NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Yau ma bayan Neehal ta gama shan ayyukanta tana zaune a kitchen tana juya miyar da Aunty Fauziyya take soyawa, ta shiga ɗaki ne shine ta ce Neehal ɗin ta cigaba da juya mata dan kar ta roqe. Wayar Aunty Fauziyya dake kitchen ɗin ce ta fara ringing, cikin ɗan daga murya Neehal ta ce “Aunty ana kiran ki a waya.” Aunty Fauziyya bata amsa mata ba sai turo Aiman ta yi ya ɗauko mata wayar, kasancewar yau Friday ce suna gida. Aiman yaro ne mai k’iriniya baya abu cikin nutsuwa ko kaɗan, da gudu ya shigo kitchen ɗin ya ɗauki wayar, ya zo fita ya b’arar da taliyar da Aunty Fauziyya ta tace kafin ta bar kitchen ɗin, fiye da rabin taliyar ya zube a ƙasa. Neehal ta tashi da sauri tana faɗin “Ka ga ka yi ɓari ko?” Aiman bai saurare ta ba ya yi ɗaki da gudu yana kiran uwarsa, Aunty Fauziyya ta taso da sauri tana faɗin “Mene ne.” Ya ce “Aunty Neehal ce ta b’arar miki da taliya.” Ai bai ƙarasa ba Aunty Fauziyya ta fito a fusace ta shiga kitchen ɗin, Tafa hannuwa ta shiga yi tana faɗin “Eh lallai, tun da ba Ubanki ne ya nemo ba ba kuma Uwarki ce ta dafa ba ai dole ki b’arar.” Neehal ta ce “Aunty ba fa ni na b’arar ba Aiman ne.” Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce “Rufe mun baki zaki ne bayani ne, shegiya mai baƙin hali, kwashe mun ita tass da hannunki, idan kin gama kuma ki zo ɗaki ki karb’i hukuncinki.” Neehal ta sa hannu ta fara kwashe taliyar, ga taliyar sai tururi take saboda ba a daɗe da sauke ta ba, Aunty Fauziyya tana barin kitchen ɗin Neehal ta ɗauki serving spoon ta cigaba da kwashe wa da shi, saboda hannunta zafi. Sai da ta kwashe duka sannan ta debo ruwa ta d’auraye ta. Ɗakin ta nufa cikin tsoro ta ce “Aunty na gama.” Aunty Fauziyya tay wani murmushi ta ce “To ƙaraso mana kika tsaya a bakin ƙofa.” Cikin ɗari ɗari Neehal ta ƙarasa idanunta taf da ruwan hawaye. Aunty Fauziyya ta kamo hannunta, kuka ta saka ta ce “Aunty dan Allah ki yi haquri.” Aunty Fauziyya ba ta kula ta ba, ta kamo hitar data jona a jikin socket ta ɗora a ƙafar Neehal. Wani irin zirrrrr Neehal ta ji ajikinta na shock ta ji kamar an d’aga ta sama. Ai bata san sanda ta k’wala ihu mai ƙarfi ba tare da fizge jikinta ta fice daga Falon da mugun gudu, gaba-d’aya jikinta rawa yake kamar mazari, cikin fitar hayyaci ta fice daga gidan gaba-d’aya, gudu take da dukkan ƙarfinta gani take kamar Aunty Fauziyya ta biyo ta zata ƙara sa mata shock ajikinta. A ƙofar gidansu Ahmad sukai cikibus, ya dawo daga masallaci da Darduma a hannunsa. Neehal ta ƙarasa gare shi ta riƙe shi gam tare da sakin kuka, har lokacin jikinta rawa yake. A ruɗe Ahmad ya shiga kiran sunanta “Princess! Princess what happened to you?” Yana ƙoƙarin d’agota daga jikinsa, ita kuwa ƙara k’ank’ameshi ta yi. Fahimtar da ya yi a firgice take sai kawai ya sunkuce ta ya shiga cikin gidan da ita. A kan kujera ya kwantar da ita, cikin kulawa ya ƙara tambayar ta da faɗin “Princess mene ya faru? kika fito ko takalmi babu a ƙafarki.” Cikin kuka ta ce “Un… Uncle shocking Aunty ta samun a jikina.” A ruɗe ya ce “Subhanallah shocking kuma Princess?” Bai jira amsar ta ba ya miƙe da sauri ya nufi ƙaramin kitchen ɗin dake falon ya ɗauko gwangwanin pick milk ta ruwa ya fasa ya juye ta a glass cup, sannan ya fito ya dawo gurin da take a kwance tana ta sauke numfarfashi. Ɗago kanta ya yi ya kafa mata cup ɗin a baki. Ba musu ta shiga sha. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta lumshe idanunta ta koma ta kwanta, Ahmad nata jera mata sannu cikin tsananin tausayinta. Ranshi ba ƙaramin ɓaci ya yi ba yau game da Aunty Fauziyya, ya rasa matsayin da zai ajiye matar akan rashin imani, da Mamy zata ji maganar nan yanda take da zuciya ya san tsaf zata iya kaita a kulle. Ƙura mata ido ya yi da idanunsa da suka fara canza launi saboda ɓacin rai, yana jin wani abu na fizgar zuciyarsa game da Neehal ɗin. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta akai_akai alamun bacci ya ɗauke ta, gyara mata kwanciya ya yi yanda zata fi jin daɗin baccin. Babbar damuwar Ahmad a duniya ɗaya ce a halin yanzu, jibi Sunday zai koma gidansu Abuja, tun last week ya gama abun da ya kawo shi Kano, amma saboda Neehal ya kasa koma wa gida, gashi parent ɗinsa sun matsu ya dawo, kasancewar shi kaɗai ne ɗansu Namiji, dama su biyu ne a gurin iyayensu daga shi sai ƙanwarsa mace, ƙanwar tashi ma ƙarama ce bata fi 4_5 years ba, 20 years ya bata. Sai bayan la’asar Neehal ta farka, ya je masallaci ya dawo ya tatar ta tashi. Ya ƙarasa kusa da ita ya ce “Kin tashi.” Ta ce “Ehh, Uncle ka kai ni gurin Mamy na yi wanka, jikina babu daɗi.” Ya ce “Mamy bata nan, amma bari na kai ki ki yi anan.” Ta ce “Toh.” Toilet ɗin dake cikin bedroom ɗinsa ya kai ta, Brush ya bata sabo da MacLean ta wanke bakinta, sannan ya haɗa mata ruwa mai dumi ta yi wanka. Bayan ta shirya ya kawo mata abinci da drinks ta zauna ta ci. Tana gamawa ta ce “Uncle Thank you so much.” Tattausan murmushinsa ya mata ya ce “Say Alhamdulillah.” Itama murmushin ta masa ta ce “Alhamdulillah.” Sannan ta tashi ta kwashe kayan ta kai kitchen, ta so tafiya gida amma ya zaunar da ita wai ta masa hira, ba musu ta zauna tana shan choculate tana masa hirar, shi kuma sai murmushi yake yana mata video a wayarsa. Sai gab da magriba suka fito daga gidan, a ƙofar gidan ya tsaya tare da hard’e hannayensa a ƙirji ya zuba mata ido. Neehal ta ce “Uncle bye.” Tare da d’aga masa hannu, numfashi ya sauke cikin wata irin murya ya ce “Princess!” Ta ce “Na’am Uncle ɗina.” Kusa da ita ya matso sosai ya kama hannunta cikin sanyin murya ya ce “I love You!” Neehal ta yi murmushi ta ce “Love You too Uncle.” Lumshe idonsa ya yi cikin jin daɗi, a hankali kuma ya sunkuyo ya yi picking forehead ɗinta sannan ya sakar mata hannunta, har ta fara tafiya ya ƙara kiranta, ta dawo da sauri, tsugunna wa ya yi dai dai tsayinta yana kallon cikin idonta ya ce “Princess, promise me you will never forget me in your life.” Neehal ta ce “I promised you Uncle.” ya ce “Sure?” Ta gyaɗa masa kai. Fuskarta ya shafa ya ce “Thank you dear.” Neehal ta masa bye_bye sannan ta juya ta fara tafiya, haka kawai ta ji jikinta ya mata wani irin sanyi. Shi kam Ahmad tsayawa ya yi yana kallonta yana jin jikinsa kamar babu laka ba tare da yasan dalili ba. Duk wannan abun da ya faru tsakanin Neehal da Ahmad Uncle Umar yana farkon layin akan machine ɗinsa yana kallonsu cikin tsananin ɓacin rai, yana shago Aunty Fauziyya ta kira shi akan ya zo gida babu lafiya, dan tun safe Neehal ta fita kuma har yanzu bata dawo gida ba, shine fa ba shiri ya baro shagon ya taho, yana shigowa layinsu Ahmad dai-dai lokacin su kuma su Neehal sun fito daga gidansu Ahmad, cikin shock ya tsaida machine ɗinsa ya tsaya yana kallonsu. Neehal ta juyo ta ga ko Ahmad ya shige gida idanunta suka sauka akan Uncle Umar wanda ya figo machine ɗinsa a fusace……….✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣1️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button