NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ku cigaba da haƙuri, ina yin garau za ku na samun Read more da yawa insha Allah.
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: ⚡NEEHAL ⚡
By
Zeey Kumurya
0️⃣2️⃣
………….A hankali ta tura ƙofar falonsa, ta yi sa’a kuwa ƙofar a buɗe ya barta, shiga ta yi gabanta na ɗan fad’uwa saboda sanin halin Yayannata da kuma tsoronsa da take masifar ji. Ya na zaune a kan kujera 2 seater ya jingina bayansa a jikin kujera idanunshi a lumshe hannunshi dafe da kanshi, Neehal ta ƙaraso kusa da shi a hankali idanunta k’ur a kansa, gabantane ya fadi ganin irin ramar da ya yi, dan ɗazu kwata_kwata bata lura ba, a ɗan ruɗe ta ce “Yaya!” Bai motsa ba balle ya nuna ya ji ta. Ba ta damu ba ta zauna a kusa dashi kamar za ta yi kuka ta kuma faɗin “Yayah ba ka da lafiya ne?” Shiru yay mata kamar ba zai amsa ba, sai kuma can ya d’ago da kansa ya na ɗan sauke numfashi ya dubeta, kallon ta ya yi na 3 seconds kafin ya daukey idonshi daga kanta tare da girgiza mata kai alamar a’a. Idanunta na kawo ruwa ta ce “Gashinan ka rame, Please yaya mai ke damunka?” Haɗe rai ya yi sosai har sai da gabanta ya fadi amma bai ce komai ba, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta wanda ta kasa tantance na banzan da ya yi da ita ne ko kuma na ganin shi cikin damuwa da ta yi?” Ta na hawayen ta ce “Yay……” cikin tsawa ya dubeta ya ce “Kin san bana son takura ko? tashi ki fita” turo ɗan karamin bakinta ta yi gaba ta na share hawayen fuskarta ta tashi ta fita, Bin ta ya yi da kallo ta ƙasan ido har ta fice, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida idanunshi ya lumshe zuciyarsa na masa ɗaci.
Haneefah ta dubi Neehal da ta tsaya jiki a sanyaye tun da ta dawo kitchen d’in ta ce “Besty me ya faru na ganki haka?” Neehal ta sauke ajiyar zuciya idanunta na cikowa da k’walla ta ce “Yaya ne” Haneefah ta ci gaba da juya miyar da take dan in da sabo ya ci ace ta saba da rashin shirin Neehal da Yayannata, kamar ba za ta kula da zancen ba sai kuma dai ta ce “Me yay miki kuma yau” Neehal cikin raunananniyar murya ta ce “Besty ba ki ga yanda Yaya ya rame ba, amma na tambayeshi meke damunshi shine ya ce mun bakomai, na roƙe shi ya faɗamun shine ya koro ni” Ta ƙarashe zancen hawaye na zubo mata akan kuncinta, Haneefah ta juyo ta fuskance ta, ta ce “Ni fa daɗina dake saurin kuka, yanzu mene abun kuka anan?” Neehal ta ce “Ba za ki gane ba ne Besty, amma ba ki ji yanda nake ji araina ba, ganin shi cikin damuwa da na yi” Haneefah ta ce “Tom shikenan ki yi masa addu’a, koma me ya ke damunsa Allah ya yaye masa ya kuma bashi lafiya” Neehal ta ce “Ameen” Haneefah ta ce “Yawwa ko ke fa, to share hawayennaki ‘yar Mama, kin san fa ke amarya ce ba na son na ga kina damuwa, kar mu kaiwa ya Anwar ke a rame” Neehal ta yi Murmushin yaƙe, saboda fad’uwar da gabanta ya yi, ta rasa me ya sa a duk lokacin da a ka yi zancen bikinta sai ta ji fad’uwar gaba, daurewa kawai ta ke yi, fita ta yi daga kitchen d’in domin ta je ta shirya, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da Mama zaune ta na karatun Alkur’ani mai girma, zama ta yi har Maman ta kai ƙarshen aya, Mama ta d’ago ta dube ta, ta ce “Kin gama girkinne?” Girgiza mata kai Neehal ta yi, Mama ta ce “Toh menene kuma na ganki haka?” Cikin damuwa Neehal ta ce “Mama Yaya ne na ga kamar bashi da Lafiya, kuma na tambayesa me ke damunsa ya ƙi faɗamun sai ma koroni ya yi” Mama ta ce “To ke halin Ameen ɗinne ba ki sani ba ko me? Kin san ba faɗa miki zai yi ba, wa ya aike ki?” Neehal ta b’ata fuska ta ce “To ba Yayana ba ne?” Mama ta ce “Kin ga Yayanki ai, Ni tashi ki je ki ƙarasa mun girki kar time ya k’ure ki bar Ni da shi” Neehal ta tashi tana turo baki gaba ta fita. Bedroom ɗinta ta shiga, rage kayan jikinta ta yi ta shiga toilet dan yin wanka.
K’arfe uku dan wasu mintuna Neehal ta gama shirinta cikin wata rantsatstsiyar doguwar rigar abaya maroon colour, wadda ta ji kwalliyar stones milk colour, rolling mayafin abayar ta yi, ta yi kyau sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba, daddad’an turarenta mai daɗin ƙamshi ta feshe jikinta da shi, zoben gold ta zira a ɗanyatsanta na tsakiyar hannun damanta, na kusa da shi kuma ta zira zoben azurfa mai kyan gaske, yatsun hannun hagunta suma fashion ɗin zobuna masu kyau ta sa musu guda biyu, tsadadden agogon hannu milk colour ta zira tare da abun hannu mai kyau, flate shoe mai kyau milk colour ta zira, wayoyinta dake kan mudubi ta kwasa ta zuba a cikin handbag ɗinta mai kyau itama milk colour. Light din ɗakin ta kashe ta janyo ƙofar ta fito ta sauko ƙasa. Haneefah ta kammala girkin cus_cus ɗin da Neehal ta ɗora, ta na zaune a falo Neehal ta sakko, Haneefah ta bita da ido tana murmushi ta ce “Kaga amaryar ya Anwar, kin yi kyau sosai” Neehal ta yi murmushi ta ce “Har na kai ki yin kyan?” Haneefah ta ce “Wane Ni, ke fa harkin fara irin shining ɗinnan na amare” Neehal ba ta kulata ba, ta nufi kitchen, Haneefah ta tashi ta koma kusa da Hajiya ta fara tashinta.
Hajiya ta buɗe ido a hankali tana salati, tashi zaune ta yi tana mutsitstsike ido, duban Haneefah da take dariya ƙasa_ƙasa ta yi ta ce “Ai dama nasan sai ke, dan Neehal dai ba za ta yi mun wannan muguntar ba, To ke da Allah, ina cikin baccina mai daɗi kin katsemun ko uban me zan miki idanna tashin Oho?” Haneefah ta tsuke fuska ta ce “Hajiya dan na tashe ki ki ci abinci ki yi Sallah, shine za ki ce mugunta, gani na yi ke bakya wasa da Sallah kuma lokacinta ya kusa” Hajiya ta ce “To yi haƙuri ai ban sa ni ba, yaushe ki ka zo gidan? ya kuma Maryam ɗin?” Haneefah ta ce ɗazu na zo ai, na tarar ki na ta sharar baccinki, Mommy kuma tananan Lafiya k’lu” sakkowar Mama ƙasa ya katse musu maganar da suke, Haneefah ta mik’e ta je ta yi hugging Mama. Mama na murmushi ta ce “Welcome, yaushe ki ka zo?” Haneefah ta ce “Na ɗan jima” Mama ta ce ” sannunki Ya Barrister?” Haneefah ta ce “Tananan klu” Mama ta kalli kofar kitchen ta ce “Neehal ba ta gama girkin ba ne, ta yi ta fito ku shirya ku tafi kar ku yi late” kafin haneefah ta ce wani abu Neehal ta fito daga kitchen d’in, Mama ta bita da kallo fuskarta ɗauke da mamakin ganin ta a shirye, Neehal ta ƙaraso kusa da su ta ce “Mama na gama abincin” Mama ta mata wani kallo ta ce “To sannu” Sannan ta juya ta kalli Haneefah ta ce “Kin taya ta girki ko?” Haneefah ta sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, Mama ta ce “Ba magana nake miki ba Haneefah?” Haneefah ta ce “Mama ƙarasa mata miya kawai na yi, na ce ta je ta shirya dan mu yi sauri mu tafi” Mama ta ce “Ba na ce ko sauke abu ki dena taya ta da shi ba, ki barta ta dinga yin komai da kanta” Haneefah ta gyad’awa Mama kai. Neehal ta ɗan turo baki gaba ta wuce za ta ɗauki jakarta, Mama ta ce “Kun ci abincinne?” Haneefah ta ce “Na k’oshi Mama, ina gama cin abinci na fito, sai dai idan mun dawo” Mama ta dubi Neehal ta ce “Ke fa?” Neehal ta ce “Ni ma haka” Mama ta ce tunda kin cika cikinki da kayan zak’i ba, ki wuce kitchen ki d’ebo abinci ki ci kar na ɓata miki rai” Neehal ta ɓata fuska, amma ba ta da zaɓi sai bin umarnin Maman, kitchen d’in ta koma ta d’ebo abinci kaɗan a plate ta dawo falon ta zauna a ƙasa ta fara ci kamar ba ta so, ta na ci ta na yamutsa fuska, kaɗan ta ci Mama ta ce ta tashi su tafi, tun da ɓata musu lokaci kawai take ba cin abincin za tay ba. Neehal na duban Mama da Hajiya ta ce “Sai mun dawo” “Mama ta ce ƙarfe nawa za ku dawo?” Neehal ta ce “8” Mama ta ce “8 ina Hospital” Neehal ta ce “Mama yau fa Saturday me za ki yi a Hospital kuma?” Mama ta ce “Akwai patients d’in da zan duba ne” Neehal ta ce “Toh, idan mun tashi zan biya Zoo road na siyo popcorn a’one” Mama ta ce “In ma a 10 ne ba damuwata ba ce, kin san Yayanki na gida ai, 8: 15 in ba ki dawo ba, ke da shi ne” Neehal ta ɓata fuska ta yi gaba, Haneefah ta yi wa su Mama sallama, Mama ta musu addu’a suka tafi, Hajiya na faɗin “Wai yaushe zaku kai ni gidan talabijin d’innan naku ne nima a hasko Ni a ciki?” Suna jin ta suka mata shiru. Parking space suka nufa suka shiga Mota Driver’n Neehal ya ja su zuwa ASTV fitaccen gidan TV’n da ya shahara a nan ƙasarmu Nigeria dama nahiyar Africa baki ɗaya.