NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya da mintuna na dare, Neehal ce kwance akan makeken gadonta Amrah kwance a kirjinta tana bacci, Afrah kuma ta rungume ta ta baya itama tana baccin. Hotuna take kallo a wayarta idanunta na zubar da hawaye tamkar an kunna famfo, a fili ta fara magana kamar haka, “UMMANAH, ABBANA, JAMIL ƊINA, ANWAR ƊINA, Allah ya ji k’anku ya gafarta muku, ya sa kuna cikin aljannatur firdausi, Allah ya toni asirin duk wanda yake da hannu a kisanku.” Kuka ta shiga rerawa ƙasa_ƙasa cikin tausayin kanta, rayuwarta ta baya na dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, kewar mahaifanta na ƙara mamaye dukkan zuciyarta, ta rasa me yasa yau suke ta faɗo mata a rai tun da ta tashi, ta daɗe tana kukan kafin bacci barawo ya yi gaba da ita.

ASALIN LABARI……….✍️

Ku yi haquri da wannan, yau na yi busy ne.

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:44] Zeey Kumurya: ⚡NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

2️⃣5️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

…………Alhaji Muhammad Gabasawa, Haifaffen garin Kano ne a wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Gabasawa, mahaifiyarsa da mahaifinsa duk na can ne. Neman kuɗi ne ya kawo shi cikin birnin Kano tun yana saurayi gurin wani cousin ɗin mahaifinsa wanda suke kira da Baffa. Su biyu rak iyayensu suka haifa a duniya, daga shi sai Yayarsa mace, itama tana zaune a Gabasawan anan take aure. Gidansu babban gida ne a garinsu kuma sananne, kasancewar gidan yawa ne kuma kakansu na da arzik’i. Kayan masarufi suke siyarwa a ƙofar Nasarawa shi da k’anin Babansa wanda yake zaune a gurinsa, kuma Alhamdulillahi suna samu sosai. K’anin baban nasa (Baffa) wanda yake gurinsa yana riƙon yarinya sunanta FATIMA ƴar wansa ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, Fatima marainiya ce mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama, da a gurin kakarta wadda ta haifi su Baffa take a Gabasawa, daga baya kuma Baffa ya ɗauko ta ya ci-gaba da riƙon ta. Soyyayyace ta shiga tsakanin Fatima da Muhammad har ta kai su ga yin aure suka tare a nan qofar Nasarawa, Muhammad ya kama musu hayar gida ɗaki ɗaya. Fatima ita kaɗai ce Ƴa a gurin mahaifinta, amma a gurin mahaifiyarta su uku ne, kasancewr mahaifinta ya rasu da dadewa har mahaifiyarta ta ƙara aure a wani gidan ta haifi maza guda biyu. Shekar Fateemah biyu da aure ta haifi ɗanta Namiji, sai dai bayan suna ba jimawa ya dinga wani irin ciwo har ya ce ga garinku nan. A lokacin ne kuma Muhammad ya samu aiki a Company’n wani hamshaqin Alhaji, kasancewar ya yi karatun boko amma iya secondary ya tsaya saboda halin rayuwa. Bayan shekara Fatima ta ƙara haihuwar ƴarta mace, sai dai itama watanni ta yi ta ce ga garinku nan. Hankalin Fateemah ya fara tashi garin tana haihuwa yaran na mutuwa, Muhammad ne ma ke tausar ta yana bata baki. A ƙauye kuwa mahaifiyarta da Kakarta suna ta aiko mata magungunan Hausa, a cewarsu jeji ne ke kashe yaran nata. A wannan lokacin suka tashi daga ƙofar Nasarawa suka koma Gadon k’aya inda Muhammad ya gina gidansa madaidaici mai kyau. Lokacin ne kuma arzik’i ya fara bunƙaso masa, saboda mutumin da yake aiki a wajensa mutumin kirki ne ga kyauta ga jama’a, kuma yana jin dad’i aiki da Muhammad kasancewar sa mai gaskiya da riƙon amana, hakan yasa ya ƙara masa matsayi a Company’nsa da suke sayar da takin zamani. A wannan shekarar ne kuma Muhammad ya ziyarci ƙasa mai tsarki ya sauke farali. Sai da aka kusa shekara biyu sannan Fateemah ta ƙara samun wanin cikin, addu’a suka duk’ufa ita da Alhaji Muhammad akan Allah ya yara mata abun da zata haifa, wannan karan ma mace ta haifa, cikin ikon Allah yarinya ta fara girma ba kamar sauran ƴan’uwanta ba, farin ciki a gurin Fateemah da Muhammad da ba zai faɗuba, sai dai watannin yarinyar bakwai ta ce ga garinku nan. Ko kaɗan Fateemah bata nuna damuwarta sosai ba, zuwa lokacin ta sare ta karbi ƙaddarar da Ubangiji ya dora mata, k’annenta Umar da Usman su ta karb’o daga gurin mahaifiyarta ta ci-gaba riƙe su a gurinta, dan gidan da mahaifiyartata take aure ba wani jin daɗin shi take ba, ana dai zaman haquri ne kawai. Umar da Usman suka ci-gaba da zama a gurin yayarsu cikin jin daɗi, lokacin ma sun fara zama samari. Alhaji Muhammad shi yake musu komai babu abun da ya rage su da shi. Fateemah ba ta yi boko ba amma ta yi ilimin Addini dai_dai gwargwado, dan da auranta ma ta yi saukar Alqur’ani mai girma a makarantar matan auren da take zuwa. Fateemah macece mai haquri ga kawaici babu ruwanta, shiyasa mijinta yake jin daɗi zama da ita. Watarana cikin dare Fateemah ta tashi da wani irin murd’awar ciki, tayta nurququsu ba tare da Alhaji Muhammad ya sani ba, har ta samu cikin ya lafa mata, sai dai kuma tana koma wa ta kwanta ta ji wani irin amai ya taso mata, da gudu ta tashi ta yi toilet ta shiga kelaya aman, kakarin amanne ya tashi Alhaji Muhammad daga bacci, sosai ya tausaya mata yay mata sannu. A wannan daren ta yi aman ya kai sau uku, ga zazzaɓi mai zafi daya rufe ta. Da safe kuma cikin ikon Allah sai ta tashi jikin da sauk’i sosai. Haka tai ta yi har kwana uku tana zazzaɓin dare, ranar na huɗu Alhaji ya ɗauke ta suka je asibiti aka dubata, gwajin farko likita ya tabbatar musu tana ɗauke da juna biyu. Murna a gurin Alhaji Muhammad ba a magana, Fateemah kam yak’e kawai take duk da ba ta san abun da Allah ze yi ba. Sosai Fateemah take shan wahala a wannan cikin kamar ba za ta kai ba, laulayi take mai wahala, ba ta iya bacci cikin dare sai kusan asuba yake ɗauke ta, kakarta ita ta zo daga Gabasawa take zaune da ita, dan ko aiki ba ta iya wa. Haka suka cigaba da rainon cikinsu har ya shiga watan haihuwa, tun cikin yana wata bakwai idan ka ga Fateemah sai ka zata ta kusa haihuwa saboda girman cikin. Ranar wata Juma’a ta tashi da nak’uda, cikin ikon Allah kuma ba ta wani sha wahala ba ta santalu ƴaƴanta guda biyu duk mata. Zo ku ga murna gurin Alhaji Muhammad da Fateemah dama sauran ahalinsu baki ɗaya, yaran kyawawa kamar Fateemah sak suka yo, sai dai ɗaya fara ce ɗayar kuma chocolate color kamar Fateemah. Wadda ta fi farin ita aka haifa sannan mai duhun. A ranar aka sallame su suka dawo gida. Kusan ɗaki guda Alhaji Muhammad ya cika da kayan babies saboda tsananin farin ciki, kodayaushe cikin addu’ar Allah ya bar masa rayan yake. Bayan kwana uku da haihuwarsu da daddare ɗaya daga cikin yaran Allah ya amshi abarsa, Hussainar ce ta rasu mai duhun kenan. Kuka sosai Fateemah ta yi akan rasuwar yarinyar, domin ba ta taɓa jin k’aunar ƴaƴan da take haifa ba kamar waɗannan Twins ɗin, ga fargabar itama ɗayar kar ta mutu. Alhaji Muhammad ya ji mutuwar yarinyar sosai shima, haka dai aka yi sunan ɗayar, Ranar suna ta ci Sunan mahaifiyarta Fateemah Zahra amma NEEHAL za’ana kiranta da shi. An sha Suna sosai wanda duk haihuwar Fateemah ba’a taɓa yin kamarsa ba. A wannan lokacin ne kuma Umar k’anin Fateemah ya gama karatun Secondary ɗinsa, bayan Result ya fito kuma an samu Alhaji Muhammad ya sama masa gurbin karatu a Bayero University Kano. Fateemah kullum cikin godewa Alhaji Muhammad take ita da mahaifiyarta na yanda baya gajiya da dawainiyar k’annenta, kama daga cinsu,shansu,surarsu,iliminsu na boko dana addini duk baya gajiya da yi musu. Dama Alhaji Muhammad mutum ne shi mai kyautatawa ƴan’uwansa na birni dana ƙauye, hakan yasa kullum yake ganin cigaba a al’amuransa. Kowa ya tashi da buƙatarsa sai ya zo gurinsa, shi kuma indai ba ta fi ƙarfinsa ba zai maka. Neehal irin yaran nanne masu shegen Kuka, musamman cikin dare ba ta barin iyayenta su rintsa, Fateemah idan ta gaji da rarrashi takance “Allah ya nuna mun ranar da zaki bar ni na huta nikam, tun daga cikin ki har yau bana samun isasshen bacci.” A duk lokacin da ta faɗi haka Alhaji Muhammad sai dai ya yi murmushi kawai. Watan Neehal bakwai kacal a duniya amma sai wayon tsiya, a lokacin rarrafe take ɗan yi amma akwai son yawo, Abbanta kullum da wayo yake fita daga gidan dan idan zai fita ta dinga ihu Kenan. Uncle Usman shine mai d’aukar ta idan ya dawo daga makaranta ya fita da ita, shi yasa tafi sabawa da shi akan Uncle Umar. Shekarta ɗaya da wata biyu Umma ta yaye ta, dan zuwa lokacin ta yi ƙafa ta fara tattakawa ga surutu duk da gwaranci take yi maganar ba ta fita sosai, ga kuma masifa, dan Yaro ɗan shekara uku ma dan tsaurin ido sai ta dinga dukansa, musamman idan aka zo gidansu, ga ta’adi komai aka ajiye sai taɓa. Neehal yarinya ce mai farin jini dan kowa sonta yake, kullum zaka ganta fess Ummanta bata barinta da k’azanta, Abbanta kuwa ba ya gajiya da yi mata siyayyar kayan sawa masu kyau da tsada. Tun tana ƙarama ba ta son hula, ana sa mata zata cire ta yar, gata da gashi mai yawa da tsayi kuma baƙi sidik. Shekararta biyu bakinta ya buɗe cui_cui sai ɗan banzan surutu kamar ta ci aku, ga tsokana kamar me. Umma kullum sai dai ta kalle ta mata addu’ar shiriyar Ubangiji. Sosai mahaifinta yake nuna mata gata kasancewar ta yarsa guda ɗaya tilo a duniya, sai dai ba irin gatan da zai ɓata ba, kuma suna mata tarbiyya dai_dai gwargwado. Shekarar Neehal uku a duniya lokacin ta fara zuwa islamiyya da boko, mahaifinta ya sai filin kusa da gidansu ya haɗe da nasa ya gina wani part ɗin, nan ma da suke ciki ya ƙara gyarashi. Dan zai ƙara aure ne ba dan ya dena don Matarsa ba, sai dan yana da halin yi kamar yadda Allah ya ce. Umma ko kaɗan ba ta damu ba akan za a mata kishiya, addu’a take kawai Allah ya kawo mata ta gari,kuma ta toshe kunnuwanta daga duk wata zuga ta k’awaye da ƴan’uwa. Neehal kam sai murna take Abbanta ya ce ya kusa kawo mata Aunty.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button