NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Wayarta dake gefenta ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar yin vibrate, ta sauke numfashi sannan ta saka hannu ta ɗauka tare da duba mai kiran. Number ce babu suna, amma da yake da sim ɗin da ba kowa ne yake kiran ta da shi ba sai makusantanta yasa ta d’aga. Cikin sassanyar muryarsa ya mata sallama hakan yasa ta gane shi ne. Ta amsa tare yin shiru ya ce, “Are you Ok?” Ta ce “Eh, me ka ji?” Ya ce “Na ji muryarki so cool.” Ta ce “Ba komai, ya ka je gida?” Ya ce “Lafiya k’alau, duk da baki kira ni kin ji ba sai da na kira ki.” Ta ce “I’m sorry, bani da Numbern ka ne.” Ya ce “Alright.” Suka yi shiru gaba-d’ayan su, ita ta rasa me yasa ta ji gaba-d’aya zuciyarta babu daɗi, kuma daga shigowar Ameen ɗakinta ne mood ɗinta ya canza, amma da tana cikin farin ciki sosai. Fahimtar hakan da Ahmad ya yi yasa ya shiga bata labarin rayuwarsu ta da cikin sigar tsokana, nan da nan ta ware ta shiga ƙyalƙyala dariya. Ahmad He is so funny at all, amma idan ya shagwab’e sai ka ɗauka yaro ɗan shekara uku ne. Sosai ta ji daɗin wayar da sukai kamar kar su daina, sai da ta ga Sadik yana ta kiran ta sannan ta masa sallama ta kira Sadik bayan ta gama haɗa kalaman da za ta yi amfani da su gurin ba shi haquri akan kiran ta da ya yi ya ji waiting call……✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣3️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………Da sauri ta d’ago ta kalle shi gabanta na fad’uwa ta ce “Doctor! wa….” Ya katse ta da faɗin “Kin yi mamaki ba, na san yanzu kina tambayar kanki ina na samo waɗannan hotunan, kuma yaushe aka yi su?” Ya ɗan ja numfashi ya ce “Neehal! Na yi mamaki sosai da kika kasa gane ni a lokacin da kika ganni, duk da nasan shekarun da yawa kuma lokacin da muka haɗu kina yarinya ƙarama, amma na san yanzu waɗannan pictures ɗin sun tuna miki da ni a rayuwarki.” Kallon fuskarsa ta shiga yi ko kiftawa ba ta yi, lokacin ɗaya idanunta suka ciko da k’walla, ta yi minti uku a tana kallonsa kallo irin na k’urilla sannan ta ce. “Uncle Ahmad! Are you the one please?” Ta faɗa cikin raunin murya da tsantsar mamaki. Ya yi murmushi cikin jin daɗin yanda ta iya tuno shi da wuri haka ya ce “Yes, kin manta ni a rayuwarki ko? kin karya alƙawarin da kika mun.” Ta girgiza masa kai cikin ƙoƙarin mai da k’wallar data tarar mata ta ce “Ban manta ka ba a cikin raina, domin a duk lokacin da zan tuno da rayuwata ta gidan Uncle Umar sai na tuna da kai da irin taimakon da ka ba ni.” Ya ce “Amma me yasa da kika ganni kika kasa gane ni.” Ta ce “I don’t know, amma kasan shekarun da yawa, kuma ranar dana ganka na ga kamar na san fuskarsa, amma na rasa a ina na santa.” Ahmad ya juyo ya fuskance sosai ya ce “Neehal, duk tsawon shekarun nan da suke wuce dai_dai da rana ɗaya ban taɓa mantaki ba a cikin raina, kodayaushe ina tunanin ki tare da fatan na sake haɗuwa dake a rayuwata, ashe ta sanadin twins Ubangiji zai ƙara haɗu mu, haɗuwar da bana fatan mu rabu har abada.” Neehal ta sauke numfashi ta ce “Ina Mamy?” Cikin mamaki ya ce “Baki manta Mamy ba?” Ta ce “Eh mana, kamar yadda ban manta ka ba itama ban manta ta ba, amma na san idan na ganta a yanzu ba zan gane ta ba, har yanzu tana unguwar su Uncle Umar?” Ya ce “A’a sun tashi daga unguwar, amma suna Kanon dai. Sai dai ita tafi shekara bata ƙasar nan, ta je Turkey, shekaran jiya ta dawo, yanzu ma daga gidanta nake.” Ya ɗan ɓata fuska sannan ya cigaba da magana “Ni fa ban ga kina murnar gani ba, ko ba ki yi farinciki da sake haɗa mu da Allah ya yi ba?” Neehal ta yi murmushi ta ce “Hmm, wlh Uncle farincikin da yake cikin Zuciyata a yanzu na haɗuwa da kai a karo biyu a rayuwata ba zai misaltu ba, kawai tsananin mamaki ne ya hana murnar tawa bayyana, gani nake ma kamar mafarki nake, Uncle Ahmad, mutumin kirki, mai taimakon bayin Allah ba tare da ya san su ba, shine mahaifin Twins ɗina? Abun kamar almala Uncle.” Ahmad ya yi murmushi yana jin zuciyarsa ta masa wasai ya ce “Ikon Allah ya fi ƙarfin komai Princess.” Ta yi shiru kawai tana kallon sa, ta kasa ɗauke idanunta daga kansa. Ya d’age mata gira ɗaya ya ce “Wannan kallon fa?” Da sauri ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, wani irin farinciki take ji a cikin ranta, kamar ta tashi tai ta tik’ar rawa haka take ji. Ya yi ƙasa da murya ya ce “Ya zaki rufe mun maganin ciwon idona? Please ki buɗen wannan kyakkyawar fuskar da idanuna ba sa gajiya da kallon ta” Ta buɗe fuskar amma sai ta yi ƙasa da kanta, wata irin kunyarsa take ji ba kaɗan ba. Ahmad da yake jin kamar ya rungume ta saboda wutar k’aunarta da take ƙara ruruwa a ransa ya ce “Now tell me, me ya faru bayan rabuwar mu.” Ba tare data d’ago ba ta ce “Ka fara faɗa mun naka, da yanda har ka yi aure ka…..” Sai kuma ta yi shiru. Ya ce “Uhm, ƙarasa faɗar abun da zaki ce mana.” Ta ɗan turo baki ta ce “Babu.” Ya gyara zama tare da faɗin. “Ranar da muka haɗu dake last, bayan na koma gida na kasa aiwatar da komai saboda tunanin ki, na farko ina tunanin kar a miki wani abu a gida saboda Uncle ɗinki ya ganmu tare. Na biyu kuma wanda shi ya fi sani cikin damuwa komawa Abuja da zan yi in yi nesa dake. Tun kafin ranar nake wannan tunanin, da farko na ɗauka tausayin ki ne yasa nake wannan tunanin, amma daga baya na gane na shak’u dake shak’uwa mai tsanani. A ranar ko baccin kirki ban iya yi ba saboda tunani. Da safe bayan na gama shiryawa kafin na fita sai da na je wajen gidanku ko Allah zai sa in ganki, amma ko me kama dake ban gani ba. Gashi ni ban san gidanku ba tunda bana ƙarasawa a hanya muke rabuwa. Haka na dawo gida jiki a sanyaye, gashi washegarin ranar ne tafiyata Abuja. Tun da na je Masallaci na yi sallar Azhar har aka kira la’asar ban koma gida ba, ina ƙofar gida ina jiran ki, ki zo wucewa, ranar ko abincin kirki ban iya ci ba. Bayan na yi Sallar la’asar na je gurin mai kayan miyan da kike siya a gurinsa na masa kwatancenki na tambaye shi ko kin zo siyan kayan miyan ranar ya ce mun A’a baki zo ba. Hankalina fa ya tashi matuƙa na ƙara komawa layinku ko zan gan ki, na tambayi wasu yara ko sun san gidanku suka ce mun bama su san ki ba. Ranar dai haka na kwana cikin tsananin damuwa. Washegari tun safe na wuce Abuja zuciyata babu daɗi ko kaɗan. Wata na uku da komawa Abuja na tafi India na yi wani course na shekara ɗaya, bayan na dawo da some weeks na fara aiki. A’isha ƴar gidan wani abokin Daddy ce, na santa sosai suna zuwa gidanmu tun kafin mu fara soyayya da Ita. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa, shine abun ma da ya ja hankalina a game da Ita. Mun kai 3 years muna soyayya kafin mu yi aure, dan sai da na jira ta ƙarasa karatunta na degree. Na ji daɗin zaman aure da A’isha sosai, saboda macece mai haquri da biyayya ga ilimin addini, ta bani kulawa da kowanne ɗa Namiji yake fatan samu a gurin Matarsa ta sunna. A’isha ta san labarinki tass a gurina, saboda yawan zancen ki da nake mata, a duk lokacin da na mata zancenki sai ta ce mun ita dai tana son ta ga Neehal ɗin nan, Allah ya nuna mata ke kafin ta mutu. Ashe baza ku taɓa haɗuwa domin a haihuwar twins Allah ya mata rasuwa. Mutuwar A’isha ta dake ni ba kaɗan ba, sanadiyyar mutuwar ta hawan jini ya kama ni saboda damuwar da na saka a raina da yawan tunani. Idan na kalli twins ne kawai nake jin sanyi a raina. Afrah suna biyu ta ci a gurina, da sunan Ummi da sunanki, Amrah kuma A’isha na yiwa takwara. A hankali radadin mutuwar A’isha ya fara raguwa a zuciyata, sai dai up to now ban ƙara kallon wata mace da sunan soyayya ba balle na yi tunanin ƙara aure, shekara biyar kenan da rasuwar A’isha. Yarana sune farincikina, su suke ɗebe mun kewar Mahaifiyarsu, kuma tun suna jarirai ni na riƙe su, Ummi ta so ɗaukar su ita da Ammi na ce bazan iya yin nesa da ƴaƴana ba su yi haquri zan riƙe su a gurina. Aka samo mun wata dattijuwa (Baaba Talatu) ita take taya ni kula da su, tun suna jarirai har time ɗin da aka sace su.” Ya sauke numfashi tare da kallon Neehal cikin ido ya ce “Duk waɗannan abubuwan da suka faru, kamanninki da tunaninki suna manne a zuciyar Ahmad Aliyu Bulama. Lokaci zuwa lokaci ina kallon pics ɗinki wanda na adana su a Email ɗina. Ni ba ma’abocin kallon TV ba ne, dan tun ina ƙarami na kallo ba ya gabana, shi yasa ban san ki ba. Na yi mamaki sosai da Aunty Mardiyya da Zahra suka ce mun shahararriyar ƴar jarida ce ke domin ban taɓa sani ba. Dan da nasani kafin yanzu da tuni na binciko inda kike na zo mun haɗu. Tun Ranar da na bar Kano ban ƙara zuwan ta ba sai last zuwan da mukai dalilin su Afrah. Ina sauka a cikin garin Kano ke kika fara faɗo mun a cikin raina, amma ko kaɗan ban yi tunanin ganinki a nan kusa ba, duk tunani ma zuwa yanzu kin yi aure. Lokacin da na yi 2 eyes dake yanayin dana tsinci kaina a ciki na shock ɗin ganin ki ba zai misaltu ba, na kasa banbance tsakanin bayyanar su Afrah da ganin ki da nayi a bazata wanne ya fi sakani farinciki, sai dai rashin gane ni da baki yi ba shi ya kashe mun gwiwa, kuma a ranar ba mu da ishashshen time ɗin zan miki bayanin da zaki iya tunawa da ni. Tunda muka koma gida tunanin ki ya hanani sakat, so nake kawai na ƙara saka ki a cikin idona, amma saboda yanda mutane suke zuwa mun murnar ganin su Afrah that is why ban samu dama na zo ganin ki ba sai yau.” Ya yi shiru yana sauke numfashi. Neehal ta d’ago da kanta wanda yake ƙasa tunda ya fara bata labarin, cikin sanyin jiki ta ce “Allah ya ji k’an Aunty A’isha ya gafarta mata.” Ahmad ya ce “Amin ya Allah.” Suka yi shiru na wasu mintuna kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Ahmad ne ya katse shirun da faɗin “A zak’e nake in ji labarin abun da ya faru da ke bayan rabuwar mu, gashi kuma na ga magriba ta gabato.” Neehal ta ce “Next time idan muka haɗu sai na baka labarin, dan yana da tsayi.” Ya ce “Gobe zan wuce Abuja, amma kafin na tafi zan biyo ta nan Insha Allah.” Neehal ta ce “Allah ya kai mu.” Ya ce “Amin.” Ta ce “Bari na zuba maka abinci, tun d’azu muna ta hira baka ci ba.” Ya ce “No, kar ki zuba am full.” Ta shagwab’e fuska tare da turo baki gaba. Ya yi murmushi ya ce “Kin san me?” Ta girgiza masa kai ita a dole fushi take da shi, tun da ba zai ci abinci ba. Ya ce “Kin ƙara kyau sosai da zaƙin murya, sai dai shagwab’arki mai kyau tun ta yarinta tana nan har yanzu, tun last zuwan da muka yi na lura da hakan, sai nake tuno da, idan na zaunar dake a gidan Mamy, sai ki shagwab’e mun ki ce, Uncle please zan tafi gida, idan na daɗe Aunty zata dake ni.” Ta rufe fuska tana murmushin da ya kufce mata ba tare da ta shirya masa ba saboda yanda ya yi maganar yana kwaikwayon muryarta. Shima ƴar dariya ya yi wadda ta ƙara fito da zallar kyawunsa. Wani irin nishad’i yake ji yau a cikin zuciyarsa, wanda rabon da ya ji irinsa tun kafin rasuwar A’isha. Neehal ita ce first love ɗinsa a duniya, a kanta ya fara sanin menene so. Wayarta dake gefenta ce ta shiga vibrate, ta duba ta ga Sadik ne yake kirancta. Ta ɗan saci kallon Ahmad ta ga ita yake kallo, sai ta ji baza ta iya d’aga wayar a gaban sa, ta ƙi pick. Tana katsewa wani kiran ya ƙara shigowa, shima har ya katse bata d’aga ba. Ahmad ya ce “Ba kiran ki ake ba, ki d’aga mana.” Zata yi magana ta ji shigowar sak’o cikin wayar, ɗauka ta yi ta cire key ta duba, ganin Sadik ne ta shiga karantawa a zuciyarta. Where Are you sweetheart inata kiran ki baki ɗauka ba, gani kuma a cikin gida na zo na ganki. ‘Ya Sadik kuma da sakaliyar yammar nan?’ ta faɗi haka a cikin ranta. Reply ta masa da faɗin Ina abu ne, na zo zan yi pick kafin na ɗauka ta katse, Okay ka ƙaraso ciki mana. Ta ajiye wayar tare da d’agowa ta kalli Ahmad wanda ya ƙura mata ido. Ta shagwab’e fuska ta ce “Ni fa kallon nan naka yana sa in ji wani abu a jikina, Please ka daina.” Ya ce “Idan kina kusa da ni ba zan taɓa iya daina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki ba Princess.” Ta yi ƙasa da kanta ba ta ce komai ba. Ya ɗauki wayarsa dake kan cinyarta ya shiga Camera ya fara ɗaukarta a hoto ba tare data sani ba. Ta d’ago zata yi magana ya katse ta sauri da faɗin, “Please Princess ko ɗaya ne.” Ta yi murmushi saboda yanda ya wani marairaice fuska. Ya ce “Yawwa, Wow da murmushin ya fi kyau.” Ya ƙarashe maganar tare da ɗaukarta hoton tana murmushin. Dai_dai nan Ameen ya buɗo ƙofar falon ya shigo………..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button