NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
A bakin gate ɗin makarantar ta yi parking motar, sai da ta duba agogon hannunta sannan ta fito ta shiga cikin school ɗin. Tana shiga ana kaɗa musu beil, yara suka fara fitowa daga classes ɗinsu da gudu. A bakin class ɗin su Afrah ta hango su, ta ƙarasa ta kama hannuwansu. Suka juyo suka kalle ta, Afrah ta ce “Aunty yau ke kika zo ɗaukar mu?” Neehal tana karɓar lunch box ɗinsu ta ce “Gashi ko kin gani.” A hankali suke tafiya har suka fito daga school ɗin, ta nufi inda ta yi parking Motarta. Wani matashi dake waya a gefe ɗaya ya ƙurawa su Afrah ido cikin tsananin mamaki. Katse wayar ya yi bayan ya cewa wanda suke wayar yana zuwa, ya nufo inda Neehal take. Neehal ta buɗe bayan Motar ta ajiye lunch box ɗin sannan ta shigar da su Afrah cikin Motar. Tana rufe musu murfin Motar matashin ya ƙaraso, kawai sai ganin mutum ta yi a gabanta. Ta ɗan ja baya ta ce “Malam lafiya?” Matashin ya mayar da dubansa ga su Afrah dake cikin Mota ta glass ya ce “Dan Allah ina kika samo waɗannan yaran?” Gaban Neehal ya faɗi amma ta dake ta ce “Kamarya? Wannan wacce irin tambaya ce.” Matashin ya ce “Na san su ne shi yasa na tambaye ki.” Neehal ta ɓata rai sosai ta ce “To ba su ka sani ba gaskiya, watakila ɓatan kai ka yi.” Bata jira amsar sa ba ta juya ta buɗe gaban Motarta ta shige, ta bar shi nan tsaye. Matashin ya matso da nufin ƙara yi mata magana, amma ganin ta yi reverse yasa shi yin baya da sauri, sai kuma ya nufi titi da gudu ya tsayar da na mai napep ya shiga, cikin sauri ya ce “Dan Allah malam waccen Motar zaka bi mun bayanta duk inda ta yi, zan biya ka ko nawa ne.” Mai napep ɗin ya ja suka tafi da sauri dan kar motar Neehal ta ɓace musu. Suna shiga layin su Neehal ita kuma ana buɗe mata gate ta shige cikin gidan. Matashin ya cewa mai napep ɗin ya tsaya, ya sauko tare da Sallamar mai napep ɗin. Sannan ya nufi gidan da ya ga ta shiga. Sai da ya fara Ƙarewa gidan kallo sannan ya nufi gate ɗin gidanya fara knocking, mintuna biyu ya ga wani soja ya buɗe ƙaramar ƙofar gidan. Ya dubi sojan dake masa kallon tara saura k’wata ya ce “Barka da yamma yallaɓai, dan Allah idan babu damuwa ka mun magana da mai_gidan nan.” Sojan ya bishi da kallo daga sama har ƙasa sannan ya ce “Baya nan.” Matashin ya ja numfashi ya ce “Matar gidan fa? Dan Allah ka mun magana da ita to.” Sojan ya ja tsaki ya ce “Malam kafin na yi counting ten ka bar gurin nan, ko kuma yanzu jikinka ya faɗa maka.” Matashin ya ce “Please I have important t….” Sojan yana jijjiga kai ya ce “Baka ji ba kenan? To ka cigaba da tsayawa.” Ya juya ya rufo ƙofar da ƙarfi. Dafe kansa matashin ya yi sannan ya juya ya fara tafiya, yana tafe yana waigen gidan, a ransa yana faɗin daga ganin wannan tamfatsetsen gidan mai gidan ba ƙaramin mutum ba ne. Sai da ya bar layin sannan ya ɗauko wayarsa ya shiga kiran wata Number……
Yana kwance rigingine akan makeken gadonsa, dawowarsa kenan daga office. Idanunsa a lumshe yana jin yanda zuciyarsa take bugawa a hankali, duk bugun da zata yi tana bugawa da tunanin kids ɗinsa a ransa. A kullum kewarsu na ƙara cika zuciyarsa, duniyar gaba-ɗaya ta yi masa zafi, yana jin gidan da yake ciki ya yi masa girma saboda rashin kids ɗinsa. Da suna nan da tuni yanzu suna jikinsa suna basa labarin abun da ya faru a school ɗinsu. Ya taune lips ɗinsa cikin k’unar zuci. “I missed you alot my kids.” Ya furta hakan a fili cikin sassanyar muryarsa mai nuni da damuwar da zuciyarsa take ciki. Ɗaya daga cikin wayoyinsa da ya ajiye akan mudubi ce ta fara ruri, yana ji amma bai ko motsa ba da niyyar ɗauka har ta katse, wani kiran ya ƙara shigowa. Tashi zaune ya yi yana sauke numfashi sannan ya sauko daga kan gadon ya je ya ɗauki wayar. Musbahu! Sunan da ya gani yana yawo akan screen ɗin wayar kenan, ya yi picking tare da kara wayar a kunnensa. Daga ɗaya ɓangaren ba tare da gaisuwa ba Musbahu ya ce “Doctor! Na ga su Afrah yanzu.” “What?” Ya faɗa cikin dokawar zuciya. Musbahu ya ƙara maimaita masa abun da ya faɗa, duk da ya san ya ji. “Musbahu! A ina ka gan su?” Ya tambaya cikin sark’ewar harshe. “A Kano.” Shima Musbahun ya bashi amsa cikin hanzari. Ya ce “Kano kuma? A Kano a ina?” Musbahu ya bashi labarin duk abun da ya faru na ganin su Afrah tare da Neehal da bin bayanta da ya yi zuwa gida. Ahmad ya zauna dab’as a bakin gado ya ce “Soldier kuma? Kuma ya hana ka shiga gidan? Kuma ta tabbatar su Afrah ka gani?” Musbahu ya ce “Wallahi Doctor sune, ai na san su sosai, tunda kana zuwa da su gida gurin Yaya.” (Musbahu k’anin wani Freind ɗin Ahmad ne mai suna Sagir.) Ahmad ya ce “Shikenan, gobe ƙarfe goma na safe Insha Allahu ina cikin garin Kano, idan na shigo zan kira ka.” Musbahu ya ce “Shikenan Doctor sai ka zo, Allah yasa a dace.” Ahmad ya ce “Ameen.” Dafe kansa ya yi yana jin kamar mafarki yake, zuciyarsa ta kasa yarda da abun da Musbahu ya sanar masa, duk da idan hakan ya kasance bai san wanne irin farin ciki zai yi ba, his kids sun kusa dawowa gare sa kenan? Addu’ar da ake ba dare ba rana ita ce Allah ya amsa yau ya bayyana masa inda yaransa suke. ‘Ya Allah! Ka tabbatar da abun da Musbahu ya faɗa.’ ya faɗi hakan a ransa yana jin kamar ya zuk’o gobe ta yi……..✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:55] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
3️⃣9️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951
…………A ɓangaren Neehal kuwa bayan sun koma gida tana cire musu kaya Amrah ta ce “Aunty yaushe zamu gurin Daddy?” Neehal ta sauke numfashi har yanzu gabanta bai far faɗuwa ba ta ce “I don’t know.” Afrah ta ɓata fuska ta ce “Aunty We Missed him alot, please ki kai mu gurinsa.” Ta yi shiru ba ta ce musu komai ba. Har ta gama cire musu kayan ta saka musu wasu zancen Daddy’nsu suke, suna ta lissafin abubuwan da yake siyo musu da abubuwan da yake musu, har wak’ar da yake musu idan za su yi bacci sai da suka bawa Neehal labari, ita dai kawai jin su take, amma zuciyarta cike take da fargabar da bata san ko ta mecece ba. Da Mama ta dawo bata faɗa mata gamuwarta da matashin nan ba, ta san idan ta sanar mata faɗa zata mata sosai akan rashin saurararsa da bata tsaya ta yi ba. Washegari da safe ta shirya su Afrah suka tafi school, ita kuma bayan ta gama breakfast ta koma ɗaki ta kwanta…….
Ƙarfe goma da mintuna na safe Doctor Ahmad ya sauka a garin Kano, garin da ya yi shekaru masu yawa rabon sa da shi, sai yau sanadiyyar kids ɗinsa Allah ya kawo shi. Babu wanda ya faɗawa abun da zai je yi Kano, daga shi sai Musbahu ne suka sani, saboda ya fi so ya musu surprise, kuma ma baya so sai ya gama faɗar anga twins a Kano kawai ya zo ya ga ba su ba ne, duk da baya fatan haka. Yana sauka ya kira Musbahu ya sanar masa ya sauka yana airport ya zo ya ɗauke sa. Mintuna ƙalilan Musbahu ya je airport ɗin, saboda dama a shirye yake, kuma daga inda yake babu nisa zuwa airport ɗin. Bayan sun gaisa Ahmad ya shiga cikin motar da musbahu ya zo a ciki suka nufo gidansu Neehal. Suna tafe Ahmad yana tambayar Musbahu ƙarin haske akan ganin su Afrah da ya yi, har da nuna masa hoton su Afrah wai ya tabbatar su ɗin kuwa ya gani? Abun da ɗaure wa Ahmad kai da Musbahu ya ce masa cikin uniform ya ga su Afran, ɗaukar su ma aka zo yi daga school. Kenan waɗanda suka tsince su ne suka saka su a makaranta? Ko kuma dai ba su Afrah ɗin Musbahu ya gani ba wasu masu kama da su ne? Tunda gashi ya ce ya yiwa wacce ta zo ɗaukar tasu magana ta ce ba waɗanda ya sani ba ne. Tambayoyi dai barkatai Ahmad yake ta yiwa kansa wanda ba shi da amsoshin su, a gefe guda kuma yana jin wani irin sauyi a cikin zuciyarsa, a haka har suka ƙarasa gidansu Neehal. Horn Musbahu ya yi a bakin makeken gate ɗin gidan, Ahmad ya ƙurawa gidan ido cikin fad’uwar gaba. Ƙaramar ƙofar gidan wani dogon soja ya buɗe yana kallon Motar tasu, a hankali Ahmad ya bude murfin Motar ya fito Musbahu ma ya biyo bayansa. Ahmad yana zuwa ya miƙawa sojan hannu cikin kamilalliyar muryarsa ya ce “Good Morning.” Musbahu ya saki ajiyar zuciya ganin ba sojan jiya ba ne, wanine daban. Sojan ya ce “Morning.” yana bin Ahmad da kallo.” Ahmad ya ce “Masu gidan suna nan?” Sojan ya ce “Mai gidan dai baya nan, amma matar gidan tana nan.” Ahmad ya ce “Idan babu damuwa a yi mana iso a gurinta.” Sojan ya ce “Wa za’a ce mata?” Ahmad ya ce “Baƙi ne daga Abuja.” Sojan ya yi shiru yana ƙarewa su Ahmad kallo, sannan ya juya ya koma cikin gidan ba tare da ya yi magana ba. Musbahu ya ce “Hmm, Daga ganin gidan nan na wani babban Sojan ne.” Ahmad ya sauke numfashi bai ce komai ba, yadda yake jin zuciyarsa kamar ya bi ta cikin gini ya shiga gidan saboda zak’uwa…… Mama tana falon ƙasa tana operating system Dije ta ƙaraso inda take bayan ta buɗe ƙofa, cikin ladabi ta ce “Hajiya wai kin yi baƙi daga Abuja.” Mama ta d’ago cikin mamaki ta ce “Baƙi kuma? Maza ko mata?” Dije ta ce “Ina tunanin dai Maza ne.” Mama ta ce “Kuma suka ce ni suke nema?” Dije ta ce “Haka sojan ya ce mun.” Mama ta ce “Okay ki ce a kaisu Guest part, ganin nan zuwa.” Dije ta amsa mata tare da komawa bakin ƙofa ta sanar da Sojan. Su Ahmad suna tsaye fiye da mintuna goma sannan Sojan ya dawo ya ce su shigo. Wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke ya zura ƙafarsa cikin gidan da Bismillah, tare da fatan dacewa. Suna tafe Musbahu yana bin gidan da kallo, a zuciyarsa yana mamakin girma irin na gidan da kuma tsaruwarsa. Ahmad kuwa hankalinsa ba ya kan wannan, shi dai burinsa ya gana da masu gidan su tattauna akan kids ɗinsa. Ba su fi 5 minutes da zama ba Mama ta ƙaraso falon fuskarta ɗauke da fara’a tana musu sannu da zuwa. Ta zauna akan kujerar dake fuskantar wadda suke a zaune. Cikin ladabi Ahmad ya gaishe ta, musbahu ma haka. Ta amsa tare da faɗin “Sai dai ban waye ku ba ƴan samari?” Ahmad ya kalli Musbahu amma bai ce komai ba saboda yanda ya ji bugun zuciyarsa na ƙaruwa. Ganin haka Musbahu ya ɗan muskuta ya ce “Daga Abuja muke .” Ya ɗan yi shiru sannan ya cigaba da magana yana nuna Ahmad. “Wannan Abokin yayana ne, watanni kusan biyar da suka wuce aka zo har gida aka ɗauke masa yaransa, anyi cikiyar anyi cikiyar amma babu labarinsu babu labarin wanda ya ce ya gan su, to ana tunanin kidnappers ne suka sace su sai akai ta tsammanin kiransu, amma har kawo yau babu wanda ya kira game da yaran. To shekaran jiya na shigo Kano gurin wani abokin kasuwancina zan karb’i kaya a hannunsa, jiya kuma kamar a mafarki sai na ga yaran wata budurwa ta zo ɗaukar su daga makaranta da yamma.” Nan ya bawa Mama labarin yanda suka yi da Neehal da biyo ta da ya yi wani soja ya kore shi. Ya ƙara da faɗin “Shine ban yi ƙasa a gwiwa ba na kira mahaifin Yaran na sanar masa, shine ya zo Kanon yau domin mu zo nan gidan mu bincika ko sune.” Tun da ya fara magana Mama take kallon Ahmad cikin tsananin shock, wata zallar kama take hango wa a fuskarsa da yaransa, wadda ita kaɗai ma ta tabbatar mata da shi ɗin mahaifinsu su Afrah ne kamar yadda Musbahu ya faɗa. Amma abin da ya bata mamaki, a ce suna nan_nan Abuja duk cikiyar su Afrah da akai ba su gani ba. Ganin yanda Mama ta yi shiru sai jikin Ahmad ya fara yin sanyi, a ransa yana faɗin “Ko dai ba su Afrah Musbahu ya gani ba, wasu yaran ne daban. Mama ta sauke numfashi ta ce “Mu ga hoton yaran nasa.” Da sauri Musbahu ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga gallery ya lalubo pictures ɗin su Afrah wanda yay ta yawo a media lokacin da aka neme su aka rasa ya tashi ya kaiwa Mama. Mama ta ƙurawa hoton ido a ranta tana faɗin “Alhamdulillah.” Yalwataccen murmushi ta saki ta dubi Musbahu ta ce “Tabbas su ka gani jiya, kuma yarinyar da ka gani ta je ɗauko su ita ta tsinto su, kusan wata biyar da suka wuce.” Ahmad ya waro ido tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske, lumshe kyawawan idanunsa ya yi a fili ya ce “Alhamdulillah³” sai kuma ya zamo daga kan kujerar da yake kai ya yi sujjada a ƙasa. Musbahu cikin murmushin farinciki shi ma ya ce “Alhamdulillah, Masha Allah, yau Allah ya bayyana mana inda su Afrah suke.” Mama ta dubi Ahmad cike da tausayawa wanda farinciki ya kusa kashe shi, wasu sanyayan hawaye ne suka zirnano daga idanunsa, jinsa yake kamar ba shi ba, kamar mafarki yake zai farka ya ga ba haka ba. A hankali ya d’ago daga sujjadar da ya yi ya dubi Mama zai yi magana amma sai ya kasa, ya ma rasa me zai ce mata saboda tsananin farin ciki. Mama ta ce “Masha Allah, nima na yi farin ciki sosai da bayyanar ku, dan kullum da fatan hakan muke kwana muke tashi, kusan kullum sai yaran sun yi zancen Daddy’nsu suna tambayar yaushe za a kai su gurinsa.” Mama ta ƙarashe zancen tare da latsa wayarta dake kan cinyarta, Numbern Daddy ta kira, bayan ya d’aga ta sanar masa abun da yake faruwa, shi ma ya yi farin ciki sosai ya ce gashi nan zuwa gidan yanzu_yanzu. Mama ta dubi Ahmad ta ce “Yaran suna School yanzu, amma bari nasa a ɗauko su, dan nasan yanda kuke zumud’in ganin su baza ku iya jiran 1 hour baku gansu ba. Ahmad ya yi murmushi mai bayyana tsantsar farin cikinsa, a ransa yana girmamawa karamci irin na waɗan nan bayin Allah, daga tsintar yara har sun saka su a school. Musbahu ya yi ƙoƙarin kiran gida ya sanar musu, amma Ahmad ya hana shi, dan yasan tsaf zai iya ganin ƴan’gidansu a Kano sun taho ganin su Afrah. Mama ta kira direbanta ta faɗa masa ya je ya ɗauko su Afrah a school, zata kira shugabar makarantar ta mata bayani kafin ya ƙarasa. Kafin direba ya dawo Mama ta bawa su Ahmad labarin yanda Neehal ta tsinci su Afrah. Musbahu ya jinjina kai cike da Al’ajabin abun ya ce “Amma al’amarin nan akwai ɗaure kai, sato su akayi kenan Allah ya kub’utar da su ko kuma yaya sai Allah.” Nan dai sukaita jimanta abun, Ahmad ya bawa Mama labarin yanda suka nemi su Afrah suka rasa lokaci ɗaya. Suna haka direba ya shigo da su Afrah, Yaran da basu lura da mutanen dake falon ba suka nufi gurin Mama, Afrah ta ce “Mama ba’a tashi daga school ba fa aka ɗauko mu.” Ahmad wanda ya ƙura musu ido cikin tsananin murnar ganinsu kamar a cikin mafarkin da ya saba yi da su, ya ce “Princess!, Jewel!” A tare yaran suka juya suka kalle shi da alamun shock a tattare da su. “Daddy,!” Suka haɗa baki gurin faɗa tare da nufar inda yake da gudu suna dariyar farinciki. Ahmad ya rungume su a ƙirjinsa yana sakin ajiyar zuciya, bai san da wacce rana zai kwatanta wannan ranar ta farinciki ba a rayuwarsa. Babu irin neman da bai musu ba, ya sha wahala ya sha jinyar rashinsu kamar ba zai rayu ba, sai da ya fitar da rai da ganin su ya sakawa ransa dangana da haqurin rashin su sannan Ubangiji ya bayyana masa su cikin aminci, bai taɓa zaton ko da zai ga yaransa zai gan su cikin kwanciyar hankali haka ba. Ya ƙara rungume su a ƙirjinsa kamar zai mai da su ciki hawayen farinciki na bin fuskarsa. Su kuwa su Afrah sai dariyar murnar ganinsa suke, suka shiga jero masa tambayoyi. “Daddy wa ya faɗa maka muna nan gidan? Ina Ummi da Aunty Zahra da Ammi da Uncle Yaseer? Suma za su zo nan gidan mu gan su? Har da Baaba Talatu? Daddy zaka tafi da mu gida ko?”