NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Babu kowa a falon duk sun fice. a parking space suka tarar da su tsaitsaye suna sallama. Su Afrah suna hango Neehal suka rugo gurinta suna faɗin “Aunty Daddy ya ce dake zamu tafi, zaki je gidanmu ko?” Neehal ta shafi kuncinsu tare da gyaɗa musu kai. Zahra ta karb’i ledar hannunta ta zira a Mota sannan ta dawo ta karb’i phone Numbern’ta. Cikin matuƙar dauriya Neehal ta ƙarasa bakin Motar da za su tafi a cikinta ta cewa Ummi. “Ku gaida gida, Allah ya tsare.” Ummi ta ce “Ameen d’iyata, sai mun kuma dawowa ko kuma in kin zo ganin ƴaƴanki.” Neehal ta murmusa bata kuma cewa komai ba, dan tana buɗe baki ta san kuka ne zai kufce mata. Ta buɗe murfin Motar ta zira su Afrah wanda suka mak’ale mata su sai da ita zasu tafi. Ganin bata shigo motar ba tana ƙoƙarin rufewa suka fasa kuka tare da ƙoƙarin fitowa. Ummi ta ce “Ah ah, me ya faru?” Afrah ta ce “Aunty, ni gurin Aunty zani.” Cikin rarrashi Ummi ta ce “Ba ga Auntin nan ba ai tare zamu tafi da ita.” Amrah ta ce “Ai bata shigo cikin Mota ba.” Neehal da k’walla ta tarar mata a ido ta yi murmushi tare da shafa fuskar Afrah ta ce “Kayana zan ɗauko yanzu zan dawo sai mu tafi.” Yarinyar ta ce “To zan biki.” Ummi ta ce “A’a Afrah ku jira ta, ta dawo.” Yaran suka saka kuka dan sun gane wayo ake musu, Neehal ta juya da sauri ta bar wajen hawaye na zuba daga idonta. Ahmad dake tsaye yana kallonsu ya bita da kallo, da sauri kuma ya bi bayanta ya sha gabanta. Ta tsaya ba tare data d’ago kanta ba. Fuskarsa cike da damuwa ganin tana kuka ya ce “I’m sorry na raba ki da yaranki ko?” Ta d’ago ta kalle shi cikin mamakinsa, shi da yaransa amma yana bata haquri. Ya yi mata murmushin nan nasa mai shegen kyau, tare da girgiza mata kai alamun ta daina kukan. Jin kukan su Afrah a kusa da ita yasa ta juya da sauri, ashe fitowa sukai daga cikin motar suka taho gurinta. Ta tsugunna ta rungume su a jikinta, sannan ta d’ago su ta musu pick a goshinsu tana murmushi. Afrah ta ce “Aunty ki zo mu tafi Please, mu dake zamu tafi.” Kafin Neehal ta ce wani abu Ahmad dake tsaye yana kallonsu cikin burgewa ya kama hannun yaran ya ce “Aunty zata ɗauko kayanta ne, mu je Mota mu jira ta.” Neehal ta miƙe tare da juyawa da sauri ta d’agawa Zahra hannu sannan ta nufi cikin gidan zuciyarta cike da kewar yaran, bayan tafiyarta ba jimawa su Ahmad suka fice daga gidan suna d’agawa su Mama hannu, sai da suka fice sannan su Mama suka koma cikin gidan.
Neehal ba ta yi kuka sosai ba kamar yadda Mama ta zata, tana komawa ɗakinta ta shiga toilet ta wanke fuskarta, sannan ta sakko ƙasa gurin Aunty A’isha suka sha hira, bayan Sallar Magriba Aunty A’isha ta tafi, tana tafiya ba jimawa Sadik ya zo. Shima ya yi tunanin zai zo ya same ta cikin damuwar rashin su Afrah, amma sai ya tarar da akasin haka, suka sha hirarsu kamar kodayaushe. Washegari da hantsi ta shirya ta je saloon aka mata wankin kai, daga nan ta wuce gidan Haneefah kamar yadda ta mata alƙawari. Sai Bayan Magriba ta dawo gida, a hakan ma dak’yar Haneefah ta barta ta taho suna ta shan hira. Bayan Sallar isha’i Zahrah ta kira ta a waya, bayan sun gaisa ta musu ya suka je gida ta haɗa ta da su Afrah. Sun daɗe suna wayar suna ta bata labarai, bayan ta sha complain ɗin rashin bin su da bata yi ba….. Ranar Monday ta fara zuwa siwes ɗinta na school, a gidan TV’nsu take yi, hakan yasa abun ya zo mata da sauk’i. Bayan tafiyar su Afrah kullum sai sun yi waya a wayar Zahra, dan yanzu duk abun Ahmad ya haqura ya bar su a gidan Ummi su cigaba da zama anan saboda abun da ya faru. Neehal ta rasa meyasa fuskar Ahmad ta ƙi bacewa daga idanunta, musamman murmushinsa da yay ta kashe ta da su a ranar, kullum sai ta yi imagine ɗinsa a cikin ranta, a gefe guda kuma tana son tuno inda ta san fuskarsa, dan tabbas ta taɓa ganinta a rayuwarta ko da a hoto ne kuwa.
Ranar Asabar da yamma ta dawo daga gurin aiki ta tarar Hameedah da Mommy’nta sun zo gidan. A gajiye take amma duk da haka ta zauna a falon ƙasa inda ta tarar da su da fara’arta ta ce “Sannunku da zuwa.” Hameedah ta mata wani shegen kallo ta ɗauke kanta. Haj. Saratu ba yabo ba fallasa ta ce “Yawwa.” Neehal ta ce “Ina yini Mommy.” Hajiya Saratu ta ce “Lafiya, ashe an yi bikin ƙawar nan taki mara kunya?” Neehal ta ce “Eh.” Cikin rashin jin daɗin mara kunyar data kira Haneefah da shi. Hajiya Saratu ta tab’e baki ta ce “Ke kuma yaushe ne naki bikin?” Neehal ta ce “Mommy idan an saka bikina ai zaku ji.” Hajiya Saratu cikin baƙin ciki ta ce “Au da akwai wanda kike kulawa yanzu kenan?” Neehal ta ce “Eh.” Cikin takaici Haj.Saratu ta ce “Wanne me rabon ɗorawa iyayensa asararsa ne? Ko kuma munafuntarsa akai ba a gaya masa matsalar da kike da ita ba?” Neehal ta yi shiru dan ta gane inda maganar Haj Saratu ta dosa. Hameedah ta ce “Kema dai Mommy banda abinki ai kin san baza a faɗa masa ba tunda ana neman a shiga daga ciki kar a tsufe a gida.” Haj. Saratu ta ce “Hakane fa daughter, shi dai Yaya Muhammad Allah ya haɗa shi da masifa, yana zaman zamansa za’a ɓata masa suna a idon duniya, daga ya fito a dinga nuna shi ana yarinya ce a gidansa ta zama annoba duk wanda zata aura sai ya mutu.” Mama dake sakkowa daga sama karaf maganganun Mommy a kunnenta, ta yi wani murmushi ta ce. “Saratu kenan.” Haj Saratu ta ce “To ƙarya na faɗa ne, ai gaskiya ce, wa ya sani ma ko dama can dangin nata sun san annoba ce ita shi yasa suka ƙi riƙe ta karta zame musu masifa.” Har Mama zata kuma magana sai kuma ta fasa, ta san dama haka Haj. Saratu take so ta tanka mata su yi ta yi, ita kuma bata da wannan lokacin. Ta dubi Neehal da take kuka sosai na kiranta annoba da Hajiya Saratu ta yi ta ce “Tashi ki wuce sama.” Ta miƙe ta zari jakarta tana share hawaye ta yi sama, Mama ta bi bayan ta, ta bar Haj. Saratu tana cigaba da faɗar bak’ak’en maganganu marasa daɗi akan Neehal. A kan kujera ta tarar da Neehal ta kifa kanta tana kuka. Mama ta janyo ta jikinta ta shiga lallashinta tana faɗin “Ki yi shiru haka kukan ya isa, kar ki ɗauki maganganunta na banza ki saka a ranki har su zo suna damunki, na san halinki da saka abu a rai.” Ta d’ago ta, ta shiga share mata hawayen fuskarta. Sosai maganganun Haj.Saratu suka daki zuciyar Neehal, musamman idan ta tuna kalmar annoba da Hajiya Saratu ta kirawo ta da ita, hakan yasa hawayenta suka ƙi tsayawa. Mama ta tashi ta shiga dakinta ta barta a falon. Haj. Saratu tana cikin mitar ta Ameen ya shigo falon, tana ganinsa ta yi shiru. Hameedah ta faɗaɗa fara’a cikin iyayi ta ce “Yaya Ameen sannu da zuwa.” Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa tare da amsa mata ciki_ciki. Ba yabo ba fallasa ya gaishe da Haj. Saratu sannan ya haye upstairs abinsa. A falo ya tarar da Neehal durk’ushe inda Mama ta barta tana kuka, ya bita da kallo tare da faɗin “What happened to you?” Neehal ta d’ago kanta jin muryarsa amma ba ta ce komai ba, ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta a ɗan ruɗe ya ce “Tell me what happened?” Neehal ta share hawayenta ta ce “Mommy ce, ta kira ni da annoba.” Sai ta kuma fashewa da kuka. Shiru ya yi cikin ɓacin rai, ya rasa uwar me Neehal ta tsarewa Haj. Saratu a rayuwa ta tsane ta. A hankali ya matso daf da ita ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam a ƙirjinsa ya shiga rarrashinta……….✍️