NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
4️⃣5️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951
………..Washegari tun kafin 7 na safe Neehal ta bar gida zuwa gurin aiki. Kafin ƙarfe ɗaya kuma ta dawo gida. A gajiye ta dawo ga yunwa dake nuk’urk’usar hanjin cikinta dan babu abun da ta ci ta tafi gurin aikin, da ta je can ma ba ta ci komai ba, gashi jiya kafin ta kwanta ta so cin abinci amma wayar da suka yi da Ahmad da Sadik yasa bata ci ba, saboda dare da ya yi. A falo ta ajiye jakarta ta zarce kitchen dan samarwa kanta abun da zata ci. Tea ta fara haɗawa ta sha, bayan ta samu nutsuwa ta fara tunanin abun da zata girka mai sauƙi for lunch, dan Mama bata nan ta je aiki, sai 2 zata dawo. Indomie ta fara dafawa ta ci a cikinta sannan ta ɗora girkin ta fito daga kitchen ɗin dan zuwa ta yi Sallah ta watsa ruwa a jikinta. A falo ta tarar da Zulai tana kallo, ta zauna tana duban Zulan ta ce “Aunty Zulai sannu da gida.” Zulai ta juyo cikin fara’a ta ce “Yawwa Neehal, kin dawo ashe? Muna daki muna ta barci ban ma ji shigowar ki ba, yanzu ma tashi na yi nay Sallah, na ce bari dai na fito in yi kallo.” Neehal ta ce “Ban ma jima da dawowa ba, bari na ƙarasa upstairs na yi Sallah, na ɗora girki dan Allah ki duba mun kafin na sakko.” Zulai ta ce “Shikenan a sauko lafiya.” Neehal ta ɗauki jakarta ta wuce sama. Wanka ta fara yi sannan ta fito ta yi sallah, bayan ta idar tana cikin shiryawa ta ji ana knocking ɗin ƙofar ɗakin. “A shigo.” Ta faɗa ba tare data tambayi waye ba. Zulai ce ta shigo bakinta ɗauke da Sallama. Ta amsa mata. Zulai ta ce “Kin yi baƙo.” Neehal ta ce “Waye?” Zulai ta ce “Babansu Afrah ne, yana falon ƙasa.” Ta ce “Okay ki ce masa gani nan zuwa.” Zulai ta amsa da “Toh.” Sannan ta juya ta fita. Ta ƙarasa simple d’aurin d’ankwalin da take yi, sannan ta ɗauki mayafinta ta yafa a ƙafaɗa ta fice.
Tunda ya jiyo taku ana sakkowa ya ƙurawa step ɗin ido cikin zak’uwa da son ganin ta. Cikin nutsuwarta ta ƙaraso cikin falon kanta a ƙasa saboda kallon da yake jifan ta da shi. Ta zauna a kujerar dake gefen sa a hankali ta ce “Ina yini Uncle.” Ya ce “Lafiya k’alau Princess.” Ta ce “Ya Mamy?” Ya ce “Tana nan k’alau, Mama bata nan ne?” Ta ce “Eh tana gurin aiki.” Ya jinjina kai tare da miƙewa ya dawo gabanta ya zauna a saman carpet.” Ta d’ago kanta da sauri ta ce “Uncle ka koma kan kujera ka zauna mana.” Ya ce “No, barni a nan, sai nafi ganin wannan kyakkyawar fuskar taki yanda ya kamata.” Ta ce “A kan kujerar ma fa zaka gani Uncle.” Ya ce “Ba kamar nan ba princess.” Saukowa ƙasan ta yi itama ta zauna a ɗan nesa da shi ba ta ce komai ba. Ya yi murmushi ya ce “Kin yi kyau sosai Princess!” A hankali ta ce “Thank you.” Ya kwaikwayi muryarta ya ce “Nima thank you.” Ta yi ɗan murmushi ta ƙara yin ƙasa da kanta, kunyarsa take ji sosai har yanzu moment ɗinsu na jiya ya kasa ɓacewa daga zuciyarta. Zulai ce ta ƙaraso inda suke hannunta ɗauke da tire mai ɗauke da drinks ta ajiye a gaban su. Ahmad ya dube ta ya ce “Na gode.” Ta ce “Babu komai yallaɓai.” Sannan ta juya ta koma kitchen dan ƙarasa girkin da Neehal ta ɗora. Neehal ta ɗan matsa kusa da tire ɗin ta ɗauki juice ta tsiyaya masa a cikin glass cup, sannan ta matso kusa da shi ta miƙa masa ba tare da ta kalli fuskarsa ba. Ƙin karɓa ya yi ya tsaya yana kallon fuskarta, ta d’ago ta kalle shi cikin sa’a suka haɗa ido, kashe mata ido ya yi wanda yasa tay saurin yin ƙasa da idonta tana turo baki gaba. Ya karɓa cup ɗin data miƙo masa tare da yin murmushi mai sauti, dama so yake ta kalle shi su haɗa ido kuma ya yi nasara. Ta koma inda take d’azu tana satar kallon sa ƙasa_ƙasa, shi kuma yana kurb’ar juice ɗinsa hankali kwance. Ya yi mata kyau ba kaɗan ba, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka amshi jikinsa, sassayan k’amshinsa mai daɗin shak’a ya cika mata hanci. ‘Yana nan a ɗan gayun sa up to now’ ta faɗi haka a ranta. Ya sha juice ɗin fiye da rabin wanda ta zuba masa sannan ya ajiye cup ɗin, ya dube ta ya ce “Idan kin gama kallon nawa sai ki cika mun alƙawari na.” Ta ɓata fuska ta ce “Ni ba kallon ka nake ba.” Ya yi murmushi ya ce “Tom Shikenan, now start from where we stopped yesterday.” Ta ce “Da me fa?” Ya mata kallan ƙasan ido ya ce “Your story mana.” Ta ja numfashi a hankali tare da runtse idonta, sannan ta fara ba shi labarin abun da ya faru bayan rabuwar su a tak’aice, daga time ɗin data farka ta gan ta a asibiti Uncle Usman ya kai ta up to now, sai dai ta ɓoye masa abu ɗaya a labarin nata, shine kashe su Anwar da akai, ta ce masa dai kawai rasuwa suke. Bai katse ta ba, har sai da ta kai aya ta yi shiru da kanta. Ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bata kuma shan wata wahalar ba bayan rabuwar su, sai ma cigaba na rayuwa data samu. Abu ɗaya ne ya ɗan taɓa masa zuciya a labarin nata har ya ji tausayinta over da ta ce masa samarinta biyu duk sun rasu, dan ya san ɗacin mutuwar masoyi tunda ya ɗanɗana da A’isha ta rasu. Cikin sanyin murya mai cike da alhini ya yiwa su Anwar da Jameel addu’ar dacewa da samun Rahamar Ubangiji. Neehal ta amsa da “Ameen Na gode, ƙarfe nawa zaka wuce Abujan?” Ya ce “Ƙarfe Shida na yamma.” Ta ce “Alright, ina son ka kai ni da gaishe da Mamy idan babu damuwa.” Ya ce “Kamar kuwa kin san tana son ta gan ki, dan na bata labarin ki.” Neehal ta ce “Har ka bata labarina?” Ya ce “Eh mana, tun a waya ma kafin na zo na ce mata aike kika tsinci su Afrah.” Ta ce “Kuma ta tuna ni?” Ya ce “Ina mata bayanin ki ta gane ki.” Ta jinjina kai sannan ta miƙe tare da faɗin “Ina zuwa.” Upstairs ta hau ta ɗauko wayarta ta kira Mama, dan ta sanar mata za su je gidan Mamy, amma Maman bata ɗauka ba. Ta duba agogo ta ga 2 ta wuce, hakan yasa ta yi tunanin may be Maman tana hanya ne, dan in tana driving bata ɗaukar waya. Sauran wayoyinta ta ɗauko ta zira a aljihun doguwar rigar jikinta, kasancewar rigar mai aljihu ce. Ta fito ta dawo downstairs, kitchen ta shiga ta duba ko Zulai ta ƙarasa abincin ta zubawa Ahmad. Ganin ta kammala har ta bar kitchen ɗin ma, sai ta ɗauko plate ta zuba masa, ta rufe da wani plate ɗin ta ɗora akan tire. Sannan ta ɗauko bowl ta zuba masa kayan salad a ciki, shima ta ɗora akan tire ɗin ta saka spoon ta ɗauko ta fito. Yana ƙasa a zaune har time ɗin bai koma kan kujera ba, ta ajiye tire ɗin a gabansa ta ce “Ga abinci Uncle.” Ya d’ago yana duban ta ya ce “Thank you so much.” Neehal ta juya ta bar falon dan bashi guri ya ci abincin ta shige ɗakinsu Dije. After some minutes ta hango Mama ta window ta shigo falon suna gaisawa da Ahmad. Ta miƙe ta fito falon. “Welcome Mama.” Ta faɗa cikin murnar dawowar Maman. Mama ta ce “Yawwa Neehal, ina hanya na ga kiran ki.” Neehal ta ce “Eh, dama za mu je gidan Mamy ne da Uncle Ahmad shine na kira na faɗa miki.” Mama ta ce “Okay to sai kun dawo ku gaishe ta.” Ta juya ga Ahmad wanda kansa ke ƙasa tun shigowar Mama ta ce. “Idan kun dawo ka shigo zan baka sak’o ka kaiwa Ummi.” Cikin girmamawa ya ce “Toh Mama Insha Allah.” Mama ta wuce sama, ita kuma ta ƙarasa inda yake. Ta kalli tiren abincin data ajiye ta ga ko taɓa shi ba ai ba, yanda ta bar shi haka yake. Ta ɓata fuska sosai ta ce “Uncle baka ci abincin ba ai.” Ya miƙe cikin son kawar da zancen abincin ya ce “Tashi mu tafi.” Ta miƙe bata ce komai ba ta je ta yiwa sallama sannan ta sakko suka tafi. Har ya fice daga falon, a waje ta tarar da shi suka jera suka ƙarasa parking space. Ya buɗe mata motar da ya zo a cikin ta ta shiga, bayan ya rufe mata murfin ya zagaya ya shiga driver seat ya kunna Motar suka fice daga gidan. Har suka ƙarasa gidan Mamy babu wanda ya ce kala a cikin su, sai cool music ne yake tashi a cikin motar. Ita fushi take a kan ya ƙi cin abinci, shi ma kuma yasan laifinsa shi yasa shi ma ya yi shiru, ya barta ta ɗan huce sai ya rarrashe ta.