NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Tun daga ranar Neehal ce take wanke_wanke da shara da mopping da aiken gidan, yanda ka san baiwa haka Fauziyya ta mayar da ita, ga masifa da tsawa da bala’i. Wani matsifaffen tsoronta Neehal take ji, gashi idan Uncle Umar ya dawo ta haɗa wa Neehal sharri a gurinsa wai ta zage ta, haka zai zo yay mata masifa shi ma kamar zai dake ta. Kullum Neehal sai ta ci kuka ta gode Allah, kuma duk wani abu na amfani da Aunty A’isha ta sako mata acikin kayanta Fauziyya ta k’wace, kama daga MacLean, sabulan Wanka hatta bargonta duk ta k’wace. Yau kwanan Neehal goma sha biyu a gidan Uncle Umar, amma gaba-d’aya ta rame ta yi duhu saboda wahala, baza ka taɓa cewa itace yar gatan Ummanta da Abbanta ba. Kitson dake kanta ya tsufa ya dugurguje, ga farcenta ya fara taruwa, ta saba duk ran Friday Aunty’nta tana yanke mata, haka ma Mama idan tana gidanta, nan kuwa wanka ma ba kullum ake barinta ta yi ba. Ga rashin ishashshen abinci, abincin da yaro ɗan shekara biyar zai ci shi ake bata, shima kuma mara daɗi. Kullum da safe tana jin k’amshi ana soya k’wai da dankali amma ita ko ganin shi bata yi, haka ma naman miya ba’a bata ko gutsire. Misalin ƙarfe Uku na yamma Neehal ce tafe tana ta zuba sauri saboda gargadi’n da Aunty Fauziyya na mata akan kar ta daɗe, kayan miya zata siyo mata a can bakin titi, kuma daga gida zuwa bakin titi da ƴar tafiya, gaba-d’aya a gajiye take saboda aikin da tasha yau har da wankin kayanta ta yi, ga rana da ake k’walla wa a garin, gashi ba ta ci abincin rana ba kuma tana jin yunwa sosai gami da ƙishirwa, Aunty Fauziyya ta ce sai ta siyo mata kayan miyar sannan zata ci abincin. Ta shiga wani layi wanda daga shi sai titi, ta ga wani k’aton gida mai kyau, wani kyakkyawan matashi da ba zai wuce shekara 25 ba ne ya fito daga ƙaramar ƙofar gidan hannunsa ɗauke da robar ruwan faro mai sanyi. Tsayawa Neehal ta yi ta ƙura wa ruwan hannunsa ido tana maida Numfashi saboda gajiya, sau ɗaya matashin ya kalleta ya ɗauke kai ya nufi Motar dake fake a gaban gidan, Neehal ganin haka yasa ta ƙarasa kusa da shi da sauri ta ce………..✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
2️⃣9️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951
………..”Uncle please zan sha ruwa.” Kallonta ya yi fuska a sake ya ce “Oh sorry Dear take it.” Neehal ta karb’i ruwan da yake miƙa mata tare da faɗin “Thank you.” Murmushinsa Mai kyau ya mata, Neehal ta buɗe robar ruwan da sauri har tana yar da kuɗin kayan miyan bata sani ba, kai robar ta yi bakinta zata sha ruwan ya katse ta da sauri ta hanyar faɗin. “No, go there ki zauna sai ki sha.” Ya ƙarashe maganar tare da nuna mata wani dakali dake kofar gidansu. Da sauri Neehal ta ƙarasa ta zauna ta fara quqqutar ruwan, sai da ta shanye tass sannan ta yarda robar. Matashin yana tsaye yana kallonta, haka kawai ya ji ya kasa tafiya, Neehal ta dafe cikinta saboda k’ullewar da ya fara mata saboda yunwar da take ji. Cike da tausayawa Matashin ya sunkuya ya ɗauki kuɗin da ta yar a ƙasa ya ƙarasa inda take, cikin tausayinta da ya d’arsar masa a zuciya lokaci ɗaya ya ce “Are you Ok?” Neehal ta girgiza masa kai ta ce “I’m felling hungry.” Ya ce “Okay, sorry, wait for me here, I will come now.” Neehal ta gyaɗa masa kai tana ƙara dafe cikinta. Cikin 5 minutes ya shiga gidansu ya fito hannunsa ɗauke da Cake wanda aka yi rapping ɗinsa, sai kuma lemon jarka guda ɗaya. Miƙa mata ya yi ta karb’a da sauri tare da kallonsa, a hankali ta ce “Thank you so much.” Sannan ta fara cin Cake ɗin, ƙura mata ido ya yi ganin yanda take cin cake ɗin cikin nutsuwa tana lumshe ido, ita kuwa Neehal daɗi Cake ɗin ya mata ba kaɗan ba. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta ɗauki leman ta sha fiye da rabin jakar, ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce “Alhamdulillah.” Sai kuma ta miƙe zumbur kamar wadda aka tsikara ta fara ƙoƙarin tafiya, katse ta ya yi ta hanyar faɗin “Zo ki ɗauki sauran mana.” Neehal ta ce “Na k’oshi ne.” Ya ce “Are you sure?” Ta gyaɗa masa kai, ya ce “To ki tafi da shi gida anjima sai ki ci.” Neehal ta waro ido waje ta ce “Aunty zata dake ni idan na je da shi gida.” Miƙa mata kuɗin data yar ya yi ya ce “You forget.” Neehal ta karb’a da sauri ta wuce. Cake ɗin data bari da lemo ya ɗauka ya shige Motarsa, yana fita titi ya hango ta a gurin mai kayan miya, an yi sa’a ita ma ta juyo suka haɗa ido, d’aga mata hannu ya yi yana murmushi itama ta mayar masa da murmushin tare da d’aga masa hannun, a gurin ya samu almajiri ya bashi ragowar Cake ɗin da lemon. Cikin sauri Neehal ta siyi kayan miyan ta koma gida, zuciyarta cike da tsoron Aunty Fauziyya, wani ɓangaren na zuciyarta ta kuwa farinciki take yau ta ci Cake ta sha lemo. Da masifa Aunty Fauziyya ta tare ta, ita dai tay shiru kawai tana kallonta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Aunty Fauziyya cikin bala’inta ta ce “Shegiyar yarinya mai kama da aljanu, ana miki magana ki tsare mutum da wasu idanunki kamar na mage.” Ta kamo kunnen Neehal ta murd’e da ƙarfi tana faɗin, “Gobe ma in ƙara aiken ki ki kuma zuwa ki zauna.” Neehal ta saka kuka saboda zafin da ta ji a kunnenta, Aunty Fauziyya ta dungurar da ita a wurin tare da daka mata tsawar ta rufe mata baki. Kayan miyan ta wanke ta bata ta kai markad’e, ko tunanin bata abinci bata yi ba gashi har la’asar ta yi. Cikin mintuna ƙalilan Neehal ta dawo daga kai markad’en da yake anan mak’otansu ake babu nisa. Sai a sannan Aunty Fauziyya ta bata abinci a wani ɗan kwano, jallop ɗin shinkafa ce da cavage ce akai. Neehal ta kai abincin ɗaki ta ajiye a bayan kayanta, dan a koshe take. Aunty Fauziyya bata barta ta huta ba, sai da ta bata wankin uniform ɗin su Aiman, Neehal ta jijjik’a ta shanya dan ba wani iya wanki ta yi ba, sai dai tai ta goggoga sabulu ajikin kaya in ta ga ya yi kumfa sai ta d’auraye ta shanya. Bayan isha’i tana zaune a ɗaki tana yi wa su Aiman Homework, dan Yaran babu abun da suka iya sai dambe da zagi, ashar kala_kala sun iya narkawa kamar ƴaƴan maguzawa. Tun da Neehal ta zo gidan ita take musu Homework da Assignment ɗin islamiyya. Jin Uncle Umar ya shigo ta miƙe ta shiga falon ta gaishe shi, Allah ya so Aunty Fauziyya tana ɗakinta da sai ta k’ulla mata wani sharrin a gurinsa. Bayan ya amsa ta ce “Uncle Ina son na koma School da Islamiyya.” Uncle Umar ya ɗan bata rai ya ce “To je ki sai na duba.” Neehal ta tashi ta koma ɗaki ta cigaba da abun da take. Aunty Fauziyya ta fito daga ɗakinta tana yamutsa fuska ta ce “Me na ji yarinyar can tana ce maka ne?” Uncle Umar ya ce “Wai Makaranta take so ta koma.” Aunty Fauziyya ta haɗe sosai ta ce “Kai kuma saka ta a makarantar zaka yi?” Ya ce “To ya zan yi, tunda Allah ya ɗora mun.” “Ka dai ɗora wa kanka.” Aunty Fauziyya ta faɗa tana keɓe fuska. Uncle Umar ya ce “Hmmm, tunanin ma makarantar da zan kaita nake, amma ina ga makarantar su Aiman zan kai ta.” “Me? Makarantar su Aiman fa ka ce, dubu ashirin da biyar ɗin zaka biya mata? Tab’! To wallahi ka nemarwa kanka sauƙi, ka nemi Government School ka kaita.” Uncle Umar ya ce “Ai na ga babu Government School a kusa ne shi ya sa.” Aunty Fauziyya ta ce “Ga ta nan ana ginawa, ka bari idan an gama ginin sai ka kai ta mana.” Daga haka suke rufe wannan chapter, suka kama wata. Washegari bayan Neehal ta gama shan akinta kamar kullum aka aike ta siyan kayan miya, yau ma ba ta ci abinci ba ta tafi, gashi abun da bata ci ma Aunty Fauziyya ta yi wato tuwo, tuwon ma miyar kuka.