NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ƙarfe 12 Aunty Sadiya ta ƙaraso gidan da atamfofi da leshuka da yadin bridal shower na k’awayen amarya, aka zube su a falo. Neehal ta na kwance a kan doguwar kujera ba ta ko motsa ba duk da ta na jin duk budurin zuwan Aunty Sadiyan, sai ma runtse idanunta da ta ƙara yi zuciyarta na bugawa. Aunty Sadiya ta kalli sashen da take ta ce “Neehal lafiya kuwa take bacci da ranar nan?” Mama ta ce “Ba ta jin daɗi ne, ciwon mararta ne ya tashi, amma na bata magani tasha, shine bacci ya ɗauketa” Aunty Sadiya cike da tausayawa ta ce “Ayya Allah ya ba ta lafiya, Amarya ba lafiya ai babu kanta, dan ma insha Allahu ta na yin Aure za ta dena ciwon marar” Mama ta ce “Allah ya sa, kin san ta da shegen shan zak’i kamar me, na hanata na hanata amma ta ƙi denawa” Aunty Sadiya ta ce “Allah ya sauwak’e, bari na kira Haneefah ta zo ta ɗibi na freinds ɗinsu” Mama ta ce “Ya kamata kam, tunda bikin ya matso su kai ɗinkuna, nima bari na ɗibi na mutanena.” Su na duba kayan su na cigaba da tattaunawa akan bikin, Mama ta na sanar da Aunty Sadiya Abubuwan da za’ayi, ba wani jan bikin za’ayi ba, Events uku kawai za’ayi, daga Kamu/Mother’s day, sai Dinner da Yini, sai bridal shower na k’awayen Amarya. Gabad’aya sun riga da sun yi bucking na events din da za’ayi, duk wata siyayya ta Amarya itama sun kammala ta, yanzu lefe kawai suke jira sai a sanya satittikan bikin. Sai da Haneefah ta zo sannan ta tashi Neehal daga baccin gasken da ya d’auketa, ta tashi zaune ta na taune lips ɗinta, ka na ganinta ka ga mai cuta, Aunty Sadiya da Haneefah suka shiga yi mata sannu. Mama ta kawo mata abinci ta ɗan tsakura ta ci ta ƙara shan magani, ranar dai haka ta wuni ba ta jin daɗi, Anwar da su ka yi waya hankalinshi ya tashi da ya ji ba ta da lafiya, sai da ya zo ya duba ta da daddare hankalinsa ya ɗan kwanta, tun da ya ga jikinta ba rijib take a kwance ba. Washegari, ta tashi jikin nata da sauƙi, dan period d’in nata bai zo ba har yau, yau ma exam d’in safe ce da su, amma ba ta dawo ba gida da wuri ba, saboda sun tsaya ɗaukar pics da friends ɗinta, tunda sun gama exam d’in sai dai fatan samun result mai kyau, suka yi sallama da freinds ɗinta su na faɗin sai sun zo bikinta, ita dai Neehal yaƙe kawai take yi dan zuciyarta babu daɗi ko kaɗan. Ta na dawowa gida Mama ta sanar mata da zuwan wadda za ta mata gyaran jiki daga Maiduguri gobe Insha Allah, Hajiya ma goben za ta zo tunda ran Lahadi za’akawo lefe amma maza ne za su kawo.

Da daddare Neehal ta na kwance a ɗakin Mama, sai juyi take akan gado saboda murd’awar da cikinta yake mata, hawaye ne kawai yake fita daga idanunta, wani amai ne ya taho mata ta tashi da gudu ta nufi toilet ta shiga kelayashi, ta na yin aman ta na jin fitar jinin a jikinta, Ta na sassauke Numfashin azaba ta gyara jikinta ta sanya pad, kuskure bakinta ta yi ta janyo ƙafarta da ta fara riƙe mata ta dawo ɗaki ta kwanta. Mama ta shigo ɗakin ta dube ta cikin tausayawa ta ce “Sannu Daughter ya jikin?” Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mama ta ce “Allah ya ƙara sauƙi” Sosai Mama take tausayin Neehal lokacin period ɗinta, saboda azaba take sha ba ta wasa ba, ciwon mara, baya, k’ugu duk take yi, ƙafafunta duka su riƙe, yau ko gurin aiki ba ta je ba, sai Haneefah ce ta je ta maye gurbinta. Time ɗin da Dad ya zo dubata bacci ya ɗauke ta. Washegari dai da ta tashi jikin nata da sauƙi sai dai ba ta warware tas ba. Da safe ta na cin Irish da soyayyen kwai ɗin da Mama ta kawo mata ta tilasta mata ta sha Ameen ya shigo ɗakin, jin kamashin turarensa ya sa ta d’ago kanta da sauri ta na kallonsa, gabanta ne ta ji ya fad’i ba ta san dalili ba, satar kallonsa ta shiga yi ta ga ya canza sosai ba kamar kwanaki ba, ramar da ya yi duk babu ita sai ma wani fresh da haske daya ƙara, lumshe idonta ta yi a hankali ta ce “Ina kwana?” Kamar bai ji ba sai kuma can ya ce “Lafiya, ya jikin? Ba ta yi mamakin sanin ba ta da lafiya da ya yi ba, domin kowa na gidan ya san time ɗin period ɗinta saboda azabar da take sha a lokacin yin period ɗin nata. Cikin raunin murya ta ce “Da sauƙi” Juyawa ya yi ya fita ganin Mama batanan, a falon ƙasa su ka haɗu da Mama ta dawo daga part din Dad, Mama ta na dubanshi ta ce “Welcome, har ka zo kenan?” Ya ce “Ehh, ina kwana?” Mama ta ce “Lafiya ƙalau, ya aiki” Ya ce “Alhamdulillah, ya naku?” Mama ta ce “Lafiya ƙalau” Zai nufi part d’in Dad Mama ta ce “Idan ka dawo ina son ganinka” Ya ce “Toh.” Misalin ƙarfe goma na safe Aunty Sadiya da Aunty A’isha da yarinyar gurinta Maryam su ka zo gidan, domin yin snacks na karɓar kayan lefe, Neehal dai ta na shan Magani ta kwanta bacci ya ɗauketa dan jiya ba ta samu wani baccin kirki ba, saboda ciwo. Yauma ba ta samu damar zuwa gurin aiki ba, Hajiya da yamma ta ƙaraso gidan da tulin kayanta dan sai bayan biki za ta tafi, wadda za ta yi wa Neehal gyaran jiki Mama ta kira ta, ta ce ta bari sai Monday tun da Neehal ɗin ba ta jin daɗi. Bayan sallar isha’i bayan su Mama sun gama aiki ta samu Ameen a ɗakinsa, Ameen ya tattara duka hankalinshi akan Mama jin ta ce za su yi Magana. Mama tana dubanshi ta ce “Gobe za ka koma Lagos ko jibi?” Ya ce “Gobe da safe” da mamaki Mama ta ce “Da safe kuma?” Ya ce “Ehh” Ta ce gobe fa za’akawo lefen Neehal kuma sai da yamma, kuma maza ne za su kawo” Ya ce “Am sorry Mum, amma ba zan samu damar tsayawa ba, dan akwai wani important thing da zan yi” Mama ta ce “Sunday ce fa, saboda gudun haka fa ya sa aka sa weekend, kar wani uzurin ya tsaida wani” ya yi shiru bai ce komai ba, Mama ta mik’e ta ce “Dole ne koma uzurin mene da kai ka jira a karb’i kayan da kai, ka ji na faɗa maka” Ta na faɗin haka ta fice daga ɗakin, Ameen ya bita da kallo.

Washegari Sunday Ranar kawo kayan lefe, tun safe su Mama su kai packagin kayan snacks d’in da soyayyen naman kaza gami da lemuka, yamma kawai suke jira masu kawo kayan su zo. Neehal yau ta lallaɓa ta shirya ta tafi gurin aiki, duk da Mama ta so hanata amma ta ce mata ta ji sauƙi za ta iya zuwa. Mama na kitchen Ameen ya shigo ya same ta da shirinsa na tafiya. Mama ta masa wani kallo bayan ta amsa sallamar da ya yi, Ya ce “Ina kwana Mum” Mama ta ce “Lafiya k’alau” Ya ce “Am sorry Mum zan wuce Lagos yanzu, nima ba son raina ba ne uzurin da zan yi a can mai ƙarfi ne” Mama ta ce “Uhm, uzurin har na fi umarnina kenan a gurinka?” Ya ce “A’a Mum, kar ki ce haka Please” Mama ta yi shiru kawai ta na kallonsa, Ya ce “Am sorry” Mama ta ce “Na yi sorry ɗin ka je Allah ya kiyaye, amma ka sani ko kananan ko ba kanan ba za’a fasa komai ba, idan ma ka ga dama karka halacci taron bikin” ya yi murmushi kawai ya ƙaraso kusa da ita ya yi hugging d’inta tare da faɗin “Thank you Mum, Allah ya sa su zo lafiya su tafi lafiya bye” Mama ba ta ce komai ba, ya sake ta ya fice. Mama ta bishi da kallo, abinda ya sa ta barshi ya tafi tasan uzurin da yake faɗa ba ƙarami ba ne, dan Ameen ba ya taɓa mata musu a kan duk wani abun da za ta sa shi ya yi, komai wuyarsa kuwa.

Ƙarfe 12 na rana Mama su na zaune a falo ita da Hajiya da uncle Mahmud da ya zo shima dan karɓar lefen ɗin, wayar ta shiga ringing, ɗauka ta yi ta duba ta ga Ammin Anwar ce ke kiranta, murmushi ta yi ta d’aga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama, ba tare da Ammi ta amsa sallamar da Mama ta mata ba, cikin tsananin ruɗu da matsanancin tashin hankali ta ce……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button