NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣0️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………Sosai Ahmad yake jin nishad’i da farinciki a duk lokacin da suka kasance tare da Neehal, sai ya ji kamar kar ta tafi ta zauna tay ta masa hirarta da muryarta mai daɗin sauraro gami da sassayan murmushinta. Har cikin ransa yake jin wani abu game da yarinyar, a da yana tunanin tausayi ne kawai, amma yanzu duk da da akwai tausayin amma da wani abu daban da ya kasa gane ko menene. Babban tashin hankalinsa yanzu befi 1 month ya rage masa ya koma gidansu ba, dama a Abuja suke wani course ne ya kawo shi Kano, dan shi bai taɓa zuwa Kano ba sai wannan time ɗin, saboda duk Relatives ɗinsu a Abuja suke both na Mamanshi dana Dad ɗinsa. Mamy ma da a Abuja take, a wurin aiki ne aka yi posting ɗin mijinta zuwa Kano shine suka dawo, itama ba tafi two years da dawowa ba. Zuciyarsa babu daɗi ya ƙaraso gida, zama ya yi akan kujera yana sauke numfashi, a hankali ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa ya latsa ya shiga kallon pictures ɗin da yay wa Neehal d’azu, ta yi kyau sosai tana ta zuba murmushi.

Zuciyar Neehal cike da tsananin tsoro da fargaba ta ƙarasa gida, ba ta ga Aunty Fauziyya a tsakar gida ba, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙarasa kitchen ta ajiye kayan miyan sannan ta nufi falo, nan ma ba ta ga Aunty Fauziyyan ba, hakan ya sa ta wuce ɗakinsu tana sauke ajiyar zuciya. Yau wani daɗi take jin jikinta ya mata, to mamy ta dirje ta tass ta fitar mata da duk wani datti da daud’a dake jikin nata. Sai wajen magriba time ɗin su Aiman sun dawo daga islamiyya ta ji maganar Aunty Fauziyya, gabanta ya yanke ya faɗi saboda tsoro. Fauziyya wadda tun kafin la’asar ta kwanta take baccin asara sai yanzu yaranta suka tashe ta, ko sallar la’asar ba ta yi ba. “Neehal! Neehal!!” Ta shiga ƙwalawa Neehal kira, Neehal ta fito da sauri tana faɗin “Na’am Aunty.” Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta jefe ta da shi kamar kodayaushe, ta ce “Ina aiken dana miki?” Neehal ta ce “Na ajiye a kitchen.” Aunty Fauziyya ta ce “Yau ma sai da kika gama yawon naki sannan kika dawo ko?” Neehal ta girgiza mata kai cikin tsoro. Aunty Fauziyya ta ce “Hmm, munafukar yarinya, zaki yi bayani ne idan wanda ya ajiye ki ya dawo gidan, zaki faɗa masa inda kike zuwa ne, in ma iskanci kike zuwa ki yi duk za ki masa bayani.” Neehal dai tay shiru kanta na ƙasa. Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ƙara cewa “Taso ni mu je ki mun tsinta.” Neehal ta tashi ta bi bayan ta, a k’aton farantin silver ta zubo shinkafa yar Hausa ta ajiye a gaban Neehal ta ce ta tsince mata, Neehal ta kalli shinkafar ta kalle ta, ta ce “Aunty ban iya ba.” Rank’washinta Aunty Fauziyya ta yi sannan ta nuna mata yanda zata yi. Neehal fa ta duk’ar da kai ta fara tsinta, ga duhun Magriba ya kawo kai da ƙyar take gani. Fitila Aunty Fauziyya ta bata ganin magriba ta yi, Neehal ta ce “Aunty bari na yi sallah sai na cigaba.” Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce “Dalla ni ki cigaba da mun aikina, algungumar yarinya kawai, sai ka ce da Sallar kike, ko kuma in kin yi lada zaki samu.” (Allah ka raba mu da jahilci.) Neehal ta turo baki gaba ta cigaba da tsintar, Nasihar Abbanta da yake mata a kodayaushe ta tuno, inda yake ce mata “Ƴar albarkata ko me kike yi idan kika ji an kira Sallah ki bar shi ki je ki yi Sallah, idan kin idar sai ki ci gaba.” Tun tana ƴar k’ank’anuwarta yake faɗa mata haka. Hawaye ne ya zubo daga cikin idanunta, da sauri ta share su dan kar Aunty Fauziyya ta gani, Allah ya rufe wa Aunty Fauziyya ido ba ta ga canzawar da Neehal ta yi ba na gyara ta da Mamy ta yi, gashi kanta da hula shi yasa ba ta lura da gashinta da ya sha gyara ba, da yau Neehal ta shiga uku. Sai wajen isha’i ta gama tsintar, duk da shinkafar bata da tsinta sosai, amma saboda bata saba ba shi yasa ta daɗe, aiko da ƙyar ta iya tashi dan bayanta ya k’age, ga cizon sauro da ta sha, Aunty Fauziyya kuwa ko sannu sai ma tukwuicin harara ta samu. Kan kujera ta je ta kwanta, yau ta ci sa’a ba’a ce ta sauka ba. Bayan Uncle Umar ya dawo yana ɗakin baccinsu yana marking papers Aunty Fauziyya dake goge Uniform ɗin su Aiman ta dube shi ta ce “Baban Iman inata zuci_zucin ka dawo in faɗa maka wani hali da yarinyar can ta tsira.” Ba tare daya d’ago ba ya ce “Wacce yarinya kenan?” Ta ce “Neehal mana.” Ya ce “Me kuma ta yi.” Ta tab’e baki ta ce “Hmm, yawon banza ta koya, idan na aiketa sai ta yi awa uku a waje, ƴar ƙarama da ita har ta san wani bin maza.” Da sauri Uncle Umar ya d’ago ya dubi Aunty Fauziyya ya ce “Haba Fauziyya, yarinyar da ba ta fi shekara goma sha ɗaya ba ita zaki ce tana bin maza? Ki dai sake wata maganar ba wannan ba gaskiya.” Aunty Fauziyya ta ce “Lallai Umar me kake nufi? Sharri zan mata ko me? Kuma idan ba maza take bi ba gidan ubanwa take zuwa idan na aike ta, har ta yi awanni.” Uncle Umar ya ajiye red biron dake hannunsa tare da miƙewa a fusace ya ya fito falo. Neehal dake kwance rub da ciki akan kujera har lokacin, ta ɗan samu baccin gajiya ya ɗauke ta ji murya Uncle Umar a tsawace yana cewa “Ke Neehal! Neehal!” A firgice ta farka tare da buɗe ido, cikin muryar bacci ta amsa masa tana ƙoƙarin tashi zaune cikin tsoro. “Gidan uban wa kike zuwa idan an aike ki?” Uncle Umar ya tambaye ta cikin tsawa, Neehal ta manne jikinta ba ta ce komai ba, Uncle Umar ya ƙara daka mata wata tsawar da faɗin “Ba dake nake ba.” Neehal bata iya ƙarya ba, hakan yasa ta fashe da kuka dan ta san idan ta faɗawa Uncle Umar inda take zuwa sai ya kusa kashe ta da duka. Masifa ya dinga surfa mata, ya kuma ce aka kuma aiken ta ta daɗe sai ya karya k’afarta. Ba ƙaramin tsorata Neehal ta yi da Uncle ɗin nata ba, hakan yasa washegari bata biya ta gidansu Ahmad ba. Shi kuwa tun da ya yawo daga inda yake zuwa aiki yake ta zuba idon ganinta amma ya ji ta shiru har yamma. Yau data koma da wuri Aunty Fauziyya ta ce “Ehh lallai, wato ni kika raina shi yasa ba kya jin maganata, shi da kike tsoronsa gashi ai kin ji faɗan sa.” Ta ƙarashe zancen tare da jan k’wafa. Neehal kam tunanin Uncle ɗinta Ahmad ta shige ɗaki tana yi, ta san yanzu ya siyo mata kayan daɗinta yana jiran ta je ta ci. Yau kwana uku Neehal bata je gidansu Ahmad ba, kullum sai dai ta kalli gidan ta wuce.

Misalin ƙarfe 2/30mp Aunty Fauziyya ta aiki Neehal siyan kayan miyan gado, dan shi kaɗai ne aikenta tunda komai na abinci Uncle Umar ya siyo ya dire, sai kuma markad’e idan babu wutar Nepa. Babu musu ta karb’a kamar kodayaushe ta tafi. Yau ma kallon gidansu Ahmad ta yi ta wuce duk kuwa da yanda zuciyarta take azalzalarta akan ta shiga, amma tsoron abun da Uncle Umar zai mata idan Aunty Fauziyya ta faɗa masa yasa take ƙin shiga. Tana shan kwana Motar Ahmad na shigowa layin, cikin tsananin murnar ganinta Ahmad ya taka burki wanda har yasa ta tsorata ta yi baya. Da sauri ya buɗe murfin Motar ya fito, da mamaki ya ce “Princess.” Neehal ta washe baki ta ce “Uncle ɗina ina yini.” Ya ce “Lafiya k’alau Princess, me yasa kwana biyu ba kya zuwa.” Neehal ta ce “Uncle ne ya hana ni, ya mun faɗa sosai, He said in aka ƙara aike na na daɗe sai zane ni.” cikin rashin jin daɗi Ahmad ya ce “Ayya I missed you alot dear.” Neehal ta ce “Me too Uncle.” Ahmad ya ce “Mu je gida in baki cake da sweet ɗinki.” Da murnarta ta ce “Toh.” Yanayin garin damuna ta fara shigowa dan shekaran jiya ma an yi ruwa, yau ma garin ya yi luf kamar hadari_hadari. Gashashshiyar kaza Ahmad ya bata da yoghurt, Neehal ta zauna ta ci ta k’oshi tay hamdala. Mantawa ta yi da wani tsoron Uncle Umar ta zauna ta shiga yi wa Ahmad hira, shi kuma yana ta aikin murmushi cikin jin daɗi da nishad’i, sai yanzu da ya ganta ma ya ƙara tabbatar da ya yi kewar ta sosai. Kiran sallar la’asar ne ya tashe su, Ahmad ya yi alwala suka fita tare ya rakata ta siyi kayan miyan sannan ya wuce masallaci ita kuma ta nufi gida. Zuwa lokacin hadari ya ƙara haɗuwa sosai har an fara Iska, sauri Neehal tay ta yi kar ruwa ya sauko tana waje, aiko ana idar da Sallah aka fara yayyafi, da gudu ta ƙarasa gidan dan har ta fara jik’ewa, kitchen ta nufa zata ajiye kayan miyan amma sai ta tarar da shi a kulle da mukulli, ga ruwan ya fara ƙarfi. Ƙofar falon ta dawo ta fara bugawa da ƙarfi tana faɗin, “Aunty! Aunty, na dawo ki buɗen ƙofa!” Amma Fauziyya tana ji ta ƙi buɗe ƙofar, gashi kaf tsakar gidan babu gurin fakewa, dan ko toilet babu duka suna cikin ɗaki, kitchen ne kawai kuma ta kulle. Gashi irin gidan nan ne da kana buɗe gate ɗinsa sai tsakar gida babu soro. Haka Neehal ta takure jikinta cikin ruwan dan bata da yanda zata yi, cikin ikon Allah kuma ruwan ya tsuge kamar da bakin kwarya, Neehal ta runtse ido tana jin saukar ruwan ajikinta. A hankali kuma ya fara ɗaukewa, sai da ya ɗauke dif sannan Aunty Fauziyya ta buɗe ƙofar falon ta fito, Neehal na tsugunne a bakin ƙofar sai rawar ɗari take saboda sanyi ta ci kuka ta gode Allah. Aunty Fauziyya ta ɗauke kayan miyanta tare da faɗin “Kar ki shigar mun ɗaki kina yarari, ki jik’a mun ɗaki.” Neehal ta miƙe ta cire komai na jikinta ta shanya a igiya, pant kawai ta bari sannan ta shige falon da sauri. Aunty Fauziyya tay dariyar mugunta ta ce “Gobe ma kya ƙara tafiya gantali Shegiyar yarinya kawai.” Ita kam tana shiga ɗaki ta yi toilet ta cire pant ɗin jikinta ta rarumi towel ta ɗaura a jikinta sannan ta tsugunna ta yi fitsarin daya matse ta. Tana fitowa ta hau kan katifa ta ja bargonsu Aiman ta lullub’a. Aiko kafin dare mura ta mata mugun kamu, ranar da tari ta kwana. Washegari duk masifar Aunty Fauziyya ba ta saka ta aiki ba, dan jikin nata ya yi zafi ba kaɗan ba, ta san ma ko ta saka ta ba iyawa zata yi ba shi yasa. Amma ta sha zagi da masifa, a cewarta cutar ma ta ƙarya ce da shegen rakin tsiya. Kwana huɗu ta yi a kwance, a ran na biyar ne ta fara samun sauƙi, shi ma sai da Uncle Umar ya ga ciwon ya ƙi ƙarewa sannan ya kaita chemist aka bata magani, aiko suna tafe yana mitar ta ja masa asarar kuɗin da ya siya mata magani, maganin da ko 1K bai kashe ba, alhalin kuma dukiyarta da duk wata kadararta tana hannunsa. Bayan ta warware aka cigaba da aikenta, kullum sai sun haɗu da Ahmad amma ta daina shiga gidansu sai dai su haɗu a ƙofar gida, yasan lokacin da ake aikenta, dan haka time ɗin yana yi zai fito ƙofar gida ya zauna zaman jiranta, saboda ta bashi labarin dukan da ruwa ya mata har ya sata zazzaɓi akan ta daɗe ranar, shi kuma saboda tsananin tausayinta shi yasa ya daina tsayar da ita, dan kar a ƙara yi mata wata muguntar. Amma duk da haka bai daina bata abubuwan da yake bata abaya ba, idan ta je gurin mai kayan miyan akwai benci wanda dan customers aka tanade sa, anan take zama ta yi sauri ta cinye abun da ya batan sannan ta koma gida. Haka rayuwa tay ta tafiya da Neehal a gidan Uncle Umar cikin wahala da azaba kala_kala a gurin Aunty Fauziyya, gurin Ahmad kawai take jin daɗi, gashi ta yi magiyar a saka ta a makaranta an ƙi, har ta gaji ma ta dai na, sai ɗan lesson ɗin da Ahmad yake mata atsaitsaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button