NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Na so page ɗin ya fi haka tsawo, amma tun daren jiya ban jin daɗi, yanzu ma dauriya na yi na muku wannan ɗin

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:50] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣5️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………..Har ta ƙarasa gida Motar tana biye da ita a baya. Sunayen Allah tsarkaka take ambata a ranta, kuma cikin k’udurarsa da ikonsa ya kawo ta gida lafiya. Sai da ta shiga layinsu sannan ta ga Motar ta daina bin ta. Tab’e baki ta yi a fili ta ce “Allah kai ne sarki, Allah ka kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri, Allah da kai na dogara kuma kariyarka nake roqa a kodayaushe.” Da haka ta shiga cikin gida ta yi parking motar sannan ta fito a gajiye ta yi cikin gidan. Zulai ce ta zo ta buɗe mata ƙofa, “Sannu da zuwa.” Ta faɗa tana bata hanya. Neehal ta ce “Yawwa Aunty zulai, ya gida.” Zulai ta ce “Lafiya k’alau.” Daga haka Neehal ta wuce sama. Ɗakinta ta nufa ta ajiye handbag ɗinta, ganin su Afrah ba sa dakin ta fito ta nufi ɗakin Mama. A kan gado ta tarar da su sun baje suna bacci, da alama kaɗaici ne ya ishe su, tunda ta san ba su fiya baccin rana ba. Mama bata nan ta je aiki, dama ta san ba zata dawo ta same ta ba. Ɗakinta ta koma ta shiga toilet ta ɗan watsa ruwa tare da yin tsarki ta ɗauro alwala, bayan ta idar da Sallah ta sauka ƙasa ta zuba abinci a ƙaramin plate ta ci. Ganin har uku ta wuce yasa ta koma sama da sauri dan shiryawa. Wayarta ta ɗauka ta ga missed call na Uncle Usman, murmushi ta yi sannan ta siyi kati daga banki a sim ɗinta na 5k sannan ta kira shi. Yana d’agawa ta ce “Assalamu alaikum.” Uncle Usman ya amsa mata, ya ƙara da faɗin “Daughter kin manta da ni ko?” Neehal ta shagwabe fuska kamar yana ganin ta ta ce “Haba Uncle ni na isa in manta da kai a rayuwata? ai ɗiyar kirki bata taɓa mantawa da ubanta ko dan neman albarkarsa.” Uncle Usman ya yi murmushi mai sauti ya ce “To ƴar gidan Uncle, ya school ya office.” Neehal ta ce “Lafiya k’alau Alhamdulillah, ina Auntynah da takwarata?” Ya ce “Suna nan k’alau, dafatan dai komai lafiya ko Neehal?” Ta ce “Lau lau my Uncle, ya kasuwa?” Ya ce “Kasuwa Alhamdulillah, gashi ma ta hana ni zuwa in ga ƴata.” Neehal ta ce “Babu komai Uncle, Allah ya taimaka. Nima Insha Allahu wannan hutun da zamu yi zan yi ƙoƙari in zo Niger ɗin.” Uncle Usman ya ce “Allah ya kai mu ya kawo ki lafiya.” Neehal ta ce “Ameen.” Ya ce “Ya Mama da Daddy da Aunty A’isha da Aunty Sadiya da wajen su Hajiya?” Ta ce “Duk sunanan lafiya k’alau.” Uncle Usman ya ce “Masha Allah, haka ake so Allah ya yi mana jagora. Ni kwa na ce Neehal har yanzu ba kya zuwa gidan Ya Umar da Gabasawa?” Neehal ta had’iye wani abu da ya tsaya mata a mak’oshi ta ce “Bana zuwa Uncle, tun da duk sun nuna ba sa son na rab’e su, kowa na je inda yake sai ya dinga wulaqanta ni kamar wadda ba jininsu ba, na rasa me nay musu, mutuwar iyayena ce lefi a gare su ko kuma riqona da Mama take yi? Dama Uncle idan iyayen mutum sun rasu sai ya zama abun ƙyamar a cikin zuri’arsu?” Ta ƙarashe zancen hawaye na zuba akan kuncinta. Uncle Usman ya danne ɓacin ransa ya ce “Don’t cry Daughter please, ba dan na saki kuka na tambaye ki ba, na tambaye ki ne saboda ina son sanin ko an samu cigaba sai dai kash bayananki sun tabbatar mun jiya i_yau ake bata sauya zani ba, amma har su Mubarak ɗin Ummi suma ba kya zuwa wajensu?” Neehal ta ce “Ai Ka san yanzu ba sa Gabasawa suna Lagos acan suke neman kuɗin su, amma Mama ta ce Insha Allahu watarana zata kai ni gurinsu da kanta, tunda ba ni da kamar su a duk faɗin duniyar nan.” Uncle Usman ya ce “Allah ya ba da iko.” A ransa yana jinjina ƙoƙari irin na Mama da kullum ita dai burinta ta ga Neehal tana zumunci da danginta kamar kowa, wani b’arin na zuciyarsa kuwa cike yake fal da tausayin Neehal. Ganin har yanzu kamar bata saki ranta ba da zancen su Uncle Umar da yay mata sai ya kawar da zancen inda cikin sigar tsokana ya ce “To a bani labarin sabon surikina.” Murmushi ne ya zubce mata ba tare da shirya yin sa ba sai dan yanayin yanda Uncle Usman ya yi maganar, don sosai take jin  k’uncin da ɓacin rai a duk lokacin data tuno da yanda danginta suka manta da rayuwarta a cikin tasu rayuwar. Uncle Usman ya ce “Ko baza a bani ba, na ji kin yi shiru!” Neehal ta ce “Ai babu ne Uncle.” Ya ce “Kai haba, Ni dai na san my Daughter bata da baƙin jini, sai dai idan korar surukan nawa take.” Neehal ta ce “Dagaske babu Uncle.” Uncle Usman ya ce “Allah ya kawo na gari to, mu sha biki mu rak’ashe.” Neehal ta yi murmushi cikin jin kunyarsa, wani b’arin na zuciyarta kuma fargaba ce fal a ciki, dan ita ba ma ta kawo wa kanta aure a yanzu, to idan ma zata yi auren wa zata aura? Sun ɗan taɓa hira kaɗan wanda gaba-d’aya zolayarta Uncle Usman yake, har sai da ya ji ta ware tana ƙyalƙyala dariya sannan suka yi sallama bayan ya ce ta gaisar masa da Mama da kyau. Bata ajiye wayar ba ta kira layin Haneefah sai da ta katse wa sannan Haneefah ta d’aga. Neehal ta ce “Matar nan kin yar da ni.” Haneefah ta ce “Faɗi da babbar murya, bacin yarwa ma har bi takanki na yi na take ƴar rainin hankali kawai.” Neehal ta yi murmushi ta ce “Me yay zafi haka Besty?” Haneefah ta ce “Abun kan wuta mana, tun jiya na kira ki amma sai yanzu zaki kira ni.” Neehal ta ce “Ki yi haquri ƙawata, yanzu dai ba ma wannan ba kina gida in zo in nuna miki wani abu.” Haneefah ta ce “Ina gida, Nima da ma akwai abun da nake son faɗa miki.” Neehal ta ce “To gani nan zuwa.” Daga haka ta katse wayar. Kukan twins ta jiyo a falo, da sauri ta fita dan ganin mene ne. Abun da bata taɓa gani sun yi ba wato faɗa shi ta tarar suna yi, Amrah tana ta dukan Afrah ita kuma tana kuka. Ɗaukar Afrah ta yi tare da hararar Amrah ta ce “Me tay miki kike dukanta?” Amrah ta ce “Ita ta fara duka na.” Afrah cikin ta ce “Ƙarya take ban dake ta ba.” Neehal ta sauke Afrah ta tsugunna ta rungume su duka a jikinta ta ce “Ku daina faɗa kun ji babu kyau.” Suka gyaɗa mata kai, Amrah ta cewa Afrah “Am sorry.” Afrah ta ce “Me too.” Neehal ta rungume su cikin k’aunarsu tana murmushi. A hankali kuma ta raba su da jikinta ta miƙe tsaye tana faɗin “Mu je in shirya Ku mu tafi unguwa.” Afrah ta ce “Aunty gurin Daddy’nmu za mu?” Neehal ta ce “A’a ai ban san inda yake ba.” Cikin sauri Amrah ta ce “Abuja, a Abuja yake.” Neehal ta ce “Tom Shikenan, soon za mu je Insha Allah.” Wanka ta musu ta shirya su sannan itama ta shirya tay wa su Dije sallama suka tafi. Ta kira layin Mama bata d’aga ba sai text message ta mata ta sanar mata ta tafi gidansu Haneefah. Abun mamaki da ɗaure kai gidansu Haneefan ma sai da ta ga Motar nan tana bin ta a baya. Kamar ɗazu addu’a ta shiga yi a ranta har suka ƙarasa. Haneefah ta yi murna sosai da ganin sabuwar Motar Neehal, kamar ita yi Motar. Bayan ta gama tsallen murna suna zaune a kan gadonta su Afrah kuma suna falo gurin Momy, Neehal ta cewa Haneefah “Me kika ce zaki faɗa mun idan na zo?” Haneefah ta ce “Hmm, jiya Abban Abuja ya zo (wan mahaifinta kenan) ya cewa Mommy Iyayen ya Faruq sun je sun tsaida ranar bikinmu nan da three months masu zuwa.” Neehal ta waro ido tana murmushi ta ce “Dagaske kike Haneefah?” Haneefah ta ce “Zan miki ƙarya ne to.” Neehal tana dariya ta ce “Ban iya guɗa ba dana rangad’a ta yau, Ya Faruq ya ga ji da iskancinki kenan na ja masa rai da kike, amma na ji daɗi sosai ƙawata, Allah ya kai mu lokacin ya sanya Alkhairi.” Haneefah ta ce “Amin, ni kuma ban ji daɗi ba, na so an fara bikinki kafin nawa na rak’ashe son raina.” Neehal ta mata gwalo ta ce “Sai kuma Allah ya yi ni zan rak’ashe ɗin a bikinki.” Haneefah ta ce “Ba komai, idan bikin naki ya zo nima aje auran zan yi a gefe in sha sha’ani na.” Neehal ta ce “Allah ya sa lokacin kina da tsohon ciki ma, sai mu ga ta tsiya.” Haneefah ta jefe ta da filo tana faɗin “Ba Amin ba muguwa ƴar buk’ulu.” Sai bayan Magriba suka koma gida, a koma wa gida dai Neehal bata ga Motar nan tana binta ba, in ma tana binta ɗin ita dai bata gan ta ba, ko dan duhu ya fara ne oho. Washegari Friday bayan Neehal ta dawo daga school da yamma Mama ta ce ta shirya su je ita da su Afrah ta yi musu shopping ɗin kayan sawa da duk wani abun buƙata. Suka shirya suka tafi, kaya sosai Neehal ta jidar wa su Afrah, sannan suka biya suka sha Ice cream sannan suka dawo gida. Yau dai ba ta ga Motar nan ta bi ta ba kwata_kwata, ko da safe da zata school. Hakan yasa ta ji hankalinta ya ɗan kwanta ba kamar jiya ba da ta kwana cikin zullumi da fargaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button