NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951
………..Sai da Haneefah ta tabbatar da bayananta sun shiga Neehal kuma sun ratsa ta sosai sannan ta miƙe dan tafiya gida tana faɗin “Mu je in yiwa Mama Sallama na ga magriba ta taho.” Neehal ta shagwaɓe fuska ta ce “Ki bari ki yi sallah mana.” Haneefah ta ce “Tafiya zan yi, zan je in yi girkin dare.” Neehal ta ce “Please dear!” Haneefah ta ce “Ikon Allah, to ki adana shagwab’arki idan yaya Sadik ya zo sai ki yi masa, amma bani zaki wa ba.” Ta ƙarashe zancen da dariyar tsokana. Neehal ta ɓata fuska ta ce “Na ji ɗin zan masa.” Suka fita daga ɗakin Haneefah tana ta tsokanarta. A ɗakin Mama suka tarar da twins suna cire uniform. Haneefah ta ce “Ashe kun dawo yanzu nake shirin tambayar su.” Mama ta ce “Yanzu nan aka ɗauko su.” Twins suka gaishe da Haneefah ta amsa, Afrah ta cewa Neehal “Aunty zamu biki.” Neehal ta harare ta ta ce “Sarakan son yawo, to ba fita zan yi ba.” Amrah ta kalli Haneefah ta ce “To Aunty ke zamu biki.” Haneefah ta yi murmushi ta ce “Shikenan, ku saka kaya sai mu tafi.” Suka shiga tsallen murna, Mama ta ce “Babu inda za su Assignment za su yi.” Lokaci ɗaya Suka ɓaɓɓata fuska kamar za su yi kuka. Neehal ta ce “Don’t cry My babies, gobe zan kai ku unguwa.” Sai suka saki ransu suka ci-gaba da sabgarsu. Haneefah ta dubi Mama ta ce “Mama zan wuce, sai da safe.” Mama ta ce “Allah ya kai mu, ki gai da gida da Mominki, Insha Allah kafin tafiyarmu Saudiyya zan zo gidan naku.” Neehal ta marairaice ta ce “Wai Mama baza ki tafi da ni ba?” Mama ta ce “In na tafi dake Neehal mu bar yaran nan a ina? Kuma ga makarantarki ma, ki bari Lokacin Hajji idan Allah ya kai mu sai ki je indai kun yi hutun school.” Haneefah ta ce “ki ƙyale ta Mama, rigima ce kawai ke damunta, yaushe ne tafiyar taku?” Mama ta ce “Biyar ga azumi Insha Allah.” Haneefah ta ce “Allah ya kai mu, sannan ta yiwa Mama Sallama suka fice ita da Neehal wadda zata ɗan taka mata. Bayan Sallar Magriba Neehal ta yiwa Sadik text kamar yadda suka yi da Haneefah zata masa.
A ɓangaren Sadik kuwa tun ranar da ya yiwa Neehal text bata masa reply ba kuma yana kiranta bata ɗauka, sai hankalinsa ya tashi. Gaba-d’aya ya ji duniyar ta masa zafi, ga wani sabon son ta dake ƙara mamaye masa zuciya da gangar jiki. Cikin kwanaki kaɗan ya rame saboda damuwar da ya saka a ransa. Hotunan Neehal su suka zama abincinsa, dan kodayaushe cikin tasa wayarsa a gaba yake yana kallon pics ɗinta. Duk wani program da take a gidan TV kuwa ba ya wuce shi. Mahaifiyarsa ta tambaye shi me yake damunsa haka duk ya fita daga hayyacinsa? Sai ya ce mata “Wani case yake ne mai wahala, ta taya shi da addu’a kawai.” Ganin abun Neehal bana ƙare ba ne shine jiya ya shirya ya je gidansu Haneefah, ya faɗa mata duk abun da ke faruwa, Haneefah ta kwantar masa da hankali ta ce zata je ta samu Neehal ɗin, kuma ta san ta yanda zata ɓullo mata kar ya damu. To bayanin Haneefah ne ma ya ɗan kwantar masa da hankali. Yau kuma yana masallaci ya ji message ya shigo wayarsa, ya yi zaton ma kamfani ne amma da ya duba sai ya ga Neehal ce ta turo masa. Jikinsa har rawa yake yi wajen shiga ya karanta message ɗin zuciyarsa cike da fargaba. Wani sanyi ya ji ya ratsa zuciyarsa gami da farin ciki mara misaltuwa ganin abun da Neehal ta turo masa, a fili ya furta Alhamdulillah yana sakin murmushi shi kaɗai. Duk wannan murnar da Sadik yake ba fa wani abu Neehal ta ce masa ba a cikin text ɗin. Ta tambayi lafiyarsa ne kawai, a ƙarshe kuma ta nuna tana son ganinsa Yau idan babu damuwa. Amma shi a gurinsa hakan alamun nasara ne, dama tun d’azu zaman jiran kiran Haneefah yake domin ta sanar masa yadda suka yi da Neehal ɗin, sai kuma ya ga text ɗin Neehal ɗinma a lokacin da bai taɓa tsammani ba. Cikin sauri ya tashi ya nufi gida, jikinsa har rawa_rawa yake dan zumud’i. Shaf_shaf ya shirya cikin wani yadi milk colour ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin k’amshi ya fito ya ɗauki hanyar gidansu Neehal.
Itama Neehal ɗin ba’a barta a baya ba, wanka ta yi ta shirya cikin wata gown purple colour wanda ta zauna das ajikinta, ta kuma haska farar fatarta. Ta shafa powder a fuskarta gami da White lipsticks a lips ɗinta. Ta yi kyau sosai fuskarta sai annuri take, ita kanta ta san She Missed him over, zuciyarta cike take da d’okin ganin kyakkyawar fuskarsa ɗauke da murmushinsa da ba ya rabo da shi kodayaushe. Tana jin wayarta ta yi ƙara ta ji gabanta ya ɗan faɗi, kamar yadda ta yi zato tana dubawa ta ga shine, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d’aga amma ba ta ce komai ba. Lumshe idonta ta yi tana sakin ajiyar zuciya a hankali jin muryar Sadik yana mata sallama, a sanyaye ta amsa masa masa. Yana jiran ta a waje kawai ya sanar mata sannan ya kashe wayar, kamar ya san kuwa da ya ce wani abun ba zata iya ce masa komai ba. Ta yafa mayafinta sannan ta fito falo, anan ta tarar da Mama ta tasa su Amrah a gaba suna Assignment. Kanta a ƙasa ta ce “Mama zan sauka ƙasa Yaya Sadik ya zo.” Mama ta bita da kallo sannan ta ce “Okay ki gaishe shi.” Su Afrah sarakan son yawo suka bi ta da kallon a tafi da su, Neehal tay murmushi ta shafi kuncinsu sannan ta fita. Inda suke zance da Anwar ta saka aka kai musu kujerun roba, tunda yau Sadik ɗin ya ƙi shigowa falo. Allah sarki rayuwa har ta tuna da sanda Anwar yake zuwa zance, ta hango zuwansa na ƙarshe gidan, sai ta ji zuciyarta ta mata rauni kamar zata yi kuka. Sai da ta mayar da k’wallar data tarar mata a ido sannan ta ƙarasa gurin cikin sanyin jiki. Tun da ta taho ya ƙura mata ido cikin shauƙin k’aunarta yana sakin ajiyar zuciya. Sai ya ga kamar ta ƙara kyau da iya tafiya a kwana biyun da bai ganta ba. Kanta a ƙasa ta ƙarasa tare da yin Sallama cikin siririyar muryarta. Sadik ya amsa mata cikin kulawa da k’auna yana jifanta da wani irin kallo da murmushin nan nasa manne a kan fuskarta. Ta zauna cikin tsananin jin kunyarsa akan abun da ta yi masa, kuma dama can ita naturally ɗinta tana da jin kunyar wanda take so. A hankali ta ce “Ina yini.” Ya ce “Lafiya k’alau sarauniyar birnin zuciyar Sadik.” Ta ɗan kalle shi amma ba yanda za su iya haɗa ido ba, sai ta ga ya ɗan rame duk da manyan kaya ya saka. Tausayinsa ta ji ya cika mata zuciya. Ganin yanda ta takure ta hana kanta sakewa sai Sadik ya fara da zolayarta da ya saba, har ya samu ta ɗan fara sakin jiki amma duk da haka ta ƙi d’ago kanta ta kalle sa. Cikin sanyin murya ta ce “Dan Allah Yaya Sadik ka yi haquri da abunda na maka, nima ba son raina ba ne, sai dan wani dalilin daban.” Sadik ya yi murmushi mai sauti ya ce “Kar ki damu Neehal, tun farko dama na fahimce ki kuma na san haka zata faru, dan haka wannan ba komai ba ne, ki manta kawai. Alfarmar da kika mun ma har na samu ganin kyakkyawar fuskarki a yau ya tabbatar mun da ina wani matsayi a gare ki, ko da kuwa matsayin mai goge miki takalmin ƙafarki kika bani zan yi farin ciki da hakan.” Neehal ta d’ago da sauri ta kalle sa, ya kashe mata ido ɗaya wanda yasa ta ji tsigar jikinta ta ɗan tashi hakan yasa ta yi saurin mayar da kanta ƙasa. Ya cigaba da magana da faɗin “Kina mamaki dan na ce miki ko da matsayin mai goge miki takalmi nake a gurinki zan yi farin ciki sosai da hakan? Neehal a yanda nake jin sonki a cikin zuciyata ko da bawanki kika mayar da ni zan yi farin ciki da hakan sosai, ni indai zan kasance dake a kodayaushe ina ganin kyakkyawar fuskarki to zan yi farin ciki gami da alfaharin haka.” Neehal ta ce “Haba Yaya Sadik ka daina faɗar haka, matsayin da kake da shi a gurina kafi ƙarfin na mulke ka sai dai kai ka mulke ni.” Cikin jin daɗin kalamanta ya ce “Are you Sure! Neehal matsayina har ya kai haka agurinki?” Ta yi murmushi tare da rufe fuskarta da hannunta. Kafin Sadik ya tafi yau sai da suka gama fuskantar junansu yanda ya kamata, har tahirinsa ya bata a tak’aice. Har sai da Mama ta kira ta a waya sannan suka yi sallama ya tafi bayan ya ce ta gaishe da Mama, tun da a suruki ya zo gidan yau ya ƙi shiga ciki.