NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A lokacin da aka yi engaged ɗin Neehal aka buɗe gidan Television na ASTV. Wani abokin Daddy ne ya buɗe, hamshaqin mai kuɗi ne kuma sananne ne a ƙasar nan. Da kwalin Deplomer aka ɗauki Neehal aiki a gidan TV’n, Haneefah kuma da S.S.C.E Daddy ya sa aka mata alfarma ita ma aka ɗauke ta. Neehal abun nema ya samu ta zama Jonorlist sai murna. Kafin Neehal ta fara aiki sai da aka kai ruwa rana da Ameen, dan da farko cewa ya yi baza ta yi ba. Mama ta ce, A nan bai isa ba kuwa, wanda zai aure ta ma bai hana ta ba sai shi ɗan karere. Har wannan lokacin dukiyar Neehal tana hannun Uncle Umar yana juya ta, babu wanda ya ce masa k’ala a kanta, su Fauziyya da aka ga Neehal a gidan TV baƙin ciki kamar ya kashe ta, musamman da ta ga yanda ta ƙara kyau ta zama ƴar gayu wanke hannu ka taɓa, gashi ko ta ina samun masoya take rututu a faɗin ƙasar nan.

CIGABAN LABARI………….✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:48] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣4️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………….Washegari bayan an yi sallar asuba, Daddy ya dawo daga masallaci Mama ta sanar masa abun da Aunty Sadiya ta faɗa mata, dan jiya bai dawo da wuri ba shi ya sa bata faɗa masa ba. Zarya yake ta yi a ɗakin baccinsa, Mama kuma tana zaune a gefen gado ta yi tagumi cikin tunanin mafita. A hankali ta ɗago da idanunta da ba su samu isasshen bacci ba a daren jiya saboda fargaba ta dubi Daddy ta ce “Daddy ka zauna mana, ka bar wannan safa da marwar ka zo mu nemi mafita akan wannan al’amarin.” Daddy ya sauke numfashi tare da goge gumin da ya kwanta a kan goshinsa ya ce “Al’amarin ne ya girgiza ni ba kaɗan ba Doctor.” Mama ta sauke tagumin data rafka bata ce komai ba. Daddy ya zauna a kan bedside locker yana fuskantar Mama ya ce “Zuciyata ta kasa yarda da wannan abun Doctor, ba zan taɓa yarda saboda Daughter ake wannan kisan ba gaskiya.” Cikin karaya Mama ta ce “Saboda me zaka ce haka? Kar fa ka manta mahaifan Neehal ma fa kashe su a kai, kuma har yau an kasa gano waɗanda suka yi kisan da kuma dalilin da yasa aka kashe sun. Haka su Jameel suma har yau an kasa gano waɗanda suka kashe su, ai ko aljanu ke kisan nan ya ci ace zuwa yanzu asirinsu ya tonu.” Daddy ya ce “Ka da ki la’akari da haka, zata iya yiyuwa mahaifan Neehal b’arayi ne suka kashe su ko kuma wani mak’iyin Abbanta, kin san idan mutum ba ya k’aunar ka a shirye yake da ya aikata  komai a kanka. Sannan na biyu kuma Jameel, mahaifinsa ɗan siyasa ne abokan hamayya babu abun da baza su iya ba suma a kan mutum, tun lokacin da aka kashe Jameel tunanin da kowa ya yi kenan ciki har da mahaifinsa. Sai kuma Anwar, wanda shi kaɗai ne ma babu wani dalili a rayuwarsa da a yi tunanin zai sa a kashe sa.” Mama ta sauke numfashi ta ce “Yanzu dai a takaice kana son ka ƙaryata abun da Sadiya ta faɗa kenan? Ko kuma kana son ka kwantar mun da hankali ne kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ganni a cikin damuwa? Daddy! Wannan maganar ba fa ƙaramar magana ba ce, ina tsoron abun da Sadiya ta faɗa ya tabbata.” Daddy ya ce “Ko kaɗan ba ina nufin na ƙaryata Sadiya ba ne domin akan aikinta take, kuma ban san hujjar data gani ta faɗi haka ba, kawai dai ina son nusar dake wani abu ne.” Mama ta ce “Wanne abu zaka nusar da ni? Hmm Daddy kenan, ni fa na riga na gano ka, kawai kana san kwantar mun da hankali akan wannan al’amarin ne.” Daddy ya yi shiru domin tabbas abun da Mama ta faɗa haka ne, yana son ya kwantar mata da hankali ne kawai amma tabbas shi ma maganar ta girgiza zuciyarsa ba kaɗan ba, ya manta rabon da ya ji abun da ya firgita zuciyarsa irin wannan. Mama ta ce “Ya Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan abun, ka tona asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al’amari da gaggawa.” Daddy ya ce “Ameen ya Allah, abun da ya dace dama mu dage da yi kenan addu’a, Insha Allahu gaskiya zata bayyana.” Kusa da Mama Daddy ya dawo ya kama hannunta ganin damuwa ƙarara a fuskarta ya ce “Please Doctor ki rage damuwar nan da kike, kin san Neehal ɗin ma idan ta ganki a haka itama zata shiga damuwar ne, ina jarumtar dana san ki da ita ne? Haba matar soja uwar soja.” Mama ta sauke numfashi ta ce “Idan ka ga na daina damuwa to naga na aurar da Neehal, shine kawai hankalina zai kwanta.” Daddy ya miƙe ya ce “Insha Allahu zaki gani, ai shi aure hab’o ne idan lokacinta ya yi dole sai ta yi, fata kawai Allah ya kawo mata miji na gari, wanda zai riqe mana ita da amana ko bayan ranmu.” Mama ta ce “Ameen ya Allah.” Daddy yana buɗe wardrobe ɗinsa ya ce “Yanzu ita Neehal ɗin akwai wanda take kulawa ne?” Mama ta ce “Gaskiya a sani na babu kowa.” Daddy ya ce “Wannan yaron da yake zuwa fa wani ɗan fari dogo haka?” Mama ta ce “Sadik kake nufi wai?” Daddy ya ce “Ehh, Barrister ne shi ko?” Mama ta ce “Ehh, a unguwar su A’isha gidansu yake.” Daddy ya ce “Allah ya tabbatar mana da Alkhairi.” Mama ta ce “Ameen.” Car key Daddy ya miƙawa Mama ya ce “Gashi ki ba wa Daughter.” Mama ta karb’a cikin mamaki ta ce “Mota ka sai mata?” Daddy ya ce “Ehh mana, alƙawarin dana mata ne tun sanda ta gama Polytechnic kika hana a bata a time ɗin.” Mama tana murmushi ta ce “Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi ya tsare, ai yanzu ta ƙara hankali zan bar ta ta yi driving ɗinta. Mun gode sosai fa Allah ya ƙara buɗi mai albarka” Daddy ya ce “Ameen ya Allah. Mama ta miƙe ta ce “Bari in je inwa Daughter albishir, na san zata yi farin ciki sosai.” Daddy ya yi murmushi cikin jin daɗin ganin Mama na murmushi, saɓanin d’azu da damuwa ke kwance a kan fuskarta. A duk duniya abun da ke d’aga masa hankali kenan ya ga iyalinsa a cikin damuwa, da yana yanda zai yi da sai ya magance wa Neehal wannan K’ADDARAR data shigo cikin rayuwarta, amma babu yanda zai yi komai rubutacce ne tun fil’azil daga Ubangiji Mai girma da ɗaukaka, amma ya ɗaukar wa kansa alk’awari sai inda ƙarfinsa ya ƙare a game da binkicen wannan al’amari, a matsayinsa na k’wararren soja.

Zaune a kan darduma Mama ta tarar da Neehal ta jingina jikinta a jikin gado, Sallamar Mama yasa ta ɗago da kanta tare da amsa mata. Mama ta zauna a bakin gado tana dubanta. Neehal ta ce “Ina kwana Mama.” Mama ta ce “Lafiya k’alau, me ya samu idanki?” Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce “kuka kika yi ko? kuka dai ba ya maganin duk wata damuwa, addu’a ita ce kawai mafita.” Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta kalli su Afrah dake bacci ta ce “ƴan rigimart taki ba su tashi ba kenan?” Neehal ta ce “Ehh ni Mama dama ina son na faɗa miki me zai hana a saka su a makaranta kafin Allah ya bayyana iyayensu, kin ga idan na tafi school ko aiki kema in kin tafi asibiti sai su kaɗai fa a gidan, su Aunty Dijee ma kin ga suna zuwa islamiyya da yamma.” Mama ta ce “Hakane kin kawo shawara mai kyau, ranar Asabar in Allah ya kai mu sai a kai su tahfiz, ranar Monday kuma sai na kai su school.” Neehal ta ce “Allah ya kai mu.” Mama ta ce Ameen, ga saqo in ji Dad ɗinki.” Neehal ta miƙa hannu dan karɓar abun da Mama take miƙo mata tana faɗin “Saqon mene?” Kafin Maman ta bata amsa ta gani da idonta, waro ido ta yi waje tana murmushi ta ce “Mama kar dai ki ce mun wannan nawa ne Dad ya siya mun Mota?” Ita ma Mama tana murmushin ta ce “Ban ce ba to, amma ni dai saqo aka bani kuma na isar.” Neehal ta rungume Mama da sauri cikin farin ciki ta ce “Alhamdulillah, amma fa Dad ya iya surprise.” Mama ta ce “D’aga mun jiki ni, sai a kula da titi sosai tare da kasancewa cikin addu’a a kodayaushe.” Neehal ta ce “Insha Allah Mamana.” A take Neehal ta tafi part ɗin Daddy ta masa godiya sosai, Mama ce ta yi musu breakfast yau dan ta san murna ba zata bar Neehal ta musu cikin nutsuwa. Ƙarfe tara da ƴan mintuna Neehal ce zaune a gaban mudubi tana ɗaura d’ankwalin atamfar dake jikinta, ɗinkin riga da skirt ne ya mata das a jikinta. Bayan ta gama ɗaura d’ankwalin ta saka ɗan kunne fashion mai kyau kalar one colour na jikin atamfar, sannan ta ɗaura agogo a left hand d’inta, ta zira abun hannu a right. Masha Allah ta yi kyau sosai small pink lips ɗinta sun sha white lipstick sai k’yalli suke. Su Afrah dake zaune a kan carpet ɗin bakin gado suna break, ganin ta miƙe ta ɗauki mayafinta dake kan gado suka miƙe su ma da sauri suna haɗa baki gurin faɗin “Zan biki Aunty.” Neehal ta kalle su ta yi murmushi sannan ta kama hannuwansu ta ce “Bana faɗa muku school zani ba, ku bari idan na dawo da yamma za mu je unguwa Insha Allah.” Suka gyaɗa mata kai ba dan ransu ya so ba. Neehal ta yi picking goshinsu sannan ta ce su tafi ɗakin Mama ta musu wanka idan sun gama break ɗin. Ta yafa mayafinta wanda ya kasance babba ne amma ba me kauri sosai ba, sannan ta ƙara fesa perfumes ɗinta ta zira plate shoe d’inta ta ɗauki jakarta da car key ɗinta ta fice daga ɗakin tana yi wa su Afrah bye_bye. A falo ta tarar da Mama ta ce mata “Mama zan tafi sai na dawo.” Mama ta ce “Allah ya kiyaye ina yaran fa?” Ta ce “Suna ɗaki suna break in sun gama na ce su zo ki musu wanka.” Mama ta ce “To Allah ya bada sa’a, ki kula da titi fa kuma kar ki manta da addu’a.” Neehal tana fita daga falon ta ce “Insha Allah Mamana, bye.” A parking space kamar yadda Daddy ya ce mata Motar ta tana can, a nan ta ganta. Ta sa key ɗinta ta buɗe murfin Motar da bismillah sannan ta yi addu’a ta shiga zuciyarta cike da farin ciki, gaba-d’aya damuwar data kwanta da ita daren jiya a ranta ta ji duk ta gushe, Daddy ya faranta mata ba kaɗan ba, a rayuwarta tana son ta ga tana driving, tun da Daddy ya so siya mata Motar amma Mama ta hana. A hankali take driving ɗin cikin nutsuwa da kula, sai dai ba ta yi nisa da tafiya ba ta ga wata Motor kamar tana binta a baya, ba ta kawo tunanin komai a ranta ba, tafi zaton may be hanya ce ta haɗa su ɗaya da mai motar, sai dai yanda take driving ɗin a hankali ya ci a ce mai Motar ya zo ya wuce ta kamar yadda wasu motocin ke yi. Cikin ikon Allah ta ƙarasa har cikin Bayero lafiya, kuma har ta zo bakin gate ɗin makarantar Motar na biye da ita a baya. Ƙarfe biyu suka gama last lecture ɗinsu, ko Sallah bata tsaya yi ba ta yi wa Freinds ɗinta sallama ta yo gida, saboda tana son ta je gidansu Haneefah ta nuna mata sabuwar Motarta.Tana fita daga get ɗin makarantar ta hau kan titi kenan ta mudubi ta ga kamar motar d’azu ce ke kuma binta, ita tama manta da batun wata motar d’azu, dan ta yi tunanin mai Motar shima Bayeron zai je a d’azun. Gabanta ya yanke ya faɗi tsoro ya fara ziyartar zuciyarta, hakan yasa ta shiga karanto Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, da hasbinallahu’wani’imal’wakil. Har ta ɗan samu nutsuwa a ranta ta cigaba da driving ɗinta. Wata zuciyar na faɗa mata ƙila ma ba Motar d’azun ba ce irinta ce kawai. Sai dai kuma kamar ɗazun duk inda ta yi nan Motar itama take bi, har tafiya ta fara yi a slow wai dan ta ga ko Motar zata zo ta wuce ta amma still dai motar tana bayan tata……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button