta ce “Ai Allah ya fi su, kuma insha Allahu zai baku nasara.” Aunty Sadiya ta ce “Allah ya amsa.” Neehal ta dubi Mama tana turo baki gaba ta ce “Mama na dawo fa.” Mama ta ce “Ai na ganki.” Neehal ta ce “Ai ba ki yi welcoming ɗina ba.” Mama ta ce “To bari in ɗauke ki in goya ki uwata.” Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta wuce sama tana ɓata rai. Aunty Sadiya ta yi murmushi zuciyarta cike da tausayin Neehal. Neehal tana shiga ɗakinta ta tarar da twins sun ba je kayan kwalliyarta akan gado suna ta yaɓa wa fuskarsu. Suna ganin ta shigo suka fara kifkifta idanuwa, dan tasha yi musu faɗa akan in ta fita su daina yi mata b’arna a ɗaki. Cike da takaici take kallonsu, ganin yanda suka bata jikinsu da bedsheet da janbaki, ta ƙaraso cikin ɗakin tana faɗin “Sannun ku da aiki.” Afrah ta nuna Amrah ta ce “Aunty ita ta ɗakko miki.” Amrah tai sauri ta ce “Ba ni ba ce ita ce.” Neehal ta ce “Ku sauka ni ku bari guri.” Sauka suka yi daga kan gadon da sauri suna mutsitstsika janbaki a ƴan’yatsunsu. Tattare kayan da suka barbazar mata akan gadon ta yi, sannan ta cire zanin gadon ta kai toilet. sai da ta sake wani sannan ta kamo su Afrah ta cire musu kayan jikinsu ta musu wanka, sukwa sai murna suke an ƙara yi musu wanka, dan suna k’aunar wanka a rayuwarsu suga suna ta facal_facal da ruwa.
Bayan Mama ta kawo wa Aunty Sadiya abinci ta ci, sannan ta tattara duka hankalinta akan Mama ta ce, “Yaya maganar Neehal ce fa ta biyo da ni.” Mama ta ce “Ina jinki Sadiya me ya faru.” Aunty Sadiya ta sauke numfashi cikin jimanta al’amarin ta ce “A binkicen da na yi ya nuna mun Mutum ɗaya ne yake kisan Jamil da Anwar!” Dammmm! Gaban Mama ya yanke ya faɗi, a razane ta ce “Ke ko Sadiya wacce shaida kika gani data tabbatar miki da haka? Kuma waye yake kisan?” Aunty Sadiya ta ce “Alamomi da yawa ne suka nuna hakan Yaya, sai dai kuma har yanzu ba mu gano wanda yake kisan ba, amma muna nan muna binkice a kan hakan kuma insha Allahu sai mun gano ko waye.” Mama ta ce “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, wannan wanne irin abu ne? wanene yake bin yarinyar nan da irin wannan sharrin? Me tai masa yake ɗaukar wa rayuwarta wannan mummunan matakin?” Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce “Shine abun da muke son sani muma.” Ƙarshen tashin hankali Mama ta shiga da jin wannan batun, da har hankalinta ya kwanta ta fara tunanin ko ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma jin wanda ya kashe Jamil shi ya kashe Anwar ya tabbatar mata da sanadin Neehal ake kisan. Duk yanda Aunty Sadiya ta so kwantar wa da Mama hankali amma hakan ya gagara, dan sosai hankalinta ya tashi da jin wannan K’ADDARAR da ta shigo cikin rayuwar Neehal, abun da yake ƙara tadawa Mama hankali shine idan ta tuna ta yanda MAHAIFAN Neehal suka bar gidan duniya, ta matsu Daddy ya dawo ta labarta masa wannan mummunan labarin dan su san ta inda za su ɓullo wa al’amarin.