NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Tana da shekara takwas kakarta Inna mahaifiyar Umma ta rasu, mutuwar Inna ta girgiza mutane da yawa, Umma ta yi kuka ita da su Uncle Umar, Neehal ma duk yarinya ce a time ɗin Amma ta ci kuka ta gode Allah. Shekarta goma sha biyu ta zana commen entrance, a lokacin ne ta samu hutun makaranta mai tsayi kusan na 3 months, Gabasawa ta fara zuwa ta yi 1 week daga nan ta dawo gida ta je gidan Baffa ƙofar Nasarawa ta musu kwana uku, daga nan ta je gidan Uncle Umar ta yi kwana biyu, dan duk da Uncle Umar yana da ƴaƴa guda biyu amma Neehal ba ta jin daɗin zaman gidan saboda matarsa ba ta da kirki, shi ma Uncle Umar ɗin kuma dama ba ya wani sakar mata fuska, hakan yasa babu wata shak’uwa mai ƙarfi a tsakaninsu, sai masifar tsoransa ma da take ji. Daga nan Gombe ta wuce gidan Hajiya (Mahaifiyar su Aunty A’isha), time ɗin ba’ayi auren Aunty Sadiya ba, kuma ga Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud suna wasa tare, shi ya sa take jin daɗin zaman Gombe. Satinta ɗaya a can ta wuce inda tafi jin daɗin zamansa akan ko’ina wato Abuja gidan Mama. Daga cewa za ta yi 2 weeks sai gashi tar tafi wata ba ta dawo ba, su Abba da Umma da Aunty sun yi kewarta, kullum suna waya a wayar Mama, idan suka tambaye ta yaushe zata dawo sai ta ce musu ta kusa amma kuma ta ƙi dawowar. Ameen ya dawo Naija time ɗin, amma ba ya Abuja yana Lagos acan ya fara aiki, zuwa time ɗin ya zama cikakken saurayi mai cikar zati da kwarjini, miskilanci kuwa da tsare gida sai abun da ya yi gaba. Neehal tana jin daɗin zama a Abuja sosai, saboda yanda Mama da Daddy suke tarairayarta tare da nuna mata tsantsar k’auna tamkar su suka haife ta. Ita kam babu abun da za ta ce da dangin Aunty A’isha sai godiya da sam barka, ƴan’uwan kishiyar babarta ne amma har sun fi wasu ƴan’uwan Abbanta kula da ita, dan idan ta je Gabasawa a yanzu da babu ran Kakarta Yayar mahaifinta wadda take kira da Ummi ita kaɗai take kula da ita, sauran cousins ɗin Abbanta kuwa tsakaninta da su gaisuwa ce kawai, amma idan zata shekara a garin babu mai aiko mata da abun biyar, amma su komai na su sa kwashi jiki su tafi gurin Abbanta ya biya musu buƙatar su. Gwara ƴan’uwan Umma su ko ba su bata komai ba, amma akwai sakin fuska kuma suna janta a jiki. Ƴaƴan Baffa kuma wanda ya rik’i Ummanta da Abbanta suma dai ba wani jin daɗin su take ba, Ƴaƴansa duka maza ne guda huɗu, duk sun yi aure sun hayayyafa, wasu ma sun haifi wanda suka girme ta, Baffan ne dai ya nuna mata k’auna da ya raye, ba ya banbanta ta da sauran jikokinsa. (Da yake tun Neehal tana shekara goma Allah ya masa rasuwa.) Akwai wani cousin ɗin Abba da yake nan Kano Yaya ne a gurin Abban, mutumin yana da kirki ga ilimin Addini, kaf cousin ɗin Abba ya fi zumunci da Abba sosai, dan tamkar uwa ɗaya uba ɗaya haka suka ɗauki junansu. Mutumin yana son Neehal sosai, dan Abba yana yawan kai masa ita, to shi kuma matsalar matarsa ce makira kuma muguwa, zata nuna babu ya kai a zahiri, amma a cikin zuciyarta ba haka ba ne, da wani abu na sharri zai same ka sai ta fi kowa murna. Duk da haka dai suna Zumunci sosai da Umma da Aunty A’isha. Dangin Abba haushin yanda Neehal take da ƴan’uwan Aunty A’isha suke ji, a cewar su wai itama Umman kwad’ayi ne yasa ta bar Neehal take shige musu, dan ta ga suna da kuɗi. Ita kuwa Umma daɗin yanda Aunty A’isha da danginta suke son Neehal take ji, ga kuma tausayin Aunty A’ishan na rashin haihuwa da Allah bai bata ba, shi yasa ta bar mata Neehal ɗin, dan komai na Neehal yana hannun Aunty A’isha, dan in ba faɗa maka aka yi ba za ka ce ba Aunty A’isha ce ta haife ta ba, dan Umma tana mata kawaici sosai akan Neehal, dan ko abu ne za ta cewa Neehal je ki gurin Mamanki ta miki kaza, Mamanki kaza, Aunty’n Neehal ma take cewa Aunty A’isha. Abba kam sosai yake jin daɗin yanda Umman take wa Aunty A’isha, hankalinsa a kwance yake tun da kan matansa a haɗe yake. Ita kuwa Aunty A’isha sosai take girmama Umma, haka ma ƴan’uwanta, babu ruwansu da wai su masu kuɗi ne ƴan’boko, ita kuma Umma ƴar talakawa ce talakawan ma na ƙauye balle su wulak’anta ko suna mata gani_gani.
Ranar wata Laraba lokacin Neehal satin ta shida da kwanaki a gidan Mama, da yamma tana bitar haddadarta da zata bayar ranar Asabar, da yake tun bata fi sati da zuwa ba Mama ta nemi islamiyya ta saka ta, da ta je sai ta ɗora daga inda ta tsaya a haddarta ta gida. Gabanta ne ta ji ya yi wata mummunar fad’uwa, runtse idanta ta yi da sauri tana karanto Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, mike wa ta yi tsam ta nufi bedroom ɗin Mama. Bayan ta yi sallama ta shiga Mama ta amsa mata ta ƙara da faɗin. “Har kin gama haddar?” Jiki a sanyaye ta zauna a gefen Mama sannan ta ce “Eh.” Mama ta ce “To ki je ki wanke panties ɗinki kar Magriba ta yi, dan nasan halinki da k’ailula sai ki yi awanni a wankin panties kawai.” Ta ce “Toh.” har ta miƙe sai kuma ta koma ta zauna ta ce “Mama yaushe zan koma gida?” Mama ta dube ta cikin mamaki ta ce “Gida kuma? Ke da kullum aka miki zancen komawar sai ki ce ba yanzu ba, amma yau kuma da kanki kike tambayar yaushe zaki koma.” Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, Mama ta cigaba da kallonta cikin nazartar ta, ta lura kamar wani abu na damunta dan wata nutsuwa ta ga ta yi, alhalin ta san Neehal da rawar kai da surutu, babu yanda za’ayi ta shigo bata ishe ta da hira ba, sai dai idan da wani dalili. Mama ta kira sunanta a hankali tare da kama hannunta ta ce “Neehal! Meke damunki? Ko baki da lafiya ne?” Girgiza mata kai ta yi alamun babu komai, Mama ta ƙara tambayarta da faɗin “Wani abun aka miki?” Nan ma girgiza kan ta ƙara yi, Mama ta ce “To me yasa kike son tafiya gida?” Neehal ta ce ” Kawai ina son ganin Ummata da Abbana da Aunty.” Mama ta sauke numfashi ta ce “To Shikenan, gobe Yayanki Ameen zai dawo, Ranar Saturday insha Allah sai na saka shi ya kai ki gida.” Neehal ta gyaɗa mata kai cikin gamsuwa duk da bata san wanda Maman ta ambata mata a matsayin Yayanta ba. Tashi ta yi ta koma ɗakinta dan yin abun da Mama ta sata. Washegari ma haka ta tashi tana jin kanta wani iri, gabanta kuma bai dena fad’uwa, Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un kawai take maimaita wa kamar yadda Mama ta koyar da ita a duk lokacin da ji ko ta ga wani abun tashin hankali. Ranar Ameen ya dawo gidan da yamma, shima ba wani jima wa ze yi ba, Ranar Sunday da zai koma. Neehal ba su haɗu ba ranar saboda wuni ta yi a ɗaki a kwance, Mama ta mata tambayar duniya ta faɗa mata me yake damunta amma amsar ɗaya ce babu komai, ƙarshe ma sai ta saka kuka, sai da suka yi waya da Abbanta da Ummanta da daddare, ta ji suna lafiya k’alau sannan ta ɗan ji daɗi a ranta. Duk da Neehal a lokacin yarinya ce amma tana da hankali, shi yasa Mama take jin daɗin zama da ita.
A Kano kuwa bayan su Umma sun gama waya da Neehal, Umma ta dubi Aunty ta ce “Aunty’n Neehal kin ga ikon Allah, yau kuma Neehal ce take cewa tana so ta dawo gida.” Aunty A’isha ta yi murmushi ta ce “Kin san halin Neehal sai ita, may be ta gaji da Abujan ne take so ta dawo.” Umma ta ce “Hakane, amma da fa da kuka take baro Abujan.” Abba ya ce “Ai kin san ba ta taɓa dadewa kamar wannan lokacin ba, shi ya sa.” Umma ta gyaɗa kai tana faɗin “Sai dai haka, amma yanzu tana dawo wa ana mata abu zaku ji tana ita gidan Mamanta zata koma dan tafi sonta.” Abba ya yi murmushi ya ce “Ai soyayyar Yaaya da Neehal sai Allah, Allah ya haɗa jininsu.” Aunty A’isha ta ce “Ai ita Yaaya tana son yara ne, musamman mata, Allah kuma bai bata ba, gashi duk yarinyar data ɗauka a Family’nmu tana ɗan yin kwanaki sai su ce su gida za su koma, kin san yara ba sa son zaman gida shiru kuma gashi ba’a fita, daga makaranta sai gida, haka take komar da su gurin iyayensu.” Umma ta ce “Allah sarki, Allah ya bata nata itama, ai ba’a fitar da rai da rabo a rayuwa.” Abba ya ce “Allah ya kawo masu albarka.” Suka amsa da Ameen gaba-d’aya. Ranar sun jima suna hira a falon Umma gwanin sha’awa, da yake ranar girkin Umma ne, sai Kusan 12pm Aunty A’isha ta koma part ɗinta. Misalin ƙarfe biyu da mintuna na dare, Abba yana zaune akan sallaya yana lazimi bayan ya idar da sallar Nafila, Umma kuma tana kan gado a kwance amma ba barci take ba, tun da suka baro falo ta kwanta amma bacci ya ƙi zuwar mata, sai wata irin faduwar gaba ce take riskarta akai_akai, addu’ar neman tsari daga sharri ta shiga karantawa a cikin zuciyarta, ana haka kawai suka ji an banko musu ƙofar ɗakin baram…………✍️