NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A’isha Sunan Matar da Abba zai aura, Ƴar asalin garin Gombe ce, mahaifanta duka na can ne kuma Fulani ne. Ƴan’boko ne na bugawa a jarida, amma bokon bata hana su yin ilimin Addini ba, ga su ƴan’gayu kyawawa. Bautar ƙasa ce ta kawo ta Kano har Allah ya haɗa ta da Abba suka fara soyayya. Su A’isha su Huɗu ne a gurin iyayensu, Fateemah (Mama) ita ce babba sai Mahmud (Uncle Mahmud) sai A’isha (Aunty A’isha) sannan auta Halimatus Sadiya ( Aunty Sadiya.) An yi bikin Abba da Aunty A’isha lafiya an gama Lafiya, a garin Gombe a ka yi komai, sai kuma ranar D’aurin Aure da Ƴan Gabasawa suka zo aka yi wuni a gidan Umma, Neehal daɗi kamar ya kashe ta ana taro a gidansu, tana ta b’arna Umma ba ta hana ta ba, balle ta faɗa ko ta dake ta. Ƴan kawo Amarya sun zo sosai daga Gombe, kwanan su ɗaya suka koma, suma ƴan Gabasawan ranar suka tattafi. Tun a washegari Aunty A’isha ta fara hidima da Neehal, duk da Umma ta hanata amma ta ƙi. Bayan kwana biyu shak’uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Aunty A’isha, dan Aunty A’isha ba ruwanta ita take mata komai, Neehal kam abun da yasa take son Aunty A’isha idan ta yi ta’adi bata faɗa kamar na Umma, Umma kuwa idan ta gaji da magana har make ta take. Da tafiya ta yi tafiya ma Neehal gurin Aunty’n ta koma da zama gaba-d’aya, Umma ta ce “Ala raka taki gona, ta huta da ciwon bakin bari_bari.” Zaman lafiya ake tsakanin Umma da Aunty A’isha, Abba kuma yana yin adalci a zamansu, hakan yasa ba’ajin kansu kwata_kwata. Duk inda Aunty A’isha zata da Neehal take zuwa ko da kuwa tafiyar kwanaki za ta yi, hakan yasa danginta duk sun saba da Neehal tamkar jininsu haka suke kallonta.

Bayan shekara biyu

An yi bikin Uncle Umar k’anin Umma, inda ya tare da amaryarsa a unguwar Sabuwar gandu, bayan ya gama degree ɗinsa ya yi service Abba ya samar masa teaching a wata secondary school. Gidan da zai zauna ma Abban ne ya siya masa, Umma ta ce gaskiya ba zai karb’a ba abun ya yi yawa, dawainiyar ta yi yawa. Abba ya ce mata “Idan ba zai musu ba wa zai yi wa? Ko tana so ta nuna masa k’annenta ba nasa ba ne.” Umma da ta ji ya faɗi haka sai ta haqura, amma fa ranar ya sha godiya da addu’oi a gurinta. Har yanzu da Neehal ta yi shekara biyar Umma ba ta kuma samun ciki ba, Aunty A’isha ma haka. Neehal kullum cikin mitar ita a haifa mata k’ani take, wataran har da kukanta, saboda Freinds ɗinta na makaranta duk yawanci suna da k’anne. A duk lokacin data faɗi haka Abba kan rarrashe ta ya ce ta yi addu’a Allah ya kawo. Neehal ta ƙara girma iyayi da surutu sun ƙaru.

Ranar wata Saturday da yamma ta dawo daga islamiyya, part ɗin Aunty’nta ta nufa direct tana k’wala mata kira, tana shiga falo ta yarda jakarta wadda Exercise book ne kawai a ciki sai pencil, ta cire ɗan mutsin hijabin jikinta shima ta yar, kanta babu d’ankwali saboda bata k’aunarshi ko kaɗan, fakakken gashin kanta da Aunty A’isha ta tsefa mata da safe ya bayyana, wanda ya sauka har ƙasan wuyanta. Har ta nufi bedroom ɗin Aunty ta tsaya turus saboda ganin wani matashi wanda ba zai wuce 17_18 years ba a zaune akan kujera yana latsa system ɗin Aunty A’isha. Neehal ta waro Ido dan bata taɓa ganinshi ba ta ce “Kaii! Waye kai, wa ya kawo ka gidanmu?” AMEEN Da bai masan da shigowar ta ba sai muryarta kawai ya ji ya mata banza, kasancewar sa muskili na bugawa a jarida. Neehal ta matso kusa da shi da ɗan ƙarfi ta ce “Kai baka ji ina maka magana.” Ko d’agowa bai yi ba balle ya kulata, Neehal ta hau kan kujerar da yake ta kai bakinta dai_dai kunnansa da iya ƙarfinta ta ce “Kai ba ka ji ne, ko kai kurma ne!” Ameen ya d’ago a mugun fusace jin zata kashe masa dodon kunne ya wurga mata wani mugun kallo tare da hankad’e ta daga kusa da shi, Allah ya so kujerar da yake kai doguwa ce ta faɗa a kanta. Da sauri ta tashi zaune tana keɓe fuska tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Sauka ta yi daga kan kujerar ta yi bedroom ɗin Aunty da gudu tana kukan shagwab’ar da babu hawaye, Aunty A’isha ta tare ta da sauri tana faɗin “Me kuma ya faru Daughter?” Neehal ta keɓe baki ta ce “Wani ne a falo ya dake n……” Hango Mama da ta yi zaune a gefen gado yasa bata ƙarasa maganar ba ta nufe ta tare da d’ane mata cinya tana faɗin “Maman Abuja, yaushe kika zo?” Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce “D’azu na zo Daughter, wane ya kika ce ya dake ki?” Neehal ta turo baki ta ce “Ni ban san shi ba, wani yaro ne a falo.” Aunty A’isha ta ce “Ba yaro ba ne Neehal Yayanki ne.” Neehal ta ce “Aini ban da Yaya, kuma su Annur da Aslam duk suna da Yaya.” Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka, Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce “Ke ma Daughter ga Yayanki nan na kawo miki kin ji? Daga yau kema kina da Yaya.” Neehal ta gyaɗa mata kai tana murmushin jin daɗi an ce ga Yayanta. Mama ta dubi Aunty A’isha ta ce “Nikam A’isha da zaku bar mun Neehal ai da naji daɗi sosai wlh, ina son yarinya mace amma Allah bai bani ba.” Aunty A’isha ta yi murmushi ta ce “Tab’ Wannan kam Ubanta ba zai iya bayar da ita ba, dan tsoka ɗaya ce a miya.” Mama ta ce “Ni shaidace kam akan k’aunar da Alhaji Muhammad yake mata.” Aunty A’isha ta kama Neehal ta cire mata uniform ɗin jikinta ta saka mata best da dogon wando. Neehal ta ce “Aunty kin dafa mun macaroni na?” Aunty A’isha ta ce “Yana kitchen na dafa miki, bari na zubo miki.” Bayan Aunty ta zubo mata macaronin da miya ta fice falo da shi a hannu, gurin Ameen ta nufa tana faɗin “Yayanah! Yayanah, Maman Abuja da Aunty sun je kai Yaya ne ko?” Cike da murna take maganar, Amma Ameen ya ƙi kulata kamar tana magana da dutse. Neehal ta matso kusa da shi sosai ta d’ebo macaronin da ya ji miya sosai a ƙaramin spoon ɗin da take cin abinci da shi ta kai bakinsa tana cewa “Yayanah ungo ka ci.” Ai macaronin be kai ga shiga bakinsa ba ya zube a jikinsa, miyar jiki ta b’ata masa white T_shirt ɗin dake jikinsa…………✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:45] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

2️⃣6️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………Cikin tsananin takaici ya d’ago yana jifan ta da wani irin kallo, ita ma kallon nashi take da kyawawan idanunta cikin shock ta turo small pink lips ɗinta gaba. Tsaki ya ja tare da ɗauke idonsa daga kanta, ajiye abincin hannunta ta yi a ƙasa ta kai hannunta jikinsa inda abincin ya zuba tana faɗin “Sorry Yayanah bari na goge maka.” Shi dai be ce mata komai ba sai harara da yake ta banka mata, maimakon ta goge masa kamar yadda ta ce sai ma ƙara damula masa miyar take a inda babu, cikin k’ufula ya buge hannun nata tare da jan wani wawan tsaki ya tashi fuuu ya nufi ɗakin da Aunty A’isha ta sauke shi, shi fa shiyasa tun farko bai so Mama ta yo wannan tafiyar da shi ba, sai da ya ce mata ba zai biyo ta ba amma ta takura masa sai ya zo, gashi nan daga zuwan shi wata tsaregar yarinya ta fara ɓata masa rai. K’wafa ya yi lokacin da yake cire rigar jikinsa, ba dan ya kai zuciyarsa nesa ba da sai ya gaggaura wa yarinyar maruka, dan ta gane shi ba sa’an wasanta ba ne. Neehal kuwa ɗakin Aunty ta yi da gudu tana kuka, Mama kuwa tana ganin Neehal ta shigo da kuka ko da ba a faɗa mata ba tasan ita da Ameen ne, dan tasan halin kayanta sarai. Tashi ta yi ta fito falo, Aunty A’isha kuwa rarrashin Neehal ta shiga yi. Ba ta ganshi a falon ba hakan yasa ta bi shi har ɗakin da yake, ta tura ƙofar ta shiga da Sallama, trolley ɗinsa da ya ɗauko riga a ciki ya saka yake zipping, ya amsa mata sallamar cikin muskilar muryarsa. Mama fuska ɗaure ta ce “Ameen! Me yarinyar mutane ta maka kake dukanta? dan na saka ka zo sai ka huce a kanta?” Kamar ba zai yi magana ba sai kuma dai ya ce “Mum ni ban dake ta ba, kawai ta zo tana samun ciwon kai ne shine na ɗan maketa.” Mama ta ce “Uhm lallai, ai gwara daka ɗan maketan, to tunda ka make ta kuwa kai zaka zo rarrashe ta.” Tana gama faɗin haka ta juya ta fice, cize lips d’insa na ƙasa ya yi, ya tashi ya fito falo. Da Mama ta koma ɗaki ta tarar Neehal ta yi shiru tana bawa Aunty A’isha labarin dalilin kukanta. Aunty A’isha ta ce “To ki yi haquri kin ji, kuma ai ke kika ɓata masa kaya dole ya dake ki, ki je ki bashi haquri ki ce masa ba za ki kuma ba kin yi yarinyar kirki tah.” Neehal ta gyaɗa mata kai ta fice daga ɗakin da saurinta. Aunty A’isha ta yi murmushi ta ce “Neehal rashin ji Ameen kuma babu haquri.” Mama ta ce “Dama da abunsa, har yanzu fushi yake na taho da shi, na rasa irin wannan muskilanci na Ameen da baya son shiga cikin mutane, ya fi son in barshi a gida yay ta fama da system da takarda, kamar a kansa aka fara study.” Aunty A’isha ta ce “Ameen halinsa sai shi kam.” Neehal tana fita ta ɗan nutsu saboda tsoron Ameen da ya dirar mata a zuciya. A hankali ta ƙaraso kusa da shi cikin sanyi ta ce “Yayanah ka yi haquri ba zan kuma ba.” Ameen ya sauke numfashi ya kamo hannunta ya ce “Shikenan na haqura, amma ki daina rashin ji da yiwa mutane ihu kin ji.” Neehal ta gyaɗa masa kai, cikin murnar ya ce ya haqura ta ce “Yayanah za ka kai ni islamiyya gobe? Nima ince wa su Noor ga Yayanah.” Ameen ya ɗan murmusa tare da gyaɗa mata kai. Ganin fa ya sake mata sai ta shiga yi masa hira tana bashi labarai kala_kala, shi dai kallon ɗan ƙaramin lips ɗinta da kyawawan idanunta kawai yake, a zuciyarsa yana mamakin surutu irin na Neehal sai ka ce Radio, ko ya ta motsa bakinta sai dimples ɗinta sun lotsa abun sha’awa. Kiran Sallar Magriba ne ya tada shi, tare suka fita da ita bayan ya yi alwala ita kuma ta yi part ɗin Ummanta. Washegari da safe Mama ta je part ɗin Umma suna hira, kamar ko wacce Sunday Aunty A’isha ta kamo Neehal ta fara yi mata kitso duk da zillewar da tai ta yi, saboda a rayuwarta ba ta k’aunar a taɓa mata kai ko kaɗan, kitso kuka, tsifa kuka, wankin kai kuka, haka Allah ya yi ta. Yauma gaba-d’aya ta cika part ɗin Aunty A’isha da ihun kukan kitson, Ameen yana daga ɗaki a kwance amma yana jiyo ihun nata, dan ware murya ta yi iya ƙarfinta, kamar wadda ake yankar naman jikinta. Da abun da ya ishe sa ne ya fito a fusace ya daka mata tsawa, ba shiri ta yi tsit sai tsiyayar hawaye kawai take, daga baya kuma sai bacci ma ya ɗauke ta. Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal tana girma kyawunta na ƙara fitowa, gata ƴar gatan Abbanta babu abunda ya rage da shi, Haka ma mahaifiyarta da Aunty’nta. Tana zuwa Gabasawa sosai musamman lokacin hutu, haka ma tana zuwa Abuja gidan Mama, amma tun daga time ɗin da Ameen suka zo gidansu ba ta ƙara ganin shi ba, saboda ya tafi Turkey karatu. Tun tana tambayar Mama shi harta manta da shi ma. Neehal yarinya ce mai ƙoƙari ga iyayi da son gayu, hakan yasa take da farin jini a ko’ina, duk inda ta shiga sai an k’aunace ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button