NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Lokacin da Aunty A’isha ta sanar da Mama rasuwar Umma da Abba kusan zaucewa ta yi ita kaɗai a ɗaki, saboda tsananin kaɗuwa dan mutuwar ta dake ta ba kaɗan ba, wayar da suka yi jiya da daddare kawai take tuna wa. Da ƙyar ta samu yar nutsuwa ta fara dawo mata sanadiyyar karanta Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, da ta shiga maimaitawa a fili. Miƙewa ta yi da ƙyar ta fito ta nufi part ɗin Daddy, tana shiga ta tarar da shi yana waya. Sai da ta jira ya gama wayar sannan ta rattabo masa abun da faru, iya rudewa shi ma Daddy ya ruɗe, ba shiri ya yi kira a waya dan asamar musu Visa zuwa Kano shi da Mama, da Ameen da Neehal. Neehal tana kwance a ɗaki Mama ta shigo ta same ta. “Neehal, tashi ki shirya zamu unguwa.” Mama ta faɗi haka cikin sanyi da raunin murya. Neehal ta tashi zaune tana duban Mama ta ce “Ina zamu Mama? Ni fa Umma da Abba nake son gani.” Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka, Mama ta daure dan kar Neehal ɗin ta gane wani abu ta ce “Daga can zamu biya gida ki ga su Umman.” Neehal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe ta shiga toilet, Mama ta bita da kallo cikin tsananin tausayinta. Tashi ta yi ta fice daga ɗakin da sauri jin kuka na neman kufce mata. Neehal kam cikin sanyin jiki sosai ta fito ta shirya, ta rasa me yasa ta ji bata wata murna duk da Mama ta ce mata za su biya ta ga Su Ummanta. Kafin ƙarfe tara su Mama sun ƙarasa Airport, cikin mintuna aka gama komai suka shiga jirgi suka yo Kano, Neehal sai kallon Ameen take cikin zuciyarta tana mamakin tsakanin kamarsu da Mama, daga gaisuwa babu abun da ya kuma haɗa su, dan shi ko kallonta bai kuma yi ba. Sai dai cikin zuciyarsa cike take taf da tausayin ta, dan Mama ta sanar masa rasuwar Mahaifan nata. Driver’n Abba ne ya je ya ɗauko su lokacin da suka sauka a Kano, Neehal ta yi mamakin hakan amma ba ta ce komai ba. Yanda Neehal ta ruɗe, ta gigice tare da firgicewa ba zai misaltu ba, balle ya faɗu, lokacin da ta yi arba da gawar iyayenta kwance duk jini ya ɓata likkafanunsu, duk da Kasancewar ta yarinya a time ɗin amma tasan mutuwa, ta san shikenan ba zata ƙara ganin Ummanta da Abbanta ba sun tafi kenan, ta yi kuka ta yi kalamai wanda sai da suka karya zuciyar duk wanda yake gurin tare da zubar mata da hawaye, haka ta rungume Aunty A’isha sukai ta kuka abun tausayi. Mama ma duk dauriyarta ranar ta ci Kuka. Saboda tsabagen Kukan da Neehal ta sha kafin dare zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, sai da aka mata allura sannan jikin nata ya ɗan yi dama, da safe kam jikin sai ya ƙara rikicewa, sai da ta yi kwana biyu ana saka mata drip tare da allurori sannan ta ji sauƙi. Umma da Abba sun yi jama’a sosai wanda suka raka su gidansu na gaskiya, dan Abba mutumin k’warai ne, kowa sai faɗar Alkhairinsa yake, haka ma Umma, gashi kuma sun yi sa’ar dace wa da Ranar Juma’a. Tun daga Ranar da akai kisan jami’an tsaro suka duk’ufa da binkice dan gano waɗanda suka yi nisan, dan har mai_gadi sun kama a tunaninsu ko da haɗin bakinsa, amma daga baya sun sake sa da suka gane babu haɗin bakinsa a kisan, ta ƙofar baya ma waɗanda suka yi kisan suka shigo gidan. Bayan sadakar bakwai kowa ya watse gida ya rage daga Neehal sai Aunty A’isha da hajiyarsu da Yayar Abba. Nan fa mutuwar ta dawowa da su Aunty A’isha da Neehal sabuwa, sai ya kasance Kullum sai sun yi kuka. Nasiha sosai Hajiya da Yayar Abba suke musu akan su yi haquri, dama duk mai rai mamaci ne, kowa jiran mutuwarsa yake fata dai kawai Allah yasa mu cika da kyau imani. Uncle Umar da Uncle Usman ma mutuwar ta dake su ba kaɗan ba, dan suma kuka wurjanjan suka dinga yi. Aunty A’isha kullum tunaninta su waye suka kashe su Umma, kuma akan wanne dalili? Dan a binkicen da akai ya nuna wanda suka yi kisan ba b’arayi ba ne turo su akai, dan babu abunda suka ɗauka a gidan. Kafin a yi arba’in Yayar Abba ta koma Gabasawa, sai Hajiya ce kaɗai take zaune da su Neehal. Kusan kullum suna waya da Mama da Daddy, Mama ta ƙara zuwa sau ɗaya ta duba su. Sosai Ubangidan Abba ya sa aka tsananta bincike dan gano wandanda suka yi kisan su Abba, amma shiru babu wani information, duk da jami’an tsaron na iya bakin ƙoƙarinsu a binkicen.
Washegari garin Arba’in Uncle ya zo da wata magana wadda ta gigita Su Aunty A’isha ta kuma ba su mamaki, ya zo ya same su suna zaune da Mama, da Yayar Abba da Aunty Sadiya, da Ammi matar Uncle Mahmud wanda duk sun zo ne saboda sadakar Arba’in su Umma. Maganar da ya musu kuwa itace akan rabon gado, wai nan da kwana uku insha Allah za su zo da Alk’ali a raba a bawa kowa nasa. Kuka Aunty A’isha ta saka tana faɗin “Ita bata son wani gado, dan ta riga ta yi rashin da har abada ba zata mai da kamarsa ba, rashin adalin mijinta da kuma Abokiyar zamanta salihar mace.” Hajiya da Yayar Abba suka ce “Haba saurin me ake, ya bari Aunty A’isha ta fita daga takaba mana.” Amma ya ƙi, wai hakan shine dai_dai. Uncle Usman kuwa k’ala bai ce ba akan maganar ba. Maganar fa ta girmama har gurin manya, dole ba son ran su Aunty A’isha ba aka raba gadon. Kasancewar Neehal ita kaɗai ce ‘yarsu Abba ya sa a cikin kadarorin Umma da Abba ya mallaka mata kafin ya rasu sai da aka raba da su Uncle Umar, haka ma na Abba sai da aka raba da Yayarsa. Aunty A’isha ma aka bata tumunin takabarta. Gidan da suke ciki a gadon Neehal ya zo. Sai dai kuma wata sabuwa batun riƙon Neehal, da farko Yayar Abba ta so tafiya da ita Gabasawa amma akace hakan ba zai yiyu ba saboda ƙauye ne, ga kuma karatun Neehal ɗin, idan ta koma Gabasawa zata tawaya. Ƴan’uwan Abba kuwa da suke cikin Kano kowa ƙin ɗaukar ta ya yi, a ganinsu wahala zata zamar musu. Aunty A’isha kuwa tun farko ita ta ce a bata Neehal ɗin zata cigaba da riƙon ta, amma Uncle Umar yay ruwa yay tsaki ya ce ba za su ba da Neehal ga bare ba, tunda ba rasa dangin da za su rike ta ta yi ba, dan haka shi zai ɗauke ta. Ai Neehal na jin haka ta dinga kuka tana faɗin Ita “Gurin Aunty’nta zata zauna, babu inda zata je.” Amma Uncle Umar ya sawa idonsa toka, ya ce “Ko kukan jini za ta yi wallahi a gidansa zata zauna, shi zai cigaba da riƙon ta.” Aunty A’isha dama ba wani shiri take da shi ba, ta san ko zata mutu tana roƙon sa ya bata Neehal ba zai bata ba, kuma babu yanda zata yi da shi tunda ɗan’uwan mahaifiyarta ne, yafi ta kusanci da Neehal ɗin. Neehal tana ji tana gani Aunty A’isha suka haɗa kayansu ita da Hajiya suka wuce Gombe, tana kuka Aunty A’isha na yi, mutuwar Abba da Umma ta dawo musu sabuwa, duk mai imani idan ya gansu a wannan lokacin yanda suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi sai ya zubar musu da k’walla, amma Uncle Umar ko ajikinsa, Neehal har shid’ewa take saboda kuka. A ranar da suka tafin da daddare yasa ta itama ta haɗa kayanta kaf ya tasa ƙeyarta suka tafi gidansa tana ta faman tsiyayar hawaye, dan ya mata tsawa akan kar ya ƙara jin kukanta…………✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:46] Zeey Kumurya: ⚡NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
2️⃣8️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951