NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ƙarfe 8 kamar yadda Neehal ta ce suka tashi daga gurin aiki, bayan sun gama gudanar da shirin ‘Yancin mata wanda suke yinsa duk Ranar Asabar da misalin ƙarfe 7 na dare zuwa 8. Su na gamawa suka yi sallama da ma’aikatan gidan TV suka nufo gida, Neehal ta yi_ta yi Haneefah ta bita ta gidansu kamar yadda take yi wani lokacin amma ta ce ita gida za ta wuce, sai da suka biya suka fara sauke ta sannan suka wuce, da yake duk ba su da nisa, gabad’aya a cikin Nasarawa G.R.A suke har ASTV’n. Driver na parking Neehal ta fito, ganin Motar Dad a gurin alamun ya dawo ta ji daɗi a ranta, dama yau gabad’aya ta yi missing ɗinsa. Part d’in Mama ta nufa, ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, gabantane ya faɗi ganin Ameen zaune shi kaɗai a falon ya na latsa waya……….✍️

Ku yi haƙuri da wannan, har yanzu jikinnawa ne sai addu’a, dan kar ku ji shiru ma yasa na yi wannan ɗin, insha Allah next page za mu shiga cikin gundarin labarin, Nagode da addu’oinku Masoya.????❤️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

0️⃣5️⃣

………….Tab’e ɗan ƙaramin bakinsa ya yi tare da ɗauke kansa daga inda suke. Neehal ta janye hannunta ta na sauke Numfashi ba ta ce komai ba, saboda abun ya mata wani banbarakwai, duk da Anwar ko hannunta bai taɓa riƙe wa ba amma sai ta ji wata irin kunyarsa ta rufe ta. A hankali ta daure ta ce “Nagode sosai Ya Anwar” Anwar ya yi murmushi ya ce “Kin ga yanda hannunki ya yi wa zoben kyau kuwa?” Neehal ta yi ɗan murmushi idanunta na kan hannunta da zoben yake sanye dass kamar an gwada ta ce “Hannun nawa ne ma ya yi wa zoben kyau, ba ma zobenne ya yi wa hannuna kyau ba?” Anwar ya ce “Eh mana, ai ke ko kwalliya ki kai ke ki ke wa kwalliyar kyau ba ita take miki ba” kafin Neehal ta ce wani abu Ameen ya ƙaraso kusa da su, Anwar ya yi sauri ya ce masa “Yayanmu Barka da dare” Ameen ya ɗan saki fuskarsa ya na mik’owa Anwar hannu ya ce “Yawwa barkan mu” suka yi musabaha Anwar ya gaisheshi ya amsa sannan ya wuce ba tare da ya kalli ko inda Neehal take ba, saɓanin ita kuma da ta zira masa na mujiya. Anwar ya kalle ta ganin ta bi Ameen da ido ya ce “Ya dai Queen?” Neehal ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta babu daɗi ganin yanda Ameen ya shareta, ya ƙi kulata, Alhalin yau ba su haɗu ba kwata_kwata, ta rasa me yasa kwana biyunnan yake mata haka, duk da ma can shi mutum ne ba mai sakewa ba kuma ga miskilanci, amma ya na nuna mata kulawa sosai a matsayinta na k’anwarshi tilo guda ɗaya…… Anwar ya katse mata tunaninta ta hanyar faɗin “Wai me yake farune na ga kamar kina cikin damuwa Neehal?” Neehal ta sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ta ce “Bakomai Ya Anwar” ya ce “Sure?” Ta gyaɗa masa kai kawai tare da ƙoƙarin boye damuwarta dan kar ya fuskanci wani abu. Anwar ya duba tsadadden agogon hannunsa ya ce “Shikenan Queen bari na je gida na ga time ɗin Sallah ya yi” Neehal ta ce “Ba ka ci cake din ba kuma?” Ya ce “Na k’oshi ne” Neehal ta bata fuska ta ce “Please ya Anwar ka ci mana” ba tare da ya ce komai ba ya buɗe Plate d’in da’aka rufe cake d’in ya d’au 1 ya gutsira ya ajiye, ya na kallonta ya ce “Thank you” Neehal ta ce “Ka ƙara Mana, wannan ai baka ci ba” ya ce “I’m sorry dear, ciki na ya cika ne” Neehal ba ta kuma komai ba, Anwar ya Mik’e ya ce “Bye sai mun yi waya?” Neehal ta mik’e ta na faɗin “Mu je in raka ka” Suka jera su na tafiya har inda ya yi parking Motarsa ta raka shi, tsayawa su ka yi ta dubeshi ta ce “Thank you so much ya Anwar for your time, da kuma kyautar da ka ba ni, Allah ya sa ka da Alkhairi ya ƙara buɗi” Anwar ya ce “Ni ma Nagode sosai dear, kuma na ji daɗi, Allah ya barmu tare” Neehal ta ce “Amin, Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ka gaida Ammi” ya ce “Amin, za ta ji Insha Allah bye” Neehal ta ɗaga masa hannu ta na murmushi, shima d’aga mata hannun ya yi ya buɗe motar sa ya shige” Neehal ta juya ta koma cikin gida. Su Dije ta faɗa wa su je su ɗauko cake ɗin su cinye, Mama da Hajiya duk suna ɗaki tasan jiran Sallah su ke yi, itama ɗakinta ta shiga ta faɗa toilet ta dauro alwala ta fito ta bi jam’i itama.

Misalin ƙarfe tara na dare Hajiya ce zaune a falon sama ita da Ameen, Hajiya sai washe baki take tana zubawa Ameen hira, da alama dai ya cika mata aljihunta da kuɗi, Neehal ce ta fito daga ɗakinta, ganin Ameen ta ɓata fuska tare da turo baki gaba, Hajiya ta bi ta da kallo ta ce “Har Auwar ɗin ya tafi?” Neehal ta gyad’a mata kai kawai, Hajiya ta ƙara faɗin “To kuma mene ki ke ta ɓata rai, kamar za ki kai duka?” Neehal ba ta kula ta ba ta zauna a kasan kujerar da suke. Ameen ya d’ago ya na kallonta a hankali ya ce “I saw your missed call since?” Neehal ta ce “Uhm” kawai, ya ce “What Happen?” muryarta na rawa ta ce “Nothing” ƙoƙarin maida kwallar da ta cika mata ido ta yi, wadda batasan dalilin ta ba. Ameen ya maida hankalinshi kan wayarsa bai ƙara cewa komai ba, Neehal ta tashi ta koma ɗakinta.

Ta na shiga ta hango wayarta na haske alamun a na kira, ɗauka ta yi ta duba ta ga Anwar ne, ɗaga wa ta yi ta kara a kunnenta ya yi sallama ta amsa masa ta ƙara da faɗin “Ka je gida lafiya?” Ya ce “Lafiya ƙalau” Ta ce “Nagode fa ya Anwar sosai” Ya ce “Kin san fa ban san yawan godiyar nan, kin kai na miki komai Neehal a rayuwarnan, kuma kin san wani abu?” Neehal ta ce “A’a” Ya ce “Wannan ring d’in kyautar da na ajiye zan miki ce ranar aurenmu, kuma kawai sai na canza shawara na ce bari na kawo miki kawai” Neehal ta ce “Aiko na ji daɗi sosai Ya Anwar ɗina, Allah ya bar k’aunah.” Ya ce “Ameen My Queen.” Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishaɗi, duk da Neehal ba ta wani jin daɗi a ranta kawai daurewa ta ke yi.

Washegari gari Uncle Mahmud k’anin Mama ya zo da sassafe ɗaukar Hajiya za su wuce Gombe, Neehal kafin ta wuce School suka yi Sallama dan lecture din safe gareta. Kwanaki na ta tafiya Rayuwa ta na wucewa, sai gashi har satika huɗu sun shud’e, a wannan week ɗinne kuma su Neehal za su gama exam ɗinsu ta second semester Level two (2), sosai Neehal ta zama silent saboda kusantowar bikinta, Tsakaninta da Ya Ameen kuwa ba ta sauya zani ba, tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai sai kuma kyauta da tsarabar da yake yo mata a duk satin duniya idan ya dawo gida weekend bai fasa mata ba, amma kwata_kwata ba ya sakewa da ita, ita kuwa Neehal hakan ba ƙaramin damunta ya ke ba.

Yau Laraba ƙarfe 12 Neehal ta fito daga exam, ta na cikin tafiya ta ji a na kiranta da faɗin “Fateema Tafeedah” juyawa ta yi ta ga best freind ɗin ta ce a school ɗin Zee, tsayawa ta yi har Zee ta ƙaraso inda take, Zee ta ce “Fateemah tafiya za ki yi” Neehal ta ce “Ehh” Zee ta ce “Tun yanzu, yau ba shiga Library kenan?” Neehal ta ce “Na gaji ne, bacci ma nake ji, da daddare kawai na yi karatun” Zee ta ce “Ok sai mun yi waya tunda gobe bamu da exam” Neehal ta ce “Ba za ki zo ke da su Meesha ku karb’i Ankonku ba?, gobe fa Aunty Sadiya za ta kawo duka” Zee ta ce “Allah ya kai mu goben, za mu shigo da yamma mu karb’a insha Allah” Suka yi sallama Neehal ta tafi. Ta na zuwa gida ta wuce sama ta shiga ɗakinta ta kwanta ta na tunanin rayuwarsu tun daga k’uruciya, haka kawai ta ji kuka ya kufce mata ta shiga rera shi, sai da ta ga ji dan kanta ta yi shiru, dan babu mai rarrashin ta a kusa, Toilet ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta zauna kanta na mata wani irin ciwo, ga yunwa dake nuk’urk’usar cikinta dan bata karya ba ta tafi school. Da k’yar ta daure ta yi Sallar sannan ta sakko ƙasa, tea ta haɗa mai kauri tasha, duk da tasha tea d’in amma ba ta dena jin ba daɗi a jikinta ba, haka dai ta daure ta shiga kiciniyar ɗora girki kar Mama ta dawo ta tarar ba ta yi ba. Washegari ta tashi ba ta jin daɗin jikinta ko kaɗan, amma ta ta’allak’a hakan da period ɗinta da ya kusa, dan ta na cin wahala ba kaɗan ba idan za ta yi. Ta na kwance a kan gadonta lullub’e da duvet Mama ta shigo ɗakin, Janye duvet d’in Mama ta yi ta na faɗin “Neehal wanne irin bacci ki ke haka har 10 ta wuce ba ki tashi ba?” Neehal ta buɗe idonta a hankali ta ce “Ba na jin daɗi ne Mama” Mama ta ce “Ayya sorry Daughter, Month ɗinki ya yi ko, ki tashi ki lallaɓa ki yi wanka ki sha ko tea ne, sai kisha magani” Neehal ta ce “Ai bai zo ba,ciwon kawai na ke ji” Mama ta ce “Ki dai tashi ki sha” Neehal ta yunk’ura ta tashi zaune tana taune lips d’inta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button