NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Tun daren jiya bata kunna wayarta ba saboda bata so ta kunna ta ga kiran Sadik ko text ɗinsa. Sukuku ta wuni yau, abokan aikinta kowa sai ya tambaye ta lafiya take kuwa? Ita kuma sai ta ce musu kanta ke ciwo, fatan samun sauqi su kai mata.Tare suka wuce gida yau da Haneefah, amma Haneefan bata jima ba ta wuce gidansu. Mama ta kai su Afrah Islamiyya kamar yadda ta ambata, islamiyyar weekend kawai ake yinta, 8_5. Babu nisa kuma daga gidan. Ɗaya daga cikin sojojin gidan Mama ta aika ya ɗauko su da time ɗin tashin su ya yi. Neehal tana kwance akan gado suka shigo, suka haye jikinta cikin murna suna ba ta labarin Islamiyyarsu, murmushin da bai kai zuci ba kawai take bin su da shi amma ta gaza ce musu ƙala, har suka haqura suka ƙyale ta suka koma gurin Mama suke ba ta labarin ita, tunda Auntin ta ƙi kula su. Da daddare tana gani Sadik yana ta kiran wayarta amma ta ƙi d’agawa, daga baya sai ga text ɗinsa, ta buɗe ta karanta amma  ta ƙi yi masa reply.

Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal ta daina d’aga kiran Sadik kwata_kwata, shi kuma ba ya gajiya kullum sai ya kira ta ba a daɗi gami da yi mata daɗaɗan text, na kalaman soyayya addu’a da fatan Alkhairi. Duk text ɗin da ya turo sai ta karanta amma fa bata reply, kuma ba ta yi block ɗinsa ba, saboda babu block ɗin mutane a tsarin rayuwarta, in dai ba abun da bai dace ba mutum yake turo mata ba. Mama ta je Gombe ta yi kwana uku ta dawo, gidan Aunty A’isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, su Zulai da Dije kuma garinsu suka je. Da tana gidan Aunty A’isha sai ga Sadik ya zo, Allah ya so tana ɗaki ba falo ba. Ashe ya saba zuwa gidan yana gaishe da Aunty A’ishan ita ba ma ta sani ba. Da Aunty A’isha ta ce a kira ta, sai ta ƙi fitowa ta ce ace bacci take yi. Duk wannan abun da Neehal take dauriya kawai take yi a ƙoƙarinta na ganin ta cire Sadik daga cikin rayuwarta, sai dai zuciyarta ta ce sam bata san wannan batun ba, dan da tunanin sa take kwana take tashi. A kwanakin nan da ta yi babu Sadik ta tabbatar wa da kanta tana son Sadik, so ba na wasa ba ma kuwa, Amma ta yi alƙawari ko son nasa zai kashe ta ba zata taɓa bari su yi soyayya ba. Ameen kuwa tun ranar da ya zo ɗin nan bata ƙara sa shi a idanta ba, tunda ya koma aiki sai weekend yake gari, weekend ɗinma idan ya zo gidan ita tana gurin aiki, bare ma ta ji Mama ta ce sau ɗaya ya ƙara zuwa tun ranar. Sai dai ita Hafsah ta zo sau biyu ta wuni, bata nuna wa Neehal komai ba saboda ganin idon Mama, ita ma Neehal ɗin haka, sai dai ba sa shigewa juna sosai. Dan Munafurci Hafsah harda cewa Mama wai Neehal bata zuwa gidanta, kamar so take ta je ɗin, Mama ta ce bata da lokaci ne shi yasa ga aiki ga school. Kamar yadda Mama ta kai su Afrah Islamiyya ta kai su makarantar boko, wadda haɗe take da islamiyya itama, Monday to wednesday sai 5:pm ake tashin su, Thursday and Friday kuma 12: pm.

Yau Talata wanda ya kama azumi saura kwana shida ga mai rabon gani. Da yamma bayan Neehal ta dawo daga school tana ɗaki tana gugar Uniform ɗin su Afrah Haneefah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Neehal ta d’ago tana dubanta ta amsa mata sallamar, “Amarya ke ce a gari yau? inji maƙi baƙo.” Haneefah ta ce “Ni ce nan, na zo mu yi wata magana ne, da zan bari sai gobe sai kuma kawai na ce bari in zo tunda babu abun da nake yi yanzun.” Neehal ta ce”Gwara da kika zo ai, Ya Mommy?” Haneefah ta ce “Tana nan k’alau.” Suka ɗan taɓa hira kafin Neehal ta ƙarasa gugar sannan ta koma bakin gado kusa da Haneefah ta ce “Wacce maganar zamu yi Besty?” Haneefah ta ce “Akan Sadik ne.” Neehal ta ɓata fuska ta ce “Me ya faru?” Haneefah ta ce “Yanayin da kika koma yanzu shi ya tabbatar mun da kin san koma menene.” Neehal ta ce “I don’t know any thing.” Haneefah ta ce “Any way dai, Jiya Sadik ya zo gida ya same ni and he told me duk yanda kuka yi, wanda kin fini sani ba sai na ƙara maimaita miki ba, amma Neehal na tambaye ki mana.” Neehal ta ce “Ina jin ki.” Haneefah ta ce “Me yasa kika yi ignoring ɗinsa? Ko kin manta Sadik ɗin ne?” Neehal ta ɗan tab’e baki ta ce “Saboda bana buƙatar sa a cikin rayuwata.” Haneefah ta yi ɗan murmushi ta ce “Bakin ki dai ya furta haka, amma fuskarki da yanayinki sun tona asirin zuciyarki. Neehal kina son Sadik! Kuma kema kin sani.” Neehal ta yi shiru saboda ba ta san me zata ce ba, sai ma k’walla data cika mata ido. Haneefah ta cigaba da magana “Ina lura dake a kwanakin nan walwalarki ta ragu sosai, kuma na san duk akan haka ne. Amma Sadik yana da wani aibu ne da ba za ki iya soyayya da shi ba? Ko kuma yana da wani halin ne mara kyau da kika fuskanta wanda mu ba mu sani ba?” Neehal ta girgiza kai cikin karaya ta ce “Ko ɗaya.” Haneefah ta ce “To me yasa ba za ki yi accept ɗinsa a cikin rayuwarki ba? Wallahi Neehal baki ga yanda Sadik ya koma ba, gaba-ɗaya ba ya cikin nutsuwarsa, kuma duk saboda ke ne.” Haneefah ta sassauta murya ta ce “Please Neehal dan Allah ki amincewa Sadik ku yi soyayya, ki tausaya masa ke ma kuma ki bawa zuciyarki abun da take so, kar ki cutar da ku dukanku.” Neehal tana hawaye ta ce “I can’t, ba zan iya ba Haneefah, na san ina son Sadik amma ba za mu yi soyayya ba, bana son na kuma yiwa iyayen kowa asarar ɗansu. Haneefah na rufe babin soyayya a rayuwata, ba zan ƙara soyayya da kowa ba!” Cike da tausayawa Haneefah ta ce “Kar ki yi haka Neehal, na sha faɗa miki ki daina faɗar irin wannan maganar, ke a karan kanki kina faɗar haka idan wani ya ji ya samu abun ɗorarwa fa?” Neehal ta ce “An yi na farko an yi na biyu, idan aka yi na uku Haneefah dole hankalin mutane zai dawo kan al’amarin, ko na faɗa ko ban faɗa ba, dole za a fara faɗar maganganu a kai na, ko so kike duk inda na yi a dinga nuna yi ana gata can, duk wanda zata aura sai ya mutu, sai…..” Haneefah ta rufe mata baki ta ce “Insha Allahu haka ba zata faru ba, in Allah ya yarda za a yi auranku da Sadik lafiya babu abun da zai faru. Ke dai ki miƙawa Allah al’amuranki, sannan ki dage da addu’a. Su ya Ammar ma kwanansu ne ya ƙare a duniya, amma ba wai dan ke aka kashe su ba.” Neehal zata yi magana Haneefah ta katse ta da faɗin “Dan Allah Neehal kar ki ɗauko abun da baki da tabbas akai ki saka a ranki Please!” Neehal ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, sai kallon ƙanwartata kawai take tana hawayen tausayin kanta. Haneefah ta baibaye Neehal da kalamai masu kwantar da hankali gami da wa’azin da ya ratsa mata zuciyata. Ta nuna mata babu wani mahaluƙi da ya isa ya maka abun da Allah bai maka ba. Neehal ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi, kuma ta ji zata karb’i Sadik a matsayin masoyi a karo na uku a rayuwarta. Sai dai wani ɓangaren na zuciyarta cike yake fal da tsoro da fargabar rashin sanin abun da zai biyu baya a soyayyar tasu. Za su yi Aure da Sadik ɗin ne kamar yadda Haneefah ta faɗa ko kuma shima za’a kashe mata shi ne?……….✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:51] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣7️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button