NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan Sallar Magriba Neehal tana sama tana yin wani Assignment Amrah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama, Neehal ta amsa mata ba tare da ta ɗago ba. Amrah ta ce “Aunty Mama ta ce ki zo Uncle Sadik ya zo.” ‘Sadik kuma?’ ta tambayi kanta gabanta na fad’uwa ba tare da ta san dalili ba. A hankali ta dubi yarinyar ta ce “Ki ce ina zuwa.” Amrah ta juya ta fice daga ɗakin da gudunta. Neehal ta tattara takardun gabanta ta ajiye akan bedside locker sannan ta ɗauko mayafi ta yafa ta fito falo. Mama tana zaune tare da su Afrah suna kallo a Falon. Neehal ta dube ta, ta ce “Mama wai Ya Sadik ne ya zo?” Mama ta ce “Eh, yana ƙasa yana jiran ki.” Bata kuma cewa komai ba ta nufi ƙasa. Yana zaune a kan kujera as always idan ta sakko gurinsa yana ta latsa waya, k’amshinsa ne ya ziyarci hancinta, ta lumshe ido tana jin wani irin yanayi na bin jikinta tare da canzawar bugun zuciyarta. Sosai Sadik ya mata kyau ba kaɗan ba, yana sanye cikin ƙananun kaya, sumar kansa baƙi sidik sai k’yalli take. Cikin sanyin jikin data rasa na mene ta ƙarasa ta zauna a kujerar kusa da shi tare yin ƙasa da idonta tana sauke numfashi a hankali. Murya ƙasa_ƙasa ta yi masa sallama. Ya d’ago kansa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata tare da mayar da wayarsa cikin aljihu. Kamar bata son magana ta ce “Ina yini.” Idanunsa na kanta Ya ce “Lafiya k’alau, ya study?” Ta ce “Alhamdulillah, ya su Maamah?” Ya ce “Suna lafiya, ta ce na gaishe ki ma.” Still kanta na ƙasa ta ƙi d’agowa ta ce “Ina amsawa, ya aiki?” Ya ce “Aiki gashi nan muna ta fama Alhamdulillah.” Ta yi shiru ba ta ce komai ba, shi ma shirun ya yi yana jiran ya ji ko zata tambaye shi dalilin yasa kwana 2 bai kira ta ba kuma bai zo ba. Tsawon three minutes suna haka, katse shirun na su ya yi da faɗin “Neehal !Kamar wani abu na damunki ko?” Lumshe idonta ta yi tana jin yanda sunanta ya ƙara daɗi a cikin muryarsa, sai ta ji kamar ta ce ya ƙara maimaitawa. Girgiza masa kai ta yi alamun a’a. Ita kanta ba zata ce ga abun da yake damunta ba, amma tabbas daga lokacin da Amrah ta zo ta faɗa mata Sadik ya zo ta ji sauyi a zuciyarta wanda bata san ko na mene ba. Sadik ya yi ƙoƙarin jan ta da hira amma ta ƙi sakin jikinta, ko d’ago kanta ta kasa yi, amma sai ta tsinci kanta da son jin muryarsa a wannan lokacin, ta ji bata son ya yi shiru da magana ko na second ɗaya ne. Shi kuwa Sadik jikinsa ne gaba-d’aya ya yi sanyi, dan yau da shirinsa ya taho na bayyana wa Neehal abun da ke zuciyarsa game da ita, amma kuma yanayin da ya ganta a ciki ya kashe masa gwiwa. Suna haka kamar a mafarki Neehal ta ji k’amshin Ameen, da sauri ta d’ago kanta ta kalli ƙofa. Shine kuwa yake ƙoƙarin shigowa falon, samun kanta ta yi da ƙura masa ido fuskarta ɗauke da murmushin da bata shirya masa ba, rabon data gan shi tun ranar da ta je gidansa, sati ɗaya kenan yau, sai ta ga ya ƙara mata kyau da haske ya yi wani fresh abunsa, alamun angoncin ya karɓe shi. Ameen ya ƙaraso inda suke fuskarsa ba yabo ba fallasa ya yiwa Sadik sallama tare da miƙa masa hannu. Cikin fara’a Sadik ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha sannan ya gaishe shi. Ko kallon inda Neehal take bai yi ba ya nufi sama, Neehal data kasa ɗauke idonta daga kansa cikin sanyin murya ta ce “Yaya ina wuni.” Ba tare da ya juyo ba ya ce “Fine.” Tare da wucewa sama abinsa ya bar musu daddad’an k’amshinsa a falon………..✍️
Yanzu labarin zai fara sauya salo, sannu_sannu bata hana zuwa…….
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:51] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
3️⃣6️⃣
…………Runtse idanunta ta yi tana jin ba daɗi akan abun da Ameen yake mata, ta rasa wanne irin mutum ne shi da ba’a gane gabansa balle bayansa, tamkar mai aljanu wata rana faran_faran, wataran kuma akasin haka. Buɗe idonta ta yi tare da daidaita nutsuwarta jin muryar Sadik yana mata magana.
Da Sallama Ameen ya shiga falon sama, Mama ta d’ago tana dubansa tare da amsa masa. Su Afrah suka tashi da sauri suka nufe shi suna faɗin “Oyoyo Uncle.” Ameen ya kama hannuwansu yana murmushinsa mai k’ayatarwa. Shafa kansu ya yi ya ce “How are you?” Amrah ta ce “We are fine Uncle.” Ya shafa fuskarta ba tare da ya kuma cewa komai ba sannan suka ƙarasa ya zauna a gefen Mama. Cikin kulawa Mama ta ce “Welcome.” Ya gyaɗa mata kai tare da faɗin “Ina yini Mum.” Mama ta ce “Lafiya k’alau, ya Hafsah?” Ya ce “Tana nan k’alau.” Mama ta ce “Komai dai lafiya babu wata matsalar ko?” Ya ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa sannan ya ce “Babu matsalar komai, Dad ba ya nan ne?” Mama ta ce “Bai dawo ba, ka san sai ya yi isha’i yake shigowa.” Ameen ya jinjina kai tare da mai da kallonsa ga Twins wanda suka ba da hankalinsu a kan kallon cartoon ɗin da suke. Mama ta ce “Bari na zubo maka abinci.” Ya ce “No, am full.” Mama ba ta kuma cewa komai ba ta cigaba da latsa counter ɗin dake jikin finger d’inta bakinta na ɗan motsi alamun lazimi take. Ameen ya dawo da dubansa gare ta ya ce “Who is that boy?” Mama ta ce “Wanne yaron kenan?” Ya ɗan yi shiru na sakanni sannan ya ce “Wanda na gan shi a downstairs yanzu.” Mama ta ce “Sadik ɗin ne baka sani ba ko ya?” Ya yi shiru bai ce komai ba. Sai ma kawar da zancen da ya yi da faɗin “Ya wajen su Hajiya, da Uncle?” Mama ta ce “Sunan nan k’alau, Next week ma Insha Allahu zani Gomben.” Ameen ya ce “Allah ya kai mu, nima Sunday Insha Allah zan tafi Lagos.” Mama ta ce “Da Hafsah zaka tafi amma?” Ya ce “No.” Tare da ɗan girgiza kansa. Mama ta ce “Kamar ya No? Zaka bar ƴar mutane ita kaɗai k’wal ne a gida? Ai ba zai yiyu ba.” Ya ce “Za’a zo a taya ta kwana daga gidansu.” Mama ta ce “Alright, Allah ya kai mu.” Ameen ya ce “Amin, but in kin je Gomben tare zaku dawo da Hajiya ko?” Mama ta ce “Da ƙyar gaskiya, dan ta ce ita da Kano sai bikin Neehal kuma.” Ya ɗan kalli Maman kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mai da dubansa ga agogon hannunsa ya ce “Mum ni zan koma, ki gaishe da Dad.” Mama ta ce “Zai ji, Allah ya kiyaye hanya, ka gai da Hafsan.” Ya amsa mata yana miƙewa sannan ya fice. Mama ta bishi da kallo a ranta tana cewa ‘He will never change daga shegen muskilancinsa, ta yi zaton idan ya yi aure abun zai ragu, amma kamar ma ƙaruwa ya yi. Da ya sakko zai wuce Sadik kawai ya kula, shi ma dan ya masa sai da safe ne. Ganin lokacin Sallah ya yi Shi ma Sadik ya yi wa Neehal sallama ya tafi, bayan ya sanar mata zai turo mata da saƙo ta waya anjima, ba ta yi tunanin komai ba ta ce sai ya turo tana jiran shi. Lokacin data koma sama Mama bata falo, sai su Afrah da bacci ya kwashe su, dama lokacin baccin nasu yayi, dan da wuri suke bacci, amma asubar fari sun tashi. Neehal ta shiga ɗakin Mama tana turo baki gaba, Mama dake shimfid’a Darduma ta dube ta amma ba ta ce komai ba. Neehal ta zauna a bakin gado kamar zata yi kuka ta ce “Mama yau Yaya bai kula ni ba, ban sani ba ko wani laifin na masa.” Mama ta ce “To nice shi da zaki zo kina cuno mun baki, ko kuma halin Ameen ɗin ne baki sani ba?” Neehal ta ƙara bata fuska ba ta ce komai ba. Mama ta ce “Tashi ki je ki yi Sallah ki ci abinci, in kin gama ki zo i want took to you.” Neehal ta ce “Toh.” Tare da tashi da fita. Bayan ta idar da Sallah ta ci abinci ta kai su Afrah ɗaki sannan ta koma ɗakin Mama. Ganin yanda Mama ta yi serious alamun magana za su yi mai mahimmanci sai ta bata duka hankalinta. Mama ɗan numfasa ta ce “Neehal! Zan tambaye ki wani abu, kuma ina son ki faɗa mun gaskiya.” Ta ɗan ji gabanta ya faɗi, amma ta daure ta ce “Insha Allah Mama zan faɗa miki gaskiya in dai na sani.” Mama ta ce “Wanne matsayi Sadik yake a gurinki?” Neehal ta dubi Mama da sauri cikin mamakin tambayartata sannan ta ce “Like Brother or Friend.” Kamar Mama zata kuma magana sai kuma ta fasa. Neehal ta ce “Wani abu ya faru ne?” Mama ta ce “Babu komai.” Neehal ta ce “Daddy bai dawo ba ne?” Mama ta ce “Ya dawo yanzun nan.” Neehal ta yi murmushi ta ce “Bari na je part ɗinsa mu yi hira.” Ta miƙe ta fita, Mama ta bita da kallo cikin tausayinta. Ba dan ta mata maganar Sadik ta kira ta ba, ta kira ta ne ta mata wata tambayar daban akan abun da yake damun a zuciyarta a kwanakin nan, amma kuma da ta yi wani tunani a yanzu sai ta fasa.