NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Uncle Usman yana fita direct titi ya yi da Neehal saɓe a kadararsa cikin sauri_sauri gudu_gudu. Yana fita titin ya tsari a daidaita ya ce ya kai shi asibiti mafi kusa da sauri dan Allah, bayan ya shiga mai a daidaitan ya ja suka tafi. Cikin mintuna ƙalilan suka ƙarasa wani private Hospital, bayan ya sallami mai adaidaita ya shiga ciki rungume da Neehal a jikinsa. Cikin sauri wasu Nurses guda biyu suka karb’i Neehal suka nufi wani ɗaki da ita dan bata taimakon gaggawa. Uncle Uwar ya zauna a reception ɗin asibitin tare da dafe kansa da hannunsa ɗaya, a hankali yake fuzgar da zazzafan numfashi cikin tsantsar ɓacin rai. Tabbas kowa ya shaida Uncle Usman yana da haquri da sanyin hali gami da sauqin hali, amma fa bai iya ɓacin rai ba. Har aka kira Magriba likitocin dake duba Neehal ba su fito ba, hakan yasa ya miƙe ya nufi masallaci. Bayan ya dawo ɗaya daga cikin Nurses da suka karb’i Neehal ta ce masa “Yawwa malam ka shiga wancan office ɗin Doctor zai yi magana da kai.” Uncle Usman ya ce “Toh.” Tare da nufar office ɗin. Bayan ya shiga sun gaisa likitan ya dube shi ya ce “Kai waye ɗinta?” Uncle Usman ya ce “K’anin mahaifiyarta ne.” Doctor ya ce “Ina mahaifiyarta ko mahaifinta?” Uncle Usman ya ce “Sun rasu.” Doctor ya jinjina kai ya ce “Allah ya ji k’ansu da rahama.” Uncle Usman ya ce “Ameen, amma ya jikin nata Doctor?” Doctor ya ce “Alhamdulillah, dan ta farfaɗo daga suman da ta yi sanadiyyar dukan da aka mata, kuma mun mata allurar rage zugi da zazzaɓin daya rufe ta lokaci ɗaya, ga wannan magunguna ne muka rubuta za a siyo yanzu kafin ta farka, sannan kuma zaka je ka biya kuɗin gado da sauran abubuwa.” Ya ƙarashe zancen tare da miƙewa Uncle Usman wata takarda. Uncle Usman ya sauke numfashi ya karb’i takardar ya ce “Zan iya ganin ta yanzu Doctor?” Ya ce “Eh, idan ka fita daga nan room mai kallo ka nan zaka shiga.” Uncle Usman ya ce “Toh Na gode sosai Doctor.” Likita ya ce “Allah ya ƙara sauƙi, nan gaba kuma a kiyaye da dukan ƙananun yara irin haka dan wataran ba za su tashi ba.” Ƙasa Uncle Usman ya yi da kansa ya ce “Insha Allahu.” Tare da ficewa daga office ɗin. Tana kwance a kan gadon asibitin tana bacci an saka mata drip. Kallonta yake cike da tausayawa, sai ajiyar zuciya take saki a kai_kai alamun ta ci kuka ta k’oshi. Ko ina ka kalla a jikinta ya yi jajur saboda duka. Uncle Usman ya shafa kanta ya ce “Allah ya baki lafiya my baby.” Sannan ya fice dan siyo mata magani. Ba jimawa ya dawo da katan ɗin ruwan jakar da yoghurt da kayan fruits. Ganin bata farka ba ya dubi Nurse ɗin da take duba ruwan da aka saka mata ya ce zai je ya dawo. Sai da ya yi Sallar isha’i sannan ya dawo bayan ya siyo mata Balango mai yawa a leda. Zama ya yi akan kajerar dake fuskantar gadon da take a kwance ya zaro wayarsa daga aljihu wadda ake ta kira tun zuwansa asibitin ba jima wa. Missed call ɗin Ummi (Yayar Abba) ya gani sai na Uncle Umar rurutu da kuma na wani abokin kasuwancinsa. Bai bi bayan kiran ɗaya daga cikinsu ba saboda wani dalili nasa, sai ma Numbern budurwarsa daya kira. Ringing biyu ta d’aga, bayan sun gaisa ya ce “Halima dan Allah idan babu damuwa zan zo gida na karb’i aron blanket da darduma, muna asibiti ne Neehal babu lafiya.” Halima ta ce “Subahanallah, me ya same ta?” Uncle Usman ya ce “Zazzaɓi take shine aka bamu gado.” Halima ta ce “Allah ya sauqaqe, ka zo ka karb’a babu matsala.” Godiya ya mata sannan suka yi sallama ya katse wayar. Wata Nurse ya ƙara ba wa amanar Neehal sannan ya bar asibitin. Gidan su Haleemah da ɗan nisa daga asibitin, hakan yasa sai da tara ta wuce ya dawo da kaya a hannu, dan har da su plates da cups da spoons sai da Halima ta haɗo shi da su, shi kuma ya biya ya siyo wa Neehal sabon brush da sosan wanka da su sabula da ƙaramin macLean gami da takalmi slifas. Sai wajen goma Neehal ta farka a zabure cikin dashashshiyar muryarta take faɗin “Uncle ka yi haquri dan Allah ba zan kuma ba.” Uncle Usman ya tashi da sauri yana cize lips ɗinta saboda takaici ya ƙasara gaban gadon. Kama hannunta ya yi ya ce “Neehal!” Neehal ta buɗe kumburarrun idonta da sauri ta ce “Uncle ɗina.” Uncle Usman ya ce “Na’am Neehal, sannu kin ji, ya jikin naki?” Gyaɗa masa kai ta yi tana bin shi da kallo alamun tana cikin mamakin ganin sa. Shafa fuskarta ya yi ya ce “I’m coming Baby.” Fita ya yi da sauri ba jimawa sai ga shi sun dawo da likita, dudduba ta ya yi bayan ya mata sannu sannan ya cire mata drip ɗin hannunta da ya ƙare a lokacin. Magungunan da Uncle Usman ya siyo Doctor ya nunnuna masa wanda zai bata yanzu. Uncle Usman ya masa godiya sannan ya fita. A hankali Neehal ta ce “Uncle zan sha ruwa.” Uncle Usman ya tayar da ita zaune ya sa mata filo a bayanta ta jingina da shi yana mata sannu. Ruwa ya dauko ya buɗe mata sannan ya kafa mata a baki, kaɗan ta sha ta cire robar daga bakinta. Lumshe ido ta yi ta ce “Uncle ina Uncle Umar da Aunty Fauziyya?” A dak’ile Uncle Usman ya ce “Suna gida.” Neehal ta buɗe idonta da ya cika da hawaye ta ce “Please Uncle ka ba su haquri su daina duka na.” Uncle Usman ya ce “Shikenan kar ki yi kuka kin ga baki da lafiya.” Neehal ta gyaɗa masa kai ta ce “Uncle ka kira mun Aunty, idan na cewa Uncle Umar ya kira mun ita baya kiran ta.” Uncle Usman ya ce “Yanzu dare ya yi ki bari sai da safe in Allah ya kai mu.” Zata kuma magana ya katse ta da faɗin “Ki yi shiru haka kin ga baki da lafiya.” Neehal ta ce “Toh.” Ya ce “Yawwa good girl mu je in kai ki ki yi brush sai ki ci abinci.” Kamata ya yi a hankali ganin yanda take yamutsa fuska alamun tana jin ciwon jikinta ya kai ta toilet ɗin ya taimaka mata ta yi brush, sannan ta yi fitsari ya kama ta suka fito. Zaunar da ita ya yi ya ɗauko balangon da ya siyo ya juye a plate ya janyo kujera gabanta ya fara bata a baki, kaɗan ta ci ta ce ta k’oshi saboda bakinta da babu daɗi. Banana ya bata ta ci ɗaya da ƙyar, sannan ya bata magungunanta ta sha ta kora da ruwa. Bayan 5 minutes ya kwantar da ita sannan ya dauk’o blanket ya lullub’e mata jikinta. Neehal tana duban sa ta ce “Yaushe ka zo Uncle?” A tak’aice Ya ce “D’azu, inane yake miki ciwo yanzu?” Neehal ta ce “Kaina da duka jikina.” Uncle Usman ya ce “Ki rufe ido ki yi bacci, Insha Allahu in kin tashi da safe zaki ji kin warke.” Neehal ta gyaɗa masa kai tare da murmushi cikin jin daɗin ganin sa. Shi ma murmushin ya yi ya ce “Ki yi addu’a kin ji daughter.” Neehal ta gyaɗa masa kai tare da lumshe idonta.
Washegari bayan Uncle Usman ya dawo daga masallaci ya tarar Neehal ta tashi zaune. Da mamaki ya ce “Har kin tashi?” Neehal ta ce “Ehh, ina kwana Uncle.” Uncle Usman ya ce “Ai sai an yi Sallah ake gaisuwa.” Neehal ta fara ƙoƙarin saukowa daga kan gadon tana faɗin “To bari na je na yi alwala sai na yi sallah.” Cikin jin daɗi Uncle Usman ya ce “Jiki ya yi sauqi kenan Masha Allah.” Neehal ta sauko daga kan gadon ta shiga toilet, duk da bata gama jin jikin nata dai-dai ba amma zazzaɓin da ciwon kai sun mata sauqi sosai, jikinta ne dai take jin shi da ɗan tsami saboda dukan da ta sha. Bayan ta fito ta tayar da Sallah akan darduma, duk da bata da Hijab sai ɗan kwalinta ta yafa. Uncle Usman ya zuba mata yughurt ɗin da ya siyo jiya a cup ya bata. Ta sha sosai kuwa saboda da yunwa ta tashi. Wajen 7 da wani abu sai ga Haleemah da ƙanwarta sun zo duba Neehal, dan jiya da Uncle Usman ya je ya faɗa mata asibitin da suke, amma ya yi mamaki lokacin data kira shi ta faɗa mishi ta shigo asibitin ya zo ya ɗauke ta, domin bai taɓa tunanin zuwanta da safiya haka ba. Da k’aton tea flaks ɗinta kuwa wanda ta ciko da ruwan zafi kamar ta san za su buƙata. Basu wani jima ba suka tafi. Tea mai kauri Uncle Usman ya haɗa wa Neehal ta sha sannan ya bata magungunanta suma ta sha. Cikin dabara Uncle Usman yake tambayar Neehal tana faɗa masa irin zaman da take a gidan Uncle Umar. Sosai ransa ya ɓaci fiye da jiya da ya ji irin azabtar da Neehal da Aunty Fauziyya take. Wayarsa ya ɗauko ya bi kiran da Uncle Umar ya masa jiya, ringing ɗaya Uncle Umar ya d’aga tare da faɗin, “Usman wannan wanne irin iskanci ne, zaka ɗauke yarinya tun jiya kuma dan wulaqanci inta kiran ka ka ƙi d’agawa, ina ka kai ta to?” Uncle Usman ya ce “Asibiti na kai ta dan ceto rayuwarta.” Ya faɗa masa sunan asibitin sannan ya kashe wayar. Da ruwan zafin da Halima ta kawo Uncle Usman ya haɗa wa Neehal ruwan wanka ta yi, kayan jikinta da ta cire ya ce ta mayar anjima zai ɗauko mata wasu a gidan Uncle Umar. Wajen 8:40 Likita ya zo ya ƙara duba ta sannan ya mata allura, tana kukan allurar bacci ya ɗauke ta.