NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ganin ta yi bacci Uncle Usman ya lalubo Numbern Aunty A’isha ya kira ta, sai da ta kusa katsewa sannan ta d’aga bakinta ɗauke da Sallama. Uncle Usman ya amsa ya ƙara da faɗin “Ina kwana Aunty dafatan kin tashi lafiya, ya su Hajiya?” Aunty A’isha ta ce “Lafiya k’alau Uncle Usman, su Hajiya suna nan k’alau, ya kwana biyu da bayan saduwa? inata kiran wayarka data Uncle Umar duk bana samun ku dafatan dai lafiya?” Uncle Usman ya ce “Lafiya k’alau, ai yanzu na koma Niger da kasuwancina ne, to idan ina can sai na sauke wannan layin, ina ta son na kira ki amma sabgogi sun sha mun kai, jiya_jiya ma na shigo garin.” Aunty A’isha ta ce “Allah sarki, Allah ya taimaka ya ba da sa’a, wancan satin ai na fita daga takaba.” Uncle Usman ya ce “Ikon Allah, lokaci ba wahala har kin fita, Allah ya ji k’an su Yaya.” Aunty A’isha ta ce “Ameen ya Allah, a satin nan ma nake son shigowa Kano zamu zo siyayya bikin Sadiya ya kusa, ya labarin Neehal kuwa? kana zuwa kana ganin ta? Kullum da ita nake kwana nake tashi a raina, kwanaki ma na so zuwa na ganta Hajiya ce ta hana ni ta ce in bari na fita daga takaba tukunna.” Uncle Usman ya ce “Hmm, bari kawai Aunty wallahi Neehal wahala kawai take sha a gidan Ya Umar gurin Matarsa, yanzu ma muna asibiti bata da lafiya saboda dukan da suka mata jiya.” A ruɗe Aunty A’isha ta ce “Subahanallahi, Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, asibiti kuma? Wannan wanne irin duka ne haka? ashe shi yasa jiya na wuni da tunaninta a cikin zuciyata, har na kasa daurewa sai da na yi zancenta a gida, Hajiya ta ce na kwantar da hankalina ai na kusa zuwa na ganta, ya jikin nata yanzu?” Uncle Usman ya ce “Da sauƙi Alhamdulillah, yanzu ma bacci take yi, Nima shekaran jiya na kira Ummi mun yi waya ne ta ce dan Allah in daure in je in dubo mata Neehal, ta tura ƴaƴanta sun ce ba su san gidan ya Umar ɗin ba, ita kuma tana fama da ciwon ƙafa baza ta iya zuwa ba, shine na zo na tarar da wannan abun takaicin. Wallahi Aunty A’isha baki ga ni ba, abun tausayi gaba-d’aya Neehal ta lalace ta yi baƙi ta rame duk ta fita hayyacinta.” Aunty Aisha tana hawaye ta ce “Shi yasa naso tafiya da ita amma Uncle Umar ya hana ashe rabon wahala ne yake kiranta.” Uncle Usman ya ce “Kar ki damu Aunty daga nan Gombe zamu zo na kawo miki Neehal da zarar ta ji sauƙi, ai kuma ta gama zama a gidan Ya Umar.” Aunty A’isha ta ce “Kana ganin Uncle Umar ɗin zai yadda Neehal ta dawo gurina da zama?” Uncle Usman ya ce “Kar ki damu da wannan na san me zance masa kuma dole ya bari. Amma dan Allah Aunty kar ki tada hankalinki fa komai ya zo ƙarshe ai dan zuwa gobe ma za’a iya ba mu sallama tunda ta ji sauƙi sosai.” Aunty A’isha ta ce “Shikenan Usman na gode sosai, idan ta tashi daga baccin ka kira ni dan Allah.” Uncle Usman ya ce “insha Allah zan kira ki, a gaishe da su Hajiya da Amarya, ace ina mata fatan Alkhairi kafin na zo.” Aunty A’isha ta ce “Duk za su ji, sai anjima.” Daga haka ya katse wayar. Ummi ya kira ya sanar mata halin da ake ciki, amma ya ɓoye mata wasu abubuwan dan kar hankalinta ya tashi sosai tunda ba ishashshiyar lafiya gare ta ba. Itama ta jajanta abun sosai ta kuma yi Allah wadai da halin Umar da Fauziyya, har ma da Ƴan’uwansu na cikin Kano wanda ko waiwayar Neehal ɗin ba sa yi alhalin suna gari ɗaya. Ta kuma yi na’am da mayar da riqon Neehal hannun Aunty A’isha da Usman ya ce mata zai yi, amma kafin su tafi Gomben ta ce ya kai mata Neehal ɗin ta gan ta……….✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:48] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣3️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………..Wajen ƙarfe goma na safe sai ga Uncle Umar a asibitin, Uncle Usman ya je ya shigo da shi. Tun kafin su shigo ɗakin ya fara masifa, Uncle Usman dai bai tanka masa ba. Har lokacin Neehal bacci take abunta. Uncle Usman ya zauna yana yi wa Uncle Umar wani kallo ya ce “Wallahi Ya Umar ka matuƙar ba ni mamaki ka kuma ba ni kunya da har kake kallo ana azabtar da Neehal amma baza ka hana ba sai ma tayawa da ka yi. To idan ka manta bari in tuna maka, mahaifin yarinyar nan shi ya fito da mu daga cikin duhun rayuwa zuwa mai haske, cinmu, shanmu, suturarmu, iliminmu, bai taɓa nuna gazawar sa ba ko a fuska balle a aikace, alhalin kuma mu ba dolensa ba ne kyautatawa ce kawai irinsa. Mutumin da yay maka duk waɗannan abubuwan sannan ya ɗora da samar maka aiki ya baka muhallin zama, hidimar bikinka rabi da kwata shi ya yi ta, dan ba ya raye ɗiyarsa guda ɗaya tak a duniya ta cancanci azabtarwa daga gare ka? A tunani na ko wani ka ga yana mata haka sai inda ƙarfin ka ya ƙare a ɗaukar mata mataki.” Uncle Umar ya yi shiru kawai yana kallon Uncle Usman amma ya rasa bakin magana. Uncle Usman ya Tab’e baki ya ce “Abu na ƙarshe daga rana irin ta yau Neehal ta bar hannunka da zama, zata koma inda ake sonta da k’aunarta saboda Allah, tun da dama kai dan dukiyarta ka karb’i riqon ta, to ka riƙe dukiyar amma ita dai baza ta ƙara kwana a gidanka ba.” Cikin fusata Uncle Umar ya ce “Ni kake faɗa wa waɗan nan maganganun Usman? Uban wa ya faɗa maka dan dukiyarta na karb’i riqon ta, wato an zugo ka zaka mun rashin kunya ko?” Uncle Usman ya yi murmushi ya ce “Calm down bro, abun duk bai kai haka ba, karɓe Neehal daga hannunka ba ya nufin za a karɓe dukiyarta daga hannunka ba ne, za’a bar maka kacigaba da juya ta domin wadda zata ɗauki Neehal bata buƙatar dukiyarta dan a gurinta ba komai ba ce.” Uncle Umar ya mike tsaye ya ce “Wai me kake nufi da nine Usman eye? Wato kana so ka ce son cinye dukiyar Neehal nake son yi ko? To wallahi babu inda zata a hannuna zata cigaba da zama har auranta.” Uncle Usman ya ce “Hmmm sai ku ji daɗin kashe ta kenan kai da matarka da duka ko? Yaya Umar, Yaya Fateemah bata cancanci haka daga gare ka ba, ka ji tsoron Allah ka tuna kai ma zaka mutu kuma kai ma ka haifi ƴaƴan nan. Yarinyar nan mai ta sani a rayuwa me ta tsare muku da kuka mayar da ita baiwa a gidanku, kuma wallahi bana ganin lefin Fauziyya sosai na fi ganin naka dan da ka tsawatar mata ba ta isa ta yi wa Neehal haka ba, amma babu komai rayuwa ce Duk abin da mutum ya shuka shi zai girba .” Uncle Umar cikin borin kunya ya ja tsaki ya fice daga ɗakin. Sai wajen 12 Neehal ta tashi daga baccin, bayan ta wanke baki Uncle Usman ya bata abincin da ya siyo mata ta ci sannan ta sha maganinta. Wayar Aunty A’isha ya kira ya haɗa su, Neehal ta dinga murna jin Muryar Aunty’nta, ta dinga tambayarta ina Maman Abuja. Bayan sun gama wayar ya kira Ummi ya haɗa su itama. Da kansa ya je har gidan Uncle Umar ya tattaro duk wani abu na Neehal ya haɗa a trolley ɗinta ya baro su daga gidan. Aunty Fauziyya ta tab’e baki ta ce “Umma ta gai da Ashsha, ala raka taki gona.” A yammacin ranar aka sallame su daga asibitin tun da Neehal ɗin ta warware sosai, sai dai zata cigaba da shan magungunanta. Gidansu Haleemah suka je ya kai mata kayayyakin da ta ba shi tare da yi mata godiya sannan suka wuce Gabasawa. Ummi ta yi kuka sosai ganin yanda Neehal ta lalace ga shatin duka b’aro_b’aro ajikinta. Kwanan su ɗaya suka wuce Gombe, nan ma Su Aunty A’isha sun sha kuka da ganin yanda Neehal ta koma. Hajiya ta dinga ja wa su Aunty Fauziyya alkaba’i. Lokacin da Neehal ta koma Gombe Mama ba sa garin ta je Saudiyya Umara daga nan ta wuce London, sai daf da bikin Aunty Sadiya ta dawo. Lokacin Neehal ta fara dawo wa hayyacinta saboda kulawar da take samu a gurin Aunty A’isha da Hajiya, har an saka ta a makaranta boko da islamiyya. Mama ta yi murna sosai da ta ga Neehal ta dawo gurin Aunty A’isha da zama. Bayan bikin Aunty Sadiya Neehal ta mak’ale wa Mama ta bita Abuja, wannan zuwan shine sanadiyyar komawarta hannun Mama gaba-d’aya da zama. Dama zuwa Kano siyayya da su Aunty A’isha suka yi ta haɗu da wani Alhaji da Allah ya yi wa matarsa rasuwa shekarar da ta wuce, shima bai taɓa haihuwa ba ya ce yana son ta kuma baya son a ja bikinsu da nisa tun da su ba yara ba ne. Cikin wata biyu bayan fahimtar juna da sukai da kuma duk wani binkicen da ya kamata aka ɗaura Auran Aunty A’isha da mutumin ta tare a nan Kano. Neehal tana jin daɗin zama a gurin Mama sosai dan babu abun da suka rage ta da shi na jin daɗin rayuwa ita da Daddy. Makaranta mai tsada Daddy ya saka ta. Cikin lokaci kaɗan Neehal ta koma Neehal ɗinta ta ainihi mai rawar kai da surutun tsiya, hakan ya sa ba sa shiri ko kaɗan da Ameen, a duk lokacin da ya zo gida to ba ta da sukuni ta dinga kumbure_kumbure a ɗaki tare da Allah Allah ya yi ya tafi. Tun Neehal tana tunawa da Ahmad a ranta har ta fara mantawa shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button