NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Washegari da safe sai ga Hajiya ta zo wai ta zo duba Ameen ne. Neehal tana bacci ta ji Maganar Hajiya a kanta. A hankali ta buɗe idanunta dake cike da bacci, cikin muryar bacci ta ce “Kai tsohuwar nan baza ki bar mutum ya yi ƙiba ba, daga zuwanki ina baccina mai daɗi kin katse mini.” Hajiya ta ce “Wanne irin baccin asara ne wannan har tsakar rana? Yaushe Faɗiman ta lalace har ta barki kike irin wannan baccin? Haka zaki je gidan mijin kina sakin baki kina sharar bacci.” Neehal ta tashi zaune tana ƴar miƙa tare da yin salati. Hajiya ta ce “Ni ki yi ki tashi ki shirya ki raka ni gidan Aminu yaron kirki irin albarka in dubo sa, duk da ma sai jiya Uwartasa ta faɗa mun rashin lafiyar tasa, ban da haka da tuni ban zo ba.” Neehal ta kalli agogon dake bangon ɗakin ta ce “Taɓ, sai dai direban Mama ya kai ki, ni school zan tafi yanzu ina da exam 12.” Bata bi takan mitar Hajiya ba ta tashi ta shige toilet. Tana fitowa ta ga wayarta dake kan gado tana haske, ta ɗauka ta ga Ameen ne yake kiranta. Ta d’aga da sallama a bakinta, Al’ameen ya amsa mata. Ta ce “Ina kwana Yaya, ya jikin naka?” Ya ce “Da sauqi, me yasa jiya kika taho baki mun sallama ba?” Ta ce “I thought ka yi bacci ne lokacin.” Ya ce “Ko dai kina sauri ki tafi saboda saurayinki zai zo?” Neehal ta ce “Allah ba haka ba ne Yaya” ya ce “Amma ai yazo ɗin ko?” Neehal ta yi shiru tana murmushi ƙasa ƙasa, ya ce “Uhm, to me yasa yau baki kira ni kin ji lafiyata ba?” Sai ta ji abun wani iri, ita da tun yana gida ma basa wata waya balle yanzu da ya yi aure, ko yana nufin dan bashi da lafiya ne bata kira ta ji jikin nashi ba? ta ce “Yanzu na tashi daga barci ne am sorry” Ya ce “Alright, i will call you later” Daga haka ya kashe wayar. Ta bi wayar da kallo kamar zata gan shi a ciki, daga baya kuma ta ajiye ta cigaba da sabgarta.

Hajiya tana duban Mama bayan ta gama rattabo mata yanda suka yi da Neehal ta ce “Wai niko Faɗima har yanzu yaran nan shiru babu labarin wani nasu?” Mama ta ce “Babu Hajiya har yanzu, tun muna zuba idon ganin kira har mun gaji.” Hajiya ta ce “Ikon Allah, to ko dai ba ƴan ƙasar nan ba ne?” Mama ta ce “Waya sani ne, sai Allah.” Hajiya ta ce “Allah ya kyauta, suna inane ma ban gansu ba.” Mama ta ce “Suna makaranta, sai yamma suke dawowa.” Hajiya ta ce “Allah sarki Janar, Allah ya saka masa da Alkhairi, shi da ba ya gajiya da aikin Allah”

Har Neehal ta shirya ta fito Hajiya bata tafi gidan Ameen, Mama ta tsayar da ita, ta ce idan ta gama girki sai ta raka ta da kanta. Tana falon ƙasa tana kallo, da Neehal zata wuce ta ce “Au baki tafi gidan Yayan ba?” Hajiya ta ce “Ban sani ba, tunda baza ki raka ni ba meye naki na tambayata na je ko ban je ba?” Neehal ta ce “Allah ya baki haquri, amma dai zaki zaunar mana har bikin Besty ko?” Hajiya ta ce “Gobe goben nan zan koma inda na fito, dubiya ce ta kawo ni dama.” Neehal ta ce “Kai Hajiyarmu ki zauna ki yi babbar Sallah a nan.” Hajiya ta ce “Um’um, in zauna ku ce na cinye muku nama, gidana zan tafi in yi sallah ta a can.” Neehal ta ce “Tom Shikenan, Ni na wuce school.” Hajiya ta ce “Allah ya tsare.” Washegari kuwa kamar yadda Hajiya ta faɗa ta koma Gombe, ko gidansu Aunty Sadiya ba ta je ba sai su suka zo gidan Maman suka gan ta. Babbar Sallah saura kwana Biyar aka kawo lefen Haneefah, Masha Allah kaya sun yi kyau, Faruq ya yi ƙoƙari sosai, kaya masu tsada ya zuba mata, akwati goma ya mata cike taf da kaya. Ranar Haneefah ta sha tsokana gurin Neehal, tun tana biye mata tana ramawa har jikinta ya fara yin sanyi ta yi shiru. Ana i gobe Sallah mai ƙunshi ta zo har gida ta yiwa Mama da su Afrah, Neehal dai ba ta yi ba saboda kar ya ƙi fita kafin bikin Haneefah. An yi bukukuwan Sallah lafiya an gama Lafiya, Neehal kam babu inda ta je saboda aikin nama, gashi hutun school kwana uku ne kacal, dan ran huɗu ga Sallah ma tana da exam. Kuma ta so wannan Sallar ta zazzaga danginta, duk da basa nemanta amma ita baza ta biye ta su ba, kamar yadda Mama take faɗa mata a kodayaushe, Ta yi zumuncinta dan Allah ba dan su ba, shi zumunci dole ne. Ranar Asabar ɗin data kama saura kwana huɗu a fara bikin Haneefah su Neehal suka gama exam, hakan yasa ta kama hidimar bikin ƙawarta gadan_gadan. Ranar Thursday akai bridal shower, Amarya ta yi kyau sosai ita da k’awayenta, an yanka Cake an cashe. Ranar Friday kuma Kamu, shima Ranar Amarya ta yi kyau har tafi jiya ma. Su Neehal ƙirjin biki an cashe sosai, dan ma Sadik yana hana ta rawar gaban hantsi duk inda ta yi yana biye da ita, wai dan kar wani ya kula ta. Ranar Asabar kuma akai Mother’s Day da yamma, da daddare kuma akai Dinner. Tunda aka fara bikin Ameen bai je ba sai ranar Dinner suka je shi da Hafsah. Aiko ranar Neehal ta ga takura, dan hana ta sakat ya yi. Tana shiga filin rawa zata hango idanunsa yana banka mata harara, ga shi ita ma kamar an mata asiri sai tay ta kallon inda yake. Ƙarshe ma tashi yay ya ja hannunta ya fara mata masifar wai tana ganin Maza a gurin amma sai Safa da Marwa take, gashi kayan jikinta sun kama ta. Allah ya taimake ta ranar Sadik bai zo ba, da bata san a gurin wa zata fi shan takura ba tsakanin shi da Ameen. Hafsah kuwa bata ma san me ake yi ba, tana can tana bawa idanta abinci, da Ameen ya tashi ma ta ɗauka waya ya tafi yi. Wata cousin ɗin su Haneefah ta cewa Neehal “Kai amma guy ɗin nan naki ya haɗu, kuma daga gani yana sonki sosai, gashi kun dace.” Neehal ta yi murmushi tace mata “Yayana ne fa, kin ga matarsa can a gefensa.” Yarinyar ta jinjina kai kawai, amma ita ta hango tsantsar kishin Neehal a tattare da Ameen. Washegari Ranar Lahadi da misalin ƙarfe Sha ɗaya na rana aka ɗaura Auran Haneefah da Angonta Umar Faruq. Tun lokacin ta fara kuka saboda tsokanarta da abokan wasa suka fara yi, jikinta ya yi sanyi duk rawar kan nan babu. Neehal ta ce “Ashe zan ga ranar da bakin tsiwar nan zai mutu.” Duk da itama jikinta ya yi sanyi dauriya kawai take. Ranar kiɗan ƙwarya aka sha a cikin gida. Kafin Magriba ƴan ɗaukar Amarya sun zo, a lokacin kukan Haneefah ya tsananta kamar zata shid’e, Neehal ma tuni ta fara kuka. Mommy ma duk yadda taso daurewa amma sai da ta yi Hawaye da za’a fita da ƴartata tilo ɗaya a duniya. Sadik ne ya kai su Neehal gidan Amarya ita da wasu k’awayen Haneefah guda biyu, sai Ameerah ƴar Uncle Mahmud da ta zo bikin itama. A lokacin Neehal ta yi ƙoƙari ta daina kukan, amma kana ganinta ka san tana cikin bad mood, Suna Mota Sadik yana mata magana ma bata responding, ta kwantar da kanta a jikin kujera idanunta a lumshe. Sai da su Afrah dake kan cinyarta yake hirar. Sune na ƙarshen barin gidan Amarya, a haka ma da dabara suka fito saboda Haneefah riƙe Neehal ta yi wai ba za su tafi ba. Gidan Amarya ya yi kyau Masha Allah, Mommy da dangin Abban Haneefah sun mata kaya na ƴaƴan gata, komai ya ji Masha Allah. Sai fatan Allah yasa gidan zamanta ne na har abada, ya kuma ba su zaman lafiya ya kau da fitina a tsakaninsu. Da wani irin ciwon kai Neehal ta dawo gida, sallah kawai ta yi ta bi lafiyar gado, ba jimawa bacci ya ɗauke ta saboda tarin gajiyar dake addabar jikinta.

Yau Laraba misalin ƙarfe huɗu da mintuna Neehal ce zaune akan darduma, ta idar da sallar la’asar. Tunanin besty’nta da ta yi kewarta take yi, tana tuna yanda suke yin komai tare, idan ɗaya zata unguwa sai ta kira ɗaya ta raka ta, idan yau wannan bata zo ba gobe sai wannan sai ta zo, su je gurin aiki tare su dawo tare. Yanzu gashi aure ya raba su, tunda Haneefah baza su wuce 1 month a Kano ba, zasu koma Kogi state, a can mijin nata yake aiki. Wayarta ce ta shiga ruri ta kai hannu ta ɗauka, murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta. Bayan ta yi picked ta ce “Ƴar halak, tunaninki nake a raina sai gashi kin kira ni.” Haneefah ta ce “Ba wani nan, ba cin ma kin manta da ni, ko kirana akai_akai bakya yi.” Neehal ta ce “So kike Yaya Faruq ya fara jin haushina kenan, yana tsaka da cin amarcinsa ni kuma ina damunsa da kira.” Haneefah ta ce “Na ji, yaushe zaki zo?” Neehal ta ce “Ran Friday Insha Allahu.” Haneefah ta ce “Allah ya kai mu, ina Mamana da twins?” Neehal ta ce “Duk suna nan lafiya k’alau.” Haneefah ta ce “My regard to them.” Neehal ta ce “Za su ji insha Allah.” Sun ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama. Neehal ta miƙe ganin biyar ta kusa ta ɗauki car key ɗinta ta fita dan ɗauko su Afrah, Mama bata nan tana gurin aiki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button