NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Sai wajen ƙarfe goma Neehal ta dawo part ɗin Mama daga gurin Daddy. Toilet ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito ta zira doguwar rigar bacci, ta kashe light ɗin ɗakin ta kunna bedside lamp sannan ta kwanta a kusa da twins. Wayoyinta ta ɗauko domin shiga yanar gizo. Message ta gani akan wayarta da Numbern Sadik, ta ma manta ita ya ce zai turo mata sak’o. Ta text ɗin kai tsaye ta fara karantawa kamar haka: Amincin Allah ya tabbata a gare ki yake ma’abociyar kyawu da nutsuwa gami da hankali. Neehal! Na daɗe ina tunanin ta yanda zan Bayyana miki abun da yake raina game da ke, amma fargabar abun da zai biyo baya yasa na kasa bayyana miki tun tuntuni, na cigaba da dakon sa a cikin zuciyata. Neehal! Ina son ki! Tun kafin na sanki a zahiri mu fara mu’amala k’aunarki ta cika duk wani gurbi na zuciyata sai dai……. Ai ba ta ƙarasa karanta message ɗin ba ta tashi zaune da sauri zuciyarta na wani irin dokawa da sauri da sauri. Ajiye wayar ta yi a gefenta ta runtse idanunta hannunta dafe a ƙirjinta, a ranta tana addu’ar Allah yasa mafarki take ba gaske ba ne Sadik ya mata text ya sanar mata wai yana sonta. Vibration ɗin da wayarta ta fara yi ne yasa ta buɗe idanunta da sauri ta ɗauki wayar ta duba, sunan Sadik taga yana yawo akan screen ɗin wayar. Kallon wayar take tare da girgiza kanta, a fili ta fara faɗin “No, no Sadik soyayyata da kai ba zata taɓa yi yu ba, dan ban shirya shiga wani tashin hankalin ba a rayuwata bayan wanda yake manne a cikin zuciyata, ban shirya ƙara rasa masoyi a karo na uku ba, ka yi haquri Sadik dan babu batun ƙara soyayya a rayuwar Neehal har abada.” Tana gama faɗar haka ta kashe wayar gaba-d’aya ganin kiran ya katse wani ya ƙara shigowa. Komawa ta yi ta kwanta tana jin haushin kanta da har ta bari suka saba da Sadik sosai haka. Tabbas biri ya yi kama da mutum, ya kamata a ce tun kafin yanzu ta gane Sadik sonta yake, idan ta yi la’akari da yanda alaƙarsu ta fara, lokacin da farko da Haneefah suke mutunci ba ita ba. Amma tunda ya samu ta fara sake masa sai kuma suke shiri fiye da wanda suka yi da shi da Haneefan ma. Me yasa tun ranar da suka fara haɗa ido da shi ta ji sauyi a cikin zuciyarta, ko kuma hakan yana nufin shine wanda zai shigo cikin rayuwarta a karo na uku a matsayin wanda zai zamo abokin rayuwarta. Tabbas idan cancanta zata duba Sadik ya cancanta ya zamo abokin rayuwarta, domin yana da duk wasu qualities ɗin da take so mijin da zata aura ya kasance yana da shi. Sai dai bata tunanin ƙaddarar data raba ta da Jamil da Anwar zata bar mata Sadik. Bata son ta jefa rayuwarta data iyayenta a cikin wani tashin hankalin, shi yasa duk wata ƙofa da wani zai nuna yana sonta ta rufe ta a rayuwarta, da zarar ta ga take_taken mutum zata taka masa burki. Ita yanzu burinta a rayuwa taga ta yi karatu mai zurfi, domin ta san shikaɗai ne zai zama gatanta a nan gaba. Wasu zafafan hawaye suka ziraro daga idanunta.Ta lumshe ido tana jin hawayen na diga akan filon da tay matashi da shi. Fuskar Sadik, murmushinsa, tafiyarsa, su kawai idanunta suke hango mata, ga muryarsa dake mata kuwwa a cikin kunnenta. Wata irin fad’uwar gaba ta ji bugun zuciyarta na ƙaruwa. Tana ƙoƙarin cire Sadik daga rayuwarta amma zuciyarta tana hasaso mata komai nasa, kenan hakan yana nufin ta kamu da sonsa ne ita ma ko kuma dama can tana son shine ne? Ta tambayi kanta, a fili ta ce “Impossible!” Cikin muryar kuka. Ta san soyayya, tunda ta yi ta kar karo biyu, ta san daɗinta kamar yadda ta san ɗacinta. A rayuwarta tana son soyayya tana son ta ga masoya, a kullum addu’arta Allah ya bata mijin da ya iya soyayya, amma zuwa yanzu ta yiwa kanta alƙawarin koda zata yi aure ta ajiye babin soyayya a rayuwarta. Saboda ita bata iya so ba, idan tana son mutum tana son shi ne da dukkan zuciyarta, irin zufaffaffen son nan take yiwa mutum mai game jiki da zuciyar ɗan’Adam. Haka tay ta tunane_tunane da sak’e_sak’e a wannan daren, bacci kam yau duk iya satarsa ya kasa sure Neehal.

Washegari bayan ta yi Sallar Asuba ta ɗauko Alqur’ani ta shiga karantawa kamar kowacce Asubahi. Kafin ta gama karatun su Afrah sun tashi daga bacci, jikinta suka zo suka ɗane suna zuba mata surutu, ta ce su yi mata shiru ba su ga karatu take ba ne. Bayan ta gama ta musu wanka ta shirya su saboda yau Asabar Mama zata kai su Tahfiz. Ita ma wankan ta yi bayan ta gama shirya su dan ƙarfe tara zata fita gurin aiki. Ta kama hannunsu suka sauka ƙasa, a kitchen ta hango Mama tana haɗawa Daddy kayan karinsa. Su Afrah suka ƙarasa kitchen ɗin da gudu suna kiran sunan Mama. “Mama! Mama! kin ga Aunty ta saka mana sabon Hijabi, ta ce yau da mu zata fita.” Mama tana dubansu da murmushi akan fuskarta ta ce “Kun yi kyau sosai ƴaƴan Aunty, ku je ga Aunty Dije can a falo ta zuba muku abinci ku yi breakfast, maza!” Da murnarsu suka juya suka fita, Neehal ta bi su da kallo sannan ta ƙarasa shiga cikin kitchen ɗin jikinta a sanyaye. “Sannu da aiki Mama, ina kwana.” Neehal ta faɗa tana duban Maman. Mama ta ce “Yawwa har kun fito kenan?” Neehal ta ce “Ehh, ina tunanin ma tafiya zan yi kar na yi late kya kai su Tahfiz ɗin kawai.” Mama ta ce “Amma dai kya tsaya ki ci abinci ai.” Neehal ta ce “A’a, yau na tashi da azumi ne, na manta ana bina wani guda ɗaya sai jiya na tuna ashe azumi bai fi saura 1 month ya rage ba, shi yasa na ga gwara in yi kar na manta kuma……” Kallon da Mama take bin ta da shi tunda ta fara magana ne yasa ta yin shiru ba tare da ta kai aya ba. Mama ta ce “Yaushe kika ko yi ƙarya Neehal ban sani ba?” Neehal ta yi ƙasa da kanta ba ta ce komai ba. Mama ta cigaba da Magana “Jiya kin tashi da kumburarrun ido alamun kin sha kuka kafin ki yi bacci, yau ma ga idanunki nan da alama ba ki yi bacci ba jiya, kuma still kin yi kuka, yanayinki da maganarki sun tabbatar mun da damuwar da na gani kwance akan fuskarki. Ba zan takura miki ki faɗa mun abun da yake damunki ba tunda ba ki yi niyyar faɗa mun ba tun farko, amma zan miki addu’a Allah ya yaye miki.” Mama tana gama faɗar haka ta juya ta cigaba da abun da take fuskarta na nuna ɓacin ranta. Neehal ta matso kusa da ita ta rungume ta tare da sakin kuka, cikin kukan ta ce “Ki yi haquri dan Allah Mama kar ki yi fushi da ni.” Mama ta sanyaya muryarta ta ce “Ba zan taɓa iya fushi dake ba Neehal, amma kin san ba zan juri ganin damuwarki ba ko?” Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta ce “To share hawayen ki faɗa mun me yake damunki.” Neehal ta share hawayen sannan ta ce “Babu komai Mama, kawai ki mun addu’a.” Mama ta bita da kallo ba ta ce komai ba. Neehal ta kama hannunta ɗaya ta ce “Ki yarda Mamana seriously ba komai, idan ma da akwai ganinki da na yi yanzu ya shafe mun duk wata damuwata.” Mama ta ce “Shikenan, amma dai always ina faɗa miki kuka ba maganin damuwa ba ne, addu’a ita ce magani, kin ji?” Neehal ta ce “Insha Allah zan daina kukan.” Mama ta ce “Ki je ki ci abinci to, sai ki je ki gaida Daddy.” Neehal ta ce “Toh.” Sannan ta juya ta fita, Mama ta bita da kallo cikin tsananin tausayinta gami da k’aunarta. Neehal ta daure ta cuccusa bread da k’wai ta kora da ruwan tea, ba ɗan tana jin yunwa ba ko ɗan tana jin daɗin abincin a bakinta ba sai dan kar Mama ta mata faɗa. Bayan ta gama ta faki idon su Afrah ta shiga part ɗin Daddy, daga nan ta wuce gurin aiki. Sai dai wani ƙarin damuwar tana fita ta ga Motar data bi bayanta shekaran jiya tana bin ta yau ma still.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button