NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Neehal ta tashi yarinya mai hankali da nutsuwa da biyayya, ga addini da tsafta, dan Mama duk ba baya ba ce a cikin waɗannan abubuwan. Dawowar Neehal hannun Mama sai dangin Mama suka ninka soyayyarsu a gareta, kowa ka ji yana Neehal ɗin Maman Abuja. Nan da nan Neehal ta ƙara saba wa da su, shak’uwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, saɓanin dangin Daddy da ba kowa ke son ta ba, musamman Maman Hameedah ƙanwar Daddy k’iri_k’iri take nuna tsanarta ga Neehal. Watarana Mama suka shirya ita da Neehal suka zo Kano, duk wani makusancin Neehal da Mama ta sani sai da ta kai ta gidansa dan ta gaishe shi, amma babu inda suka samu tarb’ar arzik’i sai gurin Ummi yayar Abba sai gidan wani cousin ɗin Abba wanda suke shiri da Abba sosai mai suna kawu Musa, shi ma dan yana gidan suka je ne, da dan ta matarsa ne ita ma baza su samu tarb’ar arzik’i ba. Uncle Umar kuwa da suka je gidansa cewa ya yi kar Neehal ɗin ta ƙara zuwa inda yake tun da ta zaɓi bare akan sa. Haka dai suka dawo Abuja rai babu daɗi, sosai Mama ta ji takaicin yanda ƴan’uwan mahaifan Neehal suka banzatar da ita, ta yi Allah wadai da zumuncin wannan zamani na ganin ido, dan ta san da iyayenta suna raye baza su mata haka ba. Neehal cikin danginta na Uwa da Uba da Uncle Usman da Ummi kawai suke waya, sai kawu Musa wani lokacin, lokaci zuwa lokaci kuma tana ziyartar Ummi. Riqon da Mama take wa Neehal ko ɗan data haifa da cikinta iya shi zata masa, Mama tana k’aunar Neehal sosai har cikin ranta, haka ma Daddy. Babu yanda za ai ka gane ba su suka haife ta ba, wanda bai sani ba ma ba ya gane wa. Dan ko a school da Fateemah Muhammad Tafida take amfani. Sunan Daddy kenan (Muhammad Tafida) amma Neehal da sunan Abbanta take amfani, Tafidan kawai ta ƙara, da yake sunan ɗaya ne duk Muhammad shi yasa ba’a gane wa. Daddy yana da kuɗi sosai kasancewar ya riƙe matakai na soja kala_kala har zuwa matakin ƙarshe wato General, kuma dama can zuri’arsu masu arzik’i ne. Asalin su Daddy su ma fulanin Gombe ne kuma ƴan’uwa ne na jini da su Mama, da Mahaifin su Daddy da Hajiyar su Mama cousin ne. Su Daddy su uku ne a wajen mahaifinsu, Yayansa Namiji mai suna Hamza sai shi, Haj.Saratu Maman Hameedah ita ce Autarsu. Iyayensu duka sun mutu ba jima wa, su ma su Mama mahaifinsu ya rasu daf da bikin Aunty A’isha da Abba. Daddy ya fara harkar siyasa, amma ganin siyasar ƙasar nan babu Allah a cikinta Mama ta ce gaskiya ya daina tun da dama bai yi wani suna acikinta ba, ba dan ya so ba haka ya haqura sai dan farincikin Maman kawai. Ameen shi kaɗai Mama da Daddy suka haifa a duniya, daga kan shi Allah bai ƙara ba su haihuwa. Kamar Ameen da Mama ɗaya sak tamkar an tsaga kara, bambamcinsu kawai shi Namiji ne Mama kuma mace ce, haka ma a halaye da d’abi’u duk nata ya yo, kama daga kan tsafta, addini, kyauta, iya mu’amala da mutane, tsare gaskiya ko mai ɗacinta, da kuma rashin tsoro. Ko dan shi Namiji ne,har ya fi Mama rashin tsoro da dakiyar zuciya, sai kuma Allah ya ɗora masa miskilanci tun yana ƙaramin sa. A ɓangaren aiki ne ya gaji Daddy shi ma ya zama soja. Sosai Neehal take tsoronsa, idan ya zo gida weekend sai ta zama salihar ƙarfi da yaji, dan abu kaɗan za tay ya balbale ta da faɗa dan yana da zafin zuciya, amma fa duk zuwan da zai yi da ƙatuwar ledarsa ta tsarabar Neehal yake zuwa, idan ƴan fara’ar suna kansa wataran yana sakar mata fuska. Neehal kam tana son Yayanta sosai, tana jinsa tamkar yayanta uwa ɗaya Uba ɗaya. Komai nata Yayanta Yayanta, sai dai wani lokacin in ta je gurinsa ya koro ta, ta dawo tana aikin turo baki, Mama ta ce mata “Dama wa ya aike ki gurinsa kin san hali.” A hakan dai shak’uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su. Shekarar Neehal shida a gurin su Mama Daddy ya yi retire, hakan yasa suka dawo Kano da zama gaba-d’aya, lokacin Neehal ta gama Secondary school tana 17_18 years. Ta yi saukar haddar Alqur’ani mai girma shekara biyu da suka wuce. A gurin registration ɗin Jamb suka haɗu da Haneefah, har suka yi musayar contact ɗin juna, sai da za su tafi gida suka gane ashe ma unguwarsu ɗaya. Tun daga time ɗin suka zama k’awaye sosai har Mama suke zumunci da Mommy’n Haneefah, ita ma Haneefah marainiya ce, mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama. A wannan lokaci Allah ya yiwa Ummi Yayar Abba rasuwa, Neehal ta ji mutuwar sosai kuma ta sha kuka. Duk da tarb’ar da Mama ta samu a gurin dangin Neehal bata daina kai ta tana gaishe da su ba, tun da jininta ne su, babu yanda zata yi da su, daga baya da Neehal ɗin ta girma da kanta ta cewa Mama dan Allah ta daina kai ta, ganin yanda suke wulaqanta ta da nuna halin ko’in kula a gareta kamar wadda ta je neman wani abu gurinsu, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa tako wa gidan Mama da sunan ya zo ganin Neehal. Ita kuwa Neehal tuni ta cire su daga ranta, yanda suka manta da ita a rayuwarsu itama ta manta da su. Da Uncle Usman ɗinta kawai take zumunci wanda shi ma ya yi aure suna zaune da matarsa a can Niger. Neehal kyakkyawa ce doguwa mai dirin jiki dai_dai misali da dogon gashi, ga ta ƴar gayu ce dan tana son gayu sosai, ko da yake ba ta ɗauka a ƙasa ba dan Mama ma akwai gayu da kwalliya, zai yi wahala ka ga hannu da ƙafarta babu jan lalle idan ka ganta baza ka ce ta haifi Ameen ba, ga iya girki, shi yasa duk ta kanainaye zuciyar Daddy, ba ya ganin kowacce mace sai ita. Aunty A’isha ta haifi yarinyarta mace mai suna Maryam, Aunty Sadiya ma ta haihu ɗanta Namiji.
Tun da Neehal ta fara zama budurwa Ameen ya daina sakar mata fuska kwata_kwata, wani lokacin kuma sai ta fito zata unguwa sai ya ce sai ta koma ta canzar shigar da ta yi ba zata fita a haka ba, babu yanda ta iya haka zata koma ta sake. Sannan ko ya ya ji k’amshin turare a jikinta kuwa sai ta koma ta sake wanka wai babu kyau ba zata fita tana k’amshi ba, janbaki wannan idan tasa sai ya ce sai ta goge shi. Mama da ta ga abun na shi bana ƙare ba ne ta taka masa burki ta ce bai isa ya takurawa Ƴarta ba, tun da ba shi ya haifar mata ita ba. Sannan fa Neehal ta samu salama ya ɗan sararara mata. Allah ya ba wa Neehal farin jinin samari tun da ta fara tasowa, amma bata kula su saboda ba a bata damar hakan ba a gida. Jameel shine saurayin data fara kulawa da sunan soyayya, ɗan Kano ne amma a Abuja suka haɗu a wani Mall, a lokacin ya takura mata da naci har sai da ta ba shi phone Number ɗinta. Tun yana kiranta tana ƙin d’aga wa har dai ta fara sake masa. Jameel matashi ne Black beauty, gashi da nutsuwa hakan yasa Neehal ta ji ya kwanta mata a rai. A hankali soyayyarsa ta fara mamaye zuciyarta. Tun kafin tafiyarsu ta yi nisa ta gabatarwa da Mama shi, Mama ta yi murna sosai ta kuma sanar da Daddy dan a san abun yi. Mahaifin Jameel ba boyayyen mutum ba ne kasancewarsa ɗan siyasa ne, Daddy ma ya san sa. Soyayya sosai Neehal suka sha da Jameel kamar ba gobe, sai dai bayan an yi Engagement ɗinsu ba jimawa ya fita aka bishi aka harbe sa ya mutu. Mutuwar Jameel ta girgiza duk wani makusancinsa ciki har da Neehal kuwa, dan tun daga lokacin da ya rasu ta zama so silent. A lokacin ne kuma Jamb ɗinsu ta fito, sai dai Neehal ba ta ci point sosai ba duk da Kasancewar tana da ƙoƙari, Haneefah kuwa ta ci point da yawa, amma ganin Neehal bata ci ba harma ta yi apply a Kano state polytechnic sai itama Haneefah ta ce can zata ta fasa zuwa University tun da besty’nta ba can zata yi ba, ita ma ta yi apply a poly. Sun fara karatu cikin nasara a Management kasancewar su duka ƴan art ne, department of mass communication suke, dama ita Neehal choice d’inta kenan, burinta a rayuwa ta ga ta zama Jonorlist. Da wata shekarar ta zagayo suka sake yin Jamb, wannan karan ma Haneefah ce ta ci Neehal ba ta ci ba. Dole tasa Haneefah ta yi apply a Bayero University Kano inda ta fara karantar law, Neehal kuma ta ci gaba da Polytechnic ɗinta. Tana siwes suka haɗu da Anwar, da farko shi ma ba ta kula shi sosai, sai daga baya ta saki jiki da shi suka fara soyayya fiye da ma wadda suka yi da Jameel. Cikin ikon Allah Neehal ta gama school ɗinta successfully, bata taɓa carry over ba balle spill, tun kafin ta gama ta siyi D.E Form a Bayero ta cike da waiting result. Bayan ta karb’i result ɗinta suka bata admission direct level two ta ɗora karatunta, lokacin ita ma Haneefah ta shiga level two ɗin, sai matakin karatunsu ya zo ɗaya. Ba jimawa da shigar ta Bayeron aka yi Engagement ɗinsu da Anwar. Duk kawo kuɗin Neehal ɗin da za’ai sai Mama ta aikawa ƴan’uwan Neehal, amma daga ƴaƴan Baffa har Uncle Umar babu mai zuwa, Kawu Musa ne kawai yake zuwa a karb’i kuɗin da shi, Uncle Usman kuma ya yi nisa ba ya samun zuwa, ya kance sai bikin Neehal ɗin zasu zo shida iyalansa.